Showing 15001 words to 18000 words out of 111233 words
takaici tashin hankali da kuntatacciyar damuwa..
Anne itama kuka ta fashe musu da shi wae ta gaji
dan ta na fara gyangyad’i ta ke k’umewa ga wari ya hanata yin barcin…
Sai da mutumin d’azu
waenda su su ke a tsaye shi da su Ya Amir ya bud’e mata wuta tukunna ta yi musu shiru…
Ya Abba kuwa mik’ewa ya yi Amal ta kwanta a kan cinyar Adda ta mik’ar da k’afafunta a wajensa da nata dan tun d’azu dama ya fahimci zazzab’i ya rufeta yanzun kuwa ya ji
numfashi ma da kyar ta ke iya jaa….
Iya wahala sun wahala
In banda kukan zuci babu abunda Aliya ta ke yi ji ta ke kamar ta had’iye zuciyarta kawai ta Mutu ko ta samu ta huta…
A tsaye mazan su ka kwana a kan k’afafunsu matan kuma a zaune kafin
Safiya gaba d’aya jikin kowa ya yi tsami masu ciwon sugar kuwa duk jikinsu ya soma suntuma gawa kuwa ta na ta sake kumbura itama.
Bayan awanni biyar…
A tare dukkanin su su ka furta kalmar “Alhamdulillah”sakamokon hasken da ya fara ratsowa na gabannin s
afiyar ranar…
Ba su ji ko alamun kiran sallah ba sai haske kawai su ka gani
Dan haka wasu a cikinsu suka kare wasu su ka yi tsarki su ka yi taimama sannan aka shiga gabatar da sallar asuba
dan zuwa wannan lokacin duk sun farka
Anne kuwa ta fuske b
a ta yi sallah ba, bayan ta gama sanar musu ba fa za a karb’a ba duk sun yi mata baanza….dama d’azu (jiya) ma
ba ta yi ba
A nata mentality d’in a yadda ta ke a fusacen nan ko
nutsuwar yin sallar ba ta da ita sannan ita har ga Allah ta ce ba a sallah i
n ba tsarki, dan ita dai ba ta tab’a jin in da aka yi tsarki da dutse ba….
Sai Aliya itama wadda ta ke jinin bik’ii ga shi pad d’inta gaba d’aya ta jik’e d’inkinta ya na yi mata wata kalar azabar zugi da jan ruwa da alamun tsami ya yi…
Zuwa wannan
lokacin ta ma kasa kuka tsabar bak’in ciki yunwa wahala da azaba sun kai k’ololuwa wajen azabtar da ita…
Kunya ce ta fara kama mazan da su ke a wajen domin kuwa daga su sai wandunansu sakamokon kayayyakinsu da su ka sassaka su ka toshe wannan ramin..d
a sauri sannan kusan a tare duk su ka juya a ka hau zak’ulo
kaya ana sassakawa……
Wani Abu mai kama da yanayin sab’ar maciji su ka gani a gaban rigar d’aya daga cikinsu wanda hakan ya sanya hankalin kowa ya tashi chaaa! Su ka tsaya turuss idanunsu a kan r
amin.
Kallon-kallo aka shiga yi a wajen jikin kowa ya na sake yin sanyi sai kuma su ka saki salati a tare yayinda wasu a
su ka rushe da kuka…
Tana kuka sosai Anne ta ce
“Ku je ku lek’a cikin ramin mana ku duba mana abunda ya ke a ciki dan Allah
In
na cutarwa ne ku kashe shi…”
Cikin daka mata tsawa wannan mutumin dai ya ce “ke dalla Malama rufa mana baki! Mai zai hana ke ki zo ki duba? In muka lek’a kuma da me za mu kashesa? Ko kin ga makamai a hannunmu ne?”
Banza ta yi da shi kawai amma ta saka
a ranta wallahi in ya sake yi mata ihu sai sun kwashi y’an kallo tabbas..
Tun d’azu ihu ya ke ta yi mata yana jin haushinta ba gaira ba dalili ko uwar me ta yi masa oho….
Dole wasu a cikinsu su ka yi sacrifice su ka sake kwab’e rigunan nasu a ka rufe
ramin laba’asa, wanda
zuwa yanzu kowa ya tabbatar da maciji ne a cikinsa.
Bayan awanni sha biyu…
zuwa wannan lokacin duk sun k’arasa fita a haiyyacinsu, Ya Abba shi kam ranar da aka kawosu ma azumi ya yi shiyasa tsabar wahala da yunwa har dishi-dis
hi ya ke gani, sauk’inta d’aya dai shi fitsari bai kamasa ba kamar yadda ya gigita ragowar har ta kai su ga ware wajen fitsari a cikin gurin.
Jikin kowa ya yi la’asar ko maganar kirki ma
ba sa iyayi….
Fitsari kuwa za a iya cewa daga Aliya sai Ya Abba da
Amal wadda duk wani ruwan jikinta ya fice da hanyar gumi da azabar zazzab’i ne kawai ba su matsa d’aya daga cikin inda sumintin wajen ya fashe wajen ya kasance zallar k’asa sun yi ba.
Ganin duhu ya soma yi sosai ya sanya su ka gabatar da sallar magrib sa
nnan aka shiga tunanin yadda za a yi da wannan ramin dan yanzu da su ka fahimci menene a ciki dole hankulansu su ka kai k’ololuwa wajen tashi kuma sun san rigunan su ba lalle su iya hanashi fitowa ba….mazan jikinsu saura wanduna matan kuma iyaka riga ne d
a zani d’an babu hijabai duk an kwace kafin su shigo ciki.
A haka har duhu ya yi musu ba su tab’uka uwar komai ba Anne da wannan mutumin suna ta fad’a kamar za su had’iye juna…
Baba ne ya daka musu tsawa duk su biyun d’an haka aka yi tsit su na mayar d
a numfashi….
Wani kalar nishi suka ji ana yi wanda ya ke baiyyana tsantsar firgici da tsoro, basu kai ga yin wani abun ba
su ka ji Aliya ta saki salati sakamokon fad’owar da ta ji Anne ta yi a kan jikinta….
Cikin tsantsar kid’ima mazan da ke a tsaye
su ka shiga tambayarta “ lafiya? Mai ya faru?”
BULAMA
✍
️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*07*
Follow our channel zaka sam
u daga farko.
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T
Da kyar ta iya ce musu
“Anne ce ta fad’i kamar ba ta numfashi ma” sai kuma ta saki kuka, dukda kuwa abubuwan da Annen ta yiyyi mata tabbas ta ji babu dad’i sosai..Uwa uwace….
Ya
Amir shima a take ya rikice hatta Amal itama k’ok’arin tashi ta shiga yi ta zauna yayinda Adda ta shiga k’ok’arin ganin ta k’arasa inda su ke ta na mai tambayarsu “mai ya faru?”
A take tsoro ya game su gaba d’aya a lokacin da Aliya ta shiga cewa
“Abu
ne ya cijeta,
kowa ya kula”
Kuma k’asa-k’asa su na ji kamar hissing d’in maciji.
Fashewa da kuka Adda ta yi haka wasu a cikin mazan da su ke a tsaye
dan kasancewarsu maza bai sanya su ka ji rashin tsoron mutuwar da su ke ganin ta tunkarosu muraran a
halin yanzun ba.
Dudduba Anne Aliya ta shiga yi sosai ta na so ta ji wajen da macijin ya cijeta ko ta samu ta d’aure mata amma ba ta gane komai ba, dukda ba ta ma da tabbacin Annen ta na raye.
Mazan ne su ka cewa su Aliyan su nutsu sosai su shafa ta
a dubata da kyau
ko za a ji alamun wani
Abun a san mai ya sameta…in macijin ne kuma a samu a d’aure mata…
Chan k’asa wajen guiwowinta duk biyun su ka ji alamun jini ya na fita.
Ba su san tak’ameme menene ba Yadikko ta bada d’an kwalinta, sannan a
ka ciri na Annen aka had’a da shi mazan su kuma su ka daidaici wajen da aka nuna musu da ake jin jinin ya na fita su ka shiga fafutukar ganin sun d’aure mata shi katamau! Suna tab’a y’an kwalayen wani smell ya na fita daga jiki mai wari da k’arni ga kuma d
anshi saboda daga Yadikkon da take ta kwance har Adda da ma matan wajen duk y’an kwalayen nasu sun shafi amai sosai musamman ma na Annnen lokacin da ta fad’a kan Aliya kanta ya gogi wani ramin da amai ya taru a ciki bai kai ga tsotsewa ba.
A hakan..ba s
a gani, su ka saita saman inda su ke jin zubar jinin wajen tsoka duka k’afafunta biyun su ka d’aure mata su one by one katamau!
D’aurin da ba na wasa ba!
Dan in da ace idanunta biyu ba ta kai ga shemewaba tabbas da tuni ta tsala masifaffiyar k’ara.
K
asancewar duk a rikice ga shi ba ma sa ganin komai kawai basira ce ya sanya ba su lura da akan wajen harbin su ka d’aure y’an kwalayen duk biyu ba kamar had’in baki
Sannan ba su lura sun d’aure mata da masifar k’arfi ba….
Mazan ne su ka tabbatar da ‘
duk yadda aka yi maciji ne sai dai su gode Allah dan da ga dukkan alamu macijin ba mai dafi bane ba
tunda gashi sarar ta na zubda jini, kuma wani a cikinsu ya tab’a ya tabbatar musu jagular vein d’inta ya na harbawa kawai dai numfashin ne ba a ji..’
Dan
haka kowa ya nutsu ya yi shiru watak’ilan ma tsorota macijin ya yi ga kuma hayaniya shiyasa ya fara irin hakan.
Dan haka dukkansu su ka yi shiru kowa ya nutsu ya yi tsit a waje d’aya Ita kam
Amal dama ba ta ma k’arasa sosai garesu ba amma still sai da
Ya Abba ya sa hannu ya janyota ya dawo da ita ta ci gaba da zama a inda ya yi
musu kamar katanga daga koma menene, ita da Adda.
Kusan awa d’aya su ka yi a haka sai da su ka
daina jin motsin komai tukunna su ka shiga neman taimako…
Sosai Ya Amir y
a ke jijjiga gate d’in ya na hawaye ya na jin Aliya ta na cewa “ta mutu fa!
Ba ta motsi, ko hannunta in na d’aga komawa ya ke yi…
Haba dan Allah,
Y’ar tasu y’ar gwal ce ne?
Saboda an mareta shine za su kashemu gaba d’aya wanne kalar rashin adalci ne w
annan? Ya za su saka mu a waje mai had’ari kalar wannan fisabilillahi…”
Ta na maganar ta na sake k’ank’ame Anne da gawar d’anta wadda ta ke ta sake suntuma sosai.
Ihu da kukan duniya babu kalar wanda ba su yi ba, amma aka k’i kulasu..haka nan su ka h
ak’ura su ka koma kowa ya zauna zuwa wannan lokacin duk sun fita a haiyyacinsu babu k’arfi babu lafiya…sama da 24hours kenan babu abinci…
Haka nan su ka shiga addu’a wasu su na kuka, sannan Ya Amir da Aliya su ka saka Anne a addu’oinsu da fatan ba ta mutu
ba, duk wannan bidirin da ake yi Baba bai ce musu ku ci kanku ba, addu’oinsa kawai
ya ke yi ya na istighfari wanda suma d’in suna kammala fafutukar d’aurewa Anne k’afafunta tamau da ife ifen neman agaji su ka jona shi…a haka su ka
dinga addu’a ba tare d
a idanunsu su na gane musu juna ba sai dai fa duk wani motsi na Amal Ya Abba ya na sane da shi sarai…..
A haka gari ya waye musu wanda su na duba Anne aka tabbatar da maciji ne ya cijeta saboda ga jini nan ya na ta fita, kuma ashe a k’afar hagu har sau b
iyu ya cijeta wajen cinya inda ya ciji d’ayar da alamun tsakiyar k’afafun nata ya shige ita kuma ta ji tsoro ta matseshi shiyasa ya yi mata a duka k’afafun a saiti d’aya, da kuma sangalalin k’afarta ta hagu nan ma maybe da ya zo fita ne, dan haka Adda ta s
ake bada d’ankwalinta aka d’aure dukda su na da tabbacin in ma dafin ne ya gama zuwa har zuciyarta sannan ba lalle mai dafi bane ba, amma gara su yi mata iyakar taimakon da su ke ganin za su iya.
sai dai sauk’in abun sun fahimci kamar ba mai dafi bane ba
dan gashi ta na a raye har zuwa lokacin pulse d’inta Sun shaida hakan, kawai dae suman ne ba su san na menene ba hala tsorata ta yi ko kuma dae wani abun da ba su san da shi ba, shiyasa ba su yi gigin kunce d’aurin da su ka yi mata ba dan basu tab’a jin ir
in hakan ba gashi sun ga k’afar tata daga inda ya cijetan su ka d’aure zuwa k’asa har ma
Da sama-sama koina ya chanja colour sosai. Yayinda ake da tabbacin itama Yadikko wani kunamar ne ya sake cizonta dan gari yana wayewa su ka ganta a sheme, babu alamun
cizon maciji a tattare da ita amma ta sheme itama,
akwai dai pulse kamar na Anne sai dai kwata-kwata ba sa motsi daga ita har Annen jijjigawar duniya an yi amma sun k’i su farka.
Macijin ya tafi sai dai ramin har yanzu bai gama rufuwa ba dan haka g
anin dare ya doso ya sanya su ka bada himma aka toshe shi da kyau su na masu
fawwalawa mai sama komai…
In ka gansu sai ka yi musu kuka kaff cikinsu Ya Abba ne kawai ya ke iya tsayuwar kirki kuma babu alamun wahala a tattare da shi amma gaba d’ayansu was
u ko idanunsu ba sa iya bud’ewa sosai…
Wari! Yunwa!
Uzuri wanda zuwa yanzu kusan kowa ya yi nasa atleast once a wajen, ne. Ga tsoro fargaba da tashin hankali gaba d’aya su suka taru suka sanya kawai wasu a cikinsu su ka fara yiwa kansu fatan mutuwa yay
inda su Aliya su ka cire rai da Anne da Yadikko dan sun san ba zai yiu a ce maciji ya cijeka ka yi awanni sama da ashirin da hud’u ba a duba ka ba sannan ka rayu..dukda mazan wajen su na ta basu assurance d’in za fa ta tashi ba ta mutu ba tunda ga shi puls
e d’Inta su na harbawa wata kilan doguwar suma ne ta yi, amma su kam gani su ke yi da kamar wuya…ana kaita asibitin ma za ta wuce.
Bayan sun idar da sallar isha, a lokacin da duhu ya wanzu tsoro ya na sake gamesu kawai su ka ji d’aya daga cikin mazan
wani tsoho sosai ya yi salati sai kuma k’arar fad’uwa wadda ya yi ta a kansu Aliya, ba su kai ga gama shiga cikin mad’aukakin tashin hankali ba su ka ji wani ya sake sakin ihu sai dai shi bai fad’i ba kuma bakinsa bai mutu ba!!!
Kamar an kunna su haka nan
su ka hau kuka su na ihu har Adda Amal kuwa masifar zazzab’i da yunwar cikinta ya sanya ko motsi ma
bata iya yi ba kawai ta shiga nanata kalmar shahada…
Da sauri Ya Amir ya mik’e kamar jiya yau ma ya hau jijjiga gate d’in dan zuwa wannan lokacin salatin
mutum na uku kenan suka ji, sannan duk su na cewa “Nima ya cije ni”
A hankali
Ya Abba wanda gaba d’aya jikinsa ya yi sanyi duniyar ta ke juyawa ma ya mik’e ya k’arasa inda ya ke jiyo muryar Ya Amir su ka kama bockler d’in a tare su na jijjigata this tim
e around da niyyar su fasheta kawai..su na a haka su ka ji wani mutumi a cikin mazan shima ya saki salati sai kuma ya soma furta kalmar shahada a hankali….
Da sauri Ya Abba ya juya ya na kiran sunan Amal!! Amal!!!
Wadda ta yi mutuwar tsaye…
Shi da Adda
kusan a tare su ka damk’o hannunta jin ta amsa da “na’am”
Cike da fargaba da masifar tsoron rasata ya janyota ya sakata a gabansa jikin k’arfen ya had’ata da k’arfen da jikinsa sosai wanda dukda halin da su ke a ciki na k’ololuwar tashin hankali da matsan
anciyar fargaba hakan bai hanasa jin wani masifaffen yanayi ya dirar masa mai wuyar misaltuwa ba…
Da kyar jikinsa ya na wani kalar karkarwa ya had’e k’afafunta a cikin nasa ya yi mata ta yadda ko abun ya zo in ma cizon ne sai dai shi ya fara cizonsa sanna
n da wani kalar masifaffen k’arfi ya ci gaba da bugun k’arfen yana sauraren siririyar muryarta ta na kuka ta na cewa “Ya Abba meye haka? Ka cika ni ba na so….”
In banda ihu da kururuwa ba bu abunda ya ke tashi a wajen
dan zuwa wannan lokacin ko ba a gay
a musu ba suna da tabbacin macijin ya ciji kusan duk mutanen wajen, sauk’in abun ma suna jin salati da muryoyin wasu har yanzu, wanda a tunaninsu gubar ba ta kai ga k’arasa game musu jiki ba ne…..
Kamar a mafarki Amal ta ji muryar Ya Asad ya ce “lights
pls…”
BULAMA
✍
️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*08*
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM....
Tarr!! Haka haske ya wadatu a waj
en, wanda hakan ya sanya su ka fahimci ashe akwai bulbs a wajen tsantsar baƙar mugunta ce ta sa aka ƙi kunna musu kenan....
Wata kalar masifaffiyar kunya ha
ɗ
e da takaici ne su ka hana Amal motsi a wajen kawai ta sunkuyar da kanta ƙasa dan tun da aka kun
na wutar Ya Asad ya kafeta da idanuwa ko kyaftawa ya gagara yi...
Ihun jama'ar da su ke a bayansu ne ya katse yanayin dan haka da Abba da Amal su ka juya yayinda Asad ko gezau bai yi ba kallonsu kawai ya ke yi, kuma da wuya ka fahimci yanayinsa.....
Macizai ne