Showing 141001 words to 144000 words out of 338813 words

Chapter 48 - MATAR TAJ COMPLETE

masu babban competitor duk da a lokacin yayi hidden identity dinshi baibar kowa ya sani ba.

Dawowarsh

i ya bashi damar bin didigi cikin ahalin, duk wani motsinsu da yanda suke tafiyar da alamarin business dinsu na hannunshi don ya zuba mutanenshi sosai a kamfanin, harma da cikin gidan, ta nan ne ya fara sanin abubuwa da dama ciki harda dalilin mutuwar fatt

u, a lokacin fadwa ta mallaki hankalinta sosai, din harta gama makaranta ma.

Saida ya fara karantarta sosai da halayenta gaba daya kafin ya tunkareta,duk wani motsinta yana ankare dashi, ya saka yaranshi na binta duk inda zataje, suna protecting dinta.

R

anar da suka sake haduwa a karo na uku shine lokacin dataje shopping, ta gama siyayya gaba daya ta bada card dinta donyin payment akayi denying biyan, kuma tasan hidaya ce tayi hakan, don sun samu misunderstanding a lokacin, fadwa ta nuna mata tanason shig

a family business dinsu hidaya ta hanata, kuma bawai tace bazatayi aiki a kamfanin bane, ah ah kawai dai ta hanata title din data nema, abin yayi ma fadwa ciwo sosai, don itama tana som ta shiga business din a dama da ita, kuma abun saiyazo da idonta ya ru

fe itama, she wants the business, she wants to have the power yanda hidayar keyi, she wants to have it all itama tunda duk gadonsu ne kowa

yana da right a kamfanin saidai hidayar tayi bake bake ta hana kowa ya samu saidai ita kanta daya.

Tana tsaye she

feels so embarrassed, a matsayinta na ya ga taheel, kuma cikin babban building din shopping center dinsu amma ta kasa nuna isa.

Harta juya zata bar wajen basit yayi appearing a gabanta, kwata kwata da farko bata ganeshi ba harya gama mata payment din sann

an yasa aka fitar mata da kayan zuwa motanta, ya dube ta yace ta zabi duk abunda takeso a wajen, idan akwai wanda takeso da baya nan dinka ta fada za a kawo mata a take.

Da farko ta nuna rashin jin dadin abunda yayi don ta dauka irin manyan nan ne masu ku

din kasar yawanci zaka gansu matansu uku suna son yammata.

She totally misunderstood him wanda hakan ya sa dole ya mata bayanin koshi waye, ta hanyar nuna mata hotunansu shida ita a wanchan lokacin, tayi mamaki sosai kuma taji dadin ganinsa, don jefi jefi

sometimes tana tunawa dashi don fattu ta shaida mata kamar dan uwanta yake, don har uncle fadwa ke ce mashi.

Yaji dadi yanda taji dadin ganinshi sosai, don yayi tunani Ta manta dashi ma gaba daya ashe abun zaizo mashi ta sauqi.

Tun daga ranar wani kusan

ci shakuwa ya sake shiga taakaninsu, babu abunda zata nema ta rasa a wajenshi, wallahi duk abunda take buqata da wanda bata buqata yake bata, gata fa sosai yake nuna mata harya fara tunanin meysa yake mata gatan, koda ta tambayeshi ya shaida mata saboda ma

haifiyarta da yanda tayi mashi halarci wannan yasa duk abunda zaiyi mata bazai iya biyan abunda fattu ta mashi ba.

Akwai ranar da fadwa ta shiga damuwa sosai, daya lura da hakan hankalinshi ya tashi sosai ya tambayeta ta fada mashi koma menene, nan ta s

haida mashi komai, yanda hidaya tafi tsayawa kan taj, ta fifitashi akansu, komai shi, ta turashi kasar waje, sai take ganin kamar ma arzikinsu shi takeson bama,ita kuma ta dau alkawarin bazata taba barin hakan ta faru ba, saboda ta dalilinshi mahaifiyarsu

ta rasu, tana mashi tsana mafi tsanani.

A take a lokacin basit ya tambayeta me takeso? Word daya kawai zata fada kuma zaiyi mata providing, kuma zai iyayin komai akanta.

Anan ne tayi questioning dinshi, meysa yake mata komai? Meysa yake bata duk abunda

takeso?.

A lokacin ne yaga that’s the perfect time da zai shaida mata koshi waye a wajenta.

Fadwa felt so terrible, hankalinta ya tashi, she couldn’t believe him, ya za ayi ya zama mahaifinta? That’s impossible.

Duk yanda yaso yayi mata explaining komai

taqi saurara, wannan yasa ya bata dan lokaci.

Daga baya ta zauna tayi dogon nazari tare da tunanin abubuwan da suka wuce a baya, akwai lokacin dataji suna magana a office ita da mahaifiyarta, a ranar ne ma bata sake barinta ta hadu dashi ba, bayan nan ma

akwai ranar data taba kamasu a office din, kusancin dataga a tattare dasu baiyi kama da wanda za ayi ma fasaara mai kyau ba saidai kuma rashin hankali yasa bata gane komai ba, nan ta fara questionining kanta what if da gaske yake? What if ita ba jinin. Ta

heel bane? Shikenan batada gadonsu? Ina bazata taba barin wannan sirrin ya bayyana ba inka da gaske ne wannan yasa ta nemi basit sukayi DNA test result ya fito 99% yarshi ce, she can’t change it dole tayi accepting shi din mahaifinta ne,kuma yana nuna mata

so ba kadan ba, son da bata samu ba wajen iyayenta.

Daga nan ne suka fara plans ita da mahaifinta, kuma yayi alkawarin supporting dinta kuma bazai taba bari a gano gaskiar alamari ba.

Cigaban labari..

Zaman da yayi bayan futar fadwa babu abunda yak

e sai Kallon wayanshi, he’s trying so hard kar maganganun daketa trending akanshi karsu dameshi amma ina ya kasa, maganganu iri iri wasu ma na yaqinin ay shi din kamarma bakinsa daya da khaal, ba a san asalinshi ba, don bashida mahaifiya, yanxu haka ma tsi

ntoshi akayi blaa blaa, maganganu dai kasu suka sosai babu dadin ji.

Hidaya makesure that blogs an yada wannan labari mara dadi jin, da suka sosai, wasu abubuwan ma da bai kamata ba.

Rufe wayar yayi ya aje tare da dafe kanshi, he has all the evidence aka

nta and he’s digging more,yanxu idan ya fiddasu to wallahi ta gama yawo gaba daya, dalili daya ne ke dakatar dashi, which is ahalin gidan, da company, yasan da zarar ya fallasa sirrikanta da Abubuwan datayi mashi harma da khaal reputation dinsu zai zube, z

a a zagesu, zq a zagi iyayensu, kuma kamfanin zaiyi kasa gaba daya wata qila ma a rufe shi, and he wouldn’t want that for the family name, wannan hardwork din mahaifinsu ne, kuma yasan khaal bazqi taba jin dadi ba, don these family has been there for decad

es, title dinsu ne, darajarsu ce sannan qimar ahalin gidan ne.

tsabar ciwo da kanshi ke mashi yasa ya dafe kan, shi kadai yasan abunda yakeji a cikin zuciyarshi, abunda bayason tunani akai don shine weakness dinshi wato zancen bashida mahaifiya.

Yana ci

kin wannan yanayin saiga call ya shugo wayarshi, harya tsinke wani call din ya sake shugowa ya dago da kanshi tare da aza rinannun idannshi kan wayar ya dauka, ganin mutallib ke kira yasashi daukan wayar tare da kaiwa kunenshi baice komai ba.

“Tajudeen!”

Yaji muryar khaal ya kira sunanshi

“Na’am” ya amsa shi jiki a mace.

“Kazo yanxu ka sameni inaso muyi magana”

Shiru ya danyi kafin ya amsa shi.

Yana aje wayar email ya shugo mashi kan cewa sai yayi presenting evidence dake nuni da akasin allegations di

n da akeyi akanshi, sannan in 2days idan baiyi presenting evidence ba, za ayi canceling maganar sauya leadership, baza a bashi kamfanin ba, dukda mahaifinshi ya shigar da sunanshi cikin ahalinsa.

He understands haka system din yake dole saiyayi providing

duk wani abu da suka buqata saidai yasan babu wanda ke pressuring abun banda hidaya don shes not giving in kwata kwata kuma ita keda da hannu da wannan al’amarin ko ba a fada mashi ba.

miqewa yayi tare da kwasar takardun shi dake kan desk din ya fita,

nan yaci karo da merk ya shaida mashi yayi informing dinshi duk yanda ake ciki anan office din kafin ya futa.

Tunda ya hau kan titi babu abunda yake sai tunani iri iri, different kinds if thoughts na yawo a kwakwalwarshi, wallahi sam baiga ana binshi ba,

saida ya kusa karasawa hideout din kamar ance ya dago kawai idanunshi ya sauka a wata baqar mota dake binshi, baikawo binshi akeba saida ya sauya hanya yaga still motar na bibiyarshi nan ne ya karama motar mugun

speed ba kadan ba, irin sosai dinnan fa ba

kadan ba trying to escape tailing dinshi da akeyi, cikin ikon allah dake he’s smart ya kufce masu.

Girgizq kanshi kawai yayi ya shiga wata hanya daban harta kaishi ga hideout din.

Yana isowa yayi parking tare da dan jinkirtawa, gaba daya he feels so weak

and tired.

Mutallib daya hango motarshi yayi saurin karasowa inda yake, tare da bude motar, tak din ya futo.

Kallo daya mutab yayi mashi yaga tsantaar damuwa a tattare dashi,sai yaji wani irin tausayinsa sosai wallahi ba kadan ba don harga allah shima s

aida yayi questioning maganar da akayi ta cewa shi din dan taintiwa ne dukda bai yarda da hakan ba saboda bai taba jin koda khaal ne yayi maganar magaifiyar taj din ba balle akaiga ya ganta.

Kallonshi taj yayi yace “i was tailed,inason ku chanza hideout k

afin komai ya daidaita, bazai yiwu mu khaal ya bayyana ba yanxu don za a iya kamashi, sonake saina fidda gaskiar allegations din da akayi mashi, i need to prove bashida laifi akan komai kafin ya bayyana gaban duniya,”

“But taj we don’t have time, suna gab

da cin mana, hidaya ta saka a nemoshi kuka ina gudun..”

“She can’t do nothing…”

Girgiza kai kawai mutab yayi suka shiga daga ciki.

Kai tsaye dakin khaal suka nufa yana zaune yayi shuru, tun dazu yake kallon abubuwan dake faruwa a yanar gizo, ranshi ya

baci sosai ba kadan ba, and he has come to conclusions zai fayyace ma duniya komai, dukda yasan ba lallai a yarda dashi ba za a iya mashi wata fassara daban wata qila ma ace shi yayi fabricating mutuwarshi, komai dai zai iya zama complicated amma yanajin h

akan ne zai iya dakatar da wannan long term qiyayyar data zama masifa, jini ba abun wasa bane, jinin dake yawo jikin taj shike yawo a jikinsu gaba dayansu.

Sallamarsu yasa ya dago ya kalli taj din ganin yanda idanunshi sukayi jaa sosai.

Zama yayi tare

da kama hannun khaal ya sumbacesa.

Mutab ya fita don ya basu waje suyi magana.

Kallonshi sosai khaal keyi ba kiftawa saiya nemi kalaman dazaiyi amfani dashi wajen yima taj din maganar da yakeso ya mashi.

Harga allah ba ayi mashi adalci ba, kuma sai yanx

u khaal ke ganin haka, tun tasowarshi babu wanda ya taba zama dashi ya mashi maganar mahaifiyarshi ba, yama cire batun mahaifiya a rayuwarshi gaba daya don bai taso ya ganta ba, baiji duminta ba, baisan dadinta ba.

Doguwar ajiyar zuciya khaal ya sauke san

nan ya dubi taj din kafin ya soma magana “Tajudeen….kai dan sunna ne kamar kowa, kuma kanada mahaifiya kamar kowa, “

Cikin saurin ya dago da rinannaun idanunshi da suka cika da ruwa badai na hawaye ba.

“Kayi hakuri, kayi hakuri, babu abunda zance maka sa

idai nace kayi hkuri, approach din mahaifanka with how they end up yasa ka shiga wannan yanayin,da rayuwa mai kunshe da kunci”

Nunfasawa khaal ya sakeyi yace “it’s high time ka nemi mahaifiyarka, baka da kamarta ayanxu, koni bazan taba maye gurbin iyayenk

a ba, don alkawarin dana dauka na kasa saukeshi”

Ya dan dakata, siraran hawaye na saukowa akan kuncinsa yayi saurin gogesu.

“Karka zauna ka cuci kanka saboda ni da kuma sunan wannan ahali namu da yan uwanka suka watsar, suka dauki duniya,…i want justic

e for you and i want to protect you don nasan bazasu barka haka ba saisun ga ka wulaqanta”

Saurin kama hannunshi taj yayi zaiyi magana khaal ya dakatar dashi, “bana buqatar ka wanke ni da laifukan da ke kaina, lets put and end to this”

“No khaal no, idan

ka bayyana yanxu komai zai iya faruwa, they can use you against me, they can do anything, zaka bayyana only when na fiddakai na wanke laifukanka”

“But tajideen tayay? How?, na tsufa, ko sun aikani gidan yari yanxu kan laifukan da banba ba komai bane, w

e can only go down together i want to end this, and this is the only way”

“I will not allow that khaal, bazan bar haka ta kasance ba, if anyone is to pay for everything sune, bakada laifin komai and i would not allow that, ka damu dani tun tasowata yiu ha

ve been there till the very end, kanada iyali ta dalilina allah kadai yasan halin da suka shiga, they need you more than i do amma you stand for me, you protected me and i will forever be grateful, now its time for me to pay back, i will bring an end to al

l of this i promise”

Shuru khaal yayi yana nazari, ya zaiyi yanxu? Tabbas yanxu idan ya bayyana bashida kwakwarar hujja akan komai za a iya kamashi, na biyu kuma hakan bazai bashi damar binciken da yakeso yayi akan wani abu da yake suspecting ba kuma ya k

asa tantancewa, yayi tunanin sharing maganganun da taj amma yafiao saiya tabbatar da hakan.

Ko mutallib baiyi maganar dashi ba kwata kwata.

Yanxu dai ba wannan ne mataalar dake gabanshi ba.

“Batun mahaifiyarka…”

Shugowar doctor dake kula da khaal yasa

suka dakata,

Miqewa tsaye taj yayi ya dubi khaal din tare da riqe hannunshi da kyau yace “inason kubar wajennan yau, nayi ma mutallib magana, please don’t ask why”

Girgiza kai kawai khaal yayi taj ya mashi sallama ya fita.

Lokacin daya futo wajen aro

und 5 pm ne, saida ya tsaya sukayi wasu maganganu da mutab cikin sirri kafin ya bar wajen.

Tana daga zaune a wani hadadden parlor ta dora kafa daya kan daya tana shan wine aka budo kofar parlor, as usual yaranshi ne ke fara shigowa dika dika dasu sunc

i baqaqen suit fuska duk maiqo.

Suna hangota duk suka wani sunkuyar dakai alamun girgimamawa, ko kallon inda suke batayi ba saima scrolling wayarta datakeyi.

Shugowar basit yasa ta dago, “princesssss”

Kauda kanta tayi ita wani a lallai fushi take, fuska

rta a hade babu fara’a kwata kwata.

Sallamar sauran yaranshi yayi ya kalleta da kyau yace “kina fushi da papi har yanxu?, toh inason ki saki ranki okay”

“Zanyi murmushi ne only if kace min an gano inda yake”

Wani abu ya danna daga gefe aka bude kofar sh

ugowa parlorn ya kalli black sannan ya miqa mashi tab din hannunshi,

Karba tayi tana kallon screen din, khaal ne a kwance aka dauko shi a hoto, wani irin makirin murmushi ta sauke.

Wani irin dadi basit yaji ganin princess dinshi na murmushi, “thanks to

wannan yaron we found him, yanxu haka doctor da sukayi hiring yana keeping eyes on him”

“Wow…what would i do without you papii”

Dariya yayi ta manya yace “yanxu duk abunda kikace haka za’ayi”

Miqewa tayi da tab din a hannunta ta tako inda black yake, ya

wani tsaya kyaam, edge din tab din ta buga mashi a kanshi saida wajen kanshi ya fidda jini tab din ta fashe “the next time na baka aiki and you messed up i will forget how important you are to, i will crunch you into pieces understood?”

“Yess ma’am” ya a

msata a ladabce

Matsawa tayi ta koma kusa da papinta tace “duk wannan matsiyacin ne ya wargaza min plans dina, I don’t even know how he gets into my scret room harya ya dauka hotunan nan, and kai kuma kaida useless yaranka kuka kasa yin abunda ya kamata

har wannan stupid driver ya samu damar raina maku hankali,”

Ta karashe tana huci kamar ta shaqe shi,hannunta basit ya kama ganin she’s loosing it kuma zata iya yin komai don ranta a bace yake gashi shi black din suna buqatarshi har zuwa yanxu, “princess c

alm down, sun rigada sunyi dealing da wannan,”

Ajiyar zuciya ta sauke hartaji daj wani irin sauqi a ranta dataji sunyi maganin driver.

“Any update? Ko har yanxu baku gani dalilin dayasa ta ajeshi a dakin ba?” Basit ya tambayi black.

“Yes sir, har zuwa

yanxu yana kulle, she only meets him privately ba tare da kowa ba, we couldn’t get conversation din da sukeyi”

“Why don’t you use your fucking head sometimes? Bunch of useless idiots, ka nemi spy recorder ka saka a dakin”

“Yes ma’am”

Kauda kai tayi

tana doka tsaki, gaba daya she’s restless, she wants all her problems gone forever.

Tunda mutallib ya kawo ma khaal bayanin mutuwar driver daya taimakeshi ya kasa cin komai, yayi shuru yana girgiza kai kawai.

Babu abunda yake a zuciyarshi sai innalill

ahi wa inna ilaiahi rajiun, gashi bp dinshi na neman hawa sosai.

Babu makawa daga bayanan mutallib yanda ya shaida mashi cewa an tsinci gawar mutumin yayi raga raga dalilin accident yasan cewa sune, kuma saboda shi ne sukayi ma mutumin haka daga taimakon

shi dayayi, wallahi hankalin khaal ya tashi sosai ba kadan ba da wannan zancen.

Bangaren taj tunda yabar wajensu khaal bai taaya ko’ina ba sai wajen detective dinnan, sun dade sosai suna zantawa, anan ne ma yakejin zancen akwai wani usb daya bama jamid

dake kunshe da evidence akan incident din khaal kuma yana tunanin abubuwan dake ciki zasu taimaka sosai wajen fidda khaal, idan da zai samo masu usb din.

Shuru taj yayi don baisan ta inda zai fara ba, hidaya ta fidda shi kasar wajen tunda dadewa ba tare d

a sanin kowa ba acewarta kenan, saidaga baya ya sani.

Yanxu ya zaiyi ya samu wannan usb din? Ta ina zai fara neman jamid? Don baisan wace kasa ta kaishi ba.

“Barad” yaron ne kadai ya fado ranshi, definitely zaisan inda babanshi yake.

Da haka sukayi sa

llama lokacin wajen karfe goma na dare.

Baiso komawa gidan ba harga Allah don ko inuwa daya bayason sharing dasu amma dole ya koma kodan ya samu jin inda jamid yake wajen barad, daman school din da yake friday ake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login