Showing 102001 words to 105000 words out of 338813 words
bedroom ta jawo b
ox dinta ta futo,duk suna zaune suna kallonta ta karaso inda taj yake tunda aka tafi da sabeeha ya kasa matsawa daga inda yake tsaya, jawo hannunshi ammu tayi yana fuskantarta ta soma magana kamar haka .
“Kayi babban kuskure tajudeen, ka tafka babban kusk
ure daka bari fatima ta kubuce maka ta fita daga rayuwarka, nasan babu abunda zance maka yanxu da zaka yarda but ina fatan zaka bude idanunka ka gane masu sonka, amma inaso ka sani yanda ta fita tabar gidan nan ta tafi da farin cikinka ta tafi da kwanciyar
hankalinka don bazaka taba samunshi ba, ita din haske ce a cikin rayuwarka tafiyarta ya mamaye ka da duhu, ita din kyauta ce daga allah a gareka ita din wata bangarece a cikin rayuwarka, ta kula dakai alokacin da baka hayyacinka bata kyamaceka ba, bata gu
jeka ba, ta kubutar dakai daga duk wani sharri, she stand by you protected you,ta shiga damuwa, wahala kunci da azaba daga hannun makusantanka dukdan saboda kai amma ta shanye ta jajirce, duk wanda ya kebanceka sai an mashi lahani nata azuciya akayi mata s
annan ka saka mata da sharri, ka zama butulu,mark my wordss…you’ll regret this”
Tana fadin haka ta ja akwatinta tabar masu gidan tana kuka “i can’t deal with all of you, I can’t”
Tsayawar nan dayayi magnagnunta ba karamin suka sukayi masa ba azuciya, gab
a daya sai yaji duniyar na juya mashi, hannunshi har wani irin rawa rawa yake, a daidai lokacin ya fara jin wani irin sauyi a tattare dashi gaba dayansa………
Ya Allah
😭
what a heart breaking moment..
✊
💋
BOSS LADIES WRITERS
💋
✊
MATAR TAJ (destined with
you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍
️
Book2
PAID
Chapter 80
Tunda aka shigar da ita motar babu abunda take sai hawaye, duk yanda taso ta hana kanta kasawa tayi, zuciyanta ya karaya sosai, at least she was expecting him to listen to her, amm
a ya rufe ido, ya fada mata to her face bayason ganinta ya tsaneta, and yana mai baqin cikin ranar data shugo rayuwarshi.
Bangaren taj yana nan tsaye kamar statue ya kasa motsawa, afiya da hidaya ko kwafa sukayi suka koma bangarensu ya rage dagashi sai
fadwa, gaba daya wani irin dadi takeji aranta ba kadan ba.
Yana cikin yanayin nan ta kamo hannunshi tana mai sauke murya kasa kasa, “don’t upset yourself cause of useless people who fooled you, they have
bad intentions against you, i know you’re hurt baby
brother just know that i will always be here for you”
Kallon daya mata saida gabanta ya fadi, ya maida dubanshi ga hannunshi data kama ta rike.
“I don’t fucking need you or whoever, and don’t you ever put your filthy hands on me”
Yana kaiwa nan ya juya
afusace ya wuce sama kamar zai tashi sama.
Yana shiga dakin ya banko kofar ya wuce closet, ashe kiran da aka mata ninke kayanshi take don gasu harta ninke akan table island din dake closet din harda nata a gefe.
Saurin dafe kanshi yayi ya runtse ido ya
wani irin naushin iska, “noooooo whyy!!! Why!!! Whyyyyyy”
Ya fada cikin ihu yana dafe table din, accessories dinshi dake wajen ya watsar gana daya a kasa ya dafe table din.
Yakai wajen minti goma a haka kafin ya wuce bathroom ya sakarma kanshi ruwan sany
i ko kayan jikinshi bai cire ba.
A taqaice dai isolating kanshi yayi, tun bayan da ya sakarma kanshi ruwan sanyi zazzabi mai zafi ya soma lullubeshi, gashi tun breakfast baisa komai cikin shi ba sai kwanciya da yayi.
Fadwa na waya afiya ta shugo tayi
saurin katse wayar, suna kallon juna suka kyalkyace da dariya afiya tace, “lets have a dinner date, bills on me”
“Sure!!..will spoil you with some goodies as well to celebrate our victory”
Haka suka dunga murnar korar sabeeha da sukayi, tafiyar da ammu
tayi ma ba wani damunsu yayi ba kwata kwata.
Afiya na fita fadwa ta kwanta kan gado tana sauke wani irin nunfashi imagining gata ga taj yana tasha jikinta making love to her, gaba daya illusion din abun yasa ta mance a wani yanayi take, sai taba jikinta
tace tana moaning auzubillahi, ta rigada tayi nisa bata jin kira kwata kwata.
Wajen karfe goma ya bude idanunshi, tun wajen karfe hudu dayayi sallah ya koma barci ko zaina jin zafin da yakeji aranshi, aiko barcin wahala ya kwashesa bai tashi ba sai y
anxu, gaba daya he feels weak, tired and lost, komai haushi yake bashi,haushin kanshi ma yakeji sosai ba kadan ba.
Dakyar ya lallaba ya miqe zaune yana dafe da kanshi kawai ya soma jin echo din muryar sabeeha a kunnenshi, cikin hanzari ya dago saiko ya ga
nta gabanshi tana mashi murmushi, “didi ka tashi? Ga coffee na kawo maka”
Harya miqa hannu kawai ya kifta ido yaga babu ita a wajen, saurin girgiza kanshi yayi ya sake bude idanunshi yayi tsuka kadan sannan ya miqe ya wuce bathroom yayi wanka da ruwan zaf
i sosai sannan ya dauro alwala dukda yanajin jiri jiri sosai.
Yana futowa daga bathroom ya saka jallabiya ya nufi wajen praying section chan ya sake hangita zaune tana jiran isowarshi suyi sallah, rai a bace ya soma magana da kanshi ya runtse idanunshi “s
top it stop itttt”
Tun bayan ya idar da sallah ya zauna kan sallayan yana azkar, abunda cikinshi bai cika yi ba sai gashi yau ya fara, wato kukan yunwa, bai taba lura da bai damu da cikinshi ba sai yau, saboda sabeeha ta dauke mai komai, 3 square meal d
inshi yarinyar nan ita ke handling, adaidai lokacin
da bai buqata ba tasan zaiji yunwa zata kawo mashi,kallon bedside watch dinshi yayi wajen 11 saura kafin su kwanta by 10 haka take kawo mashi coffee da fruit.
Haushin kanshi yakeji gaba daya for depend
ing on her unknownly.
Haka nan ya tashi ya zame jallabiyan shi ya rage dagashi sai irin dogon wandon nan, ya futa daga bedroom din, kallon sitting room dinau ya dungayi yana ganin kamar zai ganta a kwance kan couch, daya tuna karyar data mashi sai kuma ya
fara jin haushin kanshi, wata yar tsuka yayi ya nifi kitchen nan ma dai yana kunna haske ya soma ganin kamar gata tsaye tana mashi murmushi, haushi da takaicin kanshi yasa ya futa daga kitchen din rai a bace, why would he be remembering her? Whys he like
this? He hate being like this, and he çanta stop him self”
Wallahi oga a zaune ya kwana, tunda ya zauna kan couch din bedroom yayi relaxing bayanshi ya rufe ido babu abunda yake sai tunani, tunanin rayuwarshi ta baya har kawo iyanxu,he feels lonely, t
unanin lokacin dayake shi kadai a uk ne ya dawo mashi da zaman da yayi a gidan nan kafin ya tafi, same exact feeling yakeji.
Washe gari tun wajen karfe shida ya fuce daga gidan dukda yana jin zazzabi ya wuce gym wai ko dan zai samu sarari ya daina ganin
yarinyar nan duk inda ya motsa, closet ne bathroom ne kai ko’ina ganinta yake, kamshinta yakeji, he’s feeling her presence ako’ina and he hates it so so much.
Yana cikin workout kamar zai illata kanshi mutabbl yazo, yana kallonshi surprisingly, intenti
onally shi yazo wajen don yasa receptionist suna informing dinshi idan yazo.
“Hello buddy what a coincidence yaushe kazo nan,”
Shuru taj yayi bai bashi amsa ba yana abunda ke gabanshi, don ko magana baya son yi, anything da zai futo daga bakinshi yanxu b
azaima mutun dadi ba.
“Is everything okay? You’re going too far taj karka illata kanka”
Wani irin kallo taj yayi mashi tare da aje thumbells din daya dauka mai weight sosai yabar mashi wajen ya koma kan threadmill yasa speed sosai yana gudu.
Mutallib na
kallonshi yayi gudun yayi gudun har yana neman faduwa mutallib yayi saurin kashewa ya dafe hannunshi yana mai dubanshi with concern akan fuskanshi yace “please kayi hakuri, you’re hurting your self taj, what is the problem?”
Bugun mills din taj yayi rai
a bace idanunshi sunyi jaa sosai ga gumi ya gama keto mashi yace “i fucking hate liars…betrayerssss”
Saida gaban mutabb ya fadi don ya dauka dashi yake wallahi, “i’m sorry taj…what ever happens it happens for a reason”
“No she has no reason..she has no r
ight to lie to me, to fool me, to trick who d hell is she?”
Ajiyar zuciya mutabb ya sauke yana son mai son jin karin bayani yace “im sorry for meddling in your business but if you want to talk i’m here okay”
Zama sukayi taj yana ajiyar zuciya, yana mai
duban mutbb yace “you what i hate the most in my life is karya..bana son karya bana son ayi fooling
dina, but this..this girl…she lied to me, i was so invest in the pregnancy she claim is mine, i was so happy”
“You mean your wife?”
Da mamii taj ya duves
hi ya akayi ya sani, “ sorry you mentioned her once ranar da muka fita tare kace min zaka tsaya mall ka saya chocolate for your wife”
“Don’t ever call her my wife, it’s done…i never want to see her face ever again”
Tunda ya soma magana hankali mutabb y
a tashi, tabbas yasan fatima yake nufi, amma yanason yaji karashen zancen.
“Toh yanxu ya zakayi da ita?”
“Na koreta, i dont need people like her around me”
Shuru mutabble yayi yama rasa tunanin da zaiyi.
“I’m sorry amma ina ganin hakan da kayi baka kya
uta ba, what if batada kowa what if batada wajen zuwa? Are you sure you made a right decision?”
Shuru taj yayi, kwata kwata baiyi nazarin ya akayi mutabble yasan bata da kowa ba kuma bata da inda zataje ba sai maganganun nashi da sukayi tasiri aranshi.
Sai wajen karfe sha daya suka bar wajen, suna rabuwa mutabble ya bazama neman fatima, mutanen daya sani na cikin gidan securities ya fara nema, adan zaman da yayi dasu he got close to one of them nan yake shiada mashi abunda ya faru a jiyan da yanda aka t
afi da ita.
Mutallib yaji rashin dadi ba kadan ba, ayau da khaal na raye bazai bata bari a wulaqantata ba.
Around karfe sha biyu aka fiddata daga cell din, inda akayi transferring dinta zuwa domestic workers organization, mutallib ne yayi hanya akabi
tanan aka karbeta, yayi hakan ne yana gudu kar a cutar da ita don yasan tunda ta fita daga gidan tasan sirrikansu bazasu taba barinta haka ba.
Cikin gaggawaa anan organisation din sukayi clearing dinta za a maidata kasar data futo washe gari.
Da yamm
a mutallib ya buqaci ganinta nan ya masu karyar ay yar uwarsa ce shima aiki yake a wani organization din daban, babu wani dogon bincike aka barshi ya ganta.
Lokacin data futo taga mutallib tayi mamaki sosai, ba karamin tausayinta yaji ba, amma ganin ta
da yayi cikin koshin lpy yaji dadi sosai.
“Fatima kiyi hakuri…kinyi ma khaal halacci, ina fatan bazaki sake shiga irin wannan rayuwar da kika shiga ba”
Hawayen dake neman fitowa daga idanunta ta hanasu saukowa ta girgiza mashi kai kawai,kora dai taj ya m
ata korar wulaqanci, leavung her miserably, koda yake daman rayuwarta gaba daya is miserable tun daga haihuwarta, uwarta ma tayi abandoning dinta balleshi? She has no reason to complain, ita dai haka tata kaddarar take kuma ta amsa hannu bibiyu.
Wata le
da ya bata tare dayi mata fatan alkhairi bayan ya jaddada mata karta sake ace za a kaita wani waje, ko tafa alamun za a kaita wani waje ko she sense something suspicious ta kirashi a waya, nan ta shaida mashi babu waya hannunta.
Daya daga cikin wayoyinshi
ya bata kafin ya mata sallama ya tafi.
Yana tafiya ta bude ledar, ga mamakinta taga kudi ne kuma da yawa, nannade ledar tayi ta koma ciki ta doka tagumi, yanxu gove goben nan zatabar kasar nan, kuma har abada bata fatan sake sanya kafafunta a kasar.
Shi
n ko me zataje ta tadda a gida? Koma dai an mance da rayuwarta gaba daya? Shekara kusan biyu kenan.
Haka ta kwana ido biyu, ta kasa runtsawa, tayi alkawari daga ranar data guta daga kasar nan bazata kara kawo tunaninshi aranta ba, zata goge gaba daya memo
ries din zamanta dashi don babu wani amfani da zai mata.
Da daddare ganin baizo dinner ba yasa hidaya tazo har bedroom dinshi da divorce papers da papers din next guardian dinshi don har yanxu sabeeha na matsayin next kin dinshi, and she wants that auth
ority back.
Koda ta aje mashi papers din kasa cewa komai yayi, i need this papers gobe.
Tana fadin haka ta fuce yabi bayanta da kallo.
Without seconds yayi signing paper din ya aje a gefe.
Washe gari ta kama monday, tun kafin ta wuce office ya sauko ka
san ya bata papers din, tayi mamakin ganin ba duka ya bata ba saidai the most important one din daya bata shi tafi buqata so batace komai ba ta kara gaba.
Sabeeha baiwar Allah tun wajen karfe bakwai aka fitar dasu ashe ba ita kadai bace su kusan uku ne
za a maida, sauran shekarun aikin su a kasar ya cikaza a maidasu, ba kamar nata case dinba da ta shiga record don da an kaika police station to ka shiga record.
Cikin wata bus aka zubasu sai airport, kowanne aka bashi passport dinshi, ma’aikacin organiz
ation din saida ya tabbatr sunyi boarding kar su gudu don wasu abunda suke kenan kafin ya kara gaba.
Flight din nasu sai wajen yamma zai tashi, cikin airport din akwai restaurants, Akwai boutique, duban kayan jikinta na tun shekaran jiya tayi, ko sauyawa
batayi ba da tayi wanka shi take maidawa don bata da komai, haka ta futo daga gidannan.
Wannan yasa ta shiga boutique din da kudin da mutallib ya bata ta saya riguna guda biyu da pants sai sabon takalmi da yar bagpack dinnan ta yan makaranta mai kyau sann
an ta shiga bathroom ta sauya kaya ta zuba sauran da wanda ta cire cikin jakar sannan ta fito.
Wajen yamma around 6 haka jirginsu ya daga sai NIGERIA………
Lokaci guda yaji gabanshi na wani irin bugawa fat fat fat ya rasa dalilin, lokaci guda ya rasa natsuw
arshi, tunanin yarinyar nan ya addabeshi ya kasa ganema kanshi, duk motsin da zaiyi saiya tuna da ita a ko wanne lokaci, memories din dayayi loosing ko haka suka dunga mashi flashing, yanda take kula dashi, yanda koda yaushe take tare dashi in yana kuka ta
na kuka idan yana dariya tana dariya.
He’s loosing it gaba daya, ya rasa meke mashi dadi,ga maganganun da sukayi da tareeq ya tsaya mashi arai sosai, he’s hating this kind of feeling, she lie to him ta mashi karya amma meysa yakejin gaba daya kamar bashi
ba, yanajin kamar part of him is gone, magnganun ammu ne suka soma mashi yawo akai, ya soma magana da kanshi.
“No no i will never regret my decision, she’s just my maid, what’s so special about her?”
Haka ya dunga reminding kanshi, wallahi daren ranar ba
i runtsa ba ya kasa gane meke damunshi, abunci ko banjin akwai abunda yasa ma cikin shi
between jiya da yau, sai ruwa da yake yawan sha, bai ma bi takan cikin nashi ba kawata kwata cause yayi loosing appetite gaba daya.
closet ya shiga zai dauka laptop di
nshi ko zai samu ayyukanshi su dauke mashi hankali, daga gefe ya hango kayanta a jere fess fess saurin kauda kanshi yayi don ko gani baya son yi, daga gefe kamar ance ya daga idanunshi yaga chocolates din daya suyo mata ta jera su cikin wani dan bowl.
Tak
owa yayi har zuwa wajen ya dauka daya ya fito daga closet din ya zauna bakin gado yana kallon ledar, chan kuma meya tuna kawai ya wulla chan gefe ya kunna laptop dinshi, zaman da yayi a dakin ji yayi kamar ana suffocating dinshi ya koma closet din sai yaji
he feels some kind of ease daya dawo nan saboda kamshinta dayakeji, ko nashi bayaji sai nata amma ya kasa accepting saboda hakan ne.
Adaidai lokacin da ya rasa natsuwarshi haka ta kasance a wajenta don a daidai lokacin jirginsu ya daga, wani irin emoti
onal moments ta shiga tana tuna yanda tazo garin da first encounter dinsu, sanda ta shiga daki ta ganshi zaune shi kafai lokacin da baya cikin hayyacinshi the first din dayyi mata shine murmushi dayayi melting zuciyarta, da farko tana ta tsoron haduwa dash
i don ana cewa duk caregiver data tunkareshi aranar take barin gidan, gashi saita kasance itace caregiver ta farko daya fara amincewa da ita, ya kaidata bestfriend dinshi, ya bata damar kula dashi, ya zame mata wani sabon farin ciki a rayuwarta da bata tab
a samu ba, tayi kokarin hana kanta tunashi amma ta kasa, kamar ana ingiza zuciyarta, tayi rauni sosai.
5 daidia ya bude idanunshi a razane, wani irin mummunan mafarki yayi, ashe barci ne ya dan daukeshi na yan mintina kan resting chair din dake closet d
inshi, don har wajen 4 idanunshi biyu, bazaice ga abunda ya tabaka ba.
Nnamdi ezikwe international airport abuja…
Misalin karfe takwas flight dinsu ya sauka saboda time difference dake tsakani, da clearance da komai da akayi masu saida ya dauka wajen
awa biyu, tund ata sauka gabanta ke faduwa, sai yanxu takejin wani sabon tashi hankali, nan bathroom din airport ta shiga tayi alwala tayi sallah anan masallacin dake ciki kafin ta fito tana dube dube, abu na farko data farayi shine chanza kudin da mutall
ib ya bata, aiko wajen dubu dari kudin donma ta kakkashe wasu a boutique.
Tana karba ta saka su cikin bagpack dinta