Showing 222001 words to 225000 words out of 338813 words

Chapter 75 - MATAR TAJ COMPLETE

soma ji hankali a tashe ta daga hannayeta tana bugun kirjinshi gashi ya banqarota sosai b

abu damar turashi.

Me zatayi banda hawaye, tanajin yanda yake shiga ko’wanne lungu da sako na hole din lips dinta, lips dinshi na saman nata ya kama na kasan ya kama na sama, harshenta ko yasha juyi sosai ba kdan, saliva dinsu kam ya gama zama taste daya

.

Yifa yakeyi babu ji babu gani kwata kwata baijin turashi da take dadi ma shi abun ke mashi, da ya samu chance din gasping breath dinshi ba tare da ya cire bakinsu ba sai yayi wani irin intimate moaning gently alamun abun na mashi dadi sosai, shi kanshi

yasan there’s a beast within him daya sashi kasa sakinta, so yake dole da kanta tayi acknowledging presence dinshi, he has had enough of this little drama, he was giving her chance saboda guilt din abunda ya mata idan ta zabi ta nuna kamar bata sanshi ba b

azaiyi forcing dinta ba, amma bazai yarda su zama strangers ba, ya gama amincewa da he’s also here for her as her husband.

Musamman yanxu dayaji maganar mamanta zata aurar da ita what if he loose her for good?, bayan yasan shi mijinta ne har yanxu kuma au

re kan aure haramun ne.

Murda kofar maya tayi hankali a tashe, ta wuce 20mins a sitting room din main house tana jiran sabeeha babu ita ba labarin ta take hankalinta ya tashi ta fara sake sake aranta, tana isowa part din kuwa ta murda kofar tajita rife,

ay batasan sanda ta soma bugun kofar ba kamar yaqi.

Sama sama ya fara dawowa hayyacinshi, saboda kncking din, ya zare bakinshi da gaba daya danyi jaa sannan ya bude idanunshi da sukayi jaa sosai suma ya dan saketa kadan bai matsa daga jikinta ba ya duvbe

ta ganin yanda idanunta yayi gaja gaja da hawaye, lebenta garya dan kumburo kamar wadda akayima lip filler.

Smirking yayi kafin ya dan rankawafa daidai kunenta yakai bakinsa yace “

أفتقدك كثيرا لها”.

I’m sorry, I missed you bibi…”

Yana karashewa ya saket

a tare da danna pins din kofar, maya tayi hanzari budewa gabanta na faduwa, abunda batayi expecting ba kuwa ta idanunta ya gane mata,zuciyanta na gudu sosai kamar ana tsere, kallo daya ya mata ya juya ya wuce ciki, maya ta dubi sabeeha dake kokarin daidait

a natsuwarta tuni ta goge hawaynta da gaggawa tunda ya soma danna pin din kofar zai bude.



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR TAJ (destined with you

🩵



🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 101

Dagashi har ita maya ke kall

o , tama rasa me zata ce, sabeeha ko ta kanta batabi ba ta fuce daga part din maya data sandare tsabar takaici ta juyo a fusace tabi sabeehar.

Daidai tsakiyar compound din maya ta wani irin danqo hijab dinta tayo baya da ita, sabeeha dataji hijab din na n

eman shaqeta ga yanda maya ke jawota ta baya kamar zata fadi tayi hanzarin jan wajen wuyan hijab din da karfe.

Shan gabanta maya tayi kamar wata zakanya tace “uban me kukeyi a part din? Harda rufe kofa? Ehhh!!! Fadamin me kukayi?????”

Wani irin kololon b

aqin ciki ne ya tsaya ma sabeeha a maqogaro kamar ta kamata ta mata dan bura’uban duka daman gashi a hasale take kuka kawai takeson yi kuma ta huce takaici.

“Kije shi ki tambayeshi tunda shi ya rufe kofar bani ba”

Tana fadin haka ta fuzge hijab din maya

ta sake jawo hijab din nata ta finkice shi this time around saida ta fadi a kasa ta dan kurja hannu harda yar kara ta kwala.

Maya ta bita da kallo, tana sanye da atamfa doguwar riga ta kamata sosai musamman wajen kirjinta daya matse cleavages din ya fit

o sosai, rigar ta laila ce da aka bata, saboda tafi laila kirji sosai nesa ba kusa ba yasa ta dameta, cikin irin dai kayan da ake tattara ma yan aiki su saka wanda suma zasu dan mora, ganin kirjinta kawai yasa zuciyar maya ta kusa bugawa don ta fita nesa b

a kusa ba allah ya bata albarkatattun kirji luma luma gasu farare tasss, milky kamar madara ko digon abu babu a jiki irin baki bakin nan, kamar fatar jariri hasken wajen yasa sai wani glowing suke a bayyane, bata yarda a gani kwata kwata don koda yaushe ci

kin rufewa take yanda baza a taba sanin tana dasu ba, ko hadiza bazata iya cewa ga yanda kirjin sabeehar yake ba, wani kukan kura maya tayi tayo kanta zatayi dambe da ita ta hanyar jan gashin kanta data kudunduneahi ta nade don sabeehar na tsugunne bata ka

iga miqewa ba saboda fadin datayi, jan gashi takeyi kamar zata tsinka mata kai, sabeeha na kara saboda zafi sosai kan ya warware, maya kamar tayi kuka ta dora hannu aka saboda ganin datayi ma gashin ya sauko a kasa, yarrr jelar ta fado, saboda rashin gyara

da baya samu sosai na rashin kamilalllan kitso yasa take nadewa bata tajewa, idan da ta taje ya zubo ay saidai maya tayi hauka muraran, don ko gashin doki da take karawa extension din baya kaiwa irin wannan gashin, “shegiya haihuwar asara, wallahi saikin

fada min ubanme kikeyi a part dinsa, inba haka ba wallahi koni koke”

Tana fadin haka ta soma dukan sabeeha, sabeeha da zuciyarta itama ke kusa batasan sanda ta soma ramawa ba tana dukanta itama tana ramawa,“yar iska,ballagaza, daman nasan yanda kike shish

ige masa kina shiga part din da sunan kai masa abunci da gyare gyare nasan luring dinshi kike son yi ke kinga farin mutun ko,bari ki shiga gidan arziki toh wallahi ko a mafarki karki taba tunani zaki shugo zuri’ar mu, babu yayan titi a zuri’ar marasa galih

u,inda ya taka baki isa ki taka ba keba kowan kowa ba”

A harzuke sabeeha ta dago duk ta gama faffarke mata hijab dinta kiris ya rage ta soma hawaye don maganganun nan sun taba ta sosai da idan ance batada galihu baya mata zafi amma yanxu saitaji abun kama

r an chaka mata wuqa a wuya.

“Duk wannan haukar da kikeyi badan komai bane ba sai dan kinsan cewa nafiki da komai, nida kika ikirarin banida galihu, kuma na rantse da Allahn shi da kike wannan ihun akanshi na fiki daraja a idanunshi sau dari nida nake yar

aiki mara galihu saboda na mashi halarcin da ko a lahira bazai taba mantawa dani ba mahaukaciya”

Sabeeha na fadin haka ta juya maya da taji zafin kalamanta sosai babu abunda yafi tsaya mata sai cewa da sabeehan tayi ay ta fita da komai, ya za ayi yar aik

i ta fita da komai, hannu ta daga batayi wata wata ba ta wanke sabeehar dashi, ta sake daga hannu zata mareta sukaji tsawa kamar daga sama.

Cikin hanzari hamad ya karaso tare da dubansu su biyun, ganin yanda ta fafarkewa sabeeha hijabi gashi tana shirin k

ara sauke mata wani mari yasa ranshi baci kololuwa, kallo daya yayi ma sabeeha ya kauda idanunshi don bazai iya cigaba da kallonta ba kanshi ya kunce don bai taba ganinta haka ba a irin wannan yanayin sai yanxu, ya maidashi ga maya, hannun data daga ya jan

yo tare da janta da karfi, “ka sake, ka sakeni mana, ban gama da wannan yar iskar ba, mai bin maza, kaima kota baka kasha ne? Eh? Inba haka ba maisa zaka hanani koya mata hankali shegiyasa haihuwar titi”

Yana isowa sitting room din kasa ya saki hannunta t

are da turata tsakiyan carpet yace “maya!!!!!! Dont you dare curse her ever again”

“Idan nayi sai me? Eh???idan nayi sai me? “

Hannunshi na karkarwa ya daga zai watsa mata mari ya dakata tsabar bacin rai

“Ya hamad!!!!”

Laila ta dakatar dashi tare da s

aukowa badan laila ba daya wanke ta mari tass yaga karshen rashin kunyarta kwata kwata batasan darajar dan adam ba.

Laila na janta amma huci takeyi, “dan allah kizo muje, maya…”

Fusge hannunta tayi ta wuce sama kamar zata tashi, laila tabi bayanta.

Ci

je labbanshi yayi yanajin zafi aranshi, akan idanunshi ta daga hannu ta mari sabeeha sannan ta bita da mugayen maganganu, abun ya mashi zafi sosai kamar shi akayi ma.

Juyawa yayi ya futa har zuwa compound din ganin babu sabeehar a wajen yasashi hin backya

rd, yana zuwa kuwa ya ganta tsugunne bakin kofa ta hade jikinta tana hawayen takaici da baci rai, ya rasa mai zaice mata gaba daya wani irin lallashi zai mata, ita ke kuka amma shike jin zafi aranshi.

Saida tayi mai isarta ta tashi tsaye ta goge hawayen s

annan ta hude kofar baya ta kitchen ta shige batama lura da hamad ba.

Lokacin data shiga daki basira an rigada an jeme ta bude cinyoyon iska nada shiga ga ac, sai jawo masori takeyi.

Hijab din data nannado ta aje a bakin gado sannan ta nufi bandaki. Tana

shiga ta rufe kofa kukan data shanye ta sake sakinsa, tayi tayi harta godema Allah, meysa zai bayyana a

Lokacin da bata buqatarsa maysa zai bayyana a lokacin da bata murarin ko ganinshi? Bata kaunar ganinshi ko kadan, wannan kadai ya sanya mata wata qiya

yyarshi, ta gama cireshi aranta, ta gama fiddashi daga rayuwarta, meysa bazata samu peaceful rayiwa ba kamar kowa, she wanted to forget everything the pains and the torture she endured followed by wulaqancin dayayi mata yaqi yarda da ita ya saka mata halar

cin datayi masa da butulci, alokacin daya kamata ya yarda da ita ya amince da ita.

Kawai saita fara tunawa da abubuwan da suka faru a baya, yanda yayi mata korar wulaqanci aka fiddata daga gidan nan, da yanda rayuwarta ta shiga hadari duk dan saboda shi,

all that trauma ya dawo mata sabo fill.

A takaice dai takai awa guda tana tsugunne tana kuka, tana tunani kala kala, tama rasa dalilinshi na abunda ya mata dazu tunawa da tayi babu wata ragowar alaka dake tsakaninsu, bashi da damar sata dole akan komai, i

dan ta zabi tayi ignoring the fact that susan juna ra’ayinta ne don babu komai tsakaninsu, ya yanke duk wata alaka dake tsakaninsu, kuma bayan duk abunda ya mata bai chanchan yazo da fuskar kamar babu abunda ya faru ba a baya, idan ya mance abunda ya mata

ita bata mance ba.

Haka ta dunga tunani ita kadai tana shawara da zuciyarta tama gwammaci kawai tayi auren da mama tace dangin babanta zasu mata, yafi mata maybe idan ta tafi chan bazata kara waiwayon rayiwar datayi ba a baya wata kila ma karshen wahalar

ta kenan ta rayuwa, wata kila hakan ya zamo mata alkhairi.

Babu abunda yafi mata zafi game da fadanta da sabeeha kamar zagin ta datayi ta shegantata, bata taba zama ta waiwayi rayiwarta ba gaba daya saboda ta taso bata da yancin yin magana bata isaba bata

kai ba, ba tun yanxu ba take yawan tambayar kanta shin tanada uba ko bata dashi, don yanda inna ta fada mata shine kafin a haifeta ya rasu kuma shima a lafiya yake don su innar ma duk yan lafiya ne.

Ta taso dai kawai gata nan, babu gaba ba baya kamar mar

a galihu din kamar yanda sabeehar ta fada gashi batda damar tambaya sai taga fuskar nema zata iya, she can never questioned mamanta saboda tsananin tsoronta da takeji.

Tana gama koke kokenta dataga babu amfanin da zai mata ta dayro alwala ta futo.

Kaya

n jikinta ga sauya sannan ta dauka hijabin basira ta saka ta shimfida sallaya ta hau salloli.

Ta bangaren mutumin shiko yana hawa saman nan bai wuce ko’ina ba sai bathroom, ya sakar ma kanshi ruwa sosai, duk wata kofar gashi data bude a jikinsa saboda s

hauqi kokarin rufeta yake,ruwa na sauka daga kanshi zuwa kirjinshi yana tsaye babu abunda yake sai tunani.

“Yanajin kamar bai mata adalci ba, amma ina bazai iya jurewa ba, wannan shirmemm wasan da takeyi bashi da enough time for it”

The next day..

Tun

da tayi sallar subh akan sallaya bata tashi ba kusan ma dai a zaune ta kwana, wani irin zazzabi take ji yana neman rufeta sosai, ga azababben ciwon kai, dan rakubewa tayi kan sallayar ta rufe jikinta da hijab din dake jikin nata.

Tana nan kwance a hakan t

a rufe idanunta batama san gari ya waye sosai ba don har basira ta tashi itama itada bata tashi yin sallar asuba sai wajen karfe bakwai.

Ganinta kwance da mamaki basura tayi don tasan inta tashi sallar asuba saidai ta taddata a kitchen badai a daki ba, Ta

shinta basira ta soma yi, da kyar ta iya tashi zaune jikinta gaba daya ya zaka weak sosai.

Kallonta basira tayi ganin tayi wani jajaja tace “chap ya akayi yau baki rigani futa ba ko bakida lafiya ne?”

Ko bakinta kasa budewa tayi tsabar yanda ya mata nauy

i ta girgiza mata kai kawai saiga hawaye ya sauko tare da amai kamar wanda aka tunkudo shi lokaci guda, amai take kamar zata fidda kayan cikinta kuma babu komai cikin nata don ko abuncin dare bata samu taci ba saboda kidimar abunda ya mata jiya baisa ta iy

a tunawa da cikinta bama, ta koma suuu ta kwanta kamar wadda babu ruwa a jikinta.

“Kaii Bara na kira anty rabi”

Cikin sauri basira ta futa, bata jima da futa ba sai gata da anty rabi sun dawo, tunkararta rabi tayi tace “subhanallahi meke damunki sabeeh

a” gaba daya ta gama bata jikinta da ruwan amai

Dakyar ta iya sake tashi zaune ta dafe kanta saboda wani irin nauyi da yake mata muryanta kasa kasa tace “kaina na ciwo jii…jikina ci..wo”

“Subhanallahi ko zazzabi ne? Harda amai?” rabi ta fada tana tab

a wajen goshinta don jin temperature dinta.

Wani irin zafi taji sosai wanda yasa ta cire hannunta daga goshinta tace “zazzabi ne wannan ay, taimaka mata basira ta tashi bari na dauko magani sannu”

Tana fadin haka ta futa har zata shiga dakinta ta dauko

magani ta dakata tare da shiga dakin hadiza.

Da sallama ta bude kofar, a zaune ta taddata tana waya tana ganin rabi ta dan dakata daga maganar da takeson yi.

“Mun tashi lpy hadiza?”

“Lafiya lau, wani abun ya faru ne aka biyoni har daka?”

Tabe baki rab

i tayi tace” Ah ah babu komi daman sabeeha ce ke zazzabi harda amai shine nace bari na fada maki”

“Allah ya sawaqa” tana fadin haka ta koma kan wayarta.

Kallonta sosai rabi tayi da mamaki, ba tun yanxu ta lura da alakar dake tsakanin hadiza da yarta ba,

wallahi inkaga yanda takema sabeeha zaka rantse ba itace ta tsugunna ta haifeta ba ya za ayi yarki na zqzzabi kamar zata shide amma furucinki bai wuce allah ya sawaqe ba, ko alamun damuwa bai bayyana akan fuskanta ba kwata kwata.

“Koda wani abun ne?” Hadi

za tayi magana ta wani hade rai, kwafa kawai rabi tayi ta futa ta dauko magani ta dawo dakin nasu,yanda ta barsu haka ta dawo ta taddasu, taimaka mata sukayi rabi ta cire mata hijab din nata daya baci, da taimakon rabi suka je bandaki ta kuskure bakinta b

asira ta hado mata ruwa shayi ta dan sha kadan, ko sipping biyu batayi ba ruwan tea din ya dawo ya bata jikinta gaba daya, dole suka sake komawa bandaki basira kuma ta gyara dakin inda ta bata.

Zip din rigarta rabi ta soma cire mata, kwata kwata batayi tu

nanin babu rigar nono a jikinta ba, sabeeha tayi saurin dafe kirjinta, wanda hakan yasa rabi janyo zanin da suke wanka dashi ta rufe mata kirjinta dashi sannan ta cire rigar.

Da haka dai ta samu ta dauraye jikinta daga karshe ma dai rabi cemata tayi tayi

kokari ta watsa ruwan zafi ko zataji dama dama.

Hakan kuwa akayi tana fitowa ta tadda rabi zaune basira ma haka duk sun damu da ita sosai, rabi ta bata magani tasha a hakan sannan tasa riga rabi tace ta kwanta kawai.

Tun bayan futarsu samun kanta kawai t

ayi da yin hawaye,this is the second time wani ya damu da lalurarta ko rashin lafiyarta, mutun na farko shine taj ne, shima lokacin da baya cikin hayyacinsa, idan tana rashin lafiya shima aranar sai yayi rashin lafiyar nan haka zaita kuka.

Sai yanxu kuma

da rabi da basira suka tsaya akanta, duk sun damu sosai itada ba wani dade tayi dasu ba.

Abu mafi zafi shine batasan yanda uwa ke nuna damuwa akan diyarta ba, wai irin hadiza ta shiga damuwa intaga tana rashin lafiya kwata kwata babu wannan, ko sannu bata

hadata da hadiza wani lokacin ma ko magani, saidai tayi cutarta ta gama, innace ma dai ke bata magani ada kafin ta rasu, ko kawu da har yau tun bayan dawowarta batasan a wace duniyar yake ba, tun tasowarta harta saba hadiza bata taba damuwa da rashin lafi

yarta

Bayan futarsu kafin barci ya dauketa sun leko dakin yafi sau nawa, Hadiza kam ko lekowa batayi ba, inama take da wannan lokacin, yanxu damuwarta daya ce yanda zatayi ta samu wani abu daga wajen yan gidan, don in sukaji zata aurar da yarta dole zasu

bata kudi sosai,a matsayin gudunmawa badan ta kwallafa rai ba da tuni ta dauketa musamman yanxu da anne bata gidan tana asibiti ta tafi da ita chan ta aurar da ita.

Daman plan dinta bai wuce ta dauketa su tafi gidan jamila ba anan dutsen habuja saita kira

qanin ubanta yazo ayi abun a gama kawai ta huta, don a yanxu babu ahunda ta kudircema kamar ta dauketa daga gabanta kafin a samu matsala.

Misalin wajen karfe goma sha daya kuwa ta gama shirin ta tsaf cikin atamfa da mayafi ta fesa turare da maya ta bata

saboda akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login