Showing 276001 words to 279000 words out of 338813 words

Chapter 93 - MATAR TAJ COMPLETE

karaya,

yau akwai babban tashin hankali a cikin gidan innalillahi wa inna ilaihi rajiun.

''anne? kodai jikinta ne? mu koma asibiti'' sameer yayi magana cikin tashin hankali, ko sauraron abunda yake fada batayi ba tace

“rabi dagata ku shigo ciki''

tana fadi

n haka ta dubi sameer, ''ku shigo min dasu suma” tana gama fadin haka hamad ya tura wheel dinta zuwa ciki, rabi tayi gaggawar taimakawa sabeeha ta tashi tsaye, gaba daya ta galabaita, ba karamin duka bahijja ta mata ba da wannan wire, tuni hankalin maya ya

tashi ganin ana kokarin komawa da sabeeha cikin gida, sai a yanxu ta fara fuskantar abunda ke faruwa, daxu dai bawai ta maida hankali bane kan magnganun da akeyi.



hadiza na tirjewa haka jamila ta kankame hannunta guards dinan suka tasa su a gaba, hadi

za babu damar guduwa, tayi tsuru tsuru, bata taba tsammanin asirinta zai tonu cikin sauqi haka ba, tayi dana sanin sanin haduwarta da jamila, zagi kuwa babu irin wanda batayi ma jamila ba, gaba daya ta susuce, bata sanin me take fada ita kanta.

Bahijja

dai bata san yanda akayi ta shugo parlorn ba don ta shiga wani yanayi mai tafe da furgici da tashin hankali da fargaba, bin kowa kawai take da idanu gabanta na faduwa, har idanunta ya sauka kan sabeeha da tun shugowarsu ta sulale kasa sai faman kuka take k

asa kasa tana shesheqa.

duk sun zazzauna kan kujera kamar waenda aka kawowa saqon mutuwa, duk sun zubama anne idanu, nanna na gefenta ta dafe kirjinta saboda yanda yake mata nauyi. daddyn maya ko gaba daya idanunshi sunyi jaa sosai.

ga su jamila da had

iza a zaune, har zuwa lokacin jamila fa bata saki hannun hadiza ba da har lokacin zage zage take, gaba daya ta zama kamar burkitattciya,sameer ya doka mata tsawa wanda hakan yasa ta yi shuru.

Daidai nan taj ya shugo gidan da sallama, da kyar sameer ya i

ya amsa mashi, ganin yanayin kowa yasa shi tambayar ko lafiya?

nanna ce kawai ta iya cewa ya samu waje ya zauna.

Ganin anne ma ta kasa cewa komai yasa nanna cewa ''yaya…ki mana bayanin abunda ke faruwa?''

Dakyar anne ta samu ta danne zafi da dacin da

takeji aranta ta kalli rabi, wanda hakan yasa rabi ta soma magana kamar haka, ''jiya misalin wajen karfe sha biyu aka kirani daga security post kan cewa wata bakuwa tazo tana nema, ina futa sai naga wannan''

tayi nuni da jamila, ''kawar hadiza ce, don t

a taba zuwa sau daya gidan nan, saina tambayeta dalilin nemana da take sai tace wai tanason na kaita wajen anne, ni kuma nace indai bata bani kwakwaran dalili ba babu abunda zaisa na kaita, nan ne take shaida min rayuwar yar hadiza wato sabeeha na cikin ha

dari, kuma ba kowa ne ke kokarin sata cikin hadari ba sai hadizar, wadda ta kasance ba mahaifiyarta ta asali ba a cewar jamilar, jin wannan yasa na amince muka dauki drop zuwa ga asibiti wajen hajiya, muna zuwa na kaita har wajen hajiya''

tana fadin haka

ta dakata, fadila ta dubi jamila sai a lokacin ta tuna da, ta ganta asibiti kuwa tabbas lokacin ta futo daga dakin anne ita kuma a lokacin taje ganin doctor kan prescription din anne…

A day before (Abunda ya faru a jiya).

rabi da jamila na isowa asibi

ti da sallama rabi ta bude kofar bedroom din anne jamila na biye da ita, lokacin kuwa anne ce kawai a dakin, cikin sauri rabi ta karaso cikin ladabi ta gaishe da anne, jamila ko tana daga tsaye, saida rabin ta gama gaisheta kafin ta gaishe da annen itama c

ikin mutunci baza kace tazo da wani abu aranta ba.

jamila bata bama rabi damar yima anne bayanin ko ita wace ba da dalilin zuwanta kai tsaye ta fada mata yanda take da hadiza sannan tace mata tazo ne wajenta da magana mai nauyi kuma mahimmiya wadda ta sha

fi ahalinta, anne najin haka da mamaki ta buqaci rabi ta futa ta basu waje, rabi na futa jamila ta dubi anne sannan tace.

''ba komai ne ya kawo ni ba sai dan na fada maki wani sirrin da ba kowa ya sani ba dagani sai hadiza.''

Jamila ta danyi shuru kafin

ta cigaba, ''dalilin dayasa nace ya shafi ahalinki kuwa shine, fatima wato yar hadiza ba yarta bace ta asali yar bahijja ce''

confusely anne ta kalleta, jamila na ganin haka tace ''nasan bazaki manta da ranar da hadiza da bahijja suka haihu ba, tabbas a w

annan ranar muka sauya yaran ba tare da sanin kowa ba… idan baki yarda ba zaki iya yin bincike akai saiki nemeni don ni banida da asara''

jamila na kaiwa nan ta tashi sannan ta mata sallama ta futa, ko tsayawa taji me anne zatace batayi ba, zabi ne tabart

a dashi kota yarda ko kar ta yarda.

fadin irin tashin hankalin da anne ta shiga bata lokaci ne,sai kawai ta tuna ranar da aka haifesu.

jamila na futowa ko jiran rabi batayi ba ta kama hanyarta, rabi ta koma dakin anne ta mata sallam lokacin fadila ta daw

o daga wajen doc so batasan meya faru ba, rabi na komawa gida anne ta kirata a waya, tana dagawa ta umarceta data nemo mata gashin sabeeha ko kuma brush na wanke baki, rabi batayi qestioning dinta ba tayi abunda tace, tana daukan brush din sabeehar ta taho

asibitin,yanda anne ta umarceta kan cewa karta bari kowa ya sani hakan tayi kuwa.

bayan barin asibiti da rabi tayi a daidai lokacin ne kuma bahijja ta iso, saboda kiran gaggawa da anne tayi mata, itama dai tana zuwa anne tasa doctor ya deba jininta, bahi

jja was so confuse bama ita kadai ba hatta fadila, saidai ganin yanayin annen yasa basuyi questioning dinta ba.

A ranar anne tasa ayi maternity DNA test, test din dake daukan kwana biyu kafin result ya futo a ranar anne tasa ayi cikin gaggawa, misalin waj

en karfe sha biyun dare kuwa dr barau yayi mata presenting result, gabanta na faduwa ta bude result din, tabbas sabeeha yar bahijja ce ta asali, a daren dai anne kasa barci tayi tana hawaye, tashin hankalin data shiga yasa jininta hawa sosai, dakyar aka sa

mu yayi regulating, washe gari kuwa tayi insisting dole a sallameta daman a ranar ya kamata a sallamota.

''hadiza ta cucesu ta cucesu cutar da har abada batajin bahijja zata iya yafema kanta, tana rike da yarda ba tata ba while tata na rayuwar wulaqanci,

don ba tun yanxu anne ta lura da yanda hadiza ke treating yarinyar ba, ta rabata da iyayenta tun daga haihuwarta innalillahi wa inna ialihi rajiun, hadiza ta cucesu ta cucesu, gaba daya ahalin gidan, har zuwa lokacin anne ta kasa gane wani dalili ne zaisa

hadiza ta chanza yar bahijja da tata,''

cigaban labari….

anne na hawaye ta soma magana ''tabbas fatima yar bahijja ce wadda suka sauya ta da maya lokacin da aka haifesu''

take kowa ya zaro ido in so much shock, tuni maya ta nemi natsuwarta ta rasa,

tama kasa gane inda gabar maganr take, wannan wani irin magan banza sukeyi? ta tambayi kanta.

hamad ko da sameer babu abunda suke sai kallon anne baki a bude, jamila ko babu abunda take sai murmushi.

Hankali a tashe fadila ta soma magana ''ya zaayi ta

zama yar bahijja anne?'' bata kaiga karasawa ba ta dakata tunawa da ranar da aka haifi maya, tabbas in bata manta ba tare suka kai bahijja da hadiza asibiti, don ranar a tare suka fara naquda.

Jikin bahijja na tsuma ta miqe tsaye, ta tunkari inda ann

e ke zaune ga envelop a hannunta, tayi saurin karba jikinta na rawa, tundaga lokacin da anne ta soma magana ta shiga tashin hankalinda gaba daya ji take dama nunfashinta yabar jikinta.

idanunta na cike da kwalla hannunta na rawa ta bude papers din, bata g

ama bude takardar ba duka idanunta ya sauka kan sunanta, ''DNA maternity test result, Name; Hajiya bahijja santuraki, and ''Fatima,''

tana kai idanunta kasan paper din inda aka rubuta result taga an rubuta probability of maternity test 99.9%''

tana ganin

haka ta soma jin wani juyayi kunenta ya toshe gaba daya kanta yayi dummm, a take paper ta sulale, majeed dake zaune gefenta yayi saurin mikewa ya dauki papers din ya bude shima yana karanta bai kaiga dagowa ba sai jin bahijja yayi ta soma cewa ''innalilla

hi wa inna ilihi rajiun….innalillahi wa inna ilaihi rajiun, na shiga uku, innalillahi wa inna iliahi rajiun, majeed yatace da gaske, yatace…what have i done???? tana fadin haka ta sulale kasa.

shima dai takardar faduwa tayi daga hannunshi, gaba daya hannu

nshi sai faman karkarwa yake yana kallon sabeeha, tabbas tundaga ranar daya sanyata a idanunsa yaji wani abu game da ita.

Tuni nanna ta runtse idanunta sai hawaye, hadiza ko dora hannu kawai tayi aka tana kukan munafurci.

Tuni hankalin maya ya tashi ta

na daga zaune tana kallon mummynta dake hawaye tana kuka, me mummy ke magana akai?, wacece yar hadiza? wai meke faruwa ne?'' haka ta dunga tambayar kanta.

fadila da taga yanayin da suka shiga itama miqewar tayi ta dauka takardar ta soma karantowa, tuni

hawaye ya soma sulalo mata ta miqawa sameer dake gefenta takardar, tayo kan hadiza a guje, ta soma bugunta kamar an aikota, nanna na hawaye ta soma kiran fadila, ''fadila fadila '' amma ina bataji bataji bata gani,

taj da tun shugowarshi idanunshi ya k

aiga sabeeha ganin yanayin daya ganta yasa ya kasa natsuwa, controlling kanshi kawai yake saboda ita, saboda bayanson ya nuna akwai wani abu tsakaninsu badan haka ba, bayajin zai iya zama yana ganinta tana hawaye gashi baisan dalili ba, gashi babu wanda ya

bashi damar sanin abunda ke faruwa sai binsu kawai yake da ido.

karban takardar dake hannun sameer yayi shima ya soma karantawa, yana gama karantawa ya dago da kanshi ya kalli sabeeha, sannan ya maida dubanshi ga bahijja in so much shock, gaba daya yafi

shiga confusion don baisan meke faruwa ba.

''me muka maki?me muka maki?, duk abunda muka maki ta hanyar nan zaki saka mana?'' fadila ta fada tana ihu tana dukan hadiza.

hadiza fa saida ta rasa natsuwarta saboda irin dukan da fadila ke mata jamila na

daga gefe sai faman taunar gums dinta take hankali kwance, kwata kwata bata ma tunanin ko zasu sa a kamata ita da hadizar kai ko an kamata wallahi tasha don burinta ya cika,

''ya isa fadilaaa ya isa'' nanna tayi magana dakyar tana kukan tausayin bahijj

a da sabeeha data fashe da sabon kuka dukda tana cikin rudu da tashin hankali magnagnunsu na zuwa kunenta, kuma ta kasa yarda da hakan.

''ki barni nanna, ki barni na kashe tsinanniyar nan, kin cucemu kin cucemu,yau shekaru ashirin da biyu kenan, muna ba

rci cikin kwanciyar hankali ba tare da sanin yarmu na chan wata duniyar ba? a wulaqance?, ke kuma taki tana nan cikin jin dadin rayuwa? ba a rageta da komai ba? wannan wani irin baqin zalinci ne, wallahi bazaki taba samun rahamar allah ba hadiza wallahi sa

ikin gwammaci baki taba sanin ahalinnan ba''

anne dai na daga zaune ta kasa cewa komai sai hawayen da takeyi,tanajin guilt din komai, tabbas a lokacin da aka sauyasu allah ya nuna mata ta wata sigarda dan abu kadan zatayi da zaiyi preventing sauyasun da

sukayi, saidai kuma saboda yanda bason auran majeed din da bahijjan take ba yasa kwata kwata bata maida hankali ba musamman akan abunda ya shafesu, ko haihuwar ma bawai nuna jin dadinta tayi ba lokacin da bahijjar ta haihu, amma tabbas a lokacin da aka sa

uyasu allah ya nuna mata amma taqi yin komai akai, she choose to turn a blind eye on it.

fadila na tsaka da jibgarta suka soma jin jiniyar motocin DSS,

Jikin maya na rawa ta miqe hankali a tashe sai yanxu kwakwalwarta ta fayyace mata komai, suna nufin

an sauyata da sabeeha? sabeeha ce yar asalin daddy da mummy ita kuma itace yar mai aikin nan hadiza?'' bakinta na karkarwa ta dubi hadizar sannan ta dubi sabeehar ta dubi daddy da mummy, ta fashe da kuka tana juya kanta, ina bazai yuwu ba bazai yuwu ba,

bazai taba yuwuwa ba ta kasance yar mai aiki,

bakinta ra rawa ta soma magana ''wallahi karya ne, ni ce yar mummy, ni ba yar mai aiki bace, karya ne wallahi, ni kadai ce yar mummy naa'' tuni ta furgice hawaye na sauka kan fuskarta harda majina, duk suka

bita da ido, bahijja ko kasa kallon kowa tayi musamman sabeeha, ya zata kalli yarta? da wani irin ido zata kalli yarta ta asali?, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, da kanta ta so illata yarta,da kanta ta nuna tsana mafi muni gareta, ?? take ta tuna yanda

ta dunga treating sabeeha tunda ta fara ganinta, da yanda ta dunga dukanta dazu, inama ace zata iya maida hannun agogo baya?, inama ace zata bude idanunta taga mafarki takeyi, Ya allah, this is so unbearable to her, yarta tayi treating hka ba tare da sani

nta ba, maya kuma ba yarta bace?, ba asalin yarta bace yar hadiza ce, yarta ta asali takema kallon yar iska kuma barauniya? duk dan saboda zalincin hadiza???

Bahijja na kuka tana kankame da majeed tana hawaye shima sai girgiza kanshi kawai yake, idanuns

hi sunyi jaa sosai, hadiza ta cucesu ta cucesu, cutarda har abada bazasu taba mancewa ba, ta rabasu da yarsu, yarinyar da bataji ba bata gani ba, saboda wani dalili nata daban da basu san ko menene ba? shima kanshi kasa kallon sabeehar yayi, he raised yari

nyar da ba tashi ba all those years, tashi kuma tana chan uwa duniya.

Babu wanda ya lura da sumewar da maya tayi sai nanna'tayi saurin miqewa ta tunkari inda take a kwance ta tallabo kanta tausayin yarinyar ya cikata, dole zata shiga shock itama.

dak

yar hadiza ta kwace daga hannun fadila bakinta duk a faffashe ta miqe tsaye tana zare zaren ido ta fashe dariya ''kona mutu yanxu naci galaba akanki bahijja kodan saboda yarki dana juyawa rayuwa kuma na tabbatar rayuwarta ta wulaqanta tun haihuwarta,kin g

anta nan saida na tabbatar batasan wani abu waishi gata ba balle jin dadin rayuwa,kima godewa allah ban watsa ta duniya ba ta zama kwantacciyar karuwa mai lasisi koba komai na dandana maki zafin cin amanata da kikayi, ay wallahi duk abunda na maki baikai k

watankwacin abunda kikayi min ba, wallahi wallahi bahijja indai ina nunfashi bazan taba bari ki samu farin ciki ba ke bake kadai ba duka ahalin nan''

tana cikin magana batayi auni ba saiji tayi an kwasheta da mari, dagowan dazatayi sameer ya sake sauke ma

ta wani marin, a daidai lokacin kuma wasu samudawan DSS officers suka shugo, su kusan biyar rida rida dasu, baqaqe suna sanye da baqaqen kaya da bindigu abun tsoro.

daman musamman anne ta kira general director dinsu tun kafin su dawo gida, ta shiada mas

hi crime din hadizar da jamilar, daman kwana tayi da tunanin wani hukunci ne ya dace dasu,don duk abunda zatasa ayi masu batajin zai wanke laifukan abunda hadiza tayi.

Anne na daga zaune tayi instructing a fita dasu, take hankalin jamila ya tashi don bata

yi tsammanin harda ita za a hada ba amma ta dake don koba komai dai ta tona asirin hadiza hankalinta ya kwanta.

kafin a futa dasu hadiza tace ''banyi asara ba kona mutu na aje maku tabon da har ku mutu bazaku manta dashi ba,''ta karaashe tana kallon gaba

dayansu ,yanda fa hadiza ke maganganu kwata kwata babu any remorse ko regret

jamila dataga da gaske harda ita za a hada a tafi, tuni yayanta suka zo ranta, tace

''hajiya hardani za a hada? nifa yar rakiyace? itace ta shirya kuma ta gudanar da komai''

hadiza ta dubeta da fashesehn lebe tace ''au bakisan da haka ba sai yanxu? ay tunda kika tonan asiri nima saina tona naki wallahi, sai duniya tasan da hannunki kika kashe tsohon mijinki tsinanniya''

''akwai tsinanniya data wuce ke? shi uban wacchar yariny

ar da kike ikirarin kunyi aure kema ay kasheshi kikayi, au nama tuna ashefa bata da uba ko yar taki?'' jamila ta bata amsa, filin saiya zama kamar na bankade bankade.

suna kallo aka fita da ita da hadiza, yanda ma dss dinnan ke jansu kamar dabbobi.

MATAR TAJ (destined with you)

   Written by 

          Queenmarh

Book2 

PAID

Chapter 108

TAKAITACCEN LABARI

SHEKARUN BAYA DA SUKA WUCE

Gidan Alhaji santuraki, gida ne mai jama'a ta kowanne fanni tun shi kanshi alhaji santurakin na raye, ha

rya rasu ya samu shaidar taimako musamman ga waenda basuda karfi, hajiya anne ta kasance mace jajirtacciya kuma tsayayyiya mai zafin nema kamar yanda taga mahaifinta nayi, sannan ta bangaren taimako kuwa harma ta wuce mahaifinta wajen kyautatawa mutane mus

amman marasa karfi harma da waenda ke karkashinta, musamman ma'aiktanta, hadiza da inna wato mahaifiyar hadiza sun kasance ma'aikatan cikin gida tun mijin anne na raye, lokacin hadiza na budurwa inna tazo da ita gidan,anyi zama na amana da mutuntawa shekar

a da shekaru daya sanya anne daukar nauyin hadiza tayi sponsoring iliminta na boko, babu abunda ta nema ta rasa kama daga sutura mai kyau da cima mai kyau, da abubuwan da baza a rasa ba daya danganci buqatun budurwa, cikin yayan anne bahijja ce kawai tazo

sa'a daya da hadiza kuma suka shaku sosai, don bahijja tana da hakuri da son mutane, abun duniya bai rufe mata ido ba kuma kwata kwata bata taba considering hadiza yar mai aikinsu ba, wannan yasa hadiza da bahijja suka taso a tare don fadila ta girmesu, it

a harta gama karatu, idan kaga hadiza bazaka taba cewa ba yar gidan bace yar mai aiki


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login