Showing 63001 words to 66000 words out of 338813 words

Chapter 22 - MATAR TAJ COMPLETE

sama sama, wani sa’in ma har workout sukeyi a ta

re,

Bai taba nuna mashi tun asali daman ya sanshi ba sannan bai fada mashi alakarshi da khaal ba saboda ya rigada yasan ko wanene taj din, baya yarda da mutane cikin sauqi, at the same time baibar tailing hidaya ba, yanxu neman hanya yake yanda zai samu

ya gano me takeyi a chan island din, haryau maganar gawar nan da aka musanta akace ta khaal ce bata bar tsaya mashi arai ba, kuma yana ji a jikinshi akwai wata a kasa, kuma yayi alkawarin sai yayi uncovering komai.

9pm…

Wasu daga cikin Kayan da

ammu ta kawo mata na barci ta dago taba kalla daya bayan daya, duk cikin kayan babu wani na arziki sai wata doguwar riga wadda zata iya kai mata har gwaiwa, rigar ta saka a jikinta sannan ta dan goga turaren da ammu ta bata kafin ta fito, a zaune ta tadd

ashi chan saqon gado ya daura laptop kan cinyarshi yana sanye da pjs shima farare ya sauke kafarshi daya kasa.

Takowa tayi kamar wata munafuka ta zauna bakin gado, tana zama yaji kamshin nan ya bugi hancinsa, dakatawa ya danyi da aiki ya juyo ya kalleta,

yaune rana ta farko daya taba ganinta da kayan barci, duk sanda zata kwanta bata saka kayan barci ashe yana lura da duk wani movement dinta amma yake kauda ido, ganin tana neman juyowa yasa shi kauda kai, ita kuwa ganin tun dazu yake abu daya akan system t

a miqe ta fuce daga dakin, kitchen ta nufa ta yanka variety of different fruits types, tana yankawa ta wawwake ta saka a wani clear bowl sannan ta futo bayan ta kashe komai na daki,

Sallama tayi a natse kafin ta rufo kofar dakin ta tako zuwa bakin gadon

, slippers din kafarta ta cire sannan ta hau kan gado gaba daya ta zauna ta daura bowl din a kan cinyarta ta fara cin fruit din, ta gefwn idanu take kallonshi ganin hankalinshi yayi nisa wajen aiki, haka kawai wani abu ya dunga raya maga arai, tana ta cont

emplating tayi ko kartayi, dakyar dai ta samu courage din daukan slice din apple guda daya ta miqar da hannunta wajen bakinsa kamar wadda ke tsoro, chak ya tsaya ganin hannunta saitin fuskarsa, bai juyo ya kalleta ba haka zalika bai cigaba da typing dinba,



Ahankali ta bude bakinta kamar mai rada tace “di..di….ahhhh, apple ne your favorite”

Tana fadin haka tayi shuru tana jiran abunda zaiyi, tama san rejecting zaiyi har hannunta ya fara sagewa tana kokarin dauke hannun nata daga kan fuskarshi kawai ya bud

e bakinsa, yana bude ta sauke murmushi ta saka mashi apple din a bakinsa.

Ahankali ya soma tauna tundaga bakinshi har zuwa maqogaronshi tabi da kallo, har saida ya cinye, ta sake daukan wani takai daidai saitin bakinsa, ya sake bude baki ta saka mashi, ya

cigaba da danne dannen dake gabanshi, ta bangarenshi baima san lokacin daya bude mata bakin nasa ba.

Karshe dai itace tayi feeding dinshi apple dinnan tass, saida ya cinye na bowl din ta kalleshi fuskanta dauke da annashuwa tace “a karo wani?”

“No thank

s”

Yana fadin haka ya kashe laptop din ya miqe ya ajiyeta inda yake ajiyewa kafin ya shiga bandaki, ita kuma ta wuce kitchen ta wanke bowl din sannan ta ajiye ta dawo dakin, har zuwa lokacin bai futo ba don haka tayi kwnaciyarta kawai.

Yana futowa daga

bathroom ya kashe hasken dakin ya nufi chan dayan bangaren gadon ya kwanta abunshi, sabeeha data tabbatar gadon ya nufo kuma anan ya kwanta tayi mamaki sosai , sharing gado zasuyi a tare? Ko ya manta tana kwance akan gado? Tambayar data dunga ma kanta ken

an, ita kanta abun yayi mata banbarakwai, harzata tashi ta bashi gadon ta tuna da maganar ammu don haka tayi kwanciyarta kawai.

Tana cikin wannan tunanin batama san lokacin da barci ya kwasheta ba.

Bangaren taj din sharp ya manta gaba daya yau, don a gaj

iya yake, kwana biyu kwanan da yakeyi a sitting room ya fara sa mashi ciwon jiki, he’s not comfortable kwata kwata, don bai iya kwana a couch ba, yawanci ma ba kwanciyar yake ba saidai ya zauna yayi relaxing jikinshi a haka har barci ya daukeshi, kwata kwa

ta bai iya kwanciyar couch dinba amma haka yake hakura ya futo sitting room din.

Lokacin sallah nayi kamar kullum ya bude idanunshi tarr, lumshesu yayi ya sake budewa kafin ya yunkura ya tashi zaune yana mai dafe kanshi ya saka slipper ya wuce ya miqe,

juyuwan da zaiyi ya ganta kwance ta juya mashi baya, kauda kanshi yayi ya nufi toilet ya dauro alwala sannan ya futo.

Har zuwa lokacin barcinta take hankali kwance, har yayi sallah ya idar, daidai lokacin itama ta farka bakinta dauke da ambaton allah, har

da yar miqarta duk yana kallonta ta shga bathroom, …



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR TAJ (destined with you

🩵🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 70

Bayan wasu yan kwanaki…

Abubuwa da dama sun sauya,musamma ts

akaninta dashi, ya dan fara sakin jikin shi da ita, ba dan komai yayi hakan ba sai dan cikinshi dake jikinta, saidai har yanxu idan ya tuna ta yanda aka samu cikin ranshi na baci sosai, dan dole yake danne abunda ke ranshi don idan yace baya son cikin yayi

karya, bayan wannan ma ya maida hankalinshi wajen karantarta sosai, don sanin kudirinta da abunda ke ranta, abu daya daya lura da ita shine shes so soft and calm, dukda wani dogon magana baya shiga tsakaninsu haka baisa ya lura da yanda take da respect ba

wannan yasa yake dan jinta aranshi.

Monday morning Fit gym…

5pm

Gudu yake sosai kan treadmill, yana sanye da riga da gajeran wando wanda suka amshesa sosai,ya dade sosai a tsaye kunneshi a toshe da pods, saida ya dauka wajen minti talatin yana abu da

ya kafin ya kashe ya danyi relaxing tare da panting kadan kadan ga zufa na sauka akan fuskanshi,juyowan da zaiyi ya sauko daga treadmill din yayi daidai da isowar mutallib wajen fuskanshi wasai, taj ma na ganinshi ya dan murmusa abunda bai saba yima mutane

ba kwata kwata, hannu mutallib ya miqa mashi sukayi musaba, “gym buddy finally na ganka yau,kullum idan nazo da safe bana ganinka”

Kai tsaye ya amsashi, “na chanza schedule ne”

Yana fadin haka suka nufi wajen karafunan wajen,taj na gaba shima mutabblb

na biye dashi, weight bench taj ya hau ya kwanta yayin da mutabblib din ya zagayo ta wajen fuskanshi dago mashi weight ya soma dagawa,yana dagawa mutabblib na taimaka mashi, saida yayi press wajen sau biyar kafin ya dan dakata mutallib ya taimaka mashi.

“This is the perfect time, shiyasa na sauya, wajen nan ya fara zama so croudy”

Da mamaki mutabblb ke kallonshi don baiyi tsammanin zai kulashi ba bayan maganar daya mashi da farko,ba karamin dadi yake ji ba ganin kusanci na shiga tsakanin su ahankali ah

ankali.

“Thats true, yafi dadi ay idan babu hayaniya, mutun saiya samu sakewa sosai, dukda na lura saboda kai wajen ke cika yanxu” mutabblib ya karashe yana kashe mashi idanu daya harda yar dariyarshi.

“Saboda ni kuma?” Taj ya jefo mashi tambaya.

“Yea

sir, saboda kai, bakaga mata sunfi yawa ba, compare to lokacin daka fara zuwa”

Tabe baki taj yayi kafin ya miqe daga wajen, “zaka wuce ne yanxu?”

Uhm.. ya fada yana girgza mashi kai, “kaifa?”

Taj ya jefo mashi tambaya? “Eh”

Kusan a tare suka fito da k

ayayyakin gym a jikinsu, mutallib nason tambayarshi abu saidai ya rasa ta inda zai soma da kyar dai ya dake yace “why don’t we grab something light..akwai wani mini halal bar anan kasa”

Shuru taj din yayi kamar bazai yarda ba chan kuma ya amsa da “okay”

Murmusawa mutabblib yayi kafin

Kowa ya shige motarshi, suka fuce daga wajen, duban mirror taj ya soma yi yana mamakin rashin ganin motar dake yawan bibiyarshi yau kusan sati kenan kenan.

Gaban wani mini bar mutabnlib yayi parking daman taj din na biye

dashi shima ya cinno bakar lambor dinshi yayi parking kafin ya kwashe wayoyinshi ya fito.

Kusan a tare suka shiga cikin bar din suka samu waje suka zauna.

Mutallbi ne ya masu ordern beverages, tunda ya soma latsa wayarshi bai dago ba, ban taba zama irin

haka ma da mutumin daya hadu cikin abunda bai wuce wata biyu ba,kwata kwata bashi opennesss shiyasa yake komai shi kadai but this time around yanajin sakewa around wannan guy din, wannan yasa ya dan sake ko zai samu avubuwan dake ranshi su fitar mashi.

Y

anxu focus dinshi gaba daya akan yarinyar nan ne, hankalinshi gaba daya ya koma gareta, a zahiri kamar ba hakan take ba saidai a chan cikin

zuciyarshi baya sakkani bata fadi mashi arai ba musamma yanxu da cikinshi ke jikinta,kauda ido kawai yake amma deep

down yana tsananin kaunar abunda ke jikinta, cikin lokaci qanqani abun ya shigeshi ba tare da ya sani ba, tun bayan rashin lfiyan nan datayi har yayi tunanin ko cikin ne ya zube ya taorata sosai wannan yasa yake dan sassauta mata sosai, kuma ya kudirci kul

a da abunda ya shafi cikin jikin nata harma da lafiyarta, ko barci yake haka zai farka ya duba ta, don ya tabbatar tana lafiya kafin ya koma.

Kwata kwata baisan a wani mizani zai sakata ba, ma’ana yanda yakeji game da ita.

Gyaran murya mutallib yayi yana

mai fuskantar taj din daya maida hankalinshi ga wayar dake hannunshi “bismillah!”

Ajiye wayar taj yayi ya dauka moctail din yakai bakinshin kafin ya ajiye.

Hira sukayi sosai, tun taj din na baya baya dashi harya sake sosai suka dunga hira kamar abokanan

da suka san juna shekara da shekaru da yake mutabblib din is very easy going person saiya zamana ya shiga ranshi sosai,har sukayi planning fita tare don ya nuna mashi gari sosai.

Wajen karfe tara ya shigo gidan, tun daga bakin kofa ya soma jin hayaniya

r mutanen gidan, su afiya ne zaune a kujerun sitting room sai wasu kawayenta su wajen uku harda sonata anata hira, tun yamma suke abu daya babu wadda tayi tunanin tashi tayi sallah, sai hira, duk sunci hadaddun abayas kana ganinsu kasan suma yayan masu shi

ne.

Duk basu lura da shugowarshi ba don hankalinsu naga sonata data miqe ta nufi bakin stairs daidai nan sabeeha ta fito daga bangaren ammu ta nufi wajen stairs din, kodata hango sonata saida gabanta ya dan fadi don tunda ta sauko suke binta sa kallo gab

a dayansu.

Tundaga bakin kofar ya hangosu,both sonata da sabeehar, sabeeha na sanye da doguwar riga blue sai mayafin rigar data rufe kanta dashi,kallo daya ya masu ya kasa dauke idanunshi akansu.

Chan bangarensu sabeeha kota kanta batabi ba batama ts

aya sauraron maganganun datake jifanta dashi ba don kallon mahaukaciya take mata yanxu ta nufi sama harta daga kafarta daya zata hau saman batasan me ya faru ba sai kawai jinta tayi, tayi baya suuu kamar wandda aka turo baya, harta runtse idanunta jiran fa

duwa kawai take a kasa taji akasin haka, shi kanshi baisan lokacin daya zo wajen ba don gaba daya hankalinshi lokaci guda ya tashi tunda ya hangosu daga nesa kuka ya tabbatar da abunda idanunshi suka hango masa, ranshi ba karamin baci yayi ba, take idanuns

hi yayi jaa sosai tsabar bacin rai, sabeeha data luntsuma jikinshi kasa tashi tayi ta qanqameshi saboda ta tsorata and ko ba a fada mata ba tasan kamshinsa ne wannan.

Sonata na ganinshi jiki ya soma tsuma, ba karamin mamakin ganinsa tayi ba a daidai wanna

n lokacin,fatanta daya allah yasa yanxu ya shugo kuma baiga abunda ya faru ba, abunda bata sani ba kuwa shine sarai yaga komai.

Bakinta na kyarma ta washe hakoranta ta soma magana “babe ka dawo”

Jajayen idanunshi da sukayi jaaa sosai kamar an zuba garwas

hi ya zuba mata, babu abunda ke kwance a fuskanshi sai tsantsar bacin rai, ganin yanayinshi haka yasa gabanta yayi mugun faduwa.

Ahankali ya zarota daga jikinshi, ya kama damtsen hannunta ya mata nuni da sama,mutanen dake zaune a parlor babu abunda suke s

ai kura masu idanu kamar sunga tv, kowa da abunsa yake ayyanawa aranshi, waenda basu taba ganin shi ba kuwa baki bude tsavar zalama.

Sadaf sadaf sabeeha ta wuce sama ba tare da ta sake kallon inda sonata ke tsaye ba ta wuce sama abunta, shiko tana wucewa

bai sake kallon inda sonata ke tsaye ba ya mara mata baya shima.

Cije yatsa sonata tayi don ba haka taso outcome dinba, taso sabeehar ta fadi a kasa ko cikin ya bare kowa ya huta, sai kuma aka samu akasin haka, yanda taga bacin rai kwance a fuskanshi ya t

abbatar mata akwai matsala.

Muryar kawayen afiya ne ya dawo da ita daga tunanin data fada, “babe waye wannan sharp guy din? Woww.. kai amma ya hadu waiii”

Banza afiya tayi dasu don ranta ba karamin baci yake ba da zarar an fara maganarshi, ko idan akayi

noticing dinshi, ita bataga abun tada jijiyoyin wuya ba akan wannan guy din ba.

“Thats my fiancee” sonata ta katse su, dake kawayen afiyar suma yan ayi ne sai suka fashe da dariya, suka juya harshe.

Achan saman kuwa yana hawa saman ya tadda dakin fess fe

ss yanda yake, saidai bai ganta a ciki ba wannan yasa ya soma rage kayan jikinshi, bathroom ya shige dirwct ya watso ruwa mai dumi sosai a jikinshi kafin ya fito daure da towel, samun kanshi yayi da zama bakin gado bai dade da zama ba sai gata ta shugo dak

in.

Hannunta rike da tray ta hado mashi coffe da fruit data yanka mashi daman tun dazu take jira ya dawo, data gaji da zaman shine ta sauko kasa wajen ammu suka gaisa.

Dunta da hangoshi daga bakin kofa ta sauke idanunta, he’s barely half naked dagashi sa

i towel a kugunshi yana latsa waya.

Sallamarta ya amsa ciki ciki harta karaso bakin gadon ta ajiye a gefen bedside.

Tana kokarin barin wajen ya miqar da kafarshi don tabbatarda nazarin dayayi dazu, yanda take tafiya kamar bata kallon gabanta wannan yasa

tayi tipping hartayi gaba ta daidai tasuwarta.

“Are you blind? Bakida ido ne?”

Yanda yayi maganar ya tabbatar mata cikin bacin rai yayi wanann yasa ta suake muryarta kasa tace “i’m sorry ban lura bane”

“Let me warn you, daga yanxu duk inda zakije watch

your steps, kina tafiya kamar wadda bata ganin gabanta, what if kin fadi? What if wani abu ya faru dazu? Kinsan risk din faduwa with pregnancy? Are you blind ne?”

Haka ya soma jero mata tambayoyin, tama kasa gane inda ya dosa, sai kawai tayi shuru tana sa

uraronshi, chan bangarenshi saida ya saka kafarshi ya tabbatar da faduwar data kusa yi tadiyeta sonata tayi, yanxu badan yayi hanzari ba da tuni shikenan wani mumunnar abu ya faru itama da fault dinta, yanda take tafiya da wasu abubuwan cikin sanyi abun y

ana bata mashi rai, yar tsuqa yayi yabar wajen ya bufi closet, jiki a mace sabeeha ta zauna bakin gadon tayi shuru, koba a fada mata ta hango tsantsar fargaba akan fuskarshi lokacin daya tallabeta data kusa faduwa a kasan, ko ba a fada mata ba tasan saboda

cikin ne.

Ta dade zaune harya fito lokacin wajen karfe goma daidai ya nufi chan gefen gado inda yake kwanciya ya zauna kafin ya soma latsa wayarshi.

Sun dade a haka tana tunanin magnagnunshi harta fuskanshi inda ya dosa da dalilin bacin ranshi, kafin ta

yanke shwarar bashi hakuri.

Yan yatsun hannunta ta soma jujuyawa cikin sanyi ta soma magana “.. kayi hkuri, insha Allah zan kiyaye”

Tunda ta soma magana ya dakata da abunda yakeyi yana sauraron calm voice dinta, dake dare ne dakin yayi shuru, sai ya zam

a sautin nunfashin su ne kawai ke sauka kawai.

Daman tasan bazai amsa ta ba kuma ta tabbatar ya jita wannan yasa ta miqe ta wuce bathroom din ita tayi anka sannan ta sauya kaya zuwa marasa nauyi sosai kafij ta nado kanta ta shugo bedroom din.

Adaidai lok

acin ya rage haske dakin ya zama dim dim babu haske sosai, saina bedside, kallonshi tayi ganin zaune yanda ta barshi dazu saidai wannan karan ya danyi relaxing bayanshi a bakin gadon ya lumshe idanunshi,kauda idanunta tayi daga kanshi ta maida ga tray din

data kawo mashi fruit dazu da coffee ganin bai taba ba yasa taji babu dadi aranta,daukan tray din tayi ta juya ta nufi kitchen dashi, fitilin parlor ta dan rage kafin ta shiga kitchen din ta kunna lights din kitchen din.

Kallon tray din tayi babu abunda y

a taba har coffee dinma yayi sanyi, bowl din fruit din ta dauka zata saka a fridge daidai nan wutan gidan gaba daya yayi fluctuating, take gabanta ya bada wani irin damm don ko ina ya bade yayi duhu dumm ko yatsun hannunta bata hangowa.

“Innalillahi wa in

na ialaihi rajiun” ta furta ahankali, da zarar taga duhu gabanta ke faduwa sosai musamman irin wannan unexpectedly, tunawa da yanda taj ke tsoron duhu yasa gabanta faduwa,gaba daya tama manta yanxu fa ba taj din data sani a baya bane,

Cikin gaggawa ta ju

yo ko rufe fridge dinma bata ba ta fara dube dube cikin duhu, “didi didi..” ta soma furtawa ahankali, hartana bugewa da kitchen island, ba karamin bugu tayi ba amma kwata kwata bataji zafin ba ta cigaba da lalube, karaf taji an kamota, cikin furgici ta tas

hin hankali ta soma furta innalillahi a fili, allahumma ajirni fee museebati… bai bari ta karasa ba ya toshe mata bakinta da palm dinshi, dukda ciki. Duhu suke sosai hakan baisa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login