Showing 201001 words to 204000 words out of 338813 words
hadiza ba abar yarda bace ni kadai nasan koke wacece.
D
ahiru har zai wuce ya dakata ya kare masu kallo musamman jamila.
“Jamilan zango???”
Jamila najin sunanta da ake kiranta dashi lokacin da suna en mata ana shan duniya ta juyo da mamaki,”
Tana ganin dahiru gabanta ya bada dan daran dammm, dariya ya kyakya
ce dashi irin ta manya yace “jamilan zangoo, ashe rai kanga rai? Ah madallah”
“Kin sanshi ne?” Hadiza tayi magana tana kallonta ganin gaba daya bata cikin hayyacinta hankalinta ya tashi.
“Koba jamila bace wannan?”
Ya sake tambaya ganin tana kakkauda kai
, “ay ko barci nake na tashi dole in ganeki jamila ta”
Jin haka yasa jamila cije lebe ta juyo ta kalleshi tana yaqe tace “dahiru kenan, kana nan dai yanda kake an buga duniya an barta”
“Kwarai kuwa, yaushe gamo? Rabona dake shekara wajen ashirin da yan k
ai, har kinyi aure ko ay hikenan kin barni”
“Kaifa ka fiye hauka, an girma ba a san an girma ba mteww”
Kallon hadiza yayi har yana motse idanu kafin yace “wannan ba kawarki bace? Har yanxu kuna tare? Lallai amincinku mai karfi ne ba itace Wacce kika…”
“
Dahiru.. me kazo yi nan ne?”
Tayi saurin dakatar dashi hankali tashe, “yar dan uwana ce take aiki anan zan aurar da ita kinga mun kwana biyu ko?” Ya fada yana yage baki.
“Kwarai na gani kuwa”
“Ke yama sunan masu gidan?” Ya tambayi bilki tace “gidan alha
ji santuraki”
“Ku meya kawoku nan anguwar?”
“Bani lambarka zan kiraka anjima” jamila tayi cutting conversation din, ya zari wata yar nokia ya bata number.
Zasu wuce bilki tace “sai anjima hadiza na tafi”
“Toh bilki” ta amsa ta.
Suna barin wajen hadiza
ta dubi jamila tace
“? Ina kika san wannan jemamman kamar wani dan wiwi”
“hadiza mun shiga uku dahiru ne,”
“Wani dahirin?”
“Ke amma jakace, shekaru ashirin da uku da suka wuce….”
Ay bata karasa ba hadiza ta kama haba tace “ke da shi?….”
“Shine, ha
diza dahiru bashida kai wallahi, inata yi maki signal mubar wajen kika kasa ganewa, dan wiwi ne wallahi bashida kan gado, tunda har ya ganmu akwai matsala”
Haka suka tsaya kana ganinsu zakasan basuda gaskia kwata kwata.
Dahirun da bilki na barin wajen
ya dubeta yace “ina kikasan wadda naji kik kurata da hadiza”
“A gidan da nake ayki suke ita da yarta”
“Yarta?”
“Eh kawu”
“Tun yaushe suke gidan?”
“Zasu kai wata shida a gidan” ta bashi amsa
“Ta manyanta da batada aure dana jarraba sa’a ta”
Dariya b
ilki tayi sanin yanda kawun nata yanda yake da son mata ga auri saki inya auri hadiza ay bala’i zasuyi, matar nan datake jin kanta kamar masu gidan harma ta fisi kafafa.
“Ay kuwa dai kawu, gashi batada miji don kamar ya mutu,”
“Toh ko yar zan nema ne?
Tunda da kwari na zatayi kamarki?”
“Kawu na girmeta bazata wuce irin shekaru ashirin da uku ba haka”
Kyakyacewa yayi da dariya, sosai ba kadan ba “madallah..” ya fada yana tabo kudaden da anne ta basu daga aljihunsa.
Suna tafiya anne ta dubi rabi tace
, “toh yanxu gashi yan matan wuya samu suke,“
“Va danuwa hajiya, tunda ga sabeeha ga basira sai a raba masu aikin kafin sabeehar ta koma makaranta nasan za a samu wata”
“Toh hakan yayi, naga fatimar nada tsafta ta dunga zuwa bangaren deeni tana gyarawa s
afe da yamma, duk abunda ya danganci bangarensa”
“Toh hajiya” rabi ta amsa ta.
Rabi na rabuwa da anne ta kira basira da sabeeha ta shaida masu kowa da aikinta, basira kamar ta kwada ihu, tanata murnar aikin bilki zai dawo hannunta, gyaran part din nan
na da bangaren taj.
“Daga yau ke fatima zaki fara, bilki tayi na safe yamma nayi zakije ki gyara bangaren, shara mopping gyaran bandaki gyaran gado, komai, idan da lundry ma zaki dunga yi da goge.”
“Toh anty rabi”
“Dan allah banda kazanta, baya son kaza
nta ko kadan, yanayin rayuwarshi da tamu ba daya bace, kazanta kadan saita sashi amai abunka da ba dan nigeria ba”
Jinjina kai kawai sabeeha tayi, kwata kwata bata taba bada attention dinta gareshi ba sai yanxu, tadaiji ance dan anne kuma ba a kasar ya ta
so ba, amma bata taba sama ranta gani ko sanin wayeshi ba.
Jamila na tafiya hadiza ta koma gida gaba daya kamar ta burkice sabeeha na shigowa dakinsu ta taddata zaune
“Ke zo nan”
Karasowa sabeeha tayi cikin ladabi ta zauna kasa, “da kikace chan saudiy
yar meya dawo dake? Meysa aka koroki? Karki sake kimin karya? Kisan kai kikayi ko sata? Wanne daga ciki”
Idanun sabeeha ya ciciko da hawaye ta kalli maman nata tace “mama wallahi…”
“Karki fara min rantse rantse munafuka, kisa kikayi ko sata wanne daga ci
ki? Don shi kadai zaisa azo ana nemanki”
Mamaki gaba daya da confusion ya cika sabeeha, hadiza ta zaro wuya tace “ko ki fada min kona kasheki anan na huta,iskanci kikaje kikayi ko wani kika kashe?”
“Mama wallahi banyi ko daya ba,”
“Meysa ake neman ki???
? Ehhh????”
“Bansan wake nemana ba mama, wallahi ban sani ba”
“Wace iriyar rayuwa kikayi achan???”
Damm gabanta ya bada ta rasa ya zatayi, wace amsa zata bama mamanta? Ko karan hauka ke cinta bazata taba cewa aure tayi ba.
hadiza duk yanda taso ta ts
orata da wuqa bata samu komai ba kwakwara dazai nuna cewa kisa tayi.
Wunin ranar cikin zulumi da kunci sabeeha tayi shi, tasha kukanta ta gaji ta hakura sannan ta fara tunanin maganganun mamanta, wake nemanta? Wazai nemeta? Babu mai bata amsa.
Yamma na
yi wajen 4 ta shuga part din da zata dunga gyarawa, da sallama ta bude kofar kamshin diffusers ya bade ko’ina, bin ko’ina tayi da kallo wajen ya burgeta sosai ba kadan ba, har wani natsuwa takeji, haka ta fara gyaran parlor da babu datti kwata kwata ta sha
re dakin shima ta sauya bedings ta wanke bathroom kal kal kamar ba a taba shiga ba sannan ta futo ta rufo kofar.
Tana futawa ta samu dakali daga chan wajen compound din ta bama wajen baya tana tunani da nazari.
Tunda ta zauna babu tunanin wanda yake circ
ulating a ranta saina taj,duk iya kokari da take na ganin ta yakice shi ta kasa data fara ma take hana kanta ta hanyar tunawa da abunda ya mata yau ko ta kasa hana kanta.
Misalin wajen karfe shida da rabi ya shugo compund din wajen parking spot yayi par
king motarshi kafin ya nufi hanyar part dinshi, kamar ance ya juyo ya kalli wajen da take zaune kuwa ya juyo ya ganta tana kokarin miqewa, take gabanshi ya soma bugawa fat fat fat, ya kasa daga idanunshi allah allah yake kawai ta juyo yaga ko wacece a waje
n da zuciyarshi ta dakatar dashi babu dalili, tana miqewa kamar zata juyo kuma saita tsaya tare da daukan slippers dinta daya tainke ta dauka adaidai lokacin ya dawo hayyacinshi ya wuce cikin part dinshi ita kuma ta juyo.
Sallah ta shiga tayi taci abunci
sannan suka fara prepping shirin aje dinner.
Yana shiga part dinshi yabi ko’ina da kallo, duk guaran da ake mashi sai yaga na yau is times 10 of it, sai yaji dadi aranshi soaai, komai anyi organinzing to his taste.
A tare sukayi aikin kitchen ana gama
cin abunci suka tattara, harda sabeehar suka wanke ita da basira rabi kuma ta wuce don hidimar anne.
Wayar landline dake kitchen aka kira basira ta dauka kafin tace “gata”
“Tohm hajiya”
Kallon sabeeha tayi tace “hajiya nanna na kiranki, tace a yanka fru
it”
Murmushi sabeeha tayi tace toh, ta fidda komai ta yayyanka yanda ya kamata ta zuba zuma a bowl ta jera kan tray sannan ta wuce sama.
Babu hijab a jikinta tana sanye da doguwar riga kuma ta mata kyau sosai daidai jikinta, ta dan rame saboda damuwa sai
dai kuma dirin na nan yanda yake gata yar gajeruwa.
Da sallama ta bude kofar part din bayan an bata izini ta shiga, nanna na zaune sitting room ta dubeta tace “sannu yar albarka,”
“Nanna ina wuni?”
“Lafiya lau my dear, how are you? Ya exams dinku an gam
a ko? Ina fata anyi abun arziki”
Dariya tayi tace “eh nanna”
“Aje fruit din akan dining, tajudeen zaizo yasha yanxu”
Dammmm gabanta ya bada badan ta rike tray din da kyau ba zai iya subuce mata.
“Tajudeennnn” kai ina zata iya mantawa da wannan suna a r
ayuwar nan.
Aje wa tayi tace “akwai wani abun da ake buqata?” Babu yarinyar kirki, nagode, rabi tace kin karbi aikin bilki ko? Gyaran part din tajudeen ya dawo hannunki”
“Eh, dazu ma naje part din na gyara”
“Toh Masha allah,”
“Saida safe nanna”
“Toh a
llah ya kaimu”
Sabeeha ta futa, koda ta futo ta wuce sama.
Washe gari wajen karfe goma ta shiga part din nashi, already harya futa wannan ya bata damar kimtsa ko’ina, yanda ya kamata, kayan data gani a closet a ajiye a kasa kamar cikin gaggawa aka cire
su ba a tattare ba ta kwaso ta sakasu laudry, ta taaftace wajen sannan ta nufi hanyar futa, har zata futa ta dakata idanunta ya sauka kan wani wrist watch, komawa tayi tana kallon watch din da mamaki, runtse idanunta tayi tana tunanin maisa komai yake remi
nding dinta da taj, kauda tunanin tayi ta duta daga part din.
Bangaren taj ya da sassafe ya futa ya koma agency,tun ana neman jamilu har aka kasa daina nemansa, salim ya gane wala wala suke masu, wata dabara tazo kashi cikin yaran wajen ya samu daya ya sh
aqe shi da kudi sosai ya fada mashi inda jamilu yake ayko bai tsaya wasa ba ya nemo mashi address dun jamilu.
A ranar suka dauki hanyar wajen gari habuja sai dutsen habuja, suna zuwa basusha wahala ba sukayi lokacin gidan jamilu, taj yayi mamaki sosai gan
in anguwar, zuciyarshi kawia saita fara breaking sosai.
Akayi sallama da jamilu, jamila ta fito don jin ko waye, tana ganin jibgegeiyar kota gabanta ya soma faduwa, salim ya futo taj ma haka, ay sumewa ne kawai jamila batayi ba gar zata kulle gidanta sali
l ya mata sallama yace “dan allah hajiya ki dan saurare mu, muna neman jamilu ne”
“Mei sa kuke neman mijina me zai maku? Kamashi zakuyi?”
“Ah ah hajiya, babu ko daya cikin abunda kika fada, bai mana komai ba, wannan ogana ne, muna neman wata yarinya mai
suna sabeeha, kuma an Shaida mana shine marikinta.
“Babu wata sabeeha a gidan nan, bamu santa ba, wata qila kunyi mistake ne, nice matar jamilu kuma bamuda ya mace yayanmu duk maza ne, dan allah ku daina neman mijina,”
“Amma Hajiya dakin saurare mi”
“Da
llah nace maka babu wata sabeeha gidan nan” tana fadin haka ta banko kofar gidan gabanta na faduwa, jamilu dake zaune a daki yana ganin ta yace sune ko? Kamani zasuyi? Ke jamila wallahi tallahi taki ta kare na rantse da Allah”
*…
Tana rufe kofar salim ya
fada ma taj komai, da yanda tayi dening, gaba daya everything doesn’t seems right, shi kanshi salim din ya gane basuda gaskia kwata kwata daga jamilun har wannan dake ikirarin matarsa ce.
Taj fa bai hakura ba yasa salim ya tambayi mutanen dake wucewa, wa
jen mutane hudu suka tambaya kowa sai yace bai santa ba.
Wani dan yaro daya taso daga islamiyya yana wasanshi dayaga an zagaye wayar da salim ke nunawa shima ya karasa wajen don ganin me ake gani, yana ganin sabeeha yace “kai wannan na santa”
Salim yayi
saurin cewa “ina ka santa?”
“Ga gidan su chan kasan gangare, kudi salim ya bashi gar 5k yace zoka rakamu, aiko ya rakasu a kafa, gaba daya anguwar so disgusting, ko ina duk wari, taj dai bai taba zuwa iri waje haka ba baima san it exist ba sai yau, daudai
gidan hayansu sabeeha ya tsaya yace “nan ne”
Tuni landlord dake ciki ya futo tare da yaron, irin igbo man dinnan ne sai bala’i yake yazo karban kudin wata yana ganin balarabe kawai ya soma washe baki.
“Oga please do you know this girl? We heard that she
live here?”
“Ah yessoo, this girl and her mother, they never pay my rent they ran away, useless and wicked people”
“Mind your words please” taj ya fada rai adan bace.
“Where can we find them?”
“How would i know? Shey i told you they never pay me my re
nt”
“How much is your rent, “50k” ya bashi amsa
Taj yayi tsuka, rai a bace jijiyoyin kanshi na tashi, kamar yaui hauka haka yakeji, salim ya bama landlord 100k suka bar wajen saboda hamami.
Tund asuka shugo mota taj ya dage kanshi, daga jiya zuw ayau sa
lim ya gane wannan binciken yarinyar badan komai bane saidai so, duk yanda akayi mutumin nan son yarinyar yake, kuma ya hadu da ita a kasarshi ne.
“Sir zamu sameta insha allah, i still dont trust that jamilu, he definitely knows where to find her, ko kana
so musa hukuma a ciki?”
“No need for that, lets calm it a day”
Salim yaja motar sukabar wajen.
Suna cikin tafiya salim yace “sir ive assigned you the membership of the best gymnastic close to your home you can start anytime”
“Thank” taj ya amsashi gab
a daya hes fed up, ya kasa thinking straightforward.
Wajen karfe hudu suka iso, salim ya saukeshi ya shiga ciki jiki a mace.
Laila data shugo part din anne ta a zuwa direct kitcen ta wuce wajen anty rabi, tana isowa tace “anty rabi ga lunch din uncle t
aj mami tace a kawo”
“Toh bari akai mashi”
Sabeeha dake tsaye tana yankan naman sa da aka kawo za a saka a fridge rabi ta kalla tacebar naman zamu cigaba nida basira kije ki kai wannan chan part din”
“Toh anty rabi”
Ta bata ansa tare da karbar tray din
basira ta bita da harara, ita maisa baza ace takai ba.
Akan idanun laila sabeeha ta wuce part din taj, sai kawai tayi murmushi ta wuce part dinsu tare da daukan wayarta ta kura maya, “baby girl, kina ina ne? What are you doing?”
“Sleeping..”
Ta amsat
a kai tsaye, “ya muke ciki ne da bet dinmu? Banga wani sauyi ba?”
“Kina doubting dina ne?”
“No kawai dai na tambaya ne, naje part din anne nakai Favourite abunci sa da mami ta zuba mashi shine na tuna da bet dinmu”
“Meysa baki kirani ba????”
“Woo, kai
masa zakiyi?“
“Yea…”
“Haba dai…you’ll not do that, irin waennan abubuwan ba kince yan aiki ne ya kamata sunayi ba,”
Banza tayi da ita amma ta qulu sosai ba kadan ba, “waye kika bama zai kai?”
“Sabeeha, i heard that aykin part dinshi ya koma hannunta,
“
Kitt maya ta kashe wayar jikinta na bari ko dankwali bata saka ba daga ita sai wata yar vest da tight tayi packing shegen gashinta da ko ribbom din bai kamasu sosai.
Kamar zata fadi haka take tafiya gaf gaf gaf har zuwa part din, ko knocking batayi ba
ta bankade kofar, adaidai lokacin ta tadda sabeeha na jera abuncin a dining, maya na ganinta ta daka mata tsawa “keeee me kikeyi anan?”
Da mamaki sabeeha ke kallonta, “bake nakema magana ba yar matsiyara me kike anan?”
Banza tayi da ita maya ta hasala “
dan…”
“Karki sake ki zageni,aikina ya kawo ni nan ba fada dake ba,”
Daga yau karki sake shugowa nan?”
“Idan ke nakema aiki ki hanani”
Tana fadin haka ta juya abunta ta futa daga gidan kota kanta batabi ba, maya kamar ta shaqo ta ta kashe haka takeji, l
okaci gida taji shes insecured gaba daya.
Sabeeha na futa sai gashi ya sauko kasan, sanye da armless riga da gajeran dogon wando kamar zaije gym, tundaga sama yake kallonta da mamaki,”wannan yarinyar is she okay?” Ya tambayi kanshi.
“What are you doing h
ere?”
Ya tambayeta babu wasa, “uhm uncle taj, daman mami ne tace na kawo maka breakfast”
Tund aya mata kallo daya bai sake kallonta haka ba badan komai ba saidai kwata kwata babu abun burgewa a tattare da kallon nata,
“You may find your way”
Murmushi
tayi tana gyara tsayiwarta harda kwarkwasa oho shi baima san tanayi ba,
“Uncle taj, are you going to gym? Can i come along?”
Ay baiyi tunanin anan ma akwai marasa kunya ba sai yanxu,,
“You may find your way” ya sake fada yana mata nuni da hanya this ti
me around babu wasa, jiki a mace ta juya ta futa.
Sai yaji abuncin ma ya fita aranshi baici ba ya fuce.
Da daddare kowa ya hallara for dinner, hamad da nanna da maya banda anne data kasa suakowa saboda kafa.
Daga kitchen rabi ta dubi sabeeha tace “d
an allah jeki kai pepper soup dinnan nan,“
“Toh” sabeeha ta fada tana kokari daukan warmer din, ta tunkari dining area din.
Da sallama dauke a bakinta ta karaso, hamad ne ya fara dagowa jin muryanta mai sanyi, ya dade bai ganta sai yaga ta sauya gaba day
a tunda sukayi hutun school.
“Sannu ku da hidima” nanna tayi magana tana kallonta.
Murmushi kawai sabeeha tayi ta aje abuncin kan dining, harta juya ta tsaya chak kamar ruwa yacita “taj, ga pepper soup a zuba maka?”
“No nanna, this is okay” ya fada da l
arabci.
Kirjin sabeeha kamar ana lugude, yanda kasan ana buga guduma haaka take ji, ta kasaa juyowa ta wuce kitchen jikinta na bari, so take ta juya amma ta kasa, kafafunta kamar ba a jikinta suke, muryan taj taji ko kuwa kunenta ne da kwalwalwarta ke kok
arin yi mata wasa da hankali.
“Kai its impossible mai ze kawo taj nan gidan? Shida yake saudi She must be mistaken”
Basira ce ta kalleta dataga shugowanta tace “kizo mu karasa kin barni ni kadai inata fama da tukwane, duk wani abun arziki sai