Showing 243001 words to 246000 words out of 338813 words
basu kudi da yawa yace idan sunje shopping su saya duk abunda sukesu, maya ta karbe tare dayi mashi
godiya laila ma tayi godiya, sabeeha da tunda suka fito ko uppan bata ceba ta sauke kanta kasa sai a sannan ta dago ta mashi godiya.
Bayan sun gama da saloon suka kira hamad ya dauko wata motar yazo ya daukesu sai shopping, as usual sabeeha saita zama k
amar yar rakiya, taqi daukan komai saboda abunda hadiza ta fada mata, suna gamawa suka fito hamad ya maidosu gida.
Akan idanun taj dake tsaye ya futo zaije masjib suka shigo gidan, lokacin an kira sallar magrib, sabeeha na daga zaune gidan gaba duk suka
firfito, kowacce ta kwashi ledojinta ta kara gaba, saida suka shiga hamad ya dubi sabeeha yace “meysa baki sayama kanki komai ba?”
“Ya hamad bana buqata ne,”
Baija maganar ba ya tambayeta ta gama shirin komawa? “Tace mashi eh sannan sukayi sallama ta wu
ce ciki shi kuma ya nufi hanyar masjid.
Kwata kwata tunda suka tsaya shida ita basu lura da taj dake tsaye gaban apartment dinshi ba yasa hannayenshi jikin aljihunsa, ya dade tsayen nan abubuwa da dama na running a mind dinshi, hartazo ta wuce ta gabanshi
bata lura yana tsaye ba don tsakanin compound din da apartment dinshi akwai dan nisa.
Saida ta wuce kafin ya wuce masjid.
Ana idar da sallah ya shaidama nanna zaiyi dinner a bangarensa.
Bayan shigarta bangarensu hadiza kanar jiran dawowar su take ta
biyota har daki da tambayoyi iri iri, “ina kukaje? Waya saukeku?” Gaba daya yanda take magana saida ya tsorata sabeeha, ta fada mata komai in details daga yanda suka shiga mota har suka dawo gida, sauke ajiyar zuciya hadiza tayi tace “ki kama kanki, wallah
i duk sanda naga kina rabar koma waye a cikin yan gidan nan saina maki lahani, baki ba kowa,”
Maganganu fa take marasa gaba bare baya, wanda ita ka ta sabeehar ta kasa ganema maganganunta.
***
“Yau dai naga what shock me the most?“ laila tayi magana
tana kallon maya data futo daga bathroom.
“Menene?” Maya ta tanbayeta
“Wai da gaske kiran fatima kikayi?ke da kanki? Keda kika tsani yanda ake hadamu da ita, musamman idan zamuje school ko shopping”
Murmushin mugunta maya tayi tare da cewa”hmm..”
Laila
najin haka tace “ maya what are you cooking this time around?? Eh?”
“When the time comes zaki sani koma menene”
Suna cikin hira bahijja ta shugo dakinsu ta kawo masu snack data danyi, laila tace “thank you mummy”
“Ashe daddy ya kaiku dazu?” Bahijja t
a tambayesu
“Eh motan ne yaqi tashi, ya hamad yace ba ayi mata monthly service ba shiyasa” laila tayi magana.
“Wallahi mummy banason yanda ake hadamu da yarinyar nan,” maya tayi magana a shagwabe.
“Wace yarinya kenan?”
“Househelp dinnan mana, duk wani
abu da ake mana sai anne tace harda ita, i just don’t get it”
Shuru bahijja tayi tana tuna yanda aka dunga hadasu da hadiza lokacin da suke zuwa makaranta, kamar tarihi na maimaita kansa haka take ganin abun,ta rasa dalili tunda yarinyar tayi mata sata t
aji bata sonta kwata kwata balle kuma data kasance jinin hadiza? Hmm
“Ba komai next time saikuje kuyi naku daban, daman bai kamata ace ana hadaku da yan aiki ba, kowaya tsaya a matsawar shi kafin abun ya kaiga hassada, don idan tana ganin ku yan gida ne d
ole wata rana zataji kamar kun fita gata dukda an jawota an hadata daku, irin su basuda godiyar Allah”
Da mamaki laila ke kallon maya da maman nata, saitaji maganganun nasu kamar basu daceba, idan da mami ne ta tabbatar bazata fadi haka, saidai ma tace da
na kowa ne, ba laifi ne ba idan anyi ma sabeehar.
Haka tayi shuru tana jinsu suna maganar batace uppan ba.
The next day ta kasance monday, sai wajen karfe goma duk suka shirya, kamar koda yaushe itace ta fara futowa kafin sauran yayan gwal din suka fu
to.
Daman first day of resumption registration ne sai selection of courses wannan yasa suna gama abunda suke kawai hamad ya wuce dasu asibiti.
Daga asibiti sai wajen dare suka dawo gida gaba daya harda mummy.
Tun ranar nan da suka hadu da salim a asibit
i yake kiranta bata dauka, messages dinshi ma bata budewa balle tasan abunda yake nufi da ita.
Washe gari tun wajen asuba ta farka, tana wanka ta shirya ta futo kitchen, yan abubuwan da take taimakawa rabi ta soma yi kafin rabin ta futo, tana futowa suk
a gaisa rabi tace “kedai fatima badai kokari ba, sannu da aikii”
Dariya sabeeha tayi tana kokari jera plates cikin dish washer zatayi drying, sama sama suke hira ita da rabi har suka kammala breakfast rabi tabzuba mata taci.
“Ko ya zamuyi da gyaran banga
ren yallabai balarabe, gashi kina zuwa makaranta, ke kodai wani abu kikayi ne dayasa ya dakatar da gyaran bangarenshi?,”
Take gaban sabeeha ya dan fadi batace komai ba tadai dago ta kalli rabin, “ah ah nima bansan dalilin dayasa yace a dakata ba” sabeeha
tayi magana tana kokarin wanke plate data gama cin abunci, allah allah take ta futa daga kitchen din kawai.
Baifa dakatar da itaba haka kawai ta shirgama rabi karyar cewa yace adaina zuwa bangarensa kuma abun saiyazo da bai nemi azo a gyara masan ba.
Tar
a daidai suka fito gaba dayansu, a maimakon suka hamad kawai sai sukaga taj ya futo, cikin Sauri maya tace “good morning uncle taj”
“Morning” ya amsa ta laila ma ta gaishesa, sabeeha ta rakube kamar munafuka ta gaishesa kasa kasa yayi kanar bai jita ba ka
i wannan abu yayi ma maya dadi.
“Lets go..”
Ya fada, duk suka kalleshi da mamaki, maya dadi kamar ya kasheta ta shiga gidan gaba, laila ta shiga baya, sabeeha ta tsaya kamar ruwa ya cita, gabanta na faduwa ta bude bayan ta shiga ta zauna.
Ta jikin mirro
r ya dago karaf idanunshi ya suaka cikin nata tayi saurin sauke nata kasa yayi reversing motar.
Maya ko sai smiling take tana murma yau zata bada mamaki idan sukaje school, aka ganta da taj ay an dago mata mutunci sosai.
Notification din message ne ya sh
ugo mata a waya dayasa ta duba, laila ce ta turo mata “ashe ya hamad ne yayi tafiya yau da safe, yanxu naga message dinshi”
“Haba ina ya tafi?”
“Ban sani ba wallahi, it lools like office related work ne don tare da uncle sameer suka tafi”
“Wow thats nic
e allah yasa su kwana biyu kafin su dawo”
Sanin me hakan ke nufi yasa laila cewa “kardai hopes dinki su hau sama da yawa”
Banza maya tayi da ita ta soma janshi da hira, yana amsa ta sama sama.
Bini bini yake dagowa yana kallon sabeeha data sauke kanta
har suka iso school, suna isowa duk suka fito maya ta zagayo inda yake harda knocking windown shi don a rufe yake dukdan a ganta tare da shi tace “thank you uncle taj”
Girgiza mata kai kawai yayi suka wuce ciki already sabeeha ta rigasu tafiya.
Tana sh
iga first lecture dinsu tun kafin ta kaiga zama ta jiyo muryar haya “babessss!!!!!”
Da sauri ta juyo, take wata fara’a ta bayyana akan fuskar sabeeha suka rungume junansu, haya tace “kwana biyu, ya hutu? Inna kira wayanki koda yaushe a kashe”
“Wallahi ha
ya i cant recall when last na dauka waya, abubuwan dake gabana sun isheni ma banida time din waya”
“So how far muje mu zauna lets talk”
Zaka sukayi haya ta dubeta tace “i have a surprise for you”
Sabeeha excitedly tace “uhmm haya keda surprises dinki,”
Bata rufe baki ba ta dago hannunta tana nunama sabeeha zoben hannunta tace “i got engaged”
Da mamaki sabeeha ke kallonta, rayuwar yan gata kenan, kamar cristoci, “aure zakiyi? Kai masha allah na maki murna sosai allah ya sanya albarka”
“Ameen sabeeha na
gode, next year insha allah after graduation dinmu,”
“Masha allah” sabeeha ta fada tana rungumeta don har cikin zuciyarta take tayata farin ciki
“And youre going to be my best girl”
Dariya sabeeha tayi tace “allah ya nuna mana”
Suna cikin magana lectur
er dinsu ya shugo ya fara masu lectures.
Ana tsakiyar yin lectures din security ya shugo class din, magana yayi da lecturer din kafin ya futa shi kuma lecturer din yace “who’s sabeeha?”
Hankali tashe sabeeha ta daga hannunta sannan ta tashi, “someone is
looking for you”
Kallinta haya tayi tace “kodai ya hamad ne bai gaji da ganinki ba”
Saurin girgiza kai tayi tace “bashine ya kawo mu ba”
“Toh kije ki duba ko waye”
Jiki a mace ta miqe ta futa, security dunnan na tsaye tabi bayanshi suka fito, tun kafin
su karasa ga motar gabanta ya wani mugun fadi, “hes the one looking for you”
Zuge glass din motar yayi ya miqa ma security din kudi sabbi, salim ya koya mashi wannan bad character din
😂
ya gama gano yan nigeria sai kana dan basu abun hannu kake samun abu
cikin sauqi.
Kallonshi tayi shima yana kallonta babu wasa kan fuskanshi yace “get in lets have a talk”
Daga yanda yayi maganar yasa taji ya mata wani irin kwarjini ta samu kanta da shiga motar ta zauna gidan gaba ba tare da ta kalleshi ba.
Ga mamakinta
kawai taga ya rufe motar gaba daya sannan ya chanza giya tare dayin reverce son a kunne take ta fara tafiya.
Hankali tashe ta juyo ta kalleshi tace “ina zaka kaini? Ina cikin class ne fa kasa na futo”
Banza yayi da ita kamar baisan da mutun a wajen ba ya
futo daga school din.
Bakinta fa baiyi shuru ba ta soma jin hawaye na neman futo mata tace “dan Allah ka maidani,test mukeyi”
Kamar tana magana da dutse haka yayi, kamar baisan tanayi ba, yau taga ikon Allah, karshe dai jan bakinta tayi tayi shuru tana
hana kanta hawaye.
Da mamaki take kallon inda yake neman shiga, ko a tarihin rayuwarta bata taba ganin waje mai kyan gaske kamar wannan ba, idanunta bai kaiga sunan wajen ba saida ya shugi wajen check point, hankali tashe ta duba sunan dakyau sannan ta d
ubeshi “transcorp hilton hotels”
Gaba daya ta zama speechless ta kasa cewa komai, babu abunda ke yawo aranta sai menene dalilinshi na kawota nan dayayi?meysa ya kawota nan? Me zaiyi mata? Al’amarinshi yana bata tsoro, at this point tana jin kamar bata san
shi ba kamar ba taj din data sani ba a baya.
Parking yayi wajen vip parkings yana gamawa kafin ya kashe motar ya juyo yana kallonta, idanunshi sun sauya launi sosai haka zalika ko murmushi bayayi.
Bakinta na karkarwa tace “meysa ka kawo ni nan?”
Kai tsa
ye yace “you’ll find out soon, lets go”
“Wallahi babu inda zanje, ni ka maidani school”
Wani irin kallo dayayi mata saida gabanta ya fadi sosai, idanunta ya ciciko da kuka sosai.
“The will be the last time i will instruct you to do something and you rep
ly me in such manner,”
Ganin haka bazai fishe ta ba yasa ta sauke murya tace “sir please im begging you..”
Kwantar da kanshi yayi jikin bayan kujerar motar, bai taba ganin mai taurin kai irin ta ba a rayuwarshi, ayanxu kam ya gama yarda wahalar dashi tak
e son yi kawaj kuma saboda taga hes so soft towards her tunda har ya fada mata akwai aurenshi akanta dole ta aje wannn Shirmen nata suyi forcusing akan what comes next..
“You have two options fatima, koki sauka muje ciki and have a peaceful talk ko kuma n
a maidake gida na fadama kowa aurena dake kanki, i know you wouldn’t want your mama to know about it right?”
Girgiza kanta ta somayi ta rasa ya zatayi da wannan ala’amari, ay idan hadiza taji wannan zance kasheta ne kawai ya rage bazatayi ba, ya zatayi ya
nxu?? Bazata taba bari hadiza tasan cewa tayi aure a saudi ba kuma taqi fada mata.
“You’re wasting my time fatima”
Goge sauran hawayen daya gangari mata tayi sannan ta sanya hannunta jikin kofa, ya danna key din kofar ta bude, bude idanunshi yayi daya ku
llesu jin ta fita shima ya futo sannan ya rufe kofar.
Gaba yayi tana bunshi a baya kai kace ya mata dole, koda yake dolen yayi mata don batada wani option daya wuce ta bishi tunda yace magana zasuyi.
Sai faman kalle kalle take tunda suka shugo directly w
ajen receptionist din dake tsaitsaye wajen vips ya nufa, tana biye dashi sai faman sassauke kanta take, tunda suka shigo take cin karo da turawa, baqaqen fata tsilla tsilla ne a wajen.
Bai wani jima ba ya karba abunda zai karba suka wuce yana gaba tana bi
ye dashi a baya, gaba daya saita wani raina kanta, yana ankare da ita amma ya wani basar.
Danna lift yayi ya bude ya shiga, ta wani tsaya qiqam taki sanyo kafafunta ciki,dagowa tayi ta kalleshi, ya wani relaxing bayanshi jikin lift din, yana mata wnai iri
n kallo, haka kawai takejin this is not right, what if wani abu ya faru? What if…”
Tana cikin tunanin taji shi yana cewa “are you not getting in????”
Tsoro fa takeji sosai gabanta na faduwa, itace yau a hotel, da namiji? Tuni zuciyarta tayi mata gyara “m
ijinki dai,”
Wata zuciyar tace “what if ya fada ne kawai babu wani aure a tsakaninku? Kin tambayeshi shaidar hakan?”
Saurin rubtse idanunta tayi wata zuciyar tace mata “what if wani abun zai maki?, tsoron me kikji? Me zai iya maki? Taj ne fa? Dadin ki?”
Sakin madannin daya hana kofar rufewa yayi zata rufe kenan tayi saurin dawowa hayyacinta ta sanya hannunta a wajen kofar ta bude ta shugo daga ciki tana kokarin mustering courage dinta.
Smirking yayi ba tare da dubi bangare da take ba ya danna floor 13tg
floor chan sama second to the last floor.
Yanda kasan ana hautsina ruwan cikinta haka ta soma ji, har suka iso lift din ya bude.
Shine ya fara futowa kafin ta futo sannan tabi bayanshi, gaba daya floor din baifi dakuna biyar ba, shine luxury din hilton
gaba daya.
Gaban dakin ya da yayi booking ya tsaya tare da saka card din jikin kofar take kofar ta bude da kanta, ya shiga daga ciki.
Duk adduar datazo bakinta take furtawa har ta shiga itama kofar ta rufe da kanta.
Tun kafin ka shiga daga ciki zaka gan
e suite din ya hadu ya gaji da haduwa sosai ba kadan ba.
Ga sitting area ga kitchen ga dining ga kuma bedroom din a hade, its an open place, kitchen na daga gefe haka zakika wajen cin abunci sai kuma tafkekwn gado daya zagaye ko’ina, kai abundai ba a cewa
komai high class, hatta bathroom dake suite din a bude yake, sai extention din glass daya rabashi da gado, amma duk wanda ke zaune kan gadon zai hango wanda ke wanka a ciki, ko ya mutun zaiyi wanka a haka oho.
Wayanshi ya fara ajewa kan gado tare da key
din motanshi dinshi, sannan ya zauna kan wata kayatacciyar kujera ya jawo lanline din dake wajen sannan ya dana wasu numbers.
Magana ya somayi a hankali yana duban screen din tabkekiyar tv dake maqale jikin bango, da alamu kamar order yakeyi, yana gama m
agana ya aje landline din tare da kallonta tsaye jikin kofa ta kasa karasowa ciki.
Maida kanshi yayi bayan kujera ya lumshe idanunshi abubuwa da mata na yawo aranshi.”ya zaiyi ya nemi iyayent? Meysa sukayi abandoning dinta? What could happen idan ta gane
cewa wadda ke rike da ita ba itace mahaifiyarta? Ya zataji idan ta gane tanada wasu iyaye daban? Shin bata tayi aka tsinceta? Ko kuma deliberately akayi abandoning dinta? There is definitely something about her dayakejin is definitely outrageous.
Karar d
oor bell ne yasa shi dawowa daga tunanin daya shiga, ya danna wani abu a gefe sai kawai kofar ta bude, da sauri ta juyo gabanta na faduwa taga wani mutumi da fararen kaya kanar chef haka, hannunshi da wani trolly ya turo ciki, yayi saurin sunkuyar da kansh
i da girmamawa yace “good day ma’am we are so glad to have you here”
Shuru tayi ta rasa me zatace ya sake cewa “can i come in ma’am?”
Daga ciki taj yace “yes..”
Karasowa da trolly din mutumin yayi sannan ya gaisheda taj din sannan ya fara setting dining
, varieties if different types of breakfast aka kawo don yafi kala goma sha, kalacin yan gayu kenan.
Mitumin na gama jera masu yace “have a nice stay mr and mrs”
“Thanks” taj ya fada kafin mutumin ya futa.
Futar mutumin ko minti daya baiyi ba ya miqe ts
aye ya soma un buttoning farar top din dake jikinshi, cikin sauri sabeeha ta juya mashi baya kuam ya lura da hakan ya kauda ido.
Yana cire rigan ya aje ya rage dagashi sai vest din daya saka da dogon wandon rigar, ac dakin ya kure to the highest sannan ya
nufi wajen dining.
Kallon abubuwan da aka jera yayi sannan ya zauna kan high chair din.
Coffee ya fara zubama kanshi sannan ya fara sha yana kallonta ta gefen ido, ko gajiya batayi da tsayuwa.
Kwana biyu miskilanci ya matso sosai don ko magana mai tsay
i baison yi kuma hakan na faruwa ne idan damuwa ta mashi yawa sosai ko idan yana cikin bacin rai.
Saida ya gama shan coffee din tass kafin ya miqe tsaye ya soma tunkarar inda take tsaye, tana daga tsayen nan tanajin isowarshi, at the same time gabanta na
faduwa.
Yana karasowa ya kamo hannunta tare da juyo da ita.
Yana fuskantarta tana fuskantarshi taki yarda su kalli juna.
Ganin haka yasa shi jan hannunta tayi saurin dagowa ya kauwa idanunshi suka nufi dining din, saida yazo daidai kujeran daya zauna da
zu yaja kujerar sannan ya zauna akai har zuwa lokacin