Showing 180001 words to 183000 words out of 338813 words
hidaya tayi zata kwasa mata
mari fadwar tayi saurin rike hannunta tana zaro ido kamar yanayinta idan kaganta aka bata wuqa zata iya dabama mutun ba tare da second daya ba.
Duk wata uwa danta ne weakness dinta, zata iya komai akan danta koda kuwa bada ragowar nunfashinta ne.
Fadwa
na tsaye hidayar taja papers din tayi signing gaba dayansu, gaba daya komai ya tashi daga hannunta ya komawa fadwa, komai fa duk wani abu datayi inherinting.
Tana gamawa fadwa ta kwashi tanardun ta dubi wajen securities din dake wajen ta daga ma wadda ta
shugo da hidaya wajen hannu sannan ta juya ko second daya bata sake ba.
Tana gab da futa hidaya dake zaune tace “wallahil azeem idan kika sanya hannunki akan dana saina zama ajalinki”
Juyowa fadwa tayi ta mata kallo daya sannan tayi fucewarta a fusace.
Tunda ta shiga motarta take wani irin mahaukacin driving kamar zata tashi sama harta iso guest house din mahaifinta.
Tana bude kofar shugowa tayi karo da secretary din abdul basit, dagowa fadwa tayi kamar mahaukaciya ta kwasheta da mari both kuncin ta,
ta shaqo wuyanta kamar zata kasheta, abdul basit dake zaune sitting room din yana kallon komai kuma baiyi yunqurin hanata ba, ga wadda ta shaqe kamar zata mutu, bai hanata venting anger dinta ba ya qaleta yana kallonta wama zai iya hanata koshi mahaifin na
ta bai isa ba, saida secretary dinnan ta daina nunfashi ta saketa.
Tana sakinta tabi ta kanta ta wuce cikin sitting room din ta watsa jakarta a wajen ta kama kanta tana ihu.
Hannu basit ya dagama black da personal asistant dinsa suka wuce wajen secretary
din suka kwasheta suka fita ya rage daga shi sai ita.
Miqewa yayi ya kamo hannun fadwar ya rungumeta yana tapping bayanta “should i end her for you?just say a word”
Fitowa tayi daga jikinsa tana kallonsa idanunta kamar gauta tace “not yet, i want her to
be miserable, so nake naga tsoro akan fuskarta, so nake na aje mata babban tabo a zuciyarta for messing with me”
“Well you can if you want to, ba kince danta ne weakness dinta ba? Give her that pain she deserves.”
Murmushi fadwa tayi tana kallon baban n
ata ta rungumeshi sosai tace “okay!!!!”
Hidaya na komawa cell babu abunda take sai hawaye, nidai zan iya cewa ban taba ganin hidaya ta taba yin hawaye ba sai yanxu, babu wanda ya fado mata arai sai jamid.
Wazai duba mata barad? Ya zatayi da danta?Dole
tasan yanda zatayi ta kubutar da danta daga sharrinsu.
Haka nan ta kwana a zaune ko rintsawa batayi ba, maganganun da fadwa tayi mata na yawo akanta, wayo tayi underestimating dinta sosai ba kadan ba, ta kashe mijinta? Daman itace behind bacewar taj? Sa
nnan itace ta kashe khaal?.
Zaman nan datayi ko motsawa batayi ba,abunci ko da aka kawo mata ko kallonshi batayi ba har safiya.
Wani inmate call dinne ya kara zuwan mata cewa tayi visitor, koda ta buqaci sanin wanda yazo din akace mata family member ne
taqi futowa.
Da daddare kuwa da securities sukazo round checks aka tadda ta sume, dole akayi shifting dinta to clinic aka bata taimakon gaggawa.
Batama san ta sume ba sai the next very day ta samu farfadowa tana farkawa idanunta ya sauka kan doctor din
dake dubata, ruwan da aka saka mata aka cire tana kokarin miqewa zaune ta kasa saboda cuffs din da aka saka mata.
Discharging dinta akayi security suka rakata zuwa dakinta, tana shiga wani visiting call din yazo mata.
Duk a tunanin ta fadwar ce ta sake
dawowa don bata kawo ko afiya ce ko wani family member ba daban.
Security suka rakota har wajen visiting area kafin su barta a tsaye dago da kanshi yayi ya sauke akanta, saurin yin baya hidaya tayi wuth so much shock, karara akan fuskarta, hannunta ta san
ya kan fuskarta ta mutsuka idanunta don tabbatar da jamid ne a gabanta, mikewa yayi tsaye ya tunkari inda take tabi kafafunshi da kallo har zuwa hannyanshi daya sanya ya kamo nata ya zaunar da ita sannan ya dawo wajen zamanshi ya zauna.
Saurin kauda shock
din dake fuskanta tayi ta kauda idanunta irin kamar batayi mamakin ganinsa ba.
“You must have work hard on your self, Yaushe ka samu lafiya?”
Girgiza kai yayi, this is hidaya, bazata taba chanzawa ba.
“You must be happy to see how i end up here,…mind y
ou i still don’t regret my actions, i still stand on my grounds duk abunda nayi a baya”
“Nasani, babu wanda zai fadi ko wacece hidaya saini, amma inaso ki sani duk abun dayake faruwa dake yanxu baikai kwatankwacin pains din da kika saka yaron nan a ciki
ba, and alhakin sa ke binki, baku hakura ba saida kukaci galaba akanshi, ay bakiga komai ba ma tukunna you contributed in destroying alot of peoples life, dukdan saboda power, saboda arzikin da zamu mutu mu barshi, saboda hatred, kin mance kema uwace, kin
haifa kema, idan naki ne yayi experiencing abunda kikayi ma yaronnan…”
Ya dan dakata jin wani irin daci a zuciyarsa kafin ya cigaba, “yanxu ina arzikin?ina power din?
Idanunta ne yayi jaa sosai, tsakanin kwanakin datayi a wajennan yasata reflecting ab
ubuwa da dama, musamman da fadwa tayi threatening dinta akan danta, bata taba regretting abubuwan datayi ma taj ba sai yanxu, ta dandani zafin cin amana musamman ga wanda ka yarda dashi.
Shida ta nemi wulaqantawa, shida ta nemi salwantawa rayuwa ta rabash
i da kowa hatta mahaifiyarsa ta karfi da yaji ta maishesa kamar wani dan kwikwiyon da take juyawa san ranta, kuma ya yarda da ita sosai, ya bata matsayinda ko mahaifiyarsa bai bama in return tayi betraying trust da yardar daya bata da girman daya, infact b
ata taba considering dinshi
matsayin dan uwanta ba ko sau daya, dukdan saboda mahaifinsu ya auri mahaifiyarsa.
Wani abu ne ya soma sauko mata a fuska kamar hawaye, she couldn’t believe hawayen takeyi, wannan hawayen nata ya bama jamid answers din da ya
ke nema, ko zata kwana tana denying batayi nadamar abubuwan datayi a baya ba yasan yanxu tayi.
Saurin gogewa tayi ta dubeshi, “are you done?” Tana fadin haka ta miqe tsaye zata bar wajen yayi saurin dakatar da ita.
“You’re a victim as well, Its not too l
ate to repent, its not too late to make things right,”
Dan dakatawa tayi kafin ta juyo, ta kalleshi, “khaal yana raye! Bai mutu ba?”
“Bai mutu ba? Yana raye?”
“Kwarai da gaske,” ya bata amsa
“He was never dead to begin with,”
“Wa kenan????” Hidaya ta
tambayeshi kamar bata sani ba
“yar uwarki fadwa, !!!”ya bata amsa kai tsaye,
“I was one of her victims, itace sanadiyar paralyze dana samu, tana amfani dake ta hanyar cinmma burinta da boye duk wani sirrikanta.
Shuru hidaya tayi tana wani nazari, mamak
i ya gama cikata sosai.
Kamar an tsunguleta ta dago ta kalli jamid tace
“Barad…!!! He’s in danger,ka daukeshi ka boyeshi,”
“Barad??” Ya kalleta ganin yanda gaba daya ta nemi rikicewa.
“Me zai samu barad?”
Dubansa tayi dakyau hannunta gar karkarwa yak
e, “fadwa ba kanwata bace, fadwa yar abdul basit ce”
Confusely yake kallonta, “ni take hari,kuma zata iya yin komai don ganin ban bayyana wannan sirrin nata ba, you need to take barad, ka boyeshi, karta cutarmin da daa”
Gaba daya jamid ya shiga confusion
, yanxu wannan ne babban sirrin nata daman?….
Nigeria….
Karfe 5 daidai suka dawo gida, as always duk sun fita itace last, tana fitowa ta rufe motar saida ta jira hamad ya kashe motar ya fito kafin ya zagayo ya tadda ta tsaye, laptop din dake hannunsh
i ya miqa mata.
“Kiyi presentation din dashi”
Da mamaki take kallonshi don kwata kwata batayi maganar presentation dinba ya akayi ya san zata buqaci laptop?
Ganin ta tsaya yasashi “ko na aje abuna?”
Cikin hanzari ta karba murmushi ya kubce mata tayi s
aurin sunkuyar da kanta tace “thank you ya hamad”
“You’re welcome muje ciki”
A tare suka shiga main house ya bude kofa ta shiga kafin ta shiga, saida tazo wucewa part dinsu ta sake juyowa ta dubeshi bakinta ta dan motsa ahankali tace “thank you” sautin
muryanta bai futo ba amma yanda ya kura mata ido ya gane abunda ta fada, tana fadin haka ta wuce ya bita da kallo, ya sauke wani murmushi ahankali, he just loves to seeing her smiling.
Saida yaga ta shiga ya juya ya futa daga main house din.
Da sallama
ta shiga dakinsu, hadiza na zaune tana ninke bras da panties din maya datasa sabeehar ta wanke da asuba.
“Ina wuni mama”
A daqile hadiza tace “lafiya” kafin ta miqe da kayan datake ninkewa ta futa.
Sabeeha ta bita da kallo tana tunani wani abu ranta.
A gurguje tayi wanka tasa doguwra rigar da aka bata cikin kayan laila kafin ta fito zuwa kitcwhn, tana shugowa rabi dake tsaye a kitchen din tace “har kun dawo?”
“Eh anty rabi yanxu muka shugo”
“ga abuncin ki nan,”
“Tohm akwai aikin da za ayi?
“Ah ah
jeki huta abunki kawai”
Murmushi sabeeha tayi tace “toh”
Daukan abuncin tayi ta fita rabi ta bita da kallo, haka kawai take tausayin yarinyar, babu ruwanta ga respect
Da sallama anne ta shigo bangaren nanna dake zaune da laptop kan cinyarta, zakayi t
unanin aiki takeyi saidai gaba daya natsuwarta bata wajen kwata kwata.
Sallamar da nanna tayi ne yasa ta dawo hayyacinta bayan ta amsa.
Zama anne tayi suka gaisa anne ta mata ya jiki, “badai aiki kike ba hajara keda akace ki huta”
“ alhamdulillah naji s
auki ay anne”
“Inason zamuyi magana” anne ta fada tana kallonta.
Nanna tasan maganar dazatayi mata wanda a yanxu dai bashi takeson ji ba kwata kwata, amma haka nan ta daure tace “ toh yaya allah yasa lafiya”
“Tajudeen zai dawo nan gida da zama, zamanshi
a hotel bai daceba, ina amfanin zaman hotel ga gida na bari ne daman ki samu sauqi tukunna”
Take nanna ta hade rai kamar bata taba dariya ba tace “zaman me zaizo yayi anan? Bazai zauna anan ba, idan ya gama abunda ya kawoshi ya koma chan inda ya fito”
“
Hajara kinsan me kike fada kuwa? Na kasa gane maki? Wannan wani irin kafiya ne? Danki ne fa? Shekara nawa kina mararin ganin danki?”
“Yaya, banida da, na dade da ajiye zama uwa a gareshi, tunda har banida mahummaci a rayuwarsa”
“Ya isaa!! Ya isa haka nan
, saurareni da kyau hajara,karki sake ganin laifin danki na qin waiwayarki dayayi,kin tafi kin barshi yana da kananu shekaru ba tare da tunani wani hali zai shiga ba dukdan saboda laifin ubansa, mey laifinsa? Ya za’ayu bazaiyi tunanin kinyi abandoning dins
hi ba? shin kinsan irin rayiwar da yayi achan? Kinsan ya childhood dinshi ta kasance achan? Wannan abun da kikeyi ba komai bane face huce takaicin tsohon tabon dake dan qare aranki ya hanaki moving on shekaru wajen nawa ya hanaki yin aure, tun wuri ki dawo
hayyacinki ki rungumi danki karki tafka babban kuskuren da zakiyi dana’sani,”
Kuka sosai nanna keyi anne na mata fada yau ko tausayinta bataji ba don furucinta ya bata mata rai.
Ganin yanda take kuka sosai yasa anne kama hannayenta ta rukosu tace “haba
hajara kamar bakida tawakkali? Mene laifin yaron nan? Eh??ki godewa allah daya sa zaku sake ganin juna kuma wannan dama ce allah ya baki na zama uwa a karo na biyu, duk wani abu daya faru dama chan haka allah ya kaddara saiya faru bamu isa mu chanza shi ba
”
Kallon ta anne tayi tare da bata qwarun gwiwa, “danki na buqatarki hajara,ki zame mashi uwarda ya rasa tun yana shekara bakwai, ki bar komai
ya wuce, ko zamo mai karbar kaddara duk yanda tazo maki, ki mance da baya kamar ba ayi ba”
Runtse ido nanna tay
i kafin ta bude idanunta ta dafe kanta anne na ganin haka ta fara kallon gefen gadon ko zata ga maganinta idanunta ya sauka kan bedside drawer dake bude, taci karo da hotunan taj din, yana baby da lokacin daya fara tafiya, har zuwa lokacin daya girma ya za
ma saurayi.
Murmushi kawai anne tayi ta balla mata magungunan tace “dadai aje wannan kafiyar kikayi kikaja danki daya fi maki, don wallahi idan har kikayi watsi da wannan damar taki ya koma zuciyarki ce zata buga, wllah ya sawaqa”
Tana fadin haka ta fita
.
Gaba daya nanna ji tayi jikinta yayi sanyi sosai, dukfa wannan abun da take a baki ne, tunda ya rike hannunta ranar yana kuka a gabanta gaba daya ta sare, ta fara blaming kanta for komai, what kind if a mother zata tafi tabar danta ba tare da tayi wani
difon tunani ba tunawa da wannan kadai da abunda mahaifinsa ya mata kesata karaya.
Anne na fita daga part dunta ta wuce nata ta soma dialing number taj, cikin ikon allah kuwa ya dauka cikin gaggawa, kwananshi biyu kwance yana zazzabi saida salim ya kawo
mashi doctor ya dan samu sauqi.
Ko jiya da sukayi waya da anne kasa fada mata yayi abunda ke damunshi.
Yana dagawa suka gaisa ta soma magana kamar haka.
“Inason gobe ka dawo gida, ina dana ina zaman hotel, come back home kaji ko”
Shuru yyi gabanshi na
faduwa sosai, “oummi??”
“Karka damu tajudeen, tana nan tana jiranka tajudeen, allah yayi maka albarka yasa muga aurenka da yayanka tajudeen, ni zan aurar dakai ma” ta fada tana murmusawa, maganar aure datayi saida gabanshi ya fadi.
Amma ta wani bangaren
ba karamin dadin kalamanta yaji ba datayi na kan cewa oummi na jiranshi, ahankali ya furta “Alhamdulillah, take yaji duk wata ragowar rashin lafiyarshi ta kau gaba daya, saidai kuma gabanshi ba karamin bugawa yakeba sosai at the same time kuma lokaci guda
sabeeha tazo ranshi.
✊
💋
BOSS LADIES WRITERS
💋
✊
MATAR TAJ (destined with you
🩵🤍
)
Written by
Queenmarh
✍
️
Book2
PAID
Chapter 95
Saudi…
Jamid baibar detention center dinnan ba saida hidaya ta fada mashi komai, asalin fadwa
yanda ta kashe tareeq saboda shine ya fara sanin sirrinta da kuma bacewar taj, da yanda ta dunga amfani da ita don cinma burinta, dukda itama tana da nata kason a cikin duk abubuwan da suka faruwa.
Abunda yafi bama jamid mamaki shine asalin fadwar, ba
yar taheel bace? All those years haka suka dunga venting akan taj, Hating on him, ganging
up on him, suka kusa salwantar da rayuwarshi, kuma ba kowa bane kan gaba sai hidayar, ashe shine asalin dan uwanta, fadwa ce outcast cikin su, ta haramtacciyar hanya
ma aka sameta, mahaifiyar tasu da suke duk waennan abubuwan saboda ita ashe itace aje masu abun kunya.
wannan babbar ishara ce a garesu gaba dayansu musamman hidayar data dauka tsanar duniya ta dorama taj, ta wulaqanta rayuwarshi ta kusa salwantar da ra
yuwarshi saboda tsana, bai tsareta da komai ba, yanxu gashi komai ya juye mata, yar uwar datake tunanin itace jininta ta kasance batada alakar ubantaka da ita kuma ta zame mata babbar barazanar.
Shima kanshi bata barshi ba, dukdan sabod aya tsayama taj, y
ayi protecting dinshi, saboda hakan ta maidashi kamar wani enemy dinta yana matsayin mijinta.
Tunda ya samu paralyze kuwa ya zame mata mara amfani ta fiddashi daga gidan nan ta turashi kasar waje neman lafiya bata sake waiwayarsa ba, Batama san yanda akay
i ya samu lafiya ba har yazo gareta yanxu haka, duk tsawon wannan lokacin bashida tunanin daya wuce na taj da sabeeha, saboda shi kadai zai iya fadin wahalar da suka sha a wajenta, makirci iri iri daban daban dukdan akan abun duniya, dukdan saboda taj kary
a gajesu.
Babu irin maganganun da jamid bai fada mata ba cikin bacin rai sosai, ta kasa magana kwata kwata gaba daya saboda she’s guilty of everything, he vent so much of his anger akanta sannan ya nuna mata ay bataga komai ba, kamar yanda ya fada mata
bazata taba sanin zafin abunda tayi ma taj ba sai ya samu nata gashi nan ba a je ko’ina ba saboda abubuwan datayi a baya zai shafi dansu, an innocent child daman duk abunda kayi sai anyi ma naka,, a karshe ma dai fada mata yayi idan har wani abu ya samu da
nsu bazai taba yafe mata ba.
Aranar daya dawo yaji labarin kamata da akayi tunda abune ba boyayye ba kama ga matsayinta a kasar, ko’ina zai dauka don zai shafi kamfanin su, yayi mamaki sosai, wannan ne yasa yazo don ya tabbatar ma idanunshi don hidaya can
never give up so easily he wanted to see why tayi sanyi batayi amfani da tricky connections dinta ba, don zata iya yin komai akan kamfaninsu da kuma ganin duk wasu abubuwa da takeyi bai fito idon duniya ba, ashe ashe ga dalili, ga kuma labarin bacewar taj
.
Haka ya futa yabarta zaune, jiki a mace tayi la’asar kamar ba hidaya ba, ta kasa tabuka komai, komai ya juye mata gaba daya bata cikin natsuwarta saboda danta, da tanada hanyar maida hannun Agogo baya da batayi abunda tayi ba a baya, sai hankalinta
ya sake tashi sosai, don tabbas fadwa zata iya illatar mata da danta dukda ta bata abunda take nema.
Jamid na barin detention center din, gabanshi na faduwa sosai ya wuce school dinsu direct.
Gaba daya school din yau is busy saboda hutun end of the ter
ms da akayi kuma iyaye nata zuwa daukan yaransu.
Dukda yasan makarantar akwai tsaro sosai wannan baisa gabanshi faduwa ba,at the same time har zuwa lokacin he’s in so much shock.
Ay bai gama samun shock of his life ba saida aka nemi barad a school sa
ma da kasa aka rasa,