Showing 189001 words to 192000 words out of 338813 words
kwana wajen nanna din tunda ta smau sauqi w
annan yasa shugowarta main house da part din nanna ya ragu ba kamar da ba.
Kullum tana bangarensu, babu abund ake fiddata sai aikin da zatayi na gida, data zauna a daki ko karatu takeyi na shirin test da zasu fara, gaba daya ta maida hankalinta wajen kara
tun yanda ya kamata.
Duk sanda ta shugo kitchen ko sai taji yan matan gidan nan na maganar baqon daya zo wanda suke alaqantashi da dan nanna da sukaji ana fada da yanda suke zuzuta siffarshi kamar ba bahaushe ba, ba yawan shigowa cikin gida take ba, balle
zagaye cikin sauran apartment din don bata da alaqa da wajen, aikinta na nan kirchen tana gamawa daki kawai take komawa, gashi ita ba ma’abociyar shishigi ba wannan yasa bata famu da sanin mutanen gidan ba banda ya hamad.
Yau ta kasance monday morning…
Tun wajen asuba data tashi bata koma ba take karatu, gudun kar mamanta ta tashi yasa ta wuce backyard ta zauna wajen kujerun dake wajen, dake ko’ina na gidan akwai haske kamar rana.
Bata tashi daga wajen ba har saida gari ya soma haske, ta koma daki ta
aje littafanta lokacin yan aikin gidan kowa ya rigada ya futo duk sun fara aiki, kallon inda hadiza ke kwance tayi, mayafin da take lulluba dashi sabeeha ta jawo mata ta rufa mata ganin ya yaye kafin ta futa.
Daga shugowarta hadiza taji motsinta ta farka,
tabi kofar data futa da ido, Sai a lokacin tayi ta tashi tayi sallah.
Sabeeha na shugowa kitcwhn ta gaisheda rabi da sauran waenda ta tadda a wajen sannan ta basu helping hand.
Ana gama breakfast suka soma fifitowa da avubuwan karin kumallo.
Su bilki
na gaba da warmers while sabeeha na biye da suka aje kafin su juya don sake kwaso sauran warmers din.
Adaidai lokacin nanna ta sauko kasan cikin shiri, bahijja ma ta sauko kasan, suka nufi dining.
Bilki dake kokarin komawa kitchen ce tace “sabeeha dan a
llah jera plates din bari na dauko flask”
Da toh kawai ta amsa ta tana kokarin jera plates din su nanna suka karaso.
Tana ganin isowarsu tayi saurin rissinawa tace “ina kwana nanna”
Murmushi nanna tayi tana mai dubanta tace “lafiya kalau fatima, daga ta
yani kwana kika gudu kuma,”
Dan dagowa sabeeha tayi tana dan murmusa tace “anty rabi ce tace na dawo kasa”
“Toh ay shiknan, kwana biyu da ba’ayi min tausa ba sai naji kafar na min zugi kuwa”
Sunkuyar dakai saveeha tayi tace “in muka dawo daga school zan
zo nayi maki”
“Toh allah ya kaimu, allah ya bada sa’a”
Nanna na rufe baki bahijja data zuba ma sabeeha ido ta kasa daukewa tace
“Ina muka samu yarinya haka”
Dan kallonta sabeeha tayi kafin tayi saurin rissinawa har kasa cikin ladabi tace “ina kwana ha
jiya”
“Lpy kalau”
“Yar hadiza ce ay,fatima sunanta” nanna ta bata amsa.
“Wata hadiza kenan nanna?”
Sabeeha najin sun fara magana bayan sun nufu mazauni tayi saurin juyawa ta wuce kitchen.
“Hadizar dai wadda kuka taso tare tar wajen inna mai aiki”
Zar
o ido bahijja tayi da mamaki tace “hadiza dai?”
“Itafa rayuwa dai sai godiyar allah, innar ma ta rasu, ashe anan bayan gari suke zauna cikin ikon allah kawai sukazo bikin sufyan,“
Girgiza kai tayi da mamaki bayan ta gama sauraron.
Sallamar taj tasa suka
juyo gaba dayansu, nanna ta sauke murmushin su na manya, anty bahijja tace “oh rabona dakai tun ranar birthday nanna,” da turanci tayi magana wannan yasa ya danyi murmushi har hakoransa na futowa yace “good morning a natse, “morning how are you”
“Hamdull
ah!!” Ya bata amsa tare da karasawa wajen nannna suka gaisa ta tambayeshi how was his night.
Yauma nanna ce tayi serving dinshi bahijja na kallon abun gwanin ban sha’awa, sai suka burgeta sosai.
Saukowa ta soma yi daga bene hannunta rike da wayanta sai
jakarta, gaba daya hankalinta na kan waya wannan yasa bata lura da waenda ke dining ba.
“Baby kin sauko” bahijja tayi magana.
“Yes mummy, good morning!!”
“Morning dear,”
Dagowa tayi karaf idanunta ya sauka kanshi, yana gefen nanna, yauma yana sanye da
jallabiya, gashin kanta ya kwanta lub kamar na jariri, ta kasa dauke idanunta.
“Maya..come have a sit”
Nanna tayi magana, tayi firgigi ta kalleta “good morning nanna”
“Morning” ta amsa ta
Jan kujera tayi daidai da inda yake, tunda ta jaraso bai dagoba
balle tasa ran ya kalleta, yanada wani irin kwarjini, haka nan tana ganinshi komai ke kulle mata.
“Baki gaida uncle taj ba” bahijja tayi magana tana kallonta ganin irin kallon da take mashi.
Muryanta ba karyewa tace “good morning uncle taj”
Kallo daya
ya mata ya kauda idanunshi tare da dauka glass of orange juice dake gabanshi kamar baison magana yace “morning..” kai tsaye.
Wallagi jintayi kamar an tsundumata a aljanna, muryanshi akwai dadin gaske.
Yauma dai ba wani cin kirki tayi ba don gaba daya
hankalinta ta tattara zuwa gareshi kamar mayya, shiko baima san da ruwanta ba a wajen kamar she doesn’t exist gaba daya.
Wayanshi daketa faman vibration a gefen table daya aje ne ya kalla ganin sunan dake kiransa, tunda yaga kiran merk babu qaqqautawa yas
an akwai matsala wannan yasa yayi excusing kanshi ya miqe nanna ta bishi da kallo, yana tashi ko minti biyu batayi ba itama ta miqe, “mummy byee”
Ta futa, “allah ya tsare ta amsa ta.
Gaba daya daga main sitting room ya futa zuwaga harabar wajen shugowa c
ikin gidan don a tsayen nan yana hango motocin gidan dake surrounding din wajen shugowa, da alamu ma fita za ayi da motar.
Wayar ya daga tare da kaiwa kunnenshi, maya dake sauri sauri ta karaso inda yake tanajin yanda yake zuba turanci tabi bayanshi da ka
llo, hes so huge, kai yana burgeta, wani irin kamshi yake mai dadi gaske, ya wani irin saka hannunshi daya cikin aljihun jallabiyan, daya kuma ya kai wajen kunneshi, ga slippers din kafafunshi sun karbeshi sosai saboda hasken fatarsa.
Kai dole ma tasan ya
nda zqtayi ta zama so close to uncle taj, he doesn’t seem friendly amma duk yanda zatayi saitasan yanda tayi ta zama close to him.
Ta gefenshi ta raba kamar zata wuce saita juyo fuskanta dauke da murmushi tace “bye uncle”
Shi bai kalleta ba shi bai amsa
wayar da ake mashi ba saima kurama waje daya idanu dayayi.
Daga chan nesa kuwa sabeeha data biyo ta bayan backyard, direct ta wuce wajen mota, ta bama inda yake tsaye da maya baya, a daidai lokacin data juya allah ya bashi ikon kallon direction din wajen
saidai kuma side viewdinta kawai ya gani kafin ta juya baya tana sanye da abaya baqa tayi rolling kanta da mayafin.
Gaba daya tunda ya zuba ma wajen idanu ya kasa daukewa kamar wani wanda ke nazari yana calculating abu, height dunta exactly irin na sab
eeha harda jikin ma.
Maya na ganin inda yake kallo kamarma baisan tana magana ba taji wani irin maqoqon abu a zuciyar ta.
“Are there? Hello sir” maganar da akayi daga wayar ne yasashi maida hankali a wayar yace “yes yes go ahead”
Jiki a mace maya ta
wuce wajen motar, daidai nan hamad ya karaso tare laila, sabeeha dake tsaye jikin motar wajen budewar baya tana jiran isowar su batayi auni ba kawai taji an wani tureta gefe an bude motar, har littafanta na watsewa a kasa.
“Excuse me!!!” Maya tayi magana
tare da banko kofar, hamad bai lura dasu ba don sauri yakeyi don ya samu ya saukesu.
Tunda ya aje wayar da yayi da merk ya koma ciki nanna tace ya je ya shirya zasu fita tare da ita.
It was a pleasant day for him, nanna tayi driving motar suka wuce har
office dinta, inda take gudanar da business dinta, tanada cute iffice da facilities sosai daman tana harkar interior,kuma da manyan companies take dealing idan an bata kwangila irinsu nnpc da hotels.
Sun dade sosai kafin yamma su dawo.
4 nayi hamad ya
zo daukansu tare da abal daya damu saiya biyosa.
Laila ce ta fara fitowa tana hango abal a tsaye bakin mota tace “ya hamad da wannan futsararran kukazo?”
“Ke ban girmeki ba kike cemin futsararre?”
“Waka girma din? Age dinmu daya”
“Kamata yayi ki dunga
gaisheni kina kirana da yaya tunda na fuki da 5months”
“Wallahi karya ne mami tace shekarunmu daya ao don’t feel like your head is big”
Daidai nan maya ta karaso, abal ya kalleta kafin yace “hey!!! Ashe kin dawo nigeria da zama? Lol how do you cope?”
Wa
ni irin kallo ta mashi kafin tace “what sort of a question is that? Do i look depressed to you?”
Abal najin haka yasan daman mai hali ay baya chanza halinsa, tun tuni daman yar masufa ce tun suna yara, shiyasa baya ma shiga har karta.
“Nawa for you…” ta
fada yana galla mata harara.
Tsaki tayi ta bude kofar baya ta shiga, sabeeha daketa faman sauri sauri har tana haki ta iso itama, “salam! Ina wuni ya hamad”
Ganin yanda take panting yasa hamad cewa “wa alaiki salam, why are you panting”
“Inata sauri n
e karna bata maka lokaci” ta bashi amsa a natse babu hayaniya, abal ya zuba mata idanu sosai yace “ya hamad who’s that?”
Ko kallonshi baiba yace “get in”
Bude gaba abal yayi wannan yasa sabeeha tsayawa sarere ta rasa ya zatayi, saida taji horning yasa ta
saurin bude baya batama san maya ce a ta wajen ba tana bude wa ta bita da wani makirin kallo kamar a kusa take da ita tace “are you mad??? Badai tunanin zama tare damu kike ba?”
“Fatima get inn!!!” Hamad ya bata umarnin haka
“Ya hamad wallahi wannan qaz
amiyar yar aikin bazata zauna kusa dani ba saidai ta nemi abun hawa”
“Saidai ke ki sauka ki nemi abun hawan, don’t waste my time”
“Wallahi bazata zauna a bayan nan ba, munafuka kawai kina wani sunne kai kamar wata ta Allah”
A fusace ya juyo kamar zai ma
keta yace “don’t you ever insult her again, in kika sake sai ranki yayi mugun baci”
Dake bata da kunya kuma ba sanin darajar babba take ba wannan yasa ta cewa “wallahil azeem bazqta zauja a baya ba,who is she not be insulted? Ba yar aikin bace? Yar wanke
wanke”
Ay baisan sanda ya futo ba rau a bace ya bude seat din baya da take zaune yace “get outttttt, fita min a mota”
Jikin maya har tsuma yake tsabar masifa, ya dizgata gaban yar aiki, “bazan futa ba, wallahil azeem bazan futa ba akan wannan abar zaka s
ani na sauka a mota? Motar ta ubanta ce?“
Hannu ya daga zai kwasheta da mari laila tayi aaurin interfeing tace “yaya dan allah kayi hakuri, hannunshi gar karkarwa yake tsabar bacin rai,
“Ay wallahi idan ka mareni saina rama” kiri kiri fa take magana a g
abanshi kamar wani sa’anta kai yarinyar nan batada kunya sam sam, very disrespectful,
“Yaya bari na futo na zauna a bayan tare dasu”
“No karka sake ka futo,” hakad ya fada yana kallonshi, kafin ya maida dubanshi ga maya yace “ke motan na ubanki ne?”
“N
i ka zaga saboda wannan?”
“In ya making zafi zaki iya futa, find your way home”
Ay ko yana rufe baki ta bude kkfar ta futo rai a bace ya kalli sabeeha babu wasa yace “shiga”
Jiki na bari ta shiga fa zauna inda maya ta tashi, suka wuce, akan idanun maya
ta shiga motar ta zauna a seat dinta.
Suna barin wajen maya ta zaro wayarta tayi dialing number mummynta.
Bahijja dake tare da fadila suna hira tana ganin call din mayar ta dauka taka dauka ko sun dawo ne bata ganta ba,“ yes babu…”
“Mummy……..”
Miqewa b
ahijja tayi tana sauraron wayar nata tace “calm down ki fada min menene kukan me kikeyi?”
“Mummy na fada maki basa sona, kowa baya sona ni bansan mey nayi masu ba, ya hamad,sun tafi sun barni anan saboda yar aikin nan, har marina saida yayi, wai na fita a
mota na nemi mai kawoni”
“Shi hamad dinne ya mareki?”
“Eh, sun barni a school babu kowa, mummy tsun tsaneni kowa na gidan nan, marina yayi wai na fita a mota tund aba motar ubana bane”
ta karashe tana fashe wa da kuka ta katse wayar.
Kiran duniya bahi
jja tayi mata wayar a kashe tuni hankalinta ya tashi.
Fadila data lura tace menene “wai hamad ne ya barta a schoo ita dayal”
“ hamad din?”
Ay bata tsaya saurarobta ba ta miqe tace “bari naje school din”
Futowa tayi tasa cikin drivers ya dauketa suka
wuce school dinsu gaba daya hankalinta a tashe.
After few minutes da futarta saiga su hamad sun dawo, gaba daya daga laila har sabeeha da abal jikinsu duk yayi la’asar gaba dayansu.
Hanad ko hes fed up with her drama da rainin ta wannan yasa yayi magani
nta, gaba daya futoqa sukayi ya rage hamad dinne kawai sai sabeeha data kasa tafiya ta tsaya ya futo.
“Ya hamad dan allah kayi hkuri mu koma a daukota”
Yanda take magana jikinta na bari yasashi gane cewa a tsorace take
“Go inside i will get her back”
W
ani irin ajiyar zuciya ta sauke badon san rabta ba ta shiga ciki.
Wayarshi dake ringing ya dauka ganin sunan mamin shi, yana dagawa ta sima fada “kai kana ina? Me kayi ma maya? Meysa ka barta a school eh?
Haka fadila ta soma balbaleshi da fada sosai ba
tama tsaya sauraronsa ba, karshe ma dayaqi kulata kashe wayar tayi.
Kalamanta na karshe yasashi shiga motar ya futa daga gidan, wallahi badan mami ba bazai dauko ba yau dinnan saidai tasan yanda zatayi.
Bahijja na zuwa school ta samu mayar zaune a gefe
n school entrance kai kace wata abar tausayi ce, tayi jabe jabe da hawaye.
Jikin bahijja har rawa yake, tana kaunar yarta kamar me shiyasa ko kukanta batason jin ko kadan ita kadaice allah ya basu, kaunar da take mata babu measures.
Tsakanin da uwa sai
Allah, harga allah bahijja taji zafin abunda hamad yayi na barin mayar, saita fara tunanin toh kodai bason zaman mayar ake a gidan ba, tun ba yanxu ba tasan anne bason mahaifin mayar take ba, har lokacin tana tsoron kar avun ya shafi yar tata, sai yanxu ta
ke ganin abun kamar haka ne, ba sau daya ba ba sau biyu ba maya ke kira ta tana complain ba a sonta a gidan an takura mata.
Koda suka shugo gida gaba daya kowa na zazzaune a sitting room, fadilana gefe babu abunda take sai harara hamad din don anne tasa
shi ya dawo gida tunda bayijja ta tafi daukota, kuma kiri kiri anne ta hana fadial ta mashi fada har suka iso.
Maya na ganin kowa a zazzaune harda anne take tasha jinin jikinta.
Da ta wani maqale bahijja gwanin ban tausayi kai kace yankata akayi aka wats
ar.
Zama sukayi anne ta dubi hamad tace “babana meysa ka barta a school?, nasan haka kawai bazaka barta ba tunda kaina bama jagorancin kula dasu da harkar makarantarsu.”
Sunkuyar da kanshi yayi ya kasa dagowa yana jin kunyar anty bahijja sosai, sai yaji
dama bai barta ba wallahi.
“I’m sorry raina ne ya baci hakan bazata sake faruwa ba”
Anne tace “tayi maka rashin kunya ne?”
Bai bada amsa ba yayi shuru kawai anne ta kalli mayar babu wasa tace “kinyi mashi rashin kunya ne?”
Kukan munafurci ta fara “ni b
an mashi rashin kunya ba, kawai sabd nace fatima bazata zauna inda nake zaune ba shine yace na sauka tunda ba moton ubana bane” ta karashe harda share kwalla.
Laila datayi tsuru anne ta kalla tace “ke me tayi mashi?”
Yanda anne ke tambayr me maya ta ma
shi ba tare da sauraron abubuwan da ya fada ma mayan ba yasa bahijja jin babu dadi.
“Mun shiga mota ne sai yaya yace fatima ta koma baya saboda abal na zaune a gaba shine maya tace bazata zauna damu ba,”
Dan dakatawa tayi ganin irin kallon da maya ke mat
a kafin ta cigaba, “maya was insulting towards sabeeha tace wai ita dake yar aiki bazata zauna damu ba tunda ba ubanta ya saya motan ba, shine yaya yace karta sake zaginta..shine shine…”
Ta kasa karasawa anne ta sauke ajiyar zuciya tace “a gidan nan ba’a
goranta ma na kasa damu, bama wulaqanta wanda ke hidima damu, idan yar wanke wanke ce itama iyaye ne suka haifeta,ni nasan haka kawai hamad bazaice ta sauka motar nan ba, ga abunda tayi nan,ninasa yarinyar nan tana binku makaranta don itama yace kamar kowa
anan, don bata da gata bashine ya baki liberty din yi mata gori ba, karna sake jin haka, karna sake.. this should be the last time da zan sake jin haka”
Maya ta fashe ta kuka sosai ta shiga jikin mamanta bahijja ta rukota zuciyanta na mata daci, judgemen
t din bai mata dadi ba ganin yanda mayar ke kuka.
“Amma anne ba laifi bane dan tace bazata zauna da yarinyar ba, tunda su yan gi…”
Wani irin kallo anne ta mata dayasa ta rufe bakinta kawai, anne ta miqe rai a bace ta wuce sama.
Fadial ta kalli hamad tac
e “kai kuma wani iri babba ne? Are not supposed to protect them? Ka bani kunya”
Tana cikin yi mashi fada bahijja ta miqe da maya suka wuce sama, fadila saitaji babu dadi kwata kwata, bahijja akwai son yaya kamar me, bataga laifinta ba tunda maya kawai al
lah ya basu.
Suna hawa sama bahijja ta danna ma majid waya, ta insa take hawa ba tanan take sauka ba, daman tund amayar ta dawo shi take blaming don shine ya turo ta don yayi punishing dinta.
Tun daga ranar maya ta kullaci sabeeha sosai aranta