Showing 18001 words to 21000 words out of 338813 words

Chapter 7 - MATAR TAJ COMPLETE

yana buqatar hakan

Akwai neurologist specialist din dake managing health dinshi, saboda haka inason a sallameshi”

Dan dole doctor ya amince, aka bashi Referall sannan yayi discharging di

nshi.

Sai a lokacin hankalinta ya kwanta ta fito, tana futowa ta nufi dakin da aka kwantar da taj din, har zuwa lokacin yana kwance ya dafe kanshi, bashida natuswa kwata kwata, sabeeha na ganinta kawai taji gabanta ya sake faduwa, tsoronta daya allah ya

sa ba wata qulalliyar ta qulla ba, karasowa hidayar tayi ta tsaya gabanshu tace “big baby! Muje gida”

Yana jin muryar hidaya ya miqe zaune dukda kanshi na mashi ciwo, cikin izza da sautin muryarshi mai dadin sauraro calmly yace “where’s my car keys?”

Shu

ru hidaya tayi ta daburce ganin ya kafeta da idanu, “lets go with my car”

Da taimakon hidayar ya miqe tsaye, daidai nan idanunshi ya sauka kan sabeeha itama idanunta ya shige cikin nashi, ganin yana kallon sabeehar har zaiyi magana hidaya ta dakatar dashi

“muje”

Sabeeha najin haka ta biyo bayan su suka wuce parking lot inda hidaya tayi parking.

Hidaya ce ta bude mashi seat din gaba ya shige, sabeeha kuma ta shige seat din baya ita kuma hidaya ta zauna mazaunin driver, babu yanda ta iya dan dole ta umarci

sabeeha ta biyosu don tasan tabbas saiya tambayi ko wacece ita bayan wannan ma dole yanxu she has to pretend saboda karya fuskanci komai.

Tunda sukabar asibiti Tsit kake ji a cikin motar, hidaya dai har zuwa lokacin ta kasa wrapping mind dinta, fadin i

rin tashin hankalin da take ciki ma bata lokaci ne, mafita kawai take nema, abun yazo mata a daidai lokacin da bata taba tsammani ba, sai a yanxu take dana sanin qin bin shawarar fadwa, abunda ke bata confidence daya ne ganin kamar bai tuna komai ba, saida

i damuwarta daya ayanxu what if ya tuna ranar da accident din daya jawo mashi lossing memory for a year? Inaa bazata taba barin haka ba, dole she has to do koma menene don ganin bai tuna ba, she won’t allow him to remember that, idan ya tuna shikenan komai

ya wargaje, bazatayi moulding dinshi yanda ta saba ba bayan wannan ma zatayi lossing yardar dayake mata for over those years, yama za ayi ta bari ya gane she’s behind all of this? No never, she will never allow that, he trusted her all his life, itace kom

ai nashi, baya tsallake maganarta kuma bai taba ba koda sau daya ne kaf rayuwarshi, kuma ayanxu ma for the second time thats what she’s going to use.

Sabeeha dake zaune abubuwa da dama ke yawo a kwakwalwarta, sai ayanxu tunanin mutabb yazo ranta, ayanda

taji wajen likitan dayayi attending dinsu ya shaida mata su biyu kawai aka kawo asibitin, fatanta allah yasa ba wani mugun abu ne ya sameshi ba.

Bayan wannan ta soma tunanin meysa ake binsu a baya kuma akeson kashesu? Su waye suke binsu a baya? Ko hidaya

ta gano waye mutalib? Ita kadaice kawai tazo ran sabeeha a daidai wannan lokacin, kuma tasan itace ke nemansa, don mutabblib din ya fada mata da kanshi, gaba daya ta dauka mutuwa zasuyi data tuna yanda truck dinnan tayo kansu sai kawai ta runtse idanunta

tunawa da yanda taj ya damqo hannunta a lokacin harya furta allahumma ajirninfee musibati, tabbas a daidai wannan lokacin ya soma dawowa hayyacinshi don bata taba jin yayi addua neman tsari ba, ko yayi magana irin ta masu hankali ba.

Tama rasa me zataji a

ranta, dadin dawowa hayyacinshi ko akasin haka?

Tana cikin wannan tunanin ta dago da kanta ta kalleshi, gashi dai taj din data sani ne amma yanxu sai takejin kamar bashi ba, saiya sauya mata lokaci guda kamar bashi ba, wani irin kwarjini da haiba take ga

ni a tattare dashi, har zuwa lokacin idanunshi a rufe yayi relaxing akan kujerar gaba har suka karaso gida, da kafarshi ya fito daga cikin motar hidayar, yana fitowa yabi gidan da kallo, its feel strange to him sai yake jin kamar ya dade bai shugo gidan ba

, zagayowa inda yake hidaya tayi tace “muje”

Gaba yayi hidaya na bunshi a baya,sabeeha ma ta mara masu baya.

Harya daga kafarshi zai shiga sai kawai ya dakata,hidaya fa gaba daya hankalinta a tashe yake yanxu da duk wani motsinsa, ganin yaqi motsawa da

ga inda yake yasa tace “muje ka huta”

Ta kama hannunshi suka shige daga ciki, suna shiga ya fara bin gidan da kallo, suna karasowa sitting room suka tadda ammu da tareeq da fadwa a zaune, sun sakata gaba suna sauraron labarin warkewar da taj din da yayi l

okaci guda.

Ammu na ganin shugowarsu tayi saurin miqewa dukda tana jimamin mutuwar mijinta hakan baisata yi guda ba ta karaso insa yake ta rungumeshi sai hawaye, “allahu akbar allahu akbar, ina godiya ga Allah, oh my sweet boy you’re back? You remember

me? Ka tuna ni?ashe dai zuwana yayi albarka, masha Allah yanxu hankalina zai kwanta,” ta karashe tana hawaye, taffin

hannayenta na kan fuskanshi tana shafashi kamar yau ta fara ganinshi tsabar murna.

Da mamaki yake kallonta yana kallon su fadwa dake kal

lonshi harda tareeq, dukkansu ba karamin tashin hankali suke ciki ba, fadwa da hidaya sai kallon juna sukeyi kamar wasu munafukai.

Dakyar ya dake dukda yana jin zafi aranshi gashi ya zama so confuse da alamarin ya Dan rankwafo ya Rungume ammu tsam a jik

inshi yana dabbing bayanta,cikin natsuwa da muryarshi mai daukan hankali yace “how can i forget you my fav aunt,I’m sorry for making you worried “

Kallonshi ammu tayi hawayen farin ciki na sauka kan fuskanta tace “tell me meke damunka yanxu? What are fee

ling now? Are you okay?babu abunda ke damunka?”

“I’m fine ammu”

Fadwa datayi tsuru ta kasa motsawa saida tareeq ya tabo ta ta kalli taj din ta soma yaqe, tace “alhamdulillah! How are you feeling now? We were so worried about you,”

Dagowa yayi yanayin

fuskanshi lokaci guda ya sauya ganinta da yayi kawai kamar baya son magana yace, “I’m okay now!”

Kauda idonta tayi ganin irin kallon daya mata,sai yanxu ta kara tabbatar da yayi recovering, idan zaima kowa magana ko zai amsa mutun haka yake banda hidaya,

shiyasa suke mashi kallon mai ji dakai da nuna isa dukda qani ne a wajensu, kwarjini yakema kowa.

Tareeq ma baiyi shuru ba hardashi a masu nuna murnar samun lafiyar tashi a fili.

Shidai taj haka yabisu don harga allah baisan akan me suke magana ba ka

wai dai ya bisu a haka ne, kanshi fal yake da neman amsoshin tambayoyin da ke ranshi.

Ammu ce ta sake kallonshi har lokacin bata bar mamakin ganin ya samu sauqi ba compare to last time datazo lokacin mutuwar khaal, lokaci guda ya sauya kamar bashi ba, d

a yana daga tsaye sai ya dunga dariya yana wasu abubuwa kamar na yara, lokaci guda kuka ya dawo asalin taj din da suka sani shekara da shekru,sai kawia ta sake fashewa da hawaye tunaw ada yanda khaal ya damu dashi sosai, kusan kullum saiya kirata kafin ya

rasu, bashida magana saita taj, ita ce shaidar aon da khaal kema taj, ya shiga damuwa sosai lokacin da taj din ya samu amnesia ya manta komai ya manta koshi waye ma gaba daya.

“How i wish khaal na tare damu, he will be so happy to see your recovery”

Tund

a ta fara magana taj ke kallonta, bai gane inda maganar tata ta dosa ba, Hidaya kuwa na jin ammu na shirin baro mata aiki ba zato ba tsammani tayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa “mu barshi ya huta tukunna, daga baya sai muyi maganar”

“Kaje ka huta”

hidaya ta umarceshi.

Hanyar stair ya nufa cikin natsuwa majestically suka bishi da kallo, har yakai sama ya jiyo muryar ammu na magana, “jeki taimaka mashi mana”

Ta kalli sabeeha dake tsaye , hidaya ce tayi saurin dakatar da ita tace “ammu, please mu b

arshi, he’s having a tough time now, yana buqatar time shi kadai, and beside doctor yace kar a dunga damunsa”

Kallon hidayar ammu tayi sai kawai ta kauda kanta gefe ta wuce part dinta da take sauka nan kasa kusa dana su afiya, haushinta takeji sosai tun

lokacin mutuwar khaal na qin protecting iyalan khaal din datayi lokacin da aka kwace property dinshi da yanda tayi outcasting dinshi harda press conference dinnan datayi, wannan abun ya tsaya mata arai, wannan yana daya daga cikin abunda yasa ammu taji ak

wai matsala kuma akwai avunda ke faruwa a gidan wanda bata sani ba kuma khaal bai taba gaya mata ba.

Ammu na wucewa su fadwa ma suka bar parlorn ya rage daga sabeeha sai hidaya, kallon sabeeha hidaya tayi yanayin fuskanta ya sauya sosai tace “as for you

, as you can see baisan koke wacece ba, he doesn’t remember who you are cause you’re not important, koda wasa let me not see you around him not a single word from you”

Takowa tayi inda sabeehar ke tsaye hidaya tayi kafin ta kure ta da idanu fuskar nan bab

u digon imani akai tace “its not like he will be happy to have you as a wife, you are nothing but his caregiver, sannan karkiyi tuannin bansan yanda kika shugo gidannan ba a matsayin yar leken asiri, korar daga gidannan shine avu mafi sauqi, idan kinason n

a barki ki zauna a gidan nan you have to do what ever i said to you, inba haka ba i will make your life miserable, let me give you a sounding warning,not a single word from you, koda wasa naga kin rabe shi, I’m going to do my worst”

Shuru sabeeha tayi sai

da ta gama sauraronta tass, gabanta na mugun bugu, haka ta dake ta bude bakinta tana kallon hidayar cikin idanu babu tsoro ko fargabarta ko digo tace “kina tsoron karna fada mashi rayuwar da yayi a gidan nan lokacin da baya cikin hayyacinshi? ki kwantar da

hankalinki, bazan fada mashi komai ba, saidai inason ki sani allah baya barci yana kallon duk abunda ke faruwa, yanda ya dawo hayyacinshi lokaci guda alokacin da babu wanda yayi tsammanin haka, a sannu a hankali zai tuna komai, its just a matter of time d

uk karyar da zaki fada mashi bazatayi tasiri ba saboda karya fure take bata yaya,i dont care if ya karbeni a matsayin matarsa, all i know is that I’m his wife and no one can change that”

Tana kaiwa nan tabar inda hidayar ke tsaye ta nufi part din data tab

a zama a ciki, lokacin sa jamid ya kaita, daman ba tun yanxu ba take shanye duk rashin mutuncin da hidaya keyi, haka kawai taji lokaci guda wani confidence yazo mata, daman tana threatening dinta da taj dinne, tsoron kartayi mashi wani abu yasa take yin sh

uru bata cewa komai kuma bata iya tunkararta, tundaga ranar da mutallib ya fada mata cewa hidaya ce sanadin accident din taj da abubuwan data dunga yi donta cutar dashi da kwayar data dunga dura mashi wadda ta kusa illatashi tundaga ranar ta daina jin tsor

anta gaba daya kuma tayi allawarin saitayi protecting dinshi, tsoron hidayar babu abunda zai haifar mata saidai yayi ta bata damar yin abunda taga dama, yanxu kuwa data tabbatar ya samu lafiya batajin hidayar zata iya yin wani abun,ada datayi ma don taga b

ashi cikin hayyacinshi ne yanxu kuwa abunda take mai hankali bazai dauka ba, ko kusa ma bazata iya kokarin citar dashi ba ayanxu.

Tunda ta fara magana har yakai aya har tabar wajen hidaya bata gama dawowa daidai ba mamaki ya gama cikata, Ai kamar ta bug

ama hidaya guduma akai Haka taji, Saqe tayi tama kasa yin komai, bata taba expecting haka daga wajen sabeehar ba…

***

Bangaren taj jiki a mace ya shugo part dinshi yabi ko’ina da kallo, komai na part din nashi ya sauya, kamar anyi refurnishing komai,

komai looks weird to him, ga kanshi sai wani tsannain ciwo yake mashi sosai, bayason tunanin komai don da zarar ya fara tunanin yakeji kanshi na sarawa.



Abund aya lura dashi shine, duk yanda akayi wani abu ya faru dashi, ko yayi loosing memory dinshi

ko kuma he was in coma, definitely akwai abund aya sameshi, don babu yanda za ayi ace rana daya kawai ya bude idanunshi ya ganshi a 2023, how is that possible, he can recall is bayan ya dawo daga london, ko sati gida baiyi ba koma menene ya faru dashi.

Da

kyar ya lalaba kanshi ya wuce bedroom dinsa yanajin wani irin zafia ranshi ya rasa dalilin, dakin ya shige nan ma an sauya komai, duk wasu abubuwan shi na amfani babu.

Idnaunshi ne ya sauka kan gadonshi, kamar mai son tuna wani chan kuma ya kauda idanuns

hi ya sauke Sigh of relief gaba daya jikinshi ciwo yake mashi babu abunda yake nema sai shower, kai tsaye ya nufi kofar bathroom dinshi ya bude, kallon bathroom din yayi har idnaunshi ya sauka kan towels din dake rataye guda biyu, yellow da white, juyawan

da zaiyi idanunshi ya sauka kan panties dake hange akan hangers, yayi mamaki sosai ganin panties din saiya fara tunanin kodai wani yayi mashi amfani da part dinshi? To ko hes mistaken ba nan ne part dinshi ba? Ko anyi re-arranging gidan ne?” Tambayoyin da

ya dunga ma kanshi kenan.

Basar da zancen yayi ya soma rage kayan jikinshi, farar fatarshi ta bayyana sosai, kallon kanshi ya dunga yi ta mirror, ya rame sosai, he feels so light, sai yake ganin kanshi kamar bashi ba.

Ya dade sosai a bathroom yayi wanka

kafin ya fito daure da towel a kugunshi, kasa dauke idanuna nayi akanshi, gaba daya ya sauya kamar bashi ba, lallai hankali ke gani badai idanu ba, yanxu da hankalishi ya dawo jikinshi ya koma mutum completely.

closet room ya nufa yana shiga ya bude c

loset din,gaba daya babu kayanshi ko digo daya, sai set of kaya ne farare a jere a ciki sai kuma kayan mata daya gani daga gefe a Jere fess fess sai kamshi suke mai dadin gaske.

Mamaki ya dunga yi har zuwa lokacin, tsuka kawai yayi ya rufe closet din kawa

i ya futo ya wuce bedroom din ya kwanta….



💋

BOSS LADIES WRITERS

💋



MATAR TAJ (destined with you

🩵🤍

)

Written by

Queenmarh





Book2

PAID

Chapter 61

UPDATE!!!

Jiki a mace sabeeha ta shiga dakin ta na qasa, yana nan yanda y

ake babu abunda ya sauya fes fess, bin ko'ina ta soma yi da kallon ta tuna tarin abubuwa da dama, kamar yau akayi, ranar da suka tuhumeta da sata ne ya

fado mata arai, badan jamid ba da tuni sun wulaqantata, allah kdai yasan abunda hidaya zatayi mata badan

jamid ya taimaketa ba a wajen, take tausayinsa ya mamaye zuciyarta, bawan allah, yanxu da zaiji labarin taj ya samu sauqi tasan ba karamin dadi zaiji ba, musamman khaal,

''ya allah ka gafartawa wannan bawa naka, allah sarki, nasan da zaiga rana irin ta y

au sai yafi kowa farin ciki, harya mutu bashida burin daya wuce yaga didi ya samu sauqi'' tana karashewa ta fashe da kuka, kuka sosai sabeeha ta dunga yi, harga allah deep down taji dadi sosai ganin taj din ya warke, tashin hankalinta daya yanxu data lura

dukda ya dawo hayyacinci bai tuna abubuwan da suka faru ba lokacin da yake rashin lafiyar kamarma baisan meya faru dashi ba watannin da suka wuce, wannan yasa ta daura damarar duk yanda zatayi saitayi don ta taimaka mashi harya gano gaskia, threat din hida

ya bazaisa tayi qasa a gwiwa ba, indai tana matsayin matarshi protecting dinshi yanxu ta fara ma.

kwana tayi tana salloli tare da godiya ga allah sai wuraren bayan sallar asuba ta samu ta kwanta.

shima taj din sai wuraren karfe biyu ya farka na dare da

matsanancin ciwon kai,gaba daya sai yaji dakin ya mashi fadi sosai, a jikinshi yanajin kamar something is missing wanda ya kasa gano ko menene, kwata kwata baima san time din lokacin ba saboda babu waya a kusa dashi, har zuwa lokacin towel ne a kugunshi,

miqewa kawai yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala bayan ya idar ya kafama fuskarshi idanu, yana tambayar kanshi how did he loose so much weight haka, wani irin rashin lafiya yayi haka?, rashin amsar tambayoyinshi yasa yabar zancen a zuciyarshi kawai ya f

ito ya wuce closet room, cikin riga da wandunan daya gani fararen nan ya dauka daya daga ciki ya saka sannan ya futo ya wuce bedroom din ya hau kan carpet ya tada kabbara.

tunda ya tada kabbbar na natsu ina sauraron qira'arshi, lafazinsa akwai dadin saura

ron cikin kamala da natsuwa, ya dade sosai yana sallolin yana rokon allah.

Yana idarwa kamar da wasa yarinyar nan daya fara gani dazu ta fado mashi arai, yanda take mashi magana da yanda take kamo fuskarshi kamar wani sa'anta, shi mai irin yanayinta ma ba

i taba gani ba gaba daya rayuwarshi, balle kuma fuskarta, curiosity din da yake ciki yasa komai ya soma bashi haushi haka kawai ranshi ya fara bashi.

Amnesia memory loss-mutun na samun amnesia ta hanyoyi daban daban, daya daga ciki shine accident din da

ya jawo buguwa akai wanda hakan ke affecting ma'ajiyar kwakwalwa, inda mutun ke manta abubuwan daya faru a cikin rayuwarsa na yan lokaci, wasu yakan zame masu har abada basa iya tunawa da rayuwar su a baya saidai su dasa wata, wannan amnesia din yana janyo

wa wasu su zamto sun manta rayuwarsu daga lokacin da suka girma sai ya zamana sun dawo kamar kananun yara masu koyon abubuwa (dissociative amnesia), wasu daga cikin mutane idan suka warke lokaci guda suke tunawa da komai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login