Showing 198001 words to 201000 words out of 338813 words

Chapter 67 - MATAR TAJ COMPLETE

/>
Firgigi ta dawo daga dogo

n tunanin data fada, “naam”

“How was your exams?”

“Alhamdulillah” tana fadin haka ta maida kanta ga glass window din mota ta cigaba da tunanin datakeyi.

…….

Da daddare rabi ta shigo part din anne da sallama ta gaida anne kafin ta soma mata bayani.

“Hajiya daman bilki ce tace kawunta ya kira zata koma kauyensu don an saka ranar bikinta nanda sati biyu”

“Toh Masha Allah shine basu fada da wuri ba”

“Eh wai itama batasan an badata bane, kisan auran kauye basa neman shawraar yayan tun suna kananu suke

bada auren su” rabi ta bata amsa cikin ladabi.

“Toh kice mata ta nace ta kira kawun nata yazo cikin satin nan kafin ta koma, karsu mata komai na kayan daki na dauki nauyin wannan”

Cikin murna rabi tace “toh allah ya saka da alkahiri hajiya allah ya buda



Ta amsa da ameen.

Rabi na barin wajen anne ta sami bilki ta fada mata komai, a take ko ta kira kawunta ta shaida mashi komai.

Washe gari da safe kowa ya hallara kan dining, anne, nanna, maya sai laila data kwana a part din nasu don sun shirya yanx

u ita da mutuniyar tata sai kuma hamad da shugowanshi kenan.

Karasowar taj yasa duk suka maida hankalinsu gareshi, maya da laila suka gaishesa, hamad ma haka shi kuma ya gaisheda nanna da anne kafin su fara karyawa.

Hira sukey jefi jefi kowa ya maida h

ankalinsa ga abuncin da yakeci banda maya data kureshi da ido, laila tana ankare da ita don ba tun yanxu ba ta lura da hakan.

Shine ma ya fara tashi ya futa bayan ya gama saboda kiranda salim ke mashi.

Nanna ga tambayeshi harya gana yace mata eh zai dan

futa ne, bata tambayeshi ina ba saboda yanxu kam ay ya san gari kuma yanada nashi privacy din avubuwa shiyasa bata tambayehsi ba ya futa.

Yana barin wajen maya ta sauke ajiyar zuciya, lailanta kalleta da mamaki.

Bayan sun gama dinner laila da maya na

zaune dakin maya laila ta kaleta tace “wai kallon nan da kikema uncle taj na menene?”

Kallonta maya tayi tace “is there a problem inna kalleshi?”

Dariya laila tayi tace “maya are you crushing on uncle taj? If you are kima ajeshi a gefe, he definitely ha

s someone”

Rai a bace maya ta kalleta laila na ganin haka tasan cewa maya has feelings for him.

“Shi yace maki he has someone??”

“Ke yanxu kina ganin yanda ya hadu ya gaji da haduwa, gashi mai kudi sosai kuma daga saudi yake saiki yarda idan akace maki

bashida wadda yakeso, balarabiya yar kasarsu?infact banajin akwai yar nigeria da zata iya zama on his league”

Cije lebe maya tayi har yana fashewa kadan jini ya futo lokaci guda yanayinta ya sauya, tace “karya ne wallahi, karya kikeyi banza dallah zoki fu

ta karki bata min rai”

Yanda take magana kamar zata hau kan laila, laila tayi saurin cewa “it looks like ba crushing kadai kike ba maya, badai son uncle taj kike ba? Don’t start dreaming what’s impossible don wallahi yafi karfinki”

Wannan magana da lai

la tayi mata kamar ta chaka mata wuqa a wuya haka takeji, rai a bace ta kalleta tace “you wanna bet on him?”

Laila najin haka tace “uncle taj din? Bafa yaro bane”

“You wanna bet on him or not? Don ni zan nuna maki cewa idan har inason abu saina sameshi n

o matter what, karkiga wai yana da kudi kuma halfcast ne wallahi i will make him fall for me, you wanna bet??”

Dariya sosai laila ta tunda yi tana kallonta tace “okay..lets see”

….

Bayan futarshi bai tsaya ko’ina ba sai inda zasu hadu da salim, daga n

an suka wuce inda zasuje.

Tun a mota salim ya soma mashi bayanin kananun agency din da yanda suke operating wajen, kuma a gaskia illegally suke shigar da mutane kasar waje don gaskia gomnati batasan da zamansu ba.

A tare suka shiga wajen, irin local agen

cy ne haka duk wani hanya da akeyi ta cuku cuku sunayinta, duk kasar da kake son zuwa don har visa sunayi ma.

Yara ko kauye kauye suke zuwa daukansu ana masu training akaisu wata kasar don aikatau.

Da farko masu kula da wajen kin basu hadin kai sukayi

saida salim ya basu maqudan kudade tukunna kafin su kaisu wajen ogansu.

Suna zuwa ba tare da wani bata lokaci ba suka mashi bayanı, kudi babu abunda baya saka mutun yi, koda suka bada sunanta da hotonta da kuma inda tayi aikatau da shekarar, a take mutumi

n yasa yaranshi suka fara bunciken yaran da suka tura saudiyya shekara biyu da suka wuce.

An samu fatima’s da yawa saidai kwata kwata babu mai kama da ita daga ciki, su da sukaga hoton sabeehar ma daya bayar sun dauka ko batan hanya yayi, suda suke kwaso

yan qauye, kowacce yarinya idan zasu turata saisun dauki hotonta, information din iyayenta, gudun samun matsala.

Har zasu bar wajen wani tunani yazo mashi, tunda yake nemanta da fatima yake amfani bai taba kawowa ko ba sunan take amfani dashi ba sai yanxu

da abun yayi clicking a mind dinshi, ya dubi salim yace su nemi idan akwi mai suna sabeeha.

Take salim ya fada masu suka fara dubawa, suna daga zaune yaron dake buncikowa ya shugo da file din mutun daya da aka samu da irin sunan, baisha wahalar samu ba s

aboda sunan is unique.

Da aka kawo file din saida gaban taj ya fadi, har sauri yake ya bude don ya tabbatar da ita dince, yana tabbatar da ita dince ya sauke wata ajiyar zuciya, duk yanda kamanninta ya banbanta da hoton daya nuna masu bai hana shi ganeta

ba, lokacin gaba dayanta babu cimar kirki a tattare da ita tayi wani irin baqi sosai, gashi dukda ta rufe bakinta saida gatson nan ya futo.

“She’s the one” ya fada beneath his breath, ya dubi salim yace su fada mashi inda zasu sameta yanxu yanxun nan, zai

basu ko nawa ne yanason su fada mashi komai game da ita.

Salim ya fada masu tare da ajiye masu kudade dayawa a gabansu.

Ogan dayaga kudade take yasa cikin yaronsa su nemo mashi yar wani gari ce, kuma ta dalilin waye aka kawota aikatau, masu daukosu su

nada yawa don kowanne gari akwai agent dinsu.

“Wannan yarinyar oga jamilu ne ya kawota”

“Wani jamilun?” Ogan ya tambaya.

“Jamilun dake dutsen habuja, yar dan uwansa ce”

Salim ne ya fasaara masa abunda sukace, sannan ya buqaci sanin inda zasuga jamilu,

ogan yace ay agent dinsu ne bari ma

Ya kira sa.

Yana kiran jamilu wajen saunuku bai dauka ba, taj ya buqaci address din jamilun ogan give su dawo zaisa jamilu yazo har office dunshi.

Taj baiso haka ba dan ya matsu sosai, yanajin kamar bazai iya jura

har zuwa gobe ba.

Suna barin wajen daya daga cikin agent din yayi saurin kiran jamilu, aiko yayi saurin dauka, daman jiran kiransa yake tundaya kirashi yace mashi karya amsa kiran oga, akwai matsala.

yana dauka ya fada mashi komai sannan ya shaida m

ashi yanda suka sakarma oga maqudan kudi don neman yarinyar dakyar inba matsala aka samu ba.

Daman gaba dayansu baki daya agent din harma da ogannin shiyasa suke tsaka tsantsan don business dinsu illegal ne.

Da farko jamilu shi harya mance da wata sabe

eha daya kawo agency din saidaga baya ya tunata yar hadiza kawar jamila matarshi, shifa gaba daya ya tsorata sosai jin ance masu kudi ne suka zo nemanta kuma harda balarabe saiyayi tunanin ko kisan kai tayi achan kasar ne ba a gano gaskia ba saida aka maid

ota nigeria,sai yanxu ake nemanta gashi ya shugarda sunansa a matsayin mariqinta.

Yana tsaka da buga bugarsa ya koma gida ya hau kan jamila da bala’i, “mun shiga uku jamila, yarinyar nan kisan kai tayi ake nemanta, ki kira uwarta wallahi tallahi babu ru

wanmu, ke kikace mu taimaka masu a turata aikatau, yanxu danace ni marikinta ne idan ba a ganta ba aka kamani fa?”

Kokarin kwantar mashi da hankali jamila tayi harda kwada mata mari, “me gida dan allah ka kwantar da hankalinka”

“Ina zan iya kwnatar d

a hankalina shin kinma san inda suke? Wallahi jamila idan kika sani matsala igiyar aurenki ce zata tsinke, haka kikasani muka aurar da ba tare da sanin uwar tata ba, muka cinye kudin da aka bamu yanxu idan wani tsoho ne fa aka aura mata gidan aikin nata ta

kasheshi ta gudo ba a sani ba sai yanxu? Shin kinma san inda uwar tata take kuwa? Idan hadiza ta gudu fa?”

Jamila na hawaye ta kalli mijin nata tace “wallahi mai gida zan nemota bazanma fada mata me ake ciki ba sainaje naga inda take”

“Toh wallahi talla

hi kiyi hanzarin zuwgobe goben nan ki shaida mata yauwa ehe”

Tana fadin haka ya fuce.

Jamila jiki na bari ta soma dialing layin hadiza tana dauka ta soma magana “hadiza akwai matsala..”

“Wace iriyar matsala jamila”

“Ki tura min adireshin ki gobe zanzo

muyi magana”

Hankali tashe hadiza tace “ki bari ni zanzo goben”

“Ah ah tunda nace maki ki bari zanzo kawai”

Da haka sukayi sallama.

Tunda taj ya koma gida gaba daya yaji ya kasa sukuni, ya rasa mai zaiji aranshi dadi ko rashinsa, zai iya fuskantarta

kuwa? Da wani ido zai iya ganinta? Gaba daya abun ya addabeshi ya kasa cin komai.

Misalin wajen karfe tara na dare nanna ta kirashi ganin ko dinner baizo yayi ba tunda ya fita da safe, daga yanda yake amsata ta gane kamar yana cikin damuwa, ta tambayeshi

ko baya jin dadi ya shiada mata yayi loosing appetite ne kawai and yayi dinner tare da abokinsa kafin ya dawo gida.

Hankalinta bai kwanta ba ta sashi yazo part dinta.

Dole ya shirya ya wuce main part, tunda ya shugo yakejin sautin kwanuka daga wajen din

ing da Alamu kamar tattara wajen akeyi, sai maganganu dake fitowa daga wajen,bai kalli wajenba ya tunkari hanyar stairs yana dora kafanshi kan stairs din farko ya tsaya chak

“Subhanallahi Ya akayi ya fashe?” Rabi data tunkaro wajen dining din tayi inter

rupting dinsu ,

maya data matsa gefe ta kalli rabi tace “ya kike kallona, ga wadda ta fasa nan saboda tana baqin cikin masu gida, tana bakin cikin ganin munaci da luxury plates bata taba ci akan irin plate dinba bari ta fasa dan mugun hali”

Sabeeha da

ranta ya gama baci ga baqaqen maganganun data gama gaya mata ta watsa mata juice a jiki da gangan dukdan saboda ta buqaci a dafo mata indomie ta dafo sau uku tana cewa baiyi dadi ba sai an sake shine sabeehar tace taje ta dafo yanda zai mata tana shirin b

arin inda take ta watso mata plate din da indomie din a kasa plate din ya fashe.

Dukawa tayi ta soma kwashe plate din rabi ta karaso inda take kasa kasa da murya tace

“Garin yaya kika fasa? Kina menene?”

Amsanta sabeeha tayi itama yanda daga ita sai r

abi ne zasuji tace.

“Wallahi anty rabi Itace ta fasa,”

“Barshi kije ki dauko tsintsiya karkiji ciwo a hannu”

Da toh ta amsata tare da nufar hanyar kitchen daidia nan ya karaso wajen dining din don tabbatar da muryar da yaji mai kama data sabeeha dayaji

a kunneshi.

Saidai kashh yana isowa wajen ta shige kitchen sai dan glance din bacewarta a wajen daya gani.

Kallon rabi yayi dake tsaye sai maya tafayi saurin mikewa ganinshi ta sauke wani irij murmushi,

“Ina wuni yallabai” baijin hausa amma yanda rabi

tayi magana ya gane gaishesa tayi, da mamakin kansa baima san ya iya kalmar ba yace “lafiya” ashe dai ya fara dan koya Kadan kadan.

Maya ta taho inda yake cikin kaudi kamar ba itace ta gama cin mutuncin sabeeha ba ta zauna tana harare harare itama rabi ba

ta tsira ba don rashin kunya take mata

“Hey uncle taj….do you need anything?”

“No thanks” ya bata amsa ba tare da ya sake kallonta ba ya dauke kanshi ya juya, daidai nan sabeeha ta karaso”

Rabi ta girgiza kai tace “wannan yarinya akwai munafuka, ji y

anda takeyi kamar ba yanxu ta gama sababi ba”

sabeeha data jita ta dago ta kalli inda rabin ke kallo, bayanshi kawai ta kurama idanu har suka bace kata daga gani, “ya kika tsaya? Tattare wajen” rabi ta mata magana.

Sama ya wuce maya ta bishi a baya t

ana karemashi kallo ta bayan, few steps ne tsakaninsu don yanajin takunta amma hankalinshi baya jikinsa yana ga muryar dayaji datake kama data sabeeha, toh kodai yawan tunaninta ne yasashi yakejin muryarta yanxu kuma?and he feels her presence a ko’in.

Dai

dai wajen shiga part din nanna ta dakata harya shige daga ciki kafin Ta koma daki tana murmushi.

Washe gari…

Tun wajejen karfe sha daya jamila ta kira hadiza ta tura mata adireshin gidan, sannan ta shaida mata tana nan tafe.

Hadiza fa bata kwana kalau

ba don zuwan jamila da kiran da jamila ta mata dagaji ba na alkahiri bane.

Hadiza ta futo daga dakinsu ta rabi dake kitchen, “rabi dan Allah kiyi ma security magana yar uwata zata zo”

“Hajiya tasan da zuwan bakuwar taki?” Rabi ta tanbayeta

Rai a bace

hadiza tace “yar uwatace zatazo kuma hajiya ta santa”

“Toh naji” rabi ta fada tare da cigaba da abunda take.

Hadiza kamar ta shaqeta dan baqin ciki.

Daga chan wajen security aka kira cikin gida, daman rabi ce sukeda access da ita suka tambayeta akwai

mai expecting bakuwa tace eh, suka tambayi suna tace masu su barta ta shugo.

Jamila fa tundaga bakin gate idanu suka raina fata ta dunga wiki wiki dasu tana rarrabawa, aranta babu abunda take fadi sai lallai hadiza ta debo ruwa, kut…aljannar dubiya saima

i rabo”

Futowar hadiza ta backyard ta hangota daga nesa cikin sauri ta karaso insa take, “jamilaaa…”

“Naam hadiza, anan kuke? , bura..ubanchan kaiii, lallai hadiza kinyi wuta, kunama mai zafin dafi”

“Muje daga ciki” hadiza ta fada tare da jan hannunta s

ukabi ta backyard.

Ta kitchen din suka wuce jamila suka gaisa da rabi kafin hadiza takaita dakinsu.

Suna shiga daga ciki hadiza ta karo kofa harda saka key jamila har an hau gadon zamani an zauna ga ac na buga dakin.

“Bamu gaisa ba ko? Hankalina yayi ga

ba naga duniyar arziki”

“Jamila ina magnar gaisuwa kin sani cikin tashin hankali? Ey?”

“Ay kya bari nasha ruwa ko? Ina yar taki?”

“Wacce daga ciki?” Hadiza tayi tambaya, jamila ta kyalkyale da dariya.

“Jamila yanxu ba lokacin dariya bane, ki fada kin

meke tafe dake? Wace matsala ce ke tunkaro mu”

Gyara zama jamila tayi ta yaye mayafin dake kanta tace “wannan yarinyar nemanta ake,”

“Wa kenan?”

“Kinsan wa nake nufi, jiya jamilu yazo gida ya shaidamin wai wasu mutane masu kudi sunzo har agency dinnan n

emanta, kuma da alamu yanda suke kakkashe kudi don ganin sun ganota babu tantama kisan kai tayi ko kuma sata tayi ake nemanta”

Dafe kirji hadiza tayi tace “na shiga uku ni hadiza? Kisan kai?”

“Kwarai kuwa, kuma kinsan cewa jamilu shine ya kaita wajennan

a matsayin marikinta, duk wani abu datayi shi za a fara kamawa saboda haka wallahi tallahi kisan nayi,“

“Na shiga uku ni hadiza, kin tabbar kisan kai yace maki tayi?”

“Ah ah fa, hasashen mu ne inba haka ba meysa masu kudi haka zasu dunga nemanta eyy?”



Jamila wallahi wallahi bazan dauki asara ba, tun ban cimma buri na ba a duniyar nan”

“Toh ya zakiyi? Daman dalilin zuwana kenan,dan wallahi igiyar aurena na hannunki, jamilu yace zai iya sauwwake min wallahi, ki kwasheta ku koma lafiya kawai inyaso saiki

dawo”

“Jamila bazan iyaba,nayi kokarin yin haka tun ba yanxu ba”

“Toh kina nufin idan akazo a kama mu kenan?”

“Ah ah jamila zanyi tunani akai”

“Gwara dai kiyi tun wuri, ki debo mi dan abun kamusawa mana naci arziki kafin muyi arzikin?”

….

Sama rabi

ta hau sai gata da anne sun sauko har kasa, zuwa sitting room.

Wani mutumi ne a zaune don ya dan manyanta, an aje mashi bottle water da snacks a gefe yana daga zaune a kasa.

Daga ganinshi zakasan anji jiki don yana sanye da wata riga yar shara da wando

blue fatau an kure adaka, sai wage baki yake da yayi jaja saboda cin goro.

Gefenshi bilki ce zaune tana sanye da hijabi sai kayanta dake cikin jaka mai kyau, ka ganta fess fess tayi bulbul abunta.

Anne na karasowa ya sake gyara zaman babbar rigarshi da

ke kan yar sharar, “sannu hajiya sannu hajiya”

“Sannu dai” anne tayi magana kafij ta zauna

“Ina wuni hajiya? Mun sameku lafiya?”

“Lafiya lau alhamdulillahi ya mutan gida?“

“Lafiya kalau kalau kalau hajiya”

Kana ganinshi zakace wani burkitaccen mutun

ne amma da hankalinsa tsabar duniya ta bugi idanunsa ce.

“Kaine kawun nata?”

“Ee nine hajiya”

“Toh Masha Allah”

Matsowa rabi tayi da kudade aqalla zasukai wajen 500k ta aje gabanshi anne tace “ga wannan ayi mata duk wani hidiman biki, idan akwai abunda

yayi saura ma saita bilkin ta kira”

Kamar zai taugunna mata haka yake ji, sai faman gadiya yake kmar bai taba rike kudi kamar irin wannan ba.

“An gode hajiya an gode sosai, bilki marainiya bazatayi kukan maraici ba kun mata komai hajiya an gode an gode”

“Ba komai Toh bilki saduwar alkhairi allah ya bada zaman lafiya ya sanya alkahiri”

“Ameen duk suka amsa a tare bilki harda kukanta suka futo daga gidan bayan tayi sallama da kowa, basira harda hawaye, rabi ma saida taji wani iri haka sukayi sallama suka

futa.

Suna fita ya chusa kudin cikn babbar riga ya zaro goro ya fara tauna.

“Wallahi idan baki kirani ba zaki ga daaowata hadiza na fada maki,”

“Kai jamila kamar babu yarda tsakanin mu?”

“Ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login