Showing 249001 words to 252000 words out of 338813 words

Chapter 84 - MATAR TAJ COMPLETE

wani irin dadi kamar an cire mata komai, waige waige ta somayi na neman abunda zatayi tsarki dashi babu, kwata kwata batasan automatic smart wc ne ba wanda yake fidda ruwa daga jiki ya maka tsarki, gashi batasan ta yanda zatayi flusging ba don

madannan sunada yawa sosai, “toh kodai ta futa ta kirashi? Ta tambayi kanta, wannan abun kunya haka ta wuce gaban faucet din shower ta kunna ruwa ya zubo ta tsugunna tayi tsarki, tana gamawa mistakenly ta dago garin danne dannen ta ta danno wajen shower ru

wan ya zubi mata, cikin sauri tayi baya allah yaso bai jiqata sosai ba.

Sauke ajiyar zuciya tayi tana kallon bandakin yanda ya hadu ba karya, inda ya danna ya zuge glasa dinnan ta duba aranta tace “ko waye yayi inventing wannan bandakin oho? Kana wanka na

waje na hangoka ay iskanci ne wannan”

Juyawa tayi ta futa daga bandakin, hangoshi tayi yana sujjada, ta dan tsaya harya sallame.

Daidai lokacin akayi knocking, miqewa yayi yaje bakin kofar ya danna wani abu kofar ta bude wata mata ta shugo da hanger jib

ge da kaya a jiki kala kala, rarraba idanu sabeeha ta somayi har matar ta shugo ta gaisheta sannan tace “this is all of our boutique collections sir”

Kallon hanger din yayi yace “thanks”

Matar ta futa ya juyo ya kalli sabeeha yace “ki shiga kiyi wanka ki

zo kiyi sallah”

Wanka? Ni zanje nayi wanka?” Ta fada aranta, “lallai ma, saboda me zatayi wanka don zatayi sallah?” Ta sake fada aranta

“Basai nayi wanka ba, bana buqatar yin haka” ta fada tana kauda kanta

“Yes you have too, ga kaya nan, saiki dauka

wanda kikeso ki sauya”

“Bana buqata, na jikina ma ya isheni”…

Ya lura batasan cewa ta soma bata jikinta ba kuma bazai yuwu tayi sallah a haka ba.

Take ya sauya kamar bashi ba yace “don’t make me repeat my self, go…in there…and take a bath…indai baso ki

ke ki kwana anan ba, this is a command”

Lallai ma, meysa yake wasu abubuwa kamar ya ajiyeta? Ta tambayi zuciyarta, ay ya ajiye kin ne tunda da alamu ya karbi aurenki dashi, wata zuciyar ta bata amsa

badai yana tunanin zai karbi auren dayake maganar akwai

shi ba? Ay maganar aure ita dashi babu, dama chan yafi karfinta, bazama ta taba hada kanta dashi ba, menene amfanin auren? Daman dalilin tun a saudi ne abubuwan da suka faru a baya, yanxu ko daya gano komai ya dawo hayyacinsa ay babu wannan maganar.

Ka

llonshi tayi bayan ta gama wannan tunane tunanen nata, da maganar da sukayi da khaal kafin tace “i am here only because kace min zamuyi wata magana, kuma mun gama yinta, maganar aurenmu dakake cewa baka sakeni ba babu shi, tunda tun farko daman kasan dalil

in auren badan komai baneba saboda halin da kake ciki, kuma i stand by you, i protected you daga yan uwanka kafin ka koreni, koda ka dawo hayyacinka dama chan baka karbi wannan auren ba, yama za ayi ace kamar kai ka auri yar aiki,mara galihu sannan wadda b

ata da gata kamar ni kaskantacciya? Hanyar jirgi daban ta mota daban, idan auren namu yana nan then what next?? Are we going to be real couples or what?….”

Ta tambayeshi tana kallon cikin idanunsa, “lets end it here,divorce me, yanda baka buqatata a rayuw

arka haka zalika nima bana buqatarka, ni ba kowa bace face yarinyar data taba kula dakai a baya sanadiyar hakan kuma aure ya shiga tsakanina dakai,yanxu tunda bashida wani amfani sai a rabu”,

Tunda ta soma magana ya kafeta da idanu, bai taba shiga bacin r

ai kamar yau ba, ya rasa ta inda maganganunta ke dosa ita ko tayi hakan ne don ta gane inda ya nufa, mey yake nufi da ita?

Saurin controlling kanshi yayi, he’s not ready to open up, yadai san fatima is already part of him which he can never let go of, bu

t he’s not sure of his true feelings, what he has for her.

“Ban rabu dake ba achan baya i will not do so now, cause you’re part of me,idan kina tunanin bana buqatarki, toh ayanxu ne nake kan buqatarki the most, i will never let go of you”

“Why??? Why

?? Zakayi forcing dina ne? Why are you selfish, duk abunda na maka a baya? Ko danshi bazaka rabu dani ba? I have endured so much saboda kai, why cant we just part-ways kamar bamu san juna ba? Meysa”

Ta karashe tana hawaye, harga allah tunda yace mata ak

wai aurensu bai saketa ba take cikin tashin hankali, idan hadiza ta gano ta gama yawo, duk yanda zatayi saitasan yanda tayi suka rabu tun kafin a gano ma.

Daga yanda take magana ya gane a tsorace take da almarinsu shida ita kamar tana tsoron kar a gano

cewa akwai aure tsakaninsu.

Aranshi yanaji wani irin zafi sosai, bazai iya abunda take so, batada kowa yanxu daya wuce shi, yasama ranshi wannan tun lokacin daya gano bata tare da asalin iyayenta kuma bata sani ba.

“Idan har bakiyi abunda nace ba ko ab

unda nakeso, you will leave me with no other option but to tell everyone cewa we are married…,“

Yana karashewa ya zauna tare da jawo wayanshi yana dannawa.

Tunda ya gano he can threaten her da haka yasan zatayi duk abunda yace, daman abu na farko dayasan

zaisha wahala daga wajenta shine yanda zata karbesa bayan abunda ya mata a baya, kuma yasan cewa dama chan ga dalilin auren su.

Tanajin abunda ya fada ta tabbatar he just wants to use her, yanda yake tabata da yanda yake mata wasu abubuwa yasa tayi concl

uding hakan ne ma, daman waye gatanta da zai tsaya mata, haka rayuwarta ta taso sai yanda akayi da ita batada ta cewa, batada mai tsaya mata, gashi ta tabbatar bawai zai taba sonta bane, yama za ayi tayi tunanin haka?.

Jiki a mace ta juya bathroom din tan

a share hawayenta abubuwa da dama na yawo akanta, Allah kadai yasan irin tunanin da takeyi a wannan lokacin, ta soma rage kayan jikinta.

Yana ankare da ita har ta shuga bathroom din tana hawaye, kai itama dai kamar wata yarinya koda yake yarinyar ce mar

a wayo.

Gaba daya shiko ya damu da ita sosai, Yanda take kafiyar nan baiyi tunanin zatayi wankan dayace tayi ba wannan yasa ya dauoa smart remote din suite din wanda har labule yana kullewa kana daga kwance zaka iya operating komai na dakin.

So yake yaga

mai takeyi, ko kuka takeyi?

Without second thoughts ya danna glass din bathroom din.

Take ya soma dishewa ahankali, qiqam ya tsaya yana kallonta, idanunsa kamar zasu zazzago har wani ruwa ruwa yakeyi.

Chan kasan maqoshinsa ya furta “damn…..”

Tana g

ama wanka ta daura towel a jikinta ta juyo bakin kofar ta kasa futowa, knocking din kofar da akayi yasa ta dago daga waje yace “i will out for a minute”

Ya fadi hakan ne don ya bata damar shiryawa duk wani tunani da take ya fita ranta.

Bude kofar tayi ta

leko ganin baya nan yasa ta futo gaba daya ta wuce gaban hanger dinnan hannunta rike da sauran kayanta data cire, bin hanger din tayi da kallo ganin hadaddun abaya’s masu shegen kyau, guda daya ta zaro ta aje gefen gado sannan ta soma shiryawa a gurguje,

tana gamawa ta zauna ta doka uban tagumi.

Cikin abunda bai wuce minti biyu da zamanta ba sai gashi ya dawo, kiri kiri taki yarda ta hada ido dashi shima sai kakkaucewa kallonta yake saboda abunda idanunshi suka gane masa, he cant stop imagining the way he

saw her earlier naked, he felt so erouse kuma yasan idanda bai fita ba daxu anything can happen, the way he imagine her shes above beyond that, yana mata kallon yarinya karama, ashe tafi haka ba kadan ba, she’s a grown ass woman in full physically.

“lets

go” ya fada yana hana kanshi kallonta.

Kamar jira take ta miqe da sauri tasa takalminta suka futo a tare.

Lift din da suka shiga kowannensu yayi tsit babu wanda yace da dan uwansa qala shi danna waya ma yakeyi har suka fito suka shiga mota.

Ta juya

fuskanta ga window, tafiya sukayi mai dan tsayi kadan har suka iso shopping mall, suna isowa ya bude kofar expecting her to be out, baice komai ba kuwa ta futo yayi gaba ta bishi a baya.

Ciki suka shiga suna zagaye har suka iso floor din clothings da sau

ran accessories, sai a lokacin ya kalleta yace “pick abunda kike buqata”

“Bana buqatar komai” ta bashi amsa kai tsaye, baibi ta kanta ba ya shiga zarah cikin abunda bai wuce 10mins ba ya fito ya taddata tsaye hannunshi rike da paper bags sannan suka sauka

kasa suka tsaya ga apple store, nanma dai qin shiga tayi sai shine ya shiga, abunka da masu hannu da shuri, babu lokacin yin wani negotiation ko minti goma baiba, ya fito da paper bag din apple da macbook laptop, other accessories da dai sauransu.

Inda t

ake ya nufa ta wani hade rai sosai, kanar bata taba dariya ba, ya danyi smirking yace “lets go..”

Binshi tayi kamar jela har suka shiga motarsa, yaja motar suka futa daga harabar wajen, lokacin wajen karfe hudu harta wuce, time din duakansu ya shiga, kai

tsaye gida ya wuce, suna karyo kwana gabanta ya soma faduwa, ta dubeshi tace “idan aka gane fa?..ka maidani school dan allah ya hamad zaizo daukanmu”

Banza yayi da ita har aka bude gate din entrance, ya shiga da motar ciki, sabeeha kamar tayi kuma tsabar

tashin hankali, shiko ko ajikinsa.

Yana parking ya dubeta “talking of hamad, bana son na sake ganinki dashi a zaune kuna magana, ba magana kadai ba he’s not your muharram so be careful..”

Yana gama fadin haka ya miko mata jakkunan daya saya mata abubuwa

ya aje akan cinyanta, sai faman rarraba idanu take, kamar baisan me take ciki ba, gaba daya hankalinta a tashe yake, bata sani bana ko an dauko su maya, ko basu dawo ba, idan sun dawo me zata ce idan an tambayeta? Sannan idan basu dawo ba waye zatace ya da

wo da ita.

Ita bama ta abubuwan daya saya mata take ba ta dubeshi tace “ka ajesu a wajenka, bansan me zance ma mama ba idan ta ganni da abubuwan nan”

Tana fadin haka ta maidasu inda ya daukosu bayan kujerar sannan ta bude kofar hannunta na karkarwa.

Yan

a kallonta harta shige cikin gida ta kofar baya.

Babu kowa a kitchen din wannan yasa ta lallaba ta shige ciki da sauri.

Dakinsu ta bude daidai nan hadiza ta futo daga daki.

Jiki na rawa sabeeha ta duka kasa tace “ina wuni mama…”

Wani irin kallo hadiza

ta mata, ji take kamar ta kashe yarinyar nan ta huta, yarinyar ta zame mata babbar barazana, yanxu taka hakura da batun barinta ta gama makaranta daman kwadayin dan abunda zata samu ne yasa ta dakatar da ita amma yanxu so take kawai ta rabata da gidan nan

gaba daya bama nan kadai ba abujar gaba daya.

Gashi shegen dahirun nan yaqi daukan wayarsu ita da jamila, don hartayi planning kawaj ta dauketa ta tafi da ita dutsen habuja achan kawai a daura auren jamilu ya zama waliyyinta, daga nan kawai dahiru ya kara

gaba ita.

Toh gashi dan iskan nan yana neman raina masu hankali, wayarshi ma a kulle take.

Ko mutunci amsa ta bata samu ba balle ta tambayi ko ya makarata irin dai ta nuna ta damu da ita, saima wucewa datayi daman allah allah take maya ta dawo tasan yan

da zatayi ta ganta, kwana biyu kenan rabonta da ganinta, ko tanacin abunci kuwa? Shin tana buqatar wani abu da gaggawa ne?.

Chan bangaren su maya ko sai wajen 5 driver yazo ya daukesu, tana ta murna don a tunaninta taj ne zaizo harta fada ma friends din

ta.

Salim yaso ta fito su hadu amma fitik taki yarda saboda kwata kwata batasan ya hada yanda da taj.

Her personal life should be kept personal yanda babu wanda yasan da irin rayuwar datake yi.

Koda akazo daukansu suna fitowa suka shiga mota suka kamo h

anya, laila har zatayi maganar sabeeha saitaja bakinta tayi shuru gudun kar maya taji haushinta don batason tana maganar sabeeha kwata kwata tun lokacin nan da hamad yace ta sauka daga mota ta kullaci maya da hamad din akan sabeeha.

A gajiya ta shiga part

dinsu, da basira taci karo data dawo nan bangaren don taimakawa maman maya da aiki.

“Sannu da zuwa”

Ko kallonta maya batayi ba tace “hado min green smoothie ki kawo min sama”

Tana fadun haka wuce sama sai dakin mummynta direct tana shiga ta taddada bah

ijja zaune da laptop kan cinyarta suna yin wani emergency meetung da team dinta.

“Mummy…” maya ta fada, dagowa tayi ta kalleta kafin tace “excuse me for a minute. Tayi mutung call din, maya ta karaso inda take tare da ture laptop din ta zauna kanta tace “

mummy na gaji”

“Sorry Baby meeting nakeyi, go to your room”

Tashi tayi kamar zatayi kuka ta futa daga dakin a fusace.

Girgiza kai bahijja tayi, ta koma ga meeting dinta, maya ko tana futowa daidai nan basira ta hauro sama da smoothie din, maya ta kallet

a kafin ta karba tasa a baki, kurba daya tayi ta watso shi fuskar basirar tare da sakin cup din ya fashe tace “mey wannan?” Ta soma balbale basira kamar zata duketa, duk takaicin rashin dawowar taj ne yasa take wannan masifar.

Futa tayi daga part din gaba

daya ta wuce main part, tana shiga ta wuce kitchen daidai nan ta hango sabeeha dake tsaye, da mamaki take kallonta don tasan ba tare suka dawo ba, yaushe ta dawo?

“Keeee!!!” Ta kira sabeeha, sabeeha tayi banza da ita

“Keeeee!!!” Sai a lokacin sabeeha t

a juyo ta nufi hanyar futa da abuncinta a hannu, maya na ganin haka ta watsar da plate din nata “ba dake nake magana ba? Ke wai jin kanki kike wata shegiya ko?”

Rai a bace sabee tace “mey haka ya zaki zubar kin da abunci na? Wannan almabazaranci ne”

“Abu

ncin na ubanki ne ko ubanki ya say? Mutun bai iya samun waje ba mteww”

“Karki sake zakin ubana, ki zageni son ranki amma karki sake ambaron ubana”

“Me zaki iya yi? Na zagi uban naki idan kina dashi fa kenan”

Hannu saveeha ya daga zata sauke mata hadiza

tayi ha zari karasowa ta wanketa da maruka, har uku, “ko da wasa karki sake kiyi tunanin taba ta dan ubanki, ta zagekin idan ta zagekin zai futo ne a jikinki? Kunada uban ne da zagin nasa zai maki zafi? Shegiya???”

Sabeeha bata taba ganin hadiza cikin wan

nan yanayin ba sai yanxu, gaba daya rayuwarta,

Juyowa hadiza tayi tana kallon maya tace “yi hkuri hajiya karama,dan allah kar ranki ya baci saboda yarinyar nan”

Tabe baki maya tayi tace “da kin barta ta tabani wallahi da bazaku kwana gidan nan ba dagake

har ita”

Hadiza taji abu ya doki ranta tace “ko a mafarki bata isa ta bata maki rai ba ta sha, kiyi hkuri kinji, bana son ranki ya baci, da naki ya baci gwara nawa ya baci sau dubu”

“Hadamin abu mai sanyi insha ina sama”

Cikin jin dadi hadiza tace “toh

” jikinta na rawa, maya na futa hadiza ta kalli sabeeha, wata iriyar tsantsar tsana takema yarinyar.

“Futa kafin na kasheki na huta” hadiza ta fada da karfi, jiki na rawa sabeeha ta futa, rabi dake labe jikinta duk yayi sanyi.

A gabanta sabeeha ta wuce d

aki da sauri ta hau kan gado tana kuka rabi tabi bayanta cikin lallami ta soma bata hakuri.

Maya na kwance hadiz ata kawo mata abu mai sanyi, “bude wardrop dina a kasa zakiga wani kwali dauko min”

Maya tayi magana.

Budewa tayi ta zaro mata kwalin, lba

tasan kwalin menene ba amma tana kallo maya ta bude ta zaro guda daya wata yar takarda ta nannade ta zuba a juice din sannan ta kai bakinta ta shanye tass, hadiza tace “hajiya jarama menene wannan?”

“Ina ruwanki? Idan gulmq zaki dunga yimin zan hanaki shu

gowa inda nake wallahi”

“Ah ah yi hkuri, bari na making tausa naga kin gaji”

Ta karashe tana danna mata kafafunta, cikin abunda hai wuce minti biyu ba kawai ta mangare sai barci.

Hadiza na lura da tayi barci ta tashi taaye ta nufi bakin gado ta zauna ta

na kallon fuskarta tana murmushi, a hankali ta soma magana “diyata….kinfi kowa, zan iya komai akanki, zan baki duk gatan duniyar nan, bazaki taba wahala ba indai ina raye, zan juri ganinki daga nesa indai zaki samu komai na duniyar nan, gata da dukiya, kum

a bazanyi kasa a gwiwa ba saina tabbatar kin dawwama cikin arziki har karshen nunfashina, banida kowa saike…“

Toh fah…..

Ta dade tana tare da maya har ana gab da sallar magrib, kafin ta futa daga dakin.

Bahijja na gama meeting ta wuce dakin maya, gani

n batanan yasa ta suako kasa basira ta shuada mata ay ta futa, tasan duk inda zataje bazai wuce part din su laila ba ko main house wannan yas ata tsaya domin daura dinner.

Bayan futar rabi daga dakin ta kawo mata wani abuncin taci tasha panadol kafin ta

futo suka daura sanwar dare ita da rabi.

Dake hannayen taimakon gyaran gidan da girki ya ragu saboda basira ta tafi dayan bangaren yasa suka fara da wuri kuma cikin ikon allah suka gama da wuri.

Ta koma daki ta dauro alwala tayi sallah, tana idarwa ta t

ashi ta futa zuwa kitchen, tun kafin rabi ta idar da sallah ta futo ta deba dinner dinshi a tray ta futo ta backyard.

Anatse take tafiya kamar wadda kwai ya fashema, gaba daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login