Showing 99001 words to 102000 words out of 338813 words
dinta ta
na duba files fadwa ta shugo.
Kai tsaye ta samu waje ta zauna, saida hidaya ta gama abunda take kafin ta fuskanceta.
Nan fadwa ta baje mata komai abubuwan da afiya ta fada mata da hotunansu da ammu data dauka da yanda suka bama sabeeha abortion pills.
S
aida ta gama jInta tsab ta duba hotunan sannan ta kalleta tace “so???? Me kikeso nayi akai kenan? Inma cikin babu shi time will tell”
Fadwa tayi mamaki sosai jin amsar data bata, “theres no time ukty, what if yayi consumating aurensu? What if ta samu ciki
n?No never i will..i will never allow that”
Hidaya tayi mamaki react dinta saidai bata kawo komai ba tace “do you have a medical prove”
“Tunda bakida shi i dont have time for this..abubuwan dake gabana sune a gabana”
“Ukty its seems like kin manta age
nder dinmu gaba daya, kina tunanin you have wrapped him around your arms ko? Kin manta abubuwan da muka mashi ko? Ko kina tunani bazai iya karbar taheel ba aduk sanda yaso?naga kinyi sanyi sosai well let me remind you idan kin manta…”
Saurin dakatar da it
a hidaya tayi da hannunta sannan ta dubeta tace “ya isa haka…yanxu me kikeso ayi kenan”
Wani irin makirin murmushi fadwa tayi sannan fidda wayarta ta danna wani video, videon da tareeq yayi fabricating shida sabeeha lokacin daya nemi yin lalata da ita taq
i bashi hadin kai, a lokacin daya nuna ma fadwa tayi saurin airdroping video din ba tare da sanin sa ba sai hotunan data dauki sabeeha da tareeq ranar da suke backyard ita da barad,
“Tunda babu yanda zamuyi proving fooling din kowa sukeyi ita da ammu why
don’t we use this against them..musashi ya tsaneta har ya fara kokwanto shin cikin nashi ne ko ba nashi bane daganan dole ayi bincike harma da DNA”
Girgiza kai kawai hidaya tayi ta dan murmusa.
Washe gari ta kama saturday morning, kowa ya hallara akan
dining, taj, ammu, fadwa , afiya barad sai kuma hidaya.
Tunda suka zauna kowa kecin abunda ke gabanshi, har suka gama.
Hidaya ce ta fara tashi kafin ta dubesu tace, “ina sitting room idan ka gama inason magana dakai”
Girgiza mata kai kawai yayi sannan
ta futa, fadwa ma ta miqe tabi bayanta follow by afiya sai daga baya after ya gama shima ya miqe, kusan a tare suka fito shida ammu daga dining din zuwa sitting room din, daman sama zata wuce wajen sabeeha sai kuka ta dakata ganin sun zazzauna.
“Lafiya da
i?”
Ammu ta fada tana tunkarar inda suke zazzaune, hidaya dake zaune ta hade girar sama da kasa kamar an aiko mata da sakon mutuwa ta dubi ammu tace, “zaki iya zama kema,”
“Toh allah yasa dai lafiya”
Ammu na rufe baki saiga sabeeha ta sauko da head maid
dataje ta kirata.
Wallahi ganinsu zaunen nan saida gabanta ya yanke ya bada wani irin dammm da kyar dai ta daure ta karaso ammu tayi mata nuni da kusa da ita ta zauna.
Saida kowa ya zauna hidaya ta fidda hotunan dake gefenta ta watsa su gaban taj, dauka
nsu yayi daya bayan daya yana duban hotunan da mamaki, tabbas idan zai tuna ranar da kayan dake jikinta lokacin da suka fito ita da barad ne har yace mata kar ta sake fita babu hijabi, abunda yafi daure mashi kai shine har a yaushe tareeq ya isa gareta har
yana mai janyota jikinshi don jikinsu yayi kusa da juna sosai saboda angle din hoton, karban hotunan ammu tayi tace “menene wannan din”
Shuru tayi ta gama ganin hoton kafin tace “zancen banza, yaushe akayi wannan din, daman nasan wannan taqaddirin yaron
babu alkahiri a tattare dashi daman ta taba fadamin yanda yake kai mata hari,kudai wallahi da kwashe kwashen ku, ke kin kawo barauniya kw kuma kin kawo dan iska scammer”
Fadwa dake bakinta baya shuru take “kedai kawai kiyi shuru ammu bakisan komai ba,“
daukan remote dake gabanta hidaya tayi already sunyi screen mirroring daga waya zuwa tv,ta kunna nan take video ya bayyana, wallahi wallahi saika rantse ba fabricating video akayi ba da gaske ne, komai sak da jikin da fuskar hasalima dai babu wanda zaice
ba sabeeha bace a jikin video din.
Cikin sauri sabeeha ta miqe hankali tashe tana mai duban taj da ammu at the same time,
“Yanxu wannan yayi kama da shike kai mata hari? Dama chan yar hannu ce dataga shima irinta ne shine take binshi,”
Afiya tayi cha
raf..”wama yasan irin abunda sukayi a cikin gidan nan, kai wallahil azeem zan rantse maku cikin dake jikinta ma bana taj bane na wannan dan iskan ne don babu yanda za ayi ace wanda baya cikin hayyacinshi har ya iya kwanciya da mace ya biya mata buqatar ta,
as far as we know tunda suke tare tun lokacin da aka kawota babu wani abu tsakaninsu iyakacin ta kula dashi.”
Cikin hanzari ammu ta daga mata hannu rai a bace tace “wannan bashine zai baku damar yi mata qazafi ba,”
“No ammu stop it…stop defending her sh
e’s fooling us all..idan baki yarda ma ki saurar wannan”
Nan fadwa ta danna wani voice record shima dai muryar sak ta sabeeha suna conversation ita da tareeq wai har tana cewa itafa leken asiri aka kawota gidan nan kuma zata iya yin komai, idan yana buqat
ar kwanciya da ita duk sanda yakeso a shirye take saboda ta saba da harkar abundai babu dadin ji, dirty and disgusting talks.
Tunda fadwa ta danna voice din idanunshi suka soma jaa, kanshi ya fara sara mashi yanayinshi ya sauya gaba daya kamar bashi ba ra
n maza yayi mugun baci yakai kololuwa
Saurin runtse idanu ammu itama tayi ganin yanayinshi, tana mai dubansu da kyau, lallai dole tayi wani abu yanxu kafin su cimma kudirinsu, har ammu zatayi magana hidaya tayi saurin dakatar da ita tace “ammu stop it p
lease…duk wannan shaidun dake gabanki da magnganun da muka ji duk karya ne? Ko kirkira za ayi?”
Ammu kamar zatayu hawaye ta dubi taj da yayi shuru ya kasa magana tace “tajudeen yanxu ka yarda da wannan, bai kamata kuyi saurin yanke hukunci ba daga jin mag
ana babu kwakwarar hujja, ku ya akayi kuka samu wannan din?”
Tunda ammu tayi magana afiya ke neman yi mata rashin kunya, “wama ya sani ko kinsan cewa cikin ba nashi bane amma kike kakkareta”
Rai a bace ammu tace “how dare you afiya…kinsan da wa kike maga
na kuwa?are you insane ina matsayin kanwar mahaifinki?”
Sabeeha da hawaye suka gama wanke mata fuska taoro da fargaba sun gama mamayeta tayi saurin cewa “wallahi wallahi sharri ne..wallahil azeem babu abunda ke tsakanina dashi, shine ke bina,”
“Shuttt
up disgusting slut” fadwa ta daka mata tsawa, “wannan yayi maki kama da karya? How dare you sleep with my husband? Under my nose you have the audacity”
“Wallahi azeem ban taba magana dashi makamancin haka ba, shike bina kuma dana nuna mashi cewa zan tona
mashi asiri shine ya kulla min wannan sharrin”
Wani irin buga table da akayi ne yasa duk suka dago suna dubanshi, idanunshi sunyi jaa kanshi yayi rado rado “shut up!!!!!!!!!!”
Ya daka masu tsawa gaba daya kowa tasha jinin jikinta, hidaya dake jin tana da
authorities yin magana kuma ta tsaya tace “dole ayi dna test..to confirm wannan cikin nashi ne, bazai yuwu ace akwai bastard acikin family nan ba bazan taba yarda ayi tarnishing image dinmu ba never.
baima tsaya ya karasa sauraron magnganun hidaya ba ya
miqe afusace ya wuce sama.
Ammu babu abunda take sai girgiza kai ko ba a fada mata ba ya gama yarda da magnganunsu, tabbas babu ciki jikin sabeeha saboda haka duk wannan sharri ne kuma tasan sune suka kullashi amma yanxu ya zatayi ta fayyace mashi? Komai?
This is not the best moment, bata taba tsammanin they can go to this extent ba ya ilahi ta dafe kanta.
Da sauri sabeeha ta miqe tabi bayanshi hankali a tashe,
Kallon juna sukayi gaba dayansu suka murmusa don sun dana ma ammu tarko bama ita kadaiba hard
a sabeehar dole yanxu su fito da kansu su fadi gaskia, dna ko sai anyi shi idan aka tabbatar da akwai cikin kuwa dole su juya abun nanma suyi fabricating results din a maidashi dan tareeq ne.
Sabeeha data hawo saman kasa bude kofar shiga bedrrom din tay
i hannunta na karkarwa haka zalika jikinta.
Dakyar ta tattara kuzarinta ta ta tura kofar, yana Zaune bakin gado ta karaso har ibda yake ta duqa har kasa nesa dashi ta soma magana “didi…ka yarda dani, wallahil azeem sharri ne, bani bace cikin video din”
Ta karashe tana rarrafowa kusa dashi ta fara kokarin kama hannunshi yayi saurin janyewa ya miqe tsaye yana kallonta disgustingly ya juya mata baya, “get out of my sight”
Ya fada cikin bacin rai, he really needs time for now, yayi processing komai, tabbas
yasan halin fadwa da kudirinta akanshi, and anything that will come from her ba abun yarda bane saidai wannan ya dan taba shi, ya rasa dalilin dayasa gaba daya komai ya dagula mashi lissafi, zuciyarshi na boiling yana jin wani irin zafii sosai,
“Didi ka
yarda dani dan Allah listen to me please”
A zafafe ya juyo rai a bace ya kamo hannunta ya dagota tsaye rai a bace yayi baya da ita har jikin bango yaka manta da wani batun ciki, hes just blind yace “i said get the hell out of my side are you dumb? “
Ya
karashe yana saurin zame hannunshi daga nata disgustingly ya juya yabarta a tsaye feeling so shattered and scared ta futo daga dakin ta sauka kasa wajen ammu, tun kafin ta kaiga sauka kasan fadwa da afiya suka tareta, fadwa ta damqe hannunta idanunta sunyi
jaa sosai ta soma “wallahi wallahi saina wulqantaki, tunda kika shiga gonata, saikinyi regretting zuwa gidannan, tana kaiwa nan ta hankadata gefe rai a bace, cikin hanzari sabeeha ta kama hannunta inda fadwa ta rike, hawaye na gangarowa akan fuskarta, ita
bata su take ma, suna bari wajen ta tunkari dakin ammu.
Fadwa da afiya suka kalli juna fadwa ta zaro syringe din data deba jinin sabeeha dashi, ashe rikon data mata jininta suka diba.
Sabeeha data shiga dakin ammu bata lura da jinin dake dan disa ba dag
a hannunta.
A tsaye ta tadda ammu tana safa da marwa, tayi saurin Karasowa inda take tana kuka tace “ammu wallahi wallahi sharri ne”
Kama hannunta ammu tayi tace “basai kin fada ba sabeeha, nasan sharri ne kuma karya ne, zancen ciki da suke cewa nashi ne
nida ke munsan cewa babu ciki a jikinki”
Sai a lokacin sabeeha taji sanyi aranta “amma ammu shii…didi baya son ganina yace na fita..ya yarda kennan? Ya zanyi ammu?”
“Kwantar da hankalinki, just leave him alone he needs time to think trust me kinji fati
ma?”
Misalin wajen karfe sha daya ammu da sabeeha suka soma jin hayaniya anan kasa, cikin hanzari ammu ta fito tare da sabeeha dake biye da ita, a baya a daidai lokacin taj ya saukko daga sama shima, fadwa datafi kowa zaqewa tayi saurin takowa inda sabe
eha take ta wani irin jawota kamar kayan wanki ta watsa ta tsakiyan sitting room din kafin ta nunata da yatsa tace “daman na fada maki saina kawo karshen ki a gidannan”
Ran taj in yayi dubu ya gana baci yanda fadwa keta faman zaqewa its hight time for him
to stand for his wife basu da right din treating dinta haka, rai a bace ya dubi fadwa data duqa zata kamo kan sabeeha harta daga hannu zata watsa mata mari yayi saurin daka mata tsawa
“How dare you lay your hands in my wife? Waya baki wannan right din?
Ehhh answer me”
“Hahahah wace wife din? Maid din taka wulaqantacciyar? Wannan abar?”
Rai a bace ya nunata da yatsa gaba daya daga hidaya har afiya mamakin shi suke yanda ya sauya gaba daya ashe haka yakeda zafi this is the other side of him da basu taba
gani ba, “ heyyyyyyyyy!!!! Stay on your limit… i’m warning you“
“Heysss don’t shout out me saboda wannan walaqantacciyar, duk wannan abun da kakeyi Saboda an maka karyar shegen cikin ka a jikinta ko?”
Ay baisan sanda ya watsa mata wani mari ba dataga tau
raru wuu wuu,
“The next time kika kara shegantamin ciki i will make your life miserable”
Adaidai lokacin hidaya tayi stepping up ta hanyar watsa mashi takardar result din prwgnancy test da akayi har guda biyu tace “agabana kake ma sister ka ihu akan cik
in da babu shi? Ive never knew you’re a fool da za ayi fooling easily yanda akayi fooling dinmu gaba daya”
Hankali a tashe ya dago ya kalli hidaya kafin ya fara karanta paper din, pregnancy test ne gashi negative harda sunan sabeeha da nashi a jiki, he co
uldn’t believe it.
Ammu dai runtse ido tayi kawai, komai yazo mata a bazata unexpectedly.
Sabeeha tunda aka turata kasa tayi zaman dirshen babu abubda take sai innalillahi, shikennan.
Rai a bace taj ya kalli sabeeha ya kalli ammu ya kasa dauke idanunshi
kan ammu daketa faman girgiza kai, “is this true?”
Shine tambayr dayayi ma ammu kawai, babu abunda take sai juya kanta, ya dubi inda sabeeha take data hade kai da gwiwa tana kuka yace “is this fucking truth? Answer me”
Sauda sabeeha ta tsorata tsabar fu
rgici da tsoron yanayinshi “yeeee…ss”
Ta amsashi bakinta na rawa kuka ya kufce mata, runtse idanunshi kawai yayi innalillahi wa inna ilaihi rajiunwallahi fadin irin yanayin daya shiga bata lokaci ne, ya dawo asalin tajudeen dinshi wanda bashi da sauki, b
abu abunda ke bayyane akan fuskanshi sai hatred, he feels betrayed and fooled at the same time lies upon lies upon lies…kaf rayuwar bayajin akwai gaskia ta daidai da sakon daya, namiji ne shi mak tawakkali
da jajircewa but wannan abu ya tabashi ba kadan ba
, ayau ya yarda da maganar hidaya da accusation din datayi akan sabeeha 100 percent, saida ya fara trusting dinta, saida ya fara yarda da ita, ashe duk fooling dinshi take all this while, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, idanunshi sunyi jaa shi kanshi ya
koma jaa sosai.
Ammu ma na hawaye ta soma magana “muhammd trust me, ba laifinfa bane, bada niyar cutar dakai muka maka karya ba,”
“Ammu please….”
Ya dakatar da ita rai a bace, yana mai duban sabeeha yace “so this is who you are? A liar, a snitch,? You
disgust me..”
Hidaya data lura idanunshi ya rufe tayi saurin using opportunity din ta kalleshi tace “ay babu wani dogon surutu, sighn this divorce papers, police na jiranta waje, she will face the consequences of fooling all of us”
“Nooo muhammd bazai
yuwu ba, you can never do that, wallahi youll regret this i will
Never allow that” ammu tayi magana
“Why ammu? Please this is enough..can’t you see how you hurt him?Dole ya rabu da ita and thats final”
Ammu da hidaya na argument ya taho a zafafe ya finc
iko sabeeha daketa faman hawaye ya jawo kamar yana jan kaya har bakin kofar entrance ya dubeta cikin ido yace “i never want to see your face ever in my life, karki sake na sake ganin mai irin hallitarki a rayuwarnan har abada,”
Sabeeha najin abunda ya fad
a tayi saurin miqewa ta rungumwshi a jikinta tana kuka tace “didi..listen to me, wallahi i never had the intention of betraying you, bazan taba yi ba, listen to me youre making a grave mistake taj”
Wani irin ingizata yayi waje ta fadi kasa hartaji ciwo a
hannu ta sake miqewa tana kuka, “did you just say you never had the intentio? Kinsan me nafi tsana a rayuwata? Liars…liarsss ……liarsss betrayers…you fooled me, giving me false hope, how dare you do that? How dare you play with my mind and my intelligence?”
“Wallahi didi bazan taba cutar dakaiba, bazan taba cutar da rayuwarka ba,
Duk gaba daya su fito ammu na daga gefe ta kasa magana kwata kwata, afiya da fadwa ko me zasuyi banda tafawa, hidaya ma dai nade hannunta tayi tana kallon su.
Hannunshi sabeeha k
e kokarin kamawa ya daka mata wata razananniyar kara yace “i hateeee you…bana kaunar ganinki bana kaunar ganin mai kama dake a rayuwar nan, i wish you nevwr came into my life, you are nothing but a miserable human whi shattered my hopes”
Yana kaiwa aya sa
beeha ta tsaya chaaakk tana mai kallon cikin idanunshi shima yana kallon cikin nata sunkai wajen minti biyu a haka babu ko kiftawa, sabeehar ce ta dubi bangaren su fadwa daketa faman dariya sannan ta dubi inda hidaya ke tsaye ta nade hannu itama tana smirk
ing.
“You’re blaming the wrong side didi…why cant you open your eyes taj? Why can’t you see waenda ke kaunar kake nisantarwa daga rayuwarka? Why can’t you see waenda basa sonka? Waenda ke marmarin ganin ka wulqanta? Waenda ke son ganin bayanka why why???”
Kauda idanunshi yayi daga nata dayaga sun mashi kaifi sosai, share hawayen dake fuskanta tayi dukda basu fasa saukowa ba ta nade Mayafin dake daure a kanta ta yafashi a kanta sannan ta dubeshi, tace “ni fatima nayi maka alkawarin bazaka sake ganin mai k
ama dani ba har abada, nabar rayuwar ka har abada tajudeen.. ina fatan you’ll never regret this”
Tana fadin haka ta juya mashi baya hawaye mai dumi na sauka akan idanunta,
Hidaya ta dagama jami’an tsaro mata dake compound din hannu suka tafi da ita har w
ani irin ajiyar zuciya hidaya ta sauke, fadwa ko tafi kowa farin ciki ji take kamar taje ta rungumeshi, burinta ya cika ta rabashi da wannan yarinyar.
Ammu dataga dai da gaske an fitar da sabeeha daga gidan ta karfi da yaji itama ta wuce