Showing 54001 words to 57000 words out of 176422 words

Chapter 19 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

kunya sam basa shiri dashi ta gane kuma munafiki ne shine ya tunzura Ahamdu yazo yana kokarin zagar mata uwa." Hawayen da take ta kokarin

dannewa sunki dannuwa dole suka fara zuba, Ta juya yayin da yake kokarin hada ruwa miyau! ta tofa masa a bayanshi, Yayi saurin juyowa yana kallonta, shi ya d'auka ma tuntuni ta fita ashe tana tsaye, hawaye ya gani na karakaina a fuskarta, shifa bai ga abi

n kuka da damuwa anan ba, ai bai fadi wata mummunar magana kan mahaifiyarta taba, Had'a ido sukayi tace"Allah ya isa na Allah ya bimin hakkina." Ya shiga mamakin Allah ya isan da take masa, Nufar ta yayi tayi kamar ta gudu sai kuma ta yanke shawarar tsayaw

a wallahi ya daketa sai ta murd'e masa mazakuta! ta kasheshi kowa ya huta shawarar data yanke kenan....Koda ya 'karaso inda take sai taga akasin haka, dankwalin kanta ya fuzge ya mika mata fuska a hade yace."Goge min kazamin Yawun ki da kika tofa min." A

hargitse tace."Wallahi rantsuwar dan musulmi ba zan goge ba ko kasheni za kayi sai dai ka kashe."! Ya girgixa kai tare da fadin"Ni dai na fad'a miki dan na lura kin ji zafi kan maganata okey Yanzu dai bani da lokacin ki amma ki kiyaye shiga hannuna zaki ga

ne baki da wayo." dankwalin yasa ya goge miyau din ya jefa mata a fuska, taja tsaki mai karfi ta futa daga toilet din, rashin a 'bace yayi wanka ya fito......Still kuka ya tada ta tanayi sosai idanunta sunyi jage jage da hawaye, sai ya dan ji tausayinta ya

kamashi, babu shakka tana da kishi kuma duk rashin kunyarta tana martaba iyayenta, shi dai yasan bai fadi mummunar kalmar da zata tada mata da hankali ba amma ta zauna tana kuka, hakane shima nada kishin iyayensa yana gani aka taba martabarsu sai inda kar

finsa ya kare, Kaya ya sauya ya fesa turare hade da daura agogo ya dora hula saman kanshi ya kama hanya ya fita daga dakin yana jin shashshekar kukanta har cikin dodon kunnansa.

Ta jima xaune a dakin tana wannan kuka tana kuma tunanin yanayi na rayuwa

, a duniya dai babu wanda yafi saurin 'kaskanta sai talaka idan baka da kudi sai a zage ka a tozarta ka a gabanka yaushe Uwani tazo gidansa da har zai tasa ta a gaba yana cin mutuncinta, Tunda suke 'yar tsama dashi bai ta'ba 'kuntata mata irin yau ba ta di

nga jin wata iriyar tsanarsa na d'arsuwa a cikin zuciyarta shi kanshi malam mai allon mugun haushinsa takeji a ganinta duk shine yake 'kara rura wutar al'amarin........Da kyar ta tashi tayi sallah magariba ta zauna har aka tayar da isha'i ta gabatar da sal

lahr sai ta kwanta kan daddumar bakin ciki duniya ya taru yayi mata yawa.

Sai wajejan goma da rabi na dare Al'amura sukayi sauki a babban boutique d'in...(Gurin sai da 'kananun kaya irin na yara da na manya maza da mata

takalma irin su booth helf cov

er da na yara da manya duk zaka samu a gurun a goguna masu kyau deznar iri iri akwai a gurin kai mutukar kana so ka had'a dreesing na kece raini to idan ka shiga gurin ka gama saboda zaka samu duk wani abu da kake bukata )kayan dake cikin boutique din *A.M

. B* Na mussaman ne dan sai ka gama xagaye kafatanin kasuwar kwari da sabon gari wambai da duk sauran kasuwanni baka samu irin oder shi ba Ahamdu na kawo kaya masu kyau da 'karko shiyasa kullum a gurin a ciki yake da Costoms duk wani ko wata mai ji da kans

a burinshi ya shiga gurin yayi siyayya......Har wannan lokacin suna tare da Khalifa sai bayan sun tabbatar da komai yayi clear sannan suka wuce gida........ Khalifa na draving yace."Afnan fa ta damu kullum kuka takeyi wai sai ankaita gurin auntynta tun sa

nda taji muna maganar da momynta zamuje gurin amarya shikkenan take rigima wai a kaita gurin aunty amarya ita dai."

Dariya yasa yace."Ai ni rigimar wannan yarinyar ita ke had'ani da ita haka kawai tazo ta hanani baccin dare tayi zamanta wallahi bana ne

manta.'

Khalifa yace." Kai dai kawai kace kar tazo ta hanaka amarci wa zaka mayar karamin yaro okey shikkenan tun da haka kace sai na kawo ta dan haka gobe ka shirya zamu zo tare da momynta kuma tare da kayanta zamu zo tunda anyi hutun skull sai ta zau

na ta d'ebewa amarya kewa."

Murmushi yayi ya dan tura hularshi 'keye yace."Kai a tunaninka amarci nake ci da wannan yarinyar? lallai Khalifa ka mance dalilin da ya sanya na aureta ko, shin mai zai sanya ni na 'bata lokacina a kanta da har zanci amarci d

a ita." Khalifa yace."Bafa zan dauki wannan maganar ba Alaji nasan dai idan bakayi me gabadaya ba to nasan kana tatta'ba ta dole ne nasan ba zaka sanya mata ido kawai kana kallonta ba." Murmushi yayi yace."Malam kai kake wannan tunanin ni sam! wannan yarin

ya bata bani sha'awa." Dariya kawai Khalifa yayi yace."Mubar maganar kawai ni dai ba karamin yaro bane na kuma san abinda za kayi da wanda ba zakayi ba

Har cikin gidanshi Khalifa ya ajiye shi dake a motarshi suke ya bude motar ya fito suna sallama, Kh

alifa yace."Ka fadawa amarya idan Allah ya kaimu gobe tana da babbar bakuwa saboda haka sai ta shirya." Yace."Ni dai tunda ba bakuwa ta bace shikkenan." Ya juya yana kokarin shiga ciki Khalifa yace."Kayi mantuwa fa." Sai sannan ya tuna shi masa site din ba

ya ya bude ya dauko wasu manya manyan ledoji guda biyu yana fadin"Na manta shaf wallahi." Garba ne ya karaso gurin yana musu barka da zuwa ya mika hannu ya karbi ledojin hannunsa, gaba yayi da ledojin a hannunsa shi kuma ya tsaya suna sallama da khalifa.

Tsit! palon tamkar babu wani mai rai a ciki....Ya nufi bedroom dinshi nan ya tarar dashi kaca-kaca har yanzu shimfidar gadon a hargitse take kamar dai yanda ya fita ya bari sannan ga tsintsiya da makwashin shara nan a tsakiyar kafet gashi kuma bata daki

n kamar yanda ya saba idan ya shigo ya ganta kwance tana bacci bata dakin yau! Ya ajiye ledojin hannunsa ya fita daga dakin.....Bedroom din dake kusa da nashi ya murda yaji a kulle gam ya wuce dayan shi yana murdawa ya bude babu kowa a ciki....Ya bude ba k

usa dashi shima bata ciki zarginsa yafi tabbata akan ta kulle a cikin wanda ya murda yaji a rufe.....Ya dawo a gajiye shi mai zai iya asalima tsintsiya bai iya rikewa ballanta ya iya wata shara dama su Garba ne suke masa aikace aikacensa, dan haka ma yanzu

Garban ya kira yace ya shiga ya gyara masa daki shi kuma ya zauna a palo yana duba wayoyinsa yini guda

yau bai duba wayar ba test messages gasu nan rututu haka dai ya dudduba wad'anda zai iya ya bari......Mutum ne shi ma'abocin jin zafi dalili kenan da ya

sanya ba ya zama da manyan kaya a gidanshi mutukar yana gida zaka same shi da gajeran wando iya gwiwa da shart ko kuma singilet ko cikin kayan bacci yafi tu'ammali da masu mad'aurai da botira idan ya ga dama ya daure ko yasa botiran idan bai ga dama ba ya

bar kirjinsa a bude, yanzu ma wata irin zufa ce take keto masa ba abinda yake so sama da ya watsawa jikinsa ruwa, Garba na fitowa ya mike ya nufi dakin Garba ya d'ebi wayoyinsa ya bi bayansa dasu.

_*Sanyi ko Basir na sanyawa gaban ki ya 'bude!!

!! ki Haihu ki'ki kula da gabanki shima na sanya wa ki bud'e ba tare da kin fargaba, Namijin dare (ba'kin aljani) idan yana kusantar ki ya kan janyo miki masifar bud'ewar gaba, kuyi ta rigima da miji idan da tsautsayi da rashin hakuri sai kiga an rabu!!

! wane mataki ya kamata mu dauka domin mu kare kanmu daga fad'awa cikin wannan tashin hankalin!?*_

Littafin na kudi ne........!

Kika futar min da book! Ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar.

*07084653262*

*BINT

A UMAR ABBALE*

[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys

*31*

Koda ya shiga dakin kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka ya fito sanye da rigar wanka, tsayuwa yayi gaban mirror ya goge jikinsa kana ya shafa vasilin a jikinsa gami da turaran jiki y

a sanya Karamar t-shart mai yankakken hannu da boxer tamkar wani sauri dan 20 years haka ya dawo kuruciyarsa ta fito fili dama kuma in dai zai sanya 'kananun kaya haka yake zama dan saurayi sosai suke masa kyau sai da kuma bai da ra'ayin sanya su ya fita '

karkarin shi ya sanya a gida kawai....Parlor ya fito ya nufi daining komai tsaf tsaf Rabe ya jere masa kayan abinci babu alamun an ta'ba komai a gurin.....Cikin mamaki ya fara bude kulolin abin bai ga alamar wani ya d'iba, ya zuba iya dai-dai cikinsa yana

ci a nutse yana had'awa da lemo, tunaninsa duk ya ta'allaka ne kan yarinyar babu shakka shima sai yanzu da ya zauna yayi nazarin abinda yayi mata yaga bai kyauta ba, bai kamata yayi nufin tozarta uwarta a gabanta ba duk lalacewar uwarka ba zaka so wani ya

ci mata mutunci a gabanka ba, amma baya jin ko da wasa zai iya tunkarar ta da niyyar ya bata hakuri idan ta gaji da fushin za ta daina........Sai misalin sha biyu da rabi ya bar palon.....Yau kadai da zai kwanta shi kadai a dakin sai yaji wani iri tsayin k

wanakin da tayi a gidan tana kwana a dakinsa har ya saba da hakan duk da kafin suyi bacci dukaninsu sai suyi fada sau nawa hakan nayi masa dadi in dai zai ga giftawarta a dakin, shi kanshi ya fahimci zuciyarsa ta damu da yarinyar kuma ya soma zargin wani a

bu ya soma ziyarta zuciyarsa dangane da yarinyar.....Da kyar! bacci ya dauke shi mai cike da tunani da mafarkin gashi yana saduwa da ita.

To itama nata 'bangaran hakane ya kasance....Tun rana da suka rabu ta kudiri aniyar bar mishi dakinsa tunda ya kira

ta da kazama, har yana mata gorin daki kana kuma yana cin mutuncin mahaifiyarta a gabanta yasa taji sam ba zata iya had'a numfashi dashi ba domin wani irin tsanar sa takeji a cikin zuciyarta, haka ta kwana ba taci abinci ba tun bayan abincin da taci da ran

a har garin Allah ya waye babu komai a cikinta.

Shida dai-dai na safe! Ya fito daga bedroom dinshi cikin shigar Kayan motsa jiki wani wando ne da rigarshi masu dan kauri wandon iyakacinsa gwiwa kuma ya matse masa jiki sai rigar mai yankakken hannu ita

ma ta kamashi sosai power dinshi ya fito kafarshi na sanye da booth, ya nufi kofar fita ba tare da yayi tunanin buga kofar dakinta ba yasan 'batawa kansa lokaci zaiyi kawai idan ya gama abinda yake ya dubata.......Ke'batancen gurin da gym dinshi yake gir

ki ya nufa, Ya hau kai ya soma yi babu ji babu gani Garba da Hani na tsaye a gefan hagunshi da damanshi, Ya jima kan Gym din kafin ya sauka ya kwanta kasan gurin yana hutawa, sararin samaniya ya zubawa ido yana kallo yana mai da numfashi Garba ya miko mas

a sassayan ruwan swn ya mike zaune ya karba ya fara tuttulawa cikinsa, a kuwa gumi ya yanke masa kamar wanda ya watsa ruwa, wata iriyar kwanciya yayi ya soma training a haka ya kai ya kawo haka ya dinga yi ko wace jijiya dake jikinsa ta mike gashin jikinsa

ya mike tsabar yanda jikinsa ke budewa, sai da ya kai kimanin minti talatin yana mota jikinsa a kwance kana ya saurara, ya kar'ni karamin towel dake hannun Hadi, yana goge jikinsa

Kira ne ya shigo wayarshi dake hannun Hadi yana daga kwance ya mika han

nunsa ya 'karba, Hajiya babbah ce! mikewa yayi zauna ya kara wayar a kunnanshi ya risinar da murya yana gaisheta ta amsa da sakakkiyar murya tana tambayarsa iyali! sai yaji wani iri jin abinda tace wai ya iyali? ya waske da fad'in"Lafiyarsu lau hajiya ya g

ida kwana biyu uzirrika sun sha kaina ban samu na shigo mun gaisa ba." Tace."Aikam dai jama'a nata cigiyar ango ranar da nayi yini na da jama'ata kowa haka ya hakura, duk sunayi maka Allah ya sanya alkairi." Ya amsa da "Ameen Hajiyata mybe gobe ki ganni in

sha Allahu." Tace."To to ai sai mu d'aga tamu tafiyar tunda zaka zo da mun shirya zuwa gidan naka tare da matan Kawun ka Almu." Yace."To babu laifu Hajiya sai kunzo din zan tsaya jiranku duk da ina da babban uzirin da zai fitar dani goben amma babu matsala

naji dadin zuwanku." Tace."Ai ba za'ayi haka ba kuma kada mu katse maka hanzari." Yace."Ko wane irin hanzari gareni idan ina neman albarka dole in tsaya in saurari zuwanku." Taji dadin maganarshi sosai tace"To Allah yayi maka albarka Ahamdu kaima Allah ya

baka 'yaya masu yi maka biyayya." Ya amsa da "ameen ya rabbi nagode. Sallama sukayi ya mikawa Garba wayar kana ya mike da towel din a hannunshi yana karkade gwiwarshi da ta dan 'baci! Yace." Garba zan shiga in kwanta in huta yau babu in da zani Khalifa na

n zuwa tare da iyalinshi idan ya kira waya kace na kwanta nasan sai bayan axuhur za su shigo lokacin na matse insha Allah." Garba yace."Okey sir zan fad'a mishi insha Allahu." Ya kama hanyar shiga cikin gidan.......Suka ce a tashi lafiya Yallabai." Ya ams

a da "ameen." Yana daga musu hannu.....Dai-dai lokacin da ta fito daga dakin da take a dai-dai lokacin ya shigo palon......Sai da ta kusa faduwa saboda razana! masifaffiyar yunwa ce ta fito da ita wacce take baraxanar cinye mata 'yan hanji taji zata mutu t

a futu afujajan domin samawa kanta abinci....Shi kuma wannan motsa jikin da yayi cikinsa kamar anyi masa yasa haka yake ji

sai kokawa 'yayan hancinsa sukeyi...Kalon kallo aka shigayi tsakaninta dashi, fuskarsa akwai alamun sassauci ba kamar ko da yaushe ba

, Juya tayi ta koma dakin fuskarta babu walwala har yanzu haushinsa takeji......Girgiza kai yayi ya nufi daining din, Rabe ya shirya break fast kamar yanda ya saba, a nutse ya had'a komai da kanshi ya zauna yana karyawa hankali a kwance.

Gefan bed ta

zauna ta zuba tagumi! abin duniya yayi mata yawai wai shin ya za tayi da wannan kad'dararran auran da aka la'ka ba mata, komai na rayuwarta ya tsaya! ta taso da kwajinta da bajinta an tsugunar da ita guri guda, wai me take jira ne? da ba zata nemawa kanta

mafita ba, Wata zuciyar tace mata "Ta ina zaki nemawa kanki mafita cikin wannan gidan dake tsautsare da matakan tsaro? Shawarar Camas! itace abun dubawa dole duk haushinsa da takeji ta saki jiki dashi ta samu ya bata Pose dinta domin tsira da muhiman abubu

wanta dake ciki, sashe na zuciyar ta yace mata " Kinga idan yaga kin saki jiki a gidan kin karbi auran hannu bibbiyu to zai dauka kin hakura xaki zauna zaman auran dashi kuma zai sassauta matakan tsaro a kanki daga nan sai ki samu damar guduwa abinki ki k

ai su 'kara kotu daga shi har malam mai allon.! Wannan shawara ta yanke a zuciyarta.

Yana gama break fast dinshi ya nufi bedroom dinshi wanka yayi ya fito ya shiya still cikin 'kananun kayan dai, farare tas riga t_shart da wando 3Qutar mai aljuhunai gab

a da baya, gaban rigar hoton zuciya ne an rubuta heart da bakin rubutu, sosai yayi kyau ya taje saisayayyiyar sumarshi mai tafe da sajensa cikin tsari! ya fesa turarenshi mai dadin kamshi, har yayi nufin kwanciya sai idanunsa suka sauka kan ledojin da ya

shigo dasu jiya da daddare , 'Kananun kaya ne ya shigo mata dasu yasan za tayi amfani dasu tilas watarana, daukar ledojin yayi ya bude dakin......Idanunsa suka sauka a kanta zaune kan kujerar daining din da cup din tea a hannunta tana kurba tana hadawa da

plantain, Ya karasa kusa da ita saitin kafafunta ya dure ledojin ''Gashinan nasan zasuyi miki amfani watarana." Kamar yanda bai kalleta ba sanda yake maganar haka itama ko inuwarsa bata kalla, Har yayi nufin barin gurin sai kuma ya tsaya ya d'an kalleta da

gefan ido, Yarinyar nada wani irin madarar kyau! gani yake har yanzu bai gama saninta ba kullum sai ya sake ganin abinda ke burgeshi a jikinta....."amm!!! Magana yayi niyyar yi sai kuma ya dagata, Ta kalleshi sa kwala kwalan idanunta da suke furgita 'yan

maza! ta wani risinar da kwayar idon cikin tashi tana masa wani malalacin duba, ta lura da akwai magana a bakinsa sai kawai ta dauke kanta tana cigaba da kurbar tea din a yangace sai kace wata d'iyar sarakai!! Hakan da tayi masa yasa yaji wata irin shak

kar ta abinda bai ta'ba faruwa dashi ba kenan ace yana jin shakkun yiwa wata d'iya mace magana, Dauriya ya aro a take yace."Idan anjima muna da baki! nasan dai zaki shaida babban abokin nan nawa Khalifa, shine zai zo tare da Iyalinshi."! Ya kare maganar i

danunsa tsaye a kanta.

Ta'be bakinta tayi ba tare da tace masa komai ba.....Yasan taji abinda yace, sai bai tsaya sauraran iskancin da take masa ba ya kama hanya ya shige bedroom dinshi ya kule yayi kwanciyarsa.

Tana kammala breakfast din ta dauki le

dojin da ya ajiye mata ta shiga dasu dakinta.

Zazzagesu tayi kan bed tana duddubawa, had'addun kananun kaya ne da wasu lafiyayyun kayan bacci amma kuma tsaraicinsu ya fito fili duk da ita kadai ke kwana ba tajin zata iya amfani dasu a jikinta saboda tsa

ro....Za dai tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login