Showing 114001 words to 117000 words out of 176422 words

Chapter 39 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

kudi ne.....!

Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE

*alliya:

'Yr Bngr Sys

*60*

Mai allo ya dan gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Kiyi shiru ki kwantar da hankalinki ki daina kuma kuka, sanar dashi ba yana nufin cewa zaki koma gidanshi bane, A'a za sanar mishi ne domin fita hakkinshi, ba wai dan

muna neman wani abu a gurinshi ba, yana da kyau ya san cewar har yanzu kina nan dauke da cikin nashi, kuma ya samu nutsuwar zuciyarshi, ni ba zanyi miki dole ba kamar yanda nayi a farko, ba zance tilas ki koma domin ki cigaba da zama dashi ba, zaki zauna k

i samu nutsuwar zuciyarki ki haihu lafiya kana ki za'bi namijin da yayi dai-dai da rayuwarki ki aura."

Bitan tace"Wannan magana da kayi itace mai kyau, saboda haka ki daina kuka kuma ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali ko dan saboda cikin jikinki insha A

llah babu wanda zai miki tilas kan ki koma zama gidan shi tunda bakyaso to Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." Wasila ta shiga goge hawayenta tana sauke ajiyar zuciya, Bitan ta mike ta nufi wani daki minti biyu ta fito daga dakin hannunta rike da fit

ilar kwai ta gyara a nutse ta gyara fitilar ta kunna ta koma dakin.....Kimanin minti goma tayi a ciki ta fito tana fad'in "Na gyara muku shimfida sai ku kwanta ku huta mussaman ke Wasila naga alamun gajiya a tare dake kiyi bacci sosai sai ki samu sassauci

da nutsuwar zuciya." Suka mike a nutse suka shiga dakin..........Bitan ta zauna kusa da mijinta suka cigaba da tattaunawa dangane da al'amarinsu Wasilan.

Dakin na shimfide da lede sabuwa da lalubewa masu dan kauri sai katifa ma dai-dai ciya mai cin mut

um biyu jakar kayanu ajiye a gefe, dakin dai ya ishesu su biyu ba tare da wani ya takurawa wani ba.....Wasila ta cire hijab din jikinta, ta janyo akwatin kayansu tana dubawa kaya mara sa nauyi zafi takeji idan da son samu ne ma ta watsa ruwa, saboda zafin

da takeji, Da kyar ta samu wasu riga da wando irin marasa nauyi sosai ta

saka a jikinta, ta nemi ta gyara tufkar gashinta, Rashida dake kokarin kwanciya kan katifar tace"Anti Wasila ni kuwa zan baki shawara.'' Ta kalleta tana fad'in "Wace irin shawara."?

Rashida ta mi'ke zauna a hankali tace" Dan Allah ki koma gidan Ahamdu wallahi shine marufar asirinki yanzu idan kince wani auran zaki sakeyi to ai baki san wanda zaki aura ba, kin san yanzu auranan zamani nan sai a hankali, amma ni ba tun yau ba nake sha'

awar auranki dashi wallahi, kuma idan kin duba kinyi tunani fa za kiga bashi da laifi dangane da abinda ya faru a tsakaninku, ke koma yana da laifi to naki laifin yafi nashi, saboda haka nake baki shawara kan dan Allah idan yazo da niyar mai dake gidanshi

ki amince kawai ki koma zakiji dadi muma muji dadi."

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon 'yar uwar tata tace"Wato Rashida har yanzu kwadayi da hange ne cikin ranki ko? Rashida ta girgixa kanta alamun a'a.......Ta cigaba da cewa''Idan ba kwadayi ba me zai

sanya kice min in koma gidanshi? Kince nafi shi laifi Eh na yarda na fishi laifi kuma na amsa laifina amma me yasa lokacin da nayi nadama na nemi afuwarshi bai yafe min ba? lokacin da nake kuka nake neman gafarar shi a lokacin ji nakeyi zan iya zama dashi

cikin ko wane hali saboda yayi min hallaci ya kuma yi min abinda ba kowa ne zai iya ba, ni ba nufina a kasheshi ba ko a cutar dashi, amma na lura shi abinda yake zargi kenan......Kinga duk mutumin da yake zarginka hankalinsa ba zai ta'ba kwanciya dani ba,

Ni nasan koda na koma gidanshi to koma mu 'kan'kare za'ayi sabida yana zargina, sannan kuma ni bana jurar wulakancin da raini sam mutumin nan baya ganin mahaifiyarmu da daraja da mutunci ban san dalili ba ko dan yana da kudi ne oho! , naji ciwo sosai ran

ar da kuka zauna a gidanshi keda Uwani ya wulakanta ku, yana da kudi yana ganin babu wanda ya isa! sannan kice na koma gidanshi, ai ko zan koma auranshi sai ya mutunta mahaifiyata, ballanta ma bana sanyawa zuciyata cewar watarana zan koma gidanshi in cigab

a da zama a matsayin matarshi, kawai Allah ya hada kowa da dai dai shi."

Rashida tace"Wallahi ba Kwadayi bane ni kawai mutumin yake burgeni yana da kirki da tausayin talakawa kinsan dama ance dan adam tara yake bai cika goma ba, kuma ni a ganina ba wai b

aya ganin girman u

wani bane kawai dai kinsan wasu masu kudin kuma ranar da mukaje ai bai san cewar mune ba shiyasa, ni daina zan cigaba da tayaki addua kan Allah ya karkato da hankalinsa kanki gaki dauke da cikinsa ai dole ma nayi sha'awar ki koma hann

unshi kuji dadin rainon danku." Tsaki taja tana fad'in "Ranki zai 'baci mutukar kika sake yi min wannan banzar maganar."! Rashida tayi shiru tana kallonta.....Mikewa tayi taje ta kwanta tare da rufe kafafunta, maganar rashida tasa duk wani bakin cikin dake

damunta ya dawo sabo, dal! ta dinga jan tsaki tana juye juye, hawaye ta share tana sake tuno lokacin da take birgima da ihu a gidanshi tana rirrikeshi ya taimaketa ya hakura ya mai da ita yanayi mata wulakanci, ai wallahi ta bar auranshi mutukar ta cika i

ta d'in 'yar halak ce........Da kyar bacci ya dauketa mai cike da mafarkai marasa dad'i.

Washe gari da safe da rubutu ta fara karyawa malam mai allo ya fara rubuta mata a'lkur'ani ya Umarceta tayi bisimillah tasha kana ta shafe cikinta dashi, sai da ya

tabbatar tayi yanda yace din sannan hankalinshi ya kwanta...........Bayan sun karya ne, sai sukayi wanka, rashida ta taya Bitan gyaran gidan ita kuwa Wasila dama tana yin wanka ta kwanta bacci mai nauyi ya dauketa.

****

Ya tashi cike da rashin walwala d

a rashin kuzari gabakid'aya duniya tayi mishi zafi ya rasa abinda zaiyi ya samu sassauci, da kyar ya samu ya kur'bi tea kofi daya, yayi kwance kan kuje daga shi sai singlet da wando iya gwiwa, wayarshi yake dubawa, ya bude ma'adanar hotonanshi, ya lalube p

ictures dinsu yana kallo, ji yayi hankalinsa ya tashi ya mike zaune yana rawar jiki, dan wayar har sai da ta kusa faduwa ya riketa da kyau, ya kurawa fuskar wayar......Da sauri ya mike ya nufi dakinshi, drowars ya shiga budewa nan naga ya fito da Pose din

ta da sababbin wayoyin da ya siya mata, zama yayi gefan bed ya kunna wayar yana dubawa, numbobin mutum uku ya gani tashi data As sai kuma wacce yaga ansa Hdz Camas! da sauri ya dauki numbar awayarshi dan yana zargin itace numbar yarinyar da yake nema tayi

mishi karin bayani......sai da ya kira sau uku kafin A daga wayar, Camas na kokarin shiga sabuwar motarta kira ya shigo wayarta koda ta duba taga sabuwar numbar bata damu ba saboda tasan tana hurd'a da mutane sosai Ta daga wayar da sallama a bakinta.

Ya

amsa a nutse yana fad'in "Ina magana da Hadiza ko."? Tace " Eh ko kace Camas! dan haka jamaa ke kirana." Ajiyar zuciya ya sauke, wanda har sai da taji a kunnanta, ya mike ya kunnanshi makale da wayar ya fito palo ya zauna kan kujera a Yace " Nasan Zakiyi

mamakin me magana dake, Ni ne Ahamdu Mijin kawarki Wasila."

Camas taji gabanta ya yanke ya fadi har sai da wayar ta kusa faduwa, baki na rawa tace"Yallabai ina wuni." ya amsa a nutse yace."Tambayarki zanyi.' Tace."Allah yasa na sani." jikinta duk yayi san

yi dan tayi tunanin ko zai tambayeta kan kud'adan wasila ne wanda ta riga tayi fata fata dasu mussaman da taji labarin sun bar gari gabad'aya sai ta sake sakin jikinta tana facakarta da kudi.

Yace."Ko kin san ina 'kawarki suka koma da zama."? Shiru tayi

tana tunani, Yace."Ke nake sauraro." Tace"Yallabai ban sani ba wallahi dan nima sai labari naji a gari wai sunyi tafiya amma dai nafi tunanin ko can kyauyensu suka nufa Garko."

Yace."Basu nufi can ba domun kawun su ya tabbatar min da cewar basu je mish

i ba ya dai ce yana tunanin sunbi mahaifiyarsu, shin ko kin san inane garin su mahaifiyar tasu." Tayi shiru tana tunani kafin tace"Wallahi na san sunan garin amma ya kwanta min bari yanzu in kira mahaifiyata a waya nasan ita bazata rasa sani ba, insha Alla

h zan kira ka sai na fada maka."

Yace."Okey to ina sauraranki."! Camas! ta kashe waya tana tunani cikin mota, shin me yasa guy nan yake son sanin inda Wasila take, ko dai zai mayar da ita ne a matsayin matarshi, tabdijam idan hakane kuwa wallahi ba zat

a fad'a mishi ba, key tasa zata tashi mota, kiranshi ya shigo tayi banza da wayar har ta katse....Ta tashi motar ta tanaji wayarta nata famar ringnig amma taki dauka, har sai da ya gaji ya hakura.

Yana zauna rike da waya ya rasa ya zaiyi amma yarinyar n

an ta shammace shi gabakidaya ya d'o

ra buri da tunani a kanta yana tunanin koda sunanan garin da suke ya ji ya san mutukar sun shiga garin tunda ba'ki ne nemansu ba zaiyi wuya ba, bai hakura ba ya cigaba da kiran wayar yana ta adduar Allah yasa ta da

uka

kawai sai yaji ta kashe wayar ma gabad'aya, ya dinga bin wayar tashi da kallo tamkar wani zautacce.

****

Yau kwanansu hud'u a Garko hankalinsu ya kwanta sosai Wasila ta mirmure ta samu lafiya sai abun da ba'a rasa ba, kuma laulayin ya danyi sauki

sai dai jefi jefi take amai shima da safe takeyi kafin ta karya......Bata aikin komai Bitan da Rashida suke aikin gidan kullum malam mai allo cikin siyo mata kayan gon yake irinsu d'ata da goba mangwaro da sauransu, sannan kullum sai tasha rubutu da tofi

safe da dare, ita kanta yanzu ta soma samun kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya mussaman in ta juya gabas yamma kudu da arewa tana ganin 'yan uwanta da danginta na shige da fice a gidan.....Ita kanta Hajara kullum a tafe take idan bata zo yau ba to gobe z

aka ganta tazo kuma bata zuwa gidan hannunta haka kawai sai ta tazo musu da tsarabar kayan kwadayi.................

Malam mai allo da kanshi ya shiga kasuwar garin ya siyo musu abubuwan bukata dai-dai karfinshi yanzu babu wani abun da zasu nema su rasa

a gidan dai-dai silafas na yawo a tsakar gida mai allo ya siyo musu ko wanne da nashi.

******

'Bangaran Ahamdu kuwa jinya ya kwanta ta tsayin sati uku har sai da Hajjah tazo gidan tayi jinyarshi wanda sai a lokacin ma ita ta san abinda ke faruwa, a

ikuwa ta shiga yi mishi fada tamkar ta ari baki, taji ciwon abinda ya aikata shi ba yaro karami ba, an samu yayi auran kuma baije ko ina ba ya fara saki, ai mutane ma sai su daukeshi karamin mutum......Ahamdu baya so ya fada mata dalilin da ya sanya hakan

ta faru kawai dai yace mata tsautsayi ne da kaddara, ita kuma tace lallai sai ya kaita gidansu yarinyar tayi bikonta, nan yake shaida mata shima yanzu halin da ake ciki bai san inda yarinyar take ba, Hajjah ta dinga mamaki Yace."Naje can garin nasu gurun

waliyyinta shine ya tabbatar min da cewar bata gurinshi amma yafi tunanin tabi mahaifiyarta garinsu, to inda aka samu matsala shine shima bai san wane gari ne ba."Hajja dai ta dauki laifin kacokan ta dora a kanshi ta kuma ce idan haka zai dinga auran yar

an mutane yana saki to babu ubanda zai bashi auran 'yarshi mutukar ba kwad'ayayyan abin duniya bane......Tace kuma lallai idan ya samu sauki ya dauketa ya kaita can gurin mai allon a bashi hakuri a bisa abinda akayi mishi, bai musa mata ya amince da magana

rta saboda dama can baya tsallake umarinta

****

Bayan Sati biyar.......Cikin Wasila ya fito sosai dan har ya hud'a zani yayi kurcici dashi kamar an kifa 'kwarya yanzu yana matakin wata biyar da kwanaki, tayi kyau sosai ta murje ta daina laulayi yanzu

komai tana ci ta zauna lafiya ta daina amai da sauransu, sai dai kuma yanda cikin ke mata motsi a cikinta ne yake damunta, ga wani uban cin abinci da takeyi mutakar tana jin yunwa idan bataci abinci ba sai jikinta yay ta kyarma shiyasa kullum bitan cikin

d'orawa da saukewa takeyi bata bari abinci ya yanke mata, sabida Wasila ta zama rumbu.

*****

Sun shirya tsaf tsaf! shida Hajja suka fito harbar gidan nashi, ya fito da wayarshi yana neman numbar Khalifa sai kiranshi ya shigo da sauri ya kara a kunnan

shi Khalifa yace "Anya kuwa tafiyar nan dani za'ayi kuwa! Wallahi Hafsa ce ta tashi da zazzabi me zafi yanzu yanzu zan kaita a dubata muna zargin dai ko an samu 'karuwa ne."

Yace."Ayya! Allah ya sawa'ke! babu matsala bari mu tafi kawai insha Allahu zam

u shigo nida Hajjah sai mu dubata." Khalifa yace."Okey babu damuwa A mika min gaisuwa gurin aramma." Yace."Zaiji insha Allahu." Yana kokarin kashe wayar ne Khalifa yace."Allah yasa idan kaje kawai ga mutuniyar taka tana cire kafa da kyar! dan cikin nan yan

zu nasan yayi kwari." Ya d'anyi ya'ke wanda hausawa suke fad'in yafi kuka ciwo "Khalifa bana tunanin akwai cikin nan fa." Khalifa yace."Kar ka cire tsammani abokina." Yace."To Allah ya amshi adduarka." Khalifa yace."ameen ya rabbi sai kun dawo kenan."? Yac

e."Insha Allah." Kashe wayar yayi ya mayar aljihu kana ya nufi

parking spece lokacin Garba nata 'kokarin karkad'e mota Hajjah na gidan baya a zaune, kawai shima sai ya bude ya shiga ya zauna kusa da ita, Garba ya shiga ya zauna maxauninshi ya kunna m

otor a nutse suka fita daga gidan, Yayin da ma'aikatan shi ke faman yi mishi fatan alkairi da dawowa gida lafiya.

Littafin na kudine......!

Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biyaba kema keda Allah! Whasap numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys

*61*

'Katuwar tabarma ce shimfid'e a tsakar gidan, Wasila na kwance hannunta rike da mafici tana fifita zafi ake sosai a garin ga dukanin alamu ruwan sama na dab da sauka mai allo yana gefe kan buzunsa da wani ma dai-dai

cin allo a hannunshi yana rubutu, Bitan da Rashida suna daga can gefe suna aikin gyara zabbi wanda malam ya sanya d'anshi Tanimu ya yanka su saboda Wasila wai ta dinga samun kuzari da karin jini da lafiya shiyasa ba'a daukar lokaci ake soya mata kaji da d

afaffan kwai duk sanda ya fita kasuwar cikin gari kuwa sai ya siyo mata manya manya kifi masu kyau da kara lafiya.........Ya d'an kalleta tana kwance tana aikin fifita sai gumi take Yace."Da alama dai yau garin ruwa ne zai sauka shiyasa zafin ya tsananta d

a yawa." mikewa tayi zaune tana gyara daurin dankwalinta tace" Kawu malam Allah zafin nan duk ya gigitani na rasa yanda zanyi." Murmushi yay yace."Bake kad'ai ba wasila nima Allah Allah nake in gama miki rubutunan in fita insha iska a waje duba dai dik gi

rman gidanan babu iska ga rana ta game ko'ina." Bitan dake sauraron hirar tasu tace"Ai idan kaga irin wannan ranar to tabbata ta ruwa ce dan haskenta yayi yawa, dubi gabas ka gani hadari ne sosai shiyasa nake sauri in gama ayyukana kafin ruwa ya sauka." Wa

sila tace"Allah gwara ayi ruwan ko a samu sassauci ni akwana ma anayi.'' Mai allo yasa dariya yana fad'in "Wato ke kanki kika

sani ko? idan anyi an kwana ana ruwa 'yan kasuwa suce me? wani fa sai ya fita zai samo abinda zai kaiwa iyali." Tace"Allah Kawu ma

lam zafin ne ya isa Allah na tuba." Bitan tace"Aike Wasila dole ne kiji zafi saboda lalurar dake jikinki dama haka masu ciki suke da jin zafi." Tace"Aikam dubi wuyana kuraje duk sun fito, ni ruwan sanyi ma nake so." Mai allo yace."Wannan ne kuma baki isa b

a! za'ayi miki komai wanda kike so amma banda shan 'kankanra." Marairaicewa tayi tace"Kawu malam ba 'kankanra zansha ba ruwan sanyi fa nace don Allah a taimaka asiyo min." Shiru yay yana cigaba da rubutunsa, ta dinga magiya tana karyar da kai! Yace."Bari T

animu ya shigo." Da sauri tace''Kawu ka bawa rashida kud'in ai tasan gurin." Yace."Bana son aiken rashida gurin nan akwai maza." Shiru tayi tana had'iyar miyau da kyar ma'kogwaronta duk ya bushe! Kallonta yay ta bashi tausayi kwata kwata yanzu baya so yag

a abinda zai 'bata mata rai ko ya sata a damuwa, ya kalli Rashida dake wanke hannunta bayan sun gama aikin, yace."Zo kar'bi maza jeki bakin gada gurin masu siyar da ruwan sanyi ki siyo mata kar a bada mai 'kankara." Rashida tace "To ta karaso da sauri ta '

karbi kudin, hijab tasa ta kama hanya ta fita bayan ta dauki wani jug mai dan girma.

Tana fita dalleliyar motarshi ta karyo kwana zata shigo cikin layin......Yara yaran dake wasa a bakin hanya suka watse suna ihu da bin motar da kallo, Rashida na tsaye

a bakin kofar gidan motar tayi parking a wani fili dake gefen gidan.....Wucewa take kokarin yi yay gaggawar bud'e motar ya fito gabanshi na wani irin fad'uwa, babu abinda yake fad'i cikin zuciyarshi sai alhamdullihi."!!! Rashida tayi saurin dafe kirjinta t

ana kallonshi Sai kuma ta washe baki wanda kana ganinta kasan tana cikin farin ciki.......Garba ne ya bud'ewa Hajja mota ta fito tana mita da fad'in " Zaman mota ai sai ya saka ciwo tafiya ba tafiya ba 'kafafuna duk sunyi tsami.'' Hannunta ya d'an ri'ke k

ana ta gyara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login