Showing 126001 words to 129000 words out of 176422 words

Chapter 43 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

ta rintse idanunta

tana salati, dama tun a cikin mota takejin yanda cikin ke tattare mata yana dunkul

e mata guri guda, kwallah ta cika mata ido bakinta na rawa tace"Rashida 'kafana d'aya ta ri'ke gefan marata ya daure." Rashida tace"Ki daure anti wasila zaman mota ne yaja mu shiga ciki ka zauna sai in matsa miki kafafun naki." Yana tsaye suna magana d

a Garba yaga sun tsaya sai ya sallami Garba ya nufi inda suke.......Rashida na ganinshi tace"Wai kafarta ciwo take." Yace"Subahanallahi! to me ya jawo hakan."? Rashida tace "Nima ban sani ba watakila kuma zaman mota ne." Ya kalli Wasilan yaga tana kuka tan

a kokarin zama kasan gurin......Yace."Kada ki zauna anan mana tashi mu shiga ciki ki samu kiyi wanka sai ki kwanta ki huta."

Shiru tayi ta'ki tanka masa bala'in haushinsa takeji a ganinta ba kowa ne ya jawo mata wannan masifar ciwo ciwon ba sai shi.....Ga

nin tana had'a zufa a gurin rana na dukanta yasa ya sunkuya ba tare da yayi shawara da ita ba ya dauketa cak daukar jira jirai yayi mata ya nufi cikin gidan da ita......Duk da halin da take ciki sai da taji wani iri kunyar ma'aikatan gidan duk ta rufe ta t

asan dai dole idan wasu ba sugani ba wasu zasu gani Uwa uba ga 'Kanwarta Rashida, rufe idanunta kawai tayi ta 'boye fuskarta cikin 'kirjinshi.....Rashida tabi bayansu tana sinne kai fuskarta dauke da murmushi sosai mutumin yake burgeta saboda irin kulawar

da yake bawa 'yar uwarta.

Hajja tace"Subahanallahi! me ya faru haka."? Yace"Zaman mota ya sanya kafafunta tsami ta kasa tafiya dasu." Hajja tace"Aifa dama zaman mota ma ga mai lafiya babu dadi ballanta ga mai ciki sannu Wasila ka shiga da ita ciki tayi

wanka sai suci abinci su huta.'' Baice komai ba ya shige da ita bedroom dinshi, kai tsaye bad ya kwantar da ita ya nufi toliet.

Mikewa zaune tayi a hankali tana d'an mikar da kafafunta wacce tafi takura mata da ciwo ta dan tasa kad'an! ta rintse idonta

tana kiran sunan Allah can taji zillo a cikinta ta bude idanunta da sauri tana sauke ajiyar zuciya, yanzu zai isheta da kusurkusur a ciki idan ba abinci taci ba babu zaman lafiya.....Fitowa yay daga toilet din yana tattare hannun rigar dake cikin shi tayi

saurin dauke kanta ya 'karaso inda take ba tayi aune ba taji ya dauketa, da sauri ta kalleshi ya d'aga mata girarshi guda, dauke kanta tayi tana zumbura baki kamar zatayi kuka itafa wannan za'kewar da yake a kanta sam baya burgeta taga sai wani rawar jik

i yake mata tasan dai ba komai ya sanya shi yake mata hakan ba sai dan tana dauke da cikinshi.....A hankali ya dure ta tsakiyar bandakin yana mata wani munafikin kallo ya dora hannunshi a wuyanta, tureshi tayi ta jingina da bango (garu) gabanta ne ya soma

faduwa, Ya sake matsowa kusa da ita, sai kawai ta saka kuka tana ture kirjinshi, cikin taushin murya yace"Wanka zanyi miki ba wani abu ba, ke kuka baya miki wuya ko."? Cikin nauyin baki da yanayi na gajiya tace"To ka barni mana nayi da kaina da can kaine k

ake min?" Ya shiga kallonta yana girgiza kanshi, yace." Daga yau nake so duk wata d'awainiya taki ta dawo hannuna ni mutum ne mai tausayin masu lalura irin taki, insha Allah mutukar ina gida zan dinga dauke miki dukanin laluranki har Allah ya saukeki lafiy

a."

Shiru tayi tana kallonshi anya kuwa zata amince da wannan dad'in bakin nashi? itafa tafi tunanin saboda cikin sa da take dauke dashi ne yasa yake rawar jiki a kanta.......Saukar hannunsa taji a bayanta yana kokarin zuge zuf din rigarta, ta dinga ture

shi tana hawaye hakan be dameshi ba sai da ya cire mata kayan jikinta tas, ya kurawa cikinta ido da yayi kurcici a mararta, wata kwallah ce ta ciko a idanunsa, ya tsuguna gwiwa

bibbiyu 'kasan toilet din ya dinga sumbatar cikin yana shafashi da hannunshi, W

ann

an k'wallar dai da yake ta 'boyewa sai da ta sauka, yay gaggawar gogewa, tana kallonshi taji ya dan bata tausayi, dan janye jikinta tayi ta matsa gefe tana zum'bura baki.....Ya sake binta yana rike hannunta duk jikinsa yayi sanyi wani irin masifaffa

n son yarinyar yaji yana bin dukanin ilahirin jikinsa......A hankali yaja hannunta suka isa inda kwamin wanka yake ya dauketa ya shiga da ita cikin ruwan da ya had'a, ido jawur yake kallonta yana jin wani masifaffan fleening na taso mishi, soso da sabulu y

a dauka ya shiga cud'a mata jikinta yana sakin ajiyar zuciya, kamar kwai yake ta'bawa haka yake cud'ata sai da ya tabbatar ya wanke ta tas kana ya dauki towel mai kauri ya nad'eta a ciki......Daukar ta yayi ya fito da ita ya zaunar gefan gado.....Vasilin y

a dauko ya nufi inda take zaune, warware towel din ya shiga yi ta rike towel din mirya na rawa tace"Ni ka bari shafa mai ai bai da wuya zan shafa da kaina." Girgiza kansa yay saboda idan yace zaiyi magana cikin halin da yake ciki zai iya tona asirin kanshi

, ya kar'be towel din daga hannunta ya aje gefe guda, a hankali ya haye bed din ya raba 'kafafunshi ya sanyata a tsakiya ya shiga shafe mata jikinta da vasilin din, girman nonowanta da yanda suka sake kumburi da bun'kasa shine yake gigitashi yake d'imaut

a shi ya dinga kokarin daurewa duk dan kar ya nuna zulamarsa a fili al'amarin ya gagara bai san sanda ya jefar da vasilin din ba ya sanya hannuwanshi duka biyun kan nonowan ya shiga lailayasu yana jan nipples din tare da sauke masifaffiyar ajiyar zuciya...

... Da sauri ta mi'ke zaune tana kuka tana kare jikinta da blanket ta dinga watsa masa harara tana share hawaye......Hannu ya d'aga mata yana so yayi magana sai kuma ya fasa, jiki a sanyaye ya sauka daga bed din ya bude wardorve ya dauko mata riga da zani

na atamfa (vilsco) ya mika mata muryarshi a 'kasa yace."Kar'bi ki sanya." Hannunta na rawa ta kar'ba saboda bata so tayi musu yace zai 'kara kusantarta, yana mi'ka mata kayan ya kama hanya ya fice daga d'akin hankalinshi a masifar tashe.

Da 'kyar tasa k

ayan tayi kwance a bed tana siyayyar da hawaye sam bata jin zata iya sakewa dashi kamar da a yanzu babban burinta bai wuce ta rabu da cikin dake jikinta lafiya ba............Bacci ne ya fara fizgarta sam yanzu bacci bayayi mata wahala, mussaman yanzu da t

a samu daki mai cike da 'kamshi da sanyin na'urar sanyaya guri, bacci mai nauyi ya dauketa.

Jin shuru bata fito ba ya sanya Hajja tace Rashida ta shiga dakin ta gani ko lafiya? Rashida na shiga ta tadda ta kwance a bed tana bacci, murmushi kawai tayi ta

fito tace "Hajja bacci takeyi." Hajja tace tace"Koda naji ai shuru din tayi yawa, to ga abinci can ke sai ki zuba wanda zai miki kici idan ta tashi sai taci nata." Rashida tace"Nagode hajja." Daining din ta nufa domin cin abincin.

Ahmadu kuwa kai tsaye

ke'bantaccan gurin hutawarshi ya nufa dake bayan gidanshi, yayi kwance kan wani irin gado mai kamar lilo yana lilashi idanunshi a rufe abin duniya yayi mishi yawa, ada da bata kusa dashi yana daurewa amma kuma yau din nan da ya kusance ta yaji hankalinshi

ya tashi sosai wanda har baya so ya sake shiga gidan ya ganta gudun aikata abinda baiyi niyya ba, ya kuma lura da yarinyar kamar tana tsoranshi yanda take zabura idan ya kusanci jikinta tilas dama hakan ta faru a tsakaninsu tunda rabuwa ce sukayi ita das

hi mara dad'i! amma dai shi yanzu babu sauran wani 'kulli a cikin ranshi ya amince da tubanta kuma yana so suyi

zama na kwarai zaman da kowane ma'aurata keyi, ammafa ya zauna yayi tunani da nazari hakan ba zata kasance ba har sai yayi kokarin dauke idonshi

daga kanta, ba zai yuwu ba ace daga dawowarta ya fito da zulamarshi a fili dole ya dinga dauke kansa yana kuma nuna mata ba wannan ne ma'kusudin abinda ya sanya ya dawo da ita gidanshi ba, da wannan shawarar ya mike ya nufi cikin gidan dai-dai lokacin da

ake kiran sallah la'asar.....Hajja da Rashida ne zaune a palon suna kallo suna hira ya shigo sannu yay musu ya nufi bedroom dinshi hajja tace"Yana da kyau idan ka shiga ka tasheta tayi sallah barcin yamma bashi da dadi ko kad'an Mafi akasarin masu ciki k

uma sunfi s

on irinshi." Yace."Kwarai kuwa Hajja annabi ma ya hanemu da yin bacci tsakanin azuhur da la'asar bari na tasheta yanzu."

Yana shiga dakin ya tarar da ita ta tashi idanunta na kallon rufin dakin....Ya karaso kusa da ita cike da kulawa yace.

"Ki tashi kiyi sallah ina fatan 'kafar naki ya daina ciwo."? Daga masa kanta tayi yace."To alhmdullhi." Toilet ya nufa ta bishi da kallo tana ayyana abubuwa da yawa a kanshi ya fito daure da alwala ya fice daga dakin, a hankali ta sauko daga bed din ta nu

fi toliet din bakinta ta wanke sannan ta d'aura alwala ta fito, sallahr ma da kyar tayi saboda yana take jin wata shegiyar yunwa idanunta har rufewa sukeyi saboda rawar jiki wuyanta da hijab din da tayi sallah ta fito tana rarraba ido a palon......Hajja da

Rashida na daki suna sallah sai shi kad'ai ne kan kujerar daining yana had'a abinci ya hangi fitowarta, had'a ido sukayi ta dauke kanta jikinta babu kwari ta nemi kujera ta zauna, ya gama had'a abincin cikin plate ya dauko a nutse ya kawo mata inda take,

ba tayi musu ba ta 'karba ta dora saman cinyarta ta fara ci da bisimillah a bakinta ya kawo mata ruwa da lemo ya aje gabanta ya juya domin komawa daining din ta bishi da kallo tana mamakin yanda ya zama wani silent babban mutum mai kudi da shekaru gami d

a tarin ilimi na boka dana isilma shine ya mayar da kanshi bawa a gurinta, mamaki take sosai sai kuma wani sashen zuciyarta ke fad'a mata cewar "Duk wani abu da zai miki shi a yanzu yanayi miki shine saboda d'anshi ko 'yarshi da kike dauke dashi amma da b

abu cikinsa a tare dake kallo baki isheshi ba sai dai idan jarabarshi ce ta kawo shi. Girgixa kanta tayi kawai tana adduar Allah yasa ta sauka lafiya tagani zai cigaba da hidima da ita ko kuwa.

Littafin na kudi ne.....!

Kika futar min da book n

a barki da Allah! Kema kika karanta baki biya ba na barki da Allah! Whasap numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*alliya:

'Yr Bngr Sys

*65*

Koda ya kammala cin abincinshi sai ya mike a nutse ya nufi bedroom dinshi yana tafiya tamkar wanda 'kwai ya f

ashewa a ciki, shi kad'ai yasan abinda ke damunshi, hakika dawowarta gidan nashi na barazana da lafiyarshi dan tun suna cikin mota yake ta fama da joystick dinshi yana hanata aikata abinda takeso dan duk abinda yake daurewa yake yi a yanzu dai idan ba samu

yayi ya rage damuwa ba to tabbas dai ya san yau da 'kyar idan zai

iya rintsawa........Wanka yayi ya shirya cikin yadin kashmir d'an gasken milk colour mafi akasari kayanshi farare ne bai fiye sanya abu mai duhu ba duk da ya kasance farin mutum, ya tsaya

gaban mudubi yana gyara wuyan rigarshi kana kuma ya dan gyara saisayayyar sumarshi ya daura agogo a hannunshi, turaranshi mai dadin kamshi ya fesa ya fito palo hannunshi rike da hularshi yana gyarawa, Tunda ta daga kanta sau daya suka hada ido dashi ta ma

i da kanta 'kasa gabanta na fad'uwa, ganinshi tayi tamkar sabuwar hallita kamar wanda aka 'bareshi a akwali (sabo) yayi wani fresh dashi fatarshi tayi luwai luwai annuri sai sauka yake kan kyakykyawar fuskarshi.....Hajjah tace"Au na d'auka yau d'aya zaka z

auna a gida tunda matar gidan ta dawo sai ku tattauna a tsakaninku amma naga ka shirya zaka fita." Ya danyi gyaran murya yana d'ora hular a kanshi yace."Ba zan jima ba zan dawo insha Allah akwai ba'kin da zanyi zamu had'u dasu can gest house d'ina dan alre

ady ma yanzu suna can suna zaman jirana." Hajja tace"To Allah ya kiyaye a dawo lafiya." Rashida tace"Yayana Allah ya tsare." Ya amsa cike da kulawa. Ya d'an saci kallonta dai-dai lokacin data d'ago kanta suka had'a ido dashi, murmushin sa mai tsada ya sak

ar mata yana d'an d'aga mata girarashi guda kamar dai yanda ya saba, tayi gaggawar mayar da kanta 'kasa kamar bata so tace"Adawo lafiya." Bai tsammanin hakan ba sai yaji dad'i sosai yace."Amin amin." Ya nufi kofar fita, tsintar kanta tayi da binshi da kall

o har sai da ya fita sannan ta mai dauke kanta tafiyarshi ma abar kallo ce komai nashi a nutse yake ya cika namijin da ko wace mace zatayi sha'awar aure amma ita har yanzu tana shakku a kansa dan tana jin tsoron ta sake sakin jikinta dashi wani abun ya had

'asu na kuskure yazo ya saketa ko yaci mata mutunci amma itama tana hango tsantsar son da yake mata a 'kwayar idonsa.

A can gest house din nashi Khalifa ne tare da Alhaji Muktari daura dan takarar governor jahar katsina ya kawo masa ziyara tare da dashi

da mu'karrabansa, dake jam'iyarsu daya shiyasa suke zumunci kuma kusan halinsu yazo d'aya da juna, Alhaji Muktari ya ta'ba zama governor a jahar katsina yanzu yana so ya maimaitane yana kuma so ya karya al'kadarin governor dake ci a jahar tasu mai suna E

ngineer Haruna Haruni mutum ne mugu wanda yake mulki bisa zalinci halinsu d'aya da mai girma governor Lawan Rabo governor dake ci a jahar kano, duk wani 'kulla 'kulla gami da cuta da zalinci tare sukeyi dan duk abinda Lawan Rabo yayi a jahar sa to lashakka

Haruna haruni shima sai yayi a tashi jahar, Wannan dalilin ne ya sanya Alhaji Muktari zuwa gurin abokin nashi domin su shawarta abubuwan da zai amfane su ya kuma amfanin al'ummar jahohinsu...............Tunda Governor Lawan Rabo ya samu labarin zuwan Alh

aji Muktari garin sai ya dami kanshi, sosai ya kira Abokin nashi ya shaida mishi abinda ke faruwa, Haruna Haruni yace." Nasan ba zai bar garin ba tilas sai shigo ku gaisa kada ka nuna masa komai kamar yanda suke abunsu a lullube muma zamu bisu a haka, ai y

anzu ya'ki d'an zamba ne muke kan kujearar mulki sai munso wani zai hau ka daina tayar da hankalinka kan komai kuma Amadu ya daina firgitaka, komai fa na hannuka a yanzu koda Amadu ne ya cika za'be sai munyi juyin mulki ballantana kuma muna da mai matacci

ya wannan maimai d'in ko sun so ko sun'ki sai munyi idan zaka shigo katsina ka shigo a shirye domin tilas ma a wannan karon mu kauce hanya mubi matasan yaran nan a sannu su samo mana 'kananun yaran da zamu bawa mai matacciya yayi mana aiki a kansu, tabbas

dai nasan baka mance abinda ya faru ba a shekaru uku da suka gabata." Lawan Rabo ya sauke ajiyar zuciya yace."Tilas shawararka ita

ce abun dauka a gaskiya yanda naji dad'in wannan kujerar zai yi wuya na barta kai tsaye kai ni ko da d'an da na haifa za'

a bu'kata zan iya badashi tunda dai nasan ai ba gama haihuwar nayi ba.'' Haruna haruni yace."Haka ake son cikkaken namiji jarumi me a'kida, kada ka damu idan Muktari ya shigo fadar gomnati ka kar'beshi hannu biyu zamu 'bullo musu ta bayan fage, mulki dai

sai dai suga anayi insha Allah duk jama'ar da suke dashi sai ta dusheshe ranar za'be mune zamu lashe." To Wannan maganganun da sukayi ne ya sanya Governor Lawan Rabo kwantar da hankalinshi kamar tsumma a randa, ya tabbatar suna da ya'kinin akan cewar m

utukar bokan da yayi musu aiki da 'kuk'onan kawunan yara yana nan a raye cikin duniyar to sun tabbata sai sun watsa shirin su Amadu da Muktari

Amadu na isa gest house din nashi Alhaji Muktari ya soma tsokanarshi da fad'in "Da har ina cewa bari mu tafi

tunda dai mu gaisa da Khalifa ya isa kai sai ayi maka uziri tunda kana tare da Uwargida." Amadu ya zaune kan kujera yana murmshi hularshi ya cire yana kallon Khalifa yace."Nasan wanda ya fad'a maka cewar ina tare da Uwargida" Khalifa yace."Nine na fad'a m

ishi da kayi zamanka ma yayi maka uziri ko bakaji abinda yace bane." Murmushi yayi yana girgiza kanshi yace."Uwargida bata da 'koshin lafiya me kuke tunanin za'ayi."? Alhaji Muktari ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare Yace."Yana da kyau dai muje n

a dubata kafin na wuce, dan Khalifa yanzu yake shaida min an samu 'karuwa to Ubangiji Allah ya raba lafiya." Amadu yace."Ameeen ya rabbi, yace." Khalifa ya fad'a maka na samu 'karuwa shi bai fad'a maka tashi 'karuwar ba.''? Alhaji muktari ya kalli khalifa

da son jin 'karin bayani." Khalifa yasa dariya yana kallonshi shima Amadu yace."Shima iyalinshi juna biyu gareta." Alhaji Muktari ya shiga girgiza kanshi yana kallonsu da fad'in "Gaskiya mutanan nan bakwa wasa." Khalifa na dariya yace."Bama wasa ko dai ba

ka wasa Alaji matanka biyu 'yayanka shida ai kaine shugaba gwara mu da mace daya muke zaune." Alhaji muktari ya dan tura hularshi 'keya yana gyara zamanshi yace." Ai mata biyu shine jin dad'i Alaji sai ranar da kukayi zaku gane haka.'' Amadu dai murmushi y

ake yace."Duk mutumin dake da mace biyu bashi da kwanciyar hankali Alaji bana jin zan iya had'a mace biyu a gidana in dai ba Allah ne ya 'kaddara ba."

Khalifa na d'auke da murmushi a fuskarshi yace."Ni kam ina tsammanin had'a mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login