Showing 24001 words to 27000 words out of 176422 words
da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin
waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orang
e_
*Free Pege16*
Uwani ta fito daga kicin tana fad'in"Da alama dai mutumin nan ya gaji da tsayuwa ya tafi haba! jama'a wai babu dama aga Allah ya rufawa mutun asiri sai a dinga bakin ciki! kiga mutum da rigima haka kawai ka ni'ko gari gari ya gar
i kazo kace zaka dauke min 'yaya saboda munafurci nasan magulamata ne suka kai masa gulma shine shi kuma ya bazamo babbar riga yazo har gidana ya nuna min iko to ni babu wanda ya isa yace zaiyi min iko da 'yayana 'yan uwana ma ban d'agawa 'kafa ballanta wa
ni saboda haka ke Rashida maza maza ki kira Wasila a waya kice tazo yau d'in nan ta dauke mu a mota mu bar nan tunda har wannan tsohon ya soma zuwa shikkenan kuma zai ta daga mana hankali gwara kawai a nemu mu a rasa a unguwar."
Rashida tace"Ni wallahi ta
usayinsa nakeji gaskiya Uwani banji dadin abunda kikayi masa ba Kamar uba yake a gurinmu kin tozarta shi a unguwa." '' Ayyo kina so ki nuna min kinfi kaunarsa a kaina ni dana tsuguna na haifeki naci kashinki da fitsarin ki shine zaki butulce min shi me ya
ta'ba tsinana miki a rayuwa." Rashida tace"Wallahi kafin babanmu ya mutu ya fada min lokacin da aka haifeni da ya rasa yanda zaiyi da hakika can kauye ya nufa gurin Malam mai allo din ya bashi katuwar tinkiya aka rada min suna da ita." Uwani tayi kasake ta
na kallon 'yar tata ashe kafin
mijin nata ya mutu sai da ya fada musu abubuwan da suka faru a baya....."To ai hakika dama dole ce a wuyansu take idan basuyi ba ai sai a kira ki da shegiya gwara ma ki daina wannan magana dan bayan ya bada tinkiya anyi miki
rad'in suna babu abunda ya kuma tsinana miki." Rashida tace."Gaskiya dai ki daina ci masa mutunci." Uwani ta fashe da kuka tana fadin"Sai ki zageni Rashida ki fito fili kawai ki zageni yau naga matsayina a gurin ki shiyasa ni Wasila tafi min ke sau dubu du
k abunda tasan za tayi ta faranta min rai shi takeyi duk abunda nace tayi tana yi min babu musu ke kuwa fa sai dai ta nemo kudi kina daga kwance kice, to duk rashin mutuncin da kikeyi min sai na fada mata." Tana gama maganarta ta shige daki tana matse hawa
ye.....Wayarta ta dauka da Wasilan ta siya mata ta hau kiranta....Lokacin suna tare da mai girma governor suna meeting Wasila taga kiran amma bata dauka ba sai bayan sun fito daga dakin meeting din ta kira ta....Uwani na daga wayar ta fashe da kuka "Wasila
maza ki zo gida Rashida na nan tana min rashin mutunci duka na ne kawai ba tayi saboda zuwan Malam mai allo."
Rai a 'bace! ta kashe wayar ta nemi numbar Rashidar.....Rashida ta daga wayar tana zumbura baki "Wallahi Rashida ki shiga hankalin ki! dan Kut
umar ubanki me malam mai allon ya tsinana miki da har kikewa mahaifiyarki rashin kunya har kin manta irin wahalar da tasha akanmu ashe dama kika bawa malam din yaci mata mutunci kamar yanda ya saba to wallahi sai ranki yayi mugun 'baci! kan hakan." ''Aunt
y Wasila ki saurara kiji abunda yake faruwa." Rashida ce ke ta magana amma taki sauraranta sai zaginta take cikin jin haushi ta kashe wayar....Wasila ta tsaya tana mamaki! lallai Rashida bata da mutunci ta gama wahala da ita amma ta kashe mata waya....Maha
ifiyar tasu ta kira tace"Kinga Uwani na soma zargin yarinyar nan wallahi harda hadin bakinta gurin zuwan Mai allo gidanan dan haka hankalina ba zai kwanta ba komai dare zan shigo unguwar in daukeku ku zauna cikin shiri." Uwani tace"Nima dama shawarar dana
yanke kenan dan tunda malam din yazo nasan sauran ma suna tafe haka kawai su rusa mana rayuwa waye zai koma kauye ya zauna? sai dai duk abunda zasuyi suyi." Duk dai magana ta kare ku zauna cikin shiri." Uwani tace "To shikkenan sai kinzo." kashe wayar ta
yi ta iske inda Camas take zaune tana kallonta.
Har kusan karfe goma da rabi na dare Garba na layin su Wasila cikin matasa yayi basaja so yake yaga ta inda Wasila zata 'bullo, shiru asalima tunda ya zauna ko kare bai gani ba a bakin kofar gidan nasu..
...Yananan zaune mutane suka fara raguwa saboda dare kowa na tafiya gida shima sai ya yanke shawarar tafiya dama a Mashin yazo roba roba ya sanya mukuli zai kunna kenan ya hango tawowarsu Wasila jikinta sai walwali ya keyi kasancewar material din dake jik
inta mai kyalline wani bala'in kamshin turare ya bakunci hancinsa lokacin data giftashi ta suka shige ita da Camas! wace ta nufi gidansu ita kuma ta hau buga kofar gidan......Matasan dake kusa dashi ne suka fara magana kasa kasa..."Shegiya karuwa kawai ina
su Mado nanan da sunci ubanta ta gama guje gujen ta dawo karuwar banza da wofi! ai sai munci ubanta wallahi." Zaginta sukeyi suna kwashe mata albarka garba na jinsu bai ce komai ba yana nan zaune yaga sun fito ita da sauran mutanan gidan.....Gidan suka ku
lle suka wuce simi simi kamar munafuka...nan yaji matasan dake kusa dashi na fad'in"Ai babu matsiyaciyar uwa sama sa wannan matar duk itace ta sanya ta take wannan rashin mutuncin dazu fa wan mahaifinsu ne yazo suka rufe masa kofa ai
wallahi mun kusa tashi
n su daga unguwar nan." "Kai kasan me zamuyi ma yanzu."? girgiza kai yayi yace." Kone gidan zamuyi dan uwarsu in sun dawo su kwana a waje." Kai wannan shawara tayi kyau abokina." Tafawa sukayi suka mike tare.....Garba ganin sun bar gurin sai shima ya hau
mashin dinsa yabi bayan su Wasila can ya hangosu tsallaken titi inda tayi parking din motarta suka shiga a take ya bi bayansu amma yanda yake binsu a hankali ba zasu dauka su yake bi ba.
Dake unguwar masu hannu da shuni ce ko ina haske babu duhu da tar
in kazanta daga can bakin titi Garba ya tsaya ya kafe mashin dinsa a hankali yabi bayan motar inda yaga ta nufi wani estete wanda manya manya mutane ke zaune a ciki Garba yayi mamaki sosai babu shakka yarinyar samu kudi ganin motar ta tsaya a bakin gate di
n wani tangamemen gida ginin zamani, yana kallo mai gadi ya bude gate din ta shigar da motar ciki, sai ya juya da sauri ganin sucurity na nufowa inda yake, da sauri ya tashi mashin dinsa ya bar gurin a guje......A daran ya shaidawa Ahamdu unguwar da Wasila
take sam baiyi mamaki ba saboda yasan zasu iya yi mata abunda yafi haka, kudi ne gasu nan a banzace ayi abunda ya dace an'kiyi ana watsar dasu a banza a wofi jirgin sama ma zasu iya siya mata mutukar bukatarsu zata biya.
Uwani da Rashida suka gigice g
anin ubangidan da Allah ya mallakawa Wasila suka dinga shige da fice a gidan suna ta'be ta'ben abubuwa Uwani dai kusan zautuwa tayi saboda ta masifar rudewar da tayi taga uwar daula da duniyar da 'yarta ta cikinta ta samu.....Wasila tace "Ko wanne ya dauki
daki daya ya ishe shi bukatar rayuwarsa Uwani kinga Abunda Allah yayi mana ko? da kina cewa muje muyi karuwanci shine zamuyi kudi da gaggawa to wannan sana'a da nakeyi mutukar ta karbe ka nan take zakayi arziki yanzu ina da kudi cikin account dina da ban
san a dadin su ba kullum 'yan fadar mai girma governor tura min kudi suke bamu da matsalar komai a halin yanzu Allah ya yaye mana kuncin talauci ba tare da mun aikata sa'bo ba.
Uwani tace" Sai yanzu kuma na gane abunda kike nufi Wasila wallahi ni a dauk
ata yanzu babu abunda ke saurin kawo kudi da gaggawa kamar karuwanci ashe akwai sana'ar da tafi wannan to Allah nagode maka da bai sa kun dauki gurguwar shawarar da nake baku ba."
To a ranar dai da kyar su Uwani sukayi bacci dan Wasila dakinta ta shig
e tayi wanka tayi kwanciyarta bacci mai dadi ya dauketa........A furgice! ta bude idonta tana salati! ta sanya hannu ta kunna fitilar gefan dago tana bin dakin da kallo kamar me neman wani abu....Kafafunta ta zuro kasa suka sauka kan kafet, ta jima a haka
kafin ta mike ta nufi toilet fitsari kawai tayi ta dawo ta kwanta ta rufe jikinta da bargo amma banda fuskarta ta kasa kashe fitilar dakin tayi domin gani take kamar zai iya mamayarta kamar yanda ya mamaye ta cikin mafarkinta na yanzu, Tun da take a duniy
a ba ta'ba ta'ba mafarki wani d'a namiji ba sai yau! shin wai wannan mafarkin me yake nufi ne? meye ala'karta da wannan guy? ita dai tasan ba'kar gaba ce tsakaninsu to mai zai sanya yazo mata a mafarki yana mata murmushi saboda kuma tsabar wuce gona da iri
har ya rungumeta yana tatta'ba mata sassan jikinta....Tayi sauri ta sanya hannunta a ramin cibiyarta sai taji tamkar hannunsa ne a gurin a lokacin da yake shafa mata cikin mafarkinta, jin tsigar jikinta ns tashi ya sanya tayi gaggawar cire hannunta daga
gurin.....Rufin dakin ta tsurawa ido, itafa wannan mafarkin ya bata tsoro har yanzu tana hango fuskarsa da tattausan
murmushi, shin wai abunda tayi masa bai dame shi bane da har zai zo yana mata murmushi, ita ta dauka zasu kulla gaba ne ita dashi wacce taf
i ta da tsanani!!!!!!! Juyawa tayi ta rungume pillow tana lumshe ido....."Subahanallahi." Hannunsa taji a jikinsa ta mike a zabure! tana dube dube a dakin........Yau satin ta daya a gidanan amma bata ta'ba shiga tsoro da farga ba irin na yau! mikewa tayi t
a zura hijab! ta bude dakin ta futa....Dakin da su Uwani suke nan ta nufa, gani take kamar in ta zauna a dakin ita kadai mafarkinta zai iya tabbata.....Duk suna tare dake bed din babbane su Rashida da Uwani anji Ac sai bacci akeyi, ta samu ta ra'be gefens
u ta kwanta had'e da takure jikinta guri guda.......Ta jima a haka kafin bacci ya dauketa.
***
Cikin Shiri ya fito daga bedroom dinshi, Garba da Hadi na zaune a katafaran palon nashi suna ganin fitowarshi suka mike a tare gaisuwa suka mika amsa yana
mika musu hannu sukayi musabaha da juna Ahamadu bashi da girman kai da d'agawa........Yana mutumta dan adam!! Garba ya isa inda yake yana gyara masa babbar rigarshi da yake yau shigar manya kaya yayi dakarkiyar galila ce a jikinshi green color wuyan babba
r rigar anyi masa aiki na manya mutune wanda mafi aka sari masu sarauta keyi, yana gyara links dinshi Garba ya miko mishi hula zanna bukar 'yar gasken ya d'ora saman kanshi a sai ya sake wankuwa da kyau gyaran fuskarshi yayi dai-dai da tsarin askin dake k
anshi saisaye yake yi bai fiye tara suma ba amma baya kwal kwabo ana masa saidaye ne agyara masa fuskarsa dai-dai da zamani....Duk wanda ya kalleshi sai ya sake kallo babu wanda zaice ya kai matakin shekurun da yake kai a yanzu.....tare suka futa dasu Garb
a mutukar ba nisa zaiyi ba baya tafiya da securities su Garba kadai yake dauka su raka shi, Garba ya bude masa bayan mota ya shiga ya zauna Hadi ya zauna kusa dashi ya mayar da murfin motar ya rufe.....Da sauri Garba ya zauna maxaunin direba tun kafin su i
so bakin gate din mai gadi ya bude gate din.....Securities din dake zaune a bakin gate suka dinga daga masa hannu da fadin "A sauka lafiya Allah ya tsare a dawo lafiya." Shima hannunsa ya daga musu yana amsawa da "ameen." Har suka futa daga gidan......Sai
da suka hau kwalta tukkuna Garba ya tambayi inda suka nufa, ya shaida masa inda zai suje gidan Hajiya Babba dake Zooroad. Garba ya dauki hanya kamar yanda aka umarce shi.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺
romantic love story
🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE
🍒
*
*
🌍
Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mut
um zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*Free Pege17*
Hajiya Babbah na xaune a palonta tare da wasu 'yan mata guda biyu Suhairat da Salimat 'Yayan mutun d'aya ne wato Hajiya Maryam wacce ta kasance 'kanwa ga Hajiya Babbah! kasancewar Allah bai bata haihuwa ba har mijinta ya rasu.mutane ke ta
nani'ka mata 'yayansu mussaman 'yan uwanta waccan ta turo 'yarta gobe waccan ma ta turo 'yayanta jibi duk dan ganin daular dake tattare da gidan....Suhairat ce mai nacin zuwa gidan saboda kawai tayi katari da Ahamdu mutumin da ta kwallafa ranta a kanshi ta
ke masifar sonsa shi kuma bai san tana yi ba sai tayi zuwa goma gidan ba ganshi ba dan bai fiye zuwa da safe ko da yamma ba sai dare yake zuwa gaisheta, to yau dai sunji dadi jin Hajiya tace sunyiwa waya dashi yace zai shigo da wuri Suhairat ta sake gyara
fuskarsa ta fesa turare ta 'kame! a kan mujera Salimat kuwa sai dariya takeyi mata tana fad'in"Allah yasa dai ya kyasa dan na lura kinyi masifar matowa a kan mutumin nan." Suhairat tace"Ke dai bari 'yar uwa ni wallahi da zai aureni da gudu zan yarda ina ma
sifar sonsa komai nashi yana burgeni mutum kamili ga nutsuwa kamshin turaransa ma abin alfahari ne." Salimat ta dinga 'kyalkyala dariya tana tsokanar yar uwar tata......Cikin nutsuwa da kamala ya shigo palon bakinsa dauke da sallama. Dukaninsu suka mike ts
aye suna masa barka da zuwa, kamshin turaransa ne ya cika musu hanci Suhairat sai murmushi takeyi tana gyara masa gurin zama....Ya zaune a nutse yana fadin" Suhairat kune yau gidan? ina Hajiyata." Wani fari tayi da ido tace"Wallahi kuwa Mune yau a gidan Ha
jiya na daki bari na kirata." Ta juya tana tafiya cikin wata iriyar siga.....Oho bai san tanayi ba dan idanunsa na kasan kafet, Tare suka fito da Hajiya babbah tana masa barka da zuwa ya amsa yana tambayar ta gida.....Suhairat ta dauko mishi lemo da ruwa t
a tsiyaya masa ta mika mishi.....Ba tare da ya kar'ba yace."Bana jin zansha komai yanzu nagode Suhairat." Jiki a sanyaye ta ajiye cup din ta nemi guri ta zauna kusa da Hajiya......Yace."Ina ta son zuwa Allah bai nufa abubuwa sunyi yawa hajiya a gafarce ni.
" Tace."Ai babu komai Ahamdu dole ne ayi muku uziri saboda yanayin harkar taku ta jama'a bayan nan kuma nasan akwai hidimomi da yawa Allah dai ya taimaka." Ya amsa da "ameen." Palon yayi shiru Yana so yayi mata maganar dake tafe dashi amma zaman su Suhaira
t a gurin ya hanashi shi mutum ne mai sirri yafi son komai nashi a cikin tsari dan ya lura da yarinyar kanta rawa yake yasan dai zancen gizo baya wuce na koki ga yanayin yanda take masa kwarkwarsa za tace itama sonsa takeyi.
Gyaran mirya yayi a nutse ya
ce."Hajiya muhimiyar magana ce take tafe dani dan daga nan ma idan na tashi can gidan Kawu Almu zan nufa." Hajiya Babba tace "To babu laifi Ahamadu Allah dai yasa maganar dake tafe da kai irin wacce take bakina ce da nayi mutukar jin dadi." Murmushi ya sak
i wanda yasa Suhairat shagala gurin kallonsa Yace."Yana da kyau yaran nan su dan bamu guri." Hajiya ta kalli su Suhairat da suka kasa kunne suna so suji maganar ko kunya babu tace."Suhairat ku shiga ciki mana." Simi simi suka mike sam basu so hakan ba muss
aman Suhairat tafi so ya fadin maganar a gabanta da jikinta na bata wani abu.
"Hajiya na samu matar aure insha Allahu ranar juma'a ta jibi za'a daura aure." Maganar data fito daga bakinsa kenan.....Fuskarta da yalwataccan murmushi tace"Alhamdullihi Ah
amdu baka ta'ba zuwa da labarin da yayi min dadi kamar wannan ba masha Allahu to amma kuma al'amarin baiyi sauri ba
kuwa ko bazawara ce ne."? Ya girgiza kai "Budurwace Hajiya." Tace."To to masha Allah amma kuma abun yazo min bagatatan banyi shirin komai ba
ko da yake dama haka aure yake dashi da mutuwa ba'a shirya musu in lokaci yayi sai anyi, shin yarinyar 'yar wace unguwa ce kuma." Yace." Yar wata karamar hukama ce a wannan jahar sunan garin nasu Garko amma anan tayi rayuwarta Unguwar dorayi daurin auran
dai Can Garko zamuje ayi." Tace."To Ubangiji Allah yasa za'ayi damu ya tabbatar mana da alkairi." Ya amsa da "ameen Hajiyata, ni zan wuce can gidan Kawu Almu babu wani abu da kike bukata ko."? Tace." Alhamdullahi Ahamdu bana bukatar komai ka wadatani da du
k abun bukata kafin wani ya kare kasa an kawo wani babu abunda zance sai da nace Allah ya saka maka da alkairi ya jikan iyayenka." Yace."ameen Hajiyata Ubangiji Allah ya barmin ke na dinga ganinki ina jin dadi." Tayi dariya da fadin"Wace ni Ahamdu ai mutuw
a rigar kowa ce zan mutu kaima zaka mutu." Ya mike yana kallon a gogon dake daure a hannunsa yace."Duk da haka dai Hajjah ina fatan kiyi rayuwa mai tsayi a duniya tace."To Allah yasa Ahamdu Allah yayi maka albarka ya baka 'yaya masu albarka."