Showing 138001 words to 141000 words out of 176422 words

Chapter 47 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

yasa idan ya kira wayarka baka dauka."

Shuru yayi tace"Kawu kayi hakuri magana ta wuce

nima nayi alkawari insha Allahu bazan sake baku kunya ba." Yace."Masha Allahu dama haka nake so naji."

Amadu ya kar'bi wayar daga hannunta, a nutse yay sallama Kawu Habibu ya amsa cikin mutumci suka gaisa da juna, Kawu Habibu kunyar abinda yayi masa t

aso ta hanashi magana, inda shi kuma Amadu ya nuna masa komai ba komai bane ya kuma tabbatar masa da cewar abinda ya faru a baya insha Allahu ba zai sake faruwa ba a gaba..........Kawu Habibu yaji dadin maganarshi sosai da sosai dan yanzu babban burunsu sh

i da dan uwansa shine yarinyar ta zauna a dakin mijinta.

Mika mata wayar yay bayan sun gama ta karba tana fad'in "Kawu dan Allah idan ka koma gida ka bawa mai allo wayar ina so mu gaisa dashi." Kawu Habibu yace."Insha Allahu idan na koma gida zan bashi

yanzu haka nayi tafiya wani gari zan kuma kwana biyu acan sai dai na koma din." Tace."To Kawu Allah ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "ameeen." Sukayi sallama cike da kaunar junansu..........Ajiyar zuciya ta dan sauke kanta a kasa, yanzu tana masifar kaun

ar kawunanta saboda ta gane yanxu sune gatanka........Hannunsa taji cikin nata yana saka mata wani abu, ta dago kanta tana kallonshi, tana kuma kallon hannunta, wasu takardune guda biyu ya saka mata cikin hannunta........Kallonshi tayi tana neman karin ba

yani.

Yace." Kada kice komai ni nayi niyya kuma idan nayi kyauta ba'a cewa dani dan me? na jima da mallaka miki wasu kadarori nawa tun ranar da na amshi budurcinki na mallaka miki rumfunana biyu dake cikin kasuwar sabon gari, naki ne a halin yanzu halak

malak, tun daga ranar dana mallaka miki kawowa yau din nan duk wani abun da aka samu na cinikayya suna cikin

asusuna, insha Allah zamuje a bude miki account zan sa miki kudinki a ciki, bayan wannan kuma akwai sabuwar motar dana siya miki tana can gareji

a ajiye, yanzu ki rike key d'in a hannuki." Ya mi'ka mata key din motar yana murmushi.

Hannunta ne ya shiga rawa, ta rasa ma abinda zatace masa sai kawai hawaye ya 'balle mata, rungumeta yay tsam a jikinsa yana shafa bayanta, cikin shashshekar kuka tace"N

agode mijina Ubangiji Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana Allah ya rabaka da sharrin masu sharri Allah ya bamu zaman lafiya da zuria masu albarka." Ya dinga amsawa yana dan bubbuga bayanta a hankali.

****

Cikin ikon Allah da hukuncinsa komai na

tafiya dai-dai a zamantakewar auransu, ta samu nutsuwa dashi ya samu nutsuwa da ita, yayin da karatunsu na al'kur'ani yayi nisa sosai yanzu sun wuce izifi ashirin tunda kullum sau biyu yake musu kari, bangaran littafan addini kuwa sun wuce matakin su ahla

ri da fikhu yanzu manyan littafai yake musu irin su Minhajil musulum zaduzjaujen Ismawi balaga......bangaran ilimin addini Wasila da Rashida ba'a cewa komai sai godiyar Allah.

Cikinta ya shiga wata na tara, lokacin kuma ciwuka suka tsananta yau ciwo gob

e ciwo haka dai take daurewa duk sanda bala'in ya isheta sai ta shiga daki taci kukana ta koshi.............Gashi baya xama a gida sosai kusan kullum sai sun fita da jama'arshi yawon campain, wani sa'in ma

kwana sukeyi ko kuma su dawo cikin dare lokac

in ta dade da yin bacci, ga Rashida ta soma zuwa makaranta abun dai duk babu sauki ta kowanne bangare wani lokacin hajja itake zama tana debe mata kewa idan kafafunta sunyi tsami ta matsa mata a gaskiya babu abinda zata ce da matar sai dai addua.

Akwai ra

nar da Anti Kubura ita da yaranta suka zo gidan suka tarar da Hajja na matsawa Wasila kafafunta duk sai suka shiga mamaki mai tsanani yanzu kamar hajja ke aikin matsar kafa.....Anti Kubura ta kufula ranta yayi masifar 'baci ta kalli Wasilan shekeke tace"Wa

to asiri da surkullen naku na fulani ya dawo kan baiwar Allah wacce bataji ba bata gani ba, kawai saboda tsabar rashin arziki ki mike kafafu ki sanyata matsar kafafu shin itace tayi miki cikin da zaki dinga sata aikin wahala? ke ko kunya bakiji ba." ! Hajj

a tace"A'a kubura nice nasa kaina ba itace ta sani ba, to idan ma itace ta sani laifine dan na matsa mata kafafunta ai lalura ce! bana son irin abinda kikeyi kubura." Hajja ta karashe maganarta cikin jin rashin dadin abinda tayi.....Suhairat da takeji kama

r taje ta turmushe Wasilan ita da cikin jikinta tace"A'a Hajja wallahi da sake! baxai yiwu ba idan suna cin 'kasa to su kiyayi ta shuri! asirinsu da surkullansu ba zaiyi tasiri a kanki ba, shi da Yaya Amadu da yaga zai iya sai yaje yayi, amma kamar wannan

mara gata da galihu ta saki a gaba kina mata matsar kafa! ai bata isa ba idan ita bata san darajarki ba to mu mun sani."

Wasila ta soma kokarin mi'kewa ta bar musu gurin......Hajja ta dan rike hannunta tana mata sannu, hawayen dake kokarin zubo mata ta m

ayar ba tace komai ba tabar gurin, tana jin Suhairat na zaginta da kiranta 'Yar iska jahila mai bin maza." Wannan kalmomi sunyi mata ciwo sosai, kawai ta kwanta kan gado ta shiga kukan bakin ciki da takaici! Illar ka aikata mummunan abu kenan bata ta'ba z

ina ba amma gashi anzo har cikin gidanta ana kiranta da karuwa me bin maza...

Littafin na kudi ne.....!

Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar

*07084653262*alliya:

'Yr Bngr Sys

*72*

Baya

n shigar Wasila d'aki Hajja ta shiga yiwa anti kubura da Suhairat fad'a kan abinda sukayi bai dace ba suzo har gida s suna zagin matar gida......... aikin matsar kafafu itace tasa kanta ba wai Wasilan ce ta sanyata ba, tace mutukar idan kun san tashin han

kaline zai kawo ku to ku daina zuwa dan kun san idan Amadu yaji ba zaiji dadi ba bana kaunar abinda zai 'bata masa rai kamar yanda baya kaunar abinda zai 'bata min rai! Ke suhairat ki iya bakinki wallahi naji kina kiranta karuwa a gidan ubanki tayi karuwa

ncin? to wallahi kika sake Amadu yaji wannan maganar zai iya daureki kuma wallahi ba zance masa dan me ba tunda bakinki ne ya jawo miki." Da jin abinda Hajja take fada sai kawai anti kubura ta fashe da kuka tana fyace majina tace"Haba Hajja ashe kudi yafi

zumunci kada fa ki manta ni dake uwarmu daya ubanmu daya, Amadu kuwa bake ce kika haifeshi ba dan mijinki ne amma kike kokarin za'barsa akaina shikkenan nagode."Anti kubura ta karasa maganar tana mikewa, tsaye suma Suka mike ransu a 'bace! Hajja tace"Yanda

kika dauki al'amarin ni ba haka na daukeshi ba Kubura nagode kwarai yau ni kikewa gurin haihuwa ko babu komai." Anti kubura ta kad'a kan 'yayanta suka fita daga gidan ransu a tsananin 'bace! Hajja kuwa sai da ta matse hawaye kafin ta mike ta shiga cikin

daki.

Rashida da ta dawo gidan duk sai ta gansu wani iri babu cikakkiyar walwala alhalin ba haka ta tafi ta barsu ba, sai da suka ke'be da 'yar uwarta take tambayarta abinda yake faruwa, Wasila na hawaye take fada mata irin zagi da cin mutuncin dasu S

uhairat da mahaifiyarta suka zo sukayi mata.

Rashida ta fusata sosai tace"Wallahi anti Wasila da ina gidan sai na rama mi ki wannan ai rashin mutuncine da iskanci su shigo har cikin gidanki suna zaginki na rantse da girman Allah duk ranar da Suhairat ta

sake zuwa gidanan ta zage ki sai na nuna mata wacece ni sai ta futa da fashashshan baki." Wasila tace"Ki kyaleta rashida tayi na farko tayi na karshe nima na dauki al'kawarin kan duk ranar da ta sake zuwa taci min fuska cikin gidana sai ta gane bata da wa

yo...........

To Yau ma bai shigo gidan da wuri ba sai kusan sha biyu da rabi na dare lokacin tayi bacci har ta gaji dan wajejan takwas ta kwanta yanzu kwanciyar ma wuya take mata sai tayi ta juye juye da zarar bacci ya dauketa bata minti talatin sa

i ta farka, jin shigowarsa dakin ya sanya ta mike zaune......Yace."Baki bacci ko jikin ne.'? Girgiza masa kai tayi,

yace."Okey bari nayi wanka ko." ba tace masa komai ba ya nufi toilet, tana zaune ya fito ya kimtsa jikinsa ya fita daga dakin

Minti biyar y

a dawo hannunsa rike da ledoji guda biyu ya aje kasan kafet ya bude fridge ya dauki lemo da ruwa........Lokacin da yake kokarin zama kasan kafet ne ya fahimci damuwa a fuskarta, ya kalleta cike da kulawa yace." Menene? Hawayen da take 'boyewa suka su'bce t

a soma kuka da shashsheka

Yaji duk wani annushuwa da farin cikin da ya shigo dashi ya dauke, jikinsa na kyarma ya zauna kusa da ita yana me rungume kafadunta da hannunsa....."Kiyi shuru ki fada min abinda ke damunki bana son wannan kukan naki." Abinda yak

e fada kenan yana goge mata fuska da hannunshi.

Kwanciya tayi a jikinsa tana cigaba da kukanta. Hankalinsa yay masifar tashi ya dinga rarrashinta da kalamai masu sanyi,da kyar tayi shuru yace."Kukan da kikeyi bai da amfani saboda yana sa hankalina tashi k

i fada min abinda ke damunki."

A hankali tace"Meye tsakaninku da Suhairat."? Sai ya shiga tunanin wacece ma Suhairat? can ya tuna yarinyar anti kubura ce kanwar Hajja. Yace."Kanwata ce me ya faru.''?

Ajiyar zuciya ta sauke tace"Ai kai baka da wa ko 'kanw

a." Yace."Eh hakane ita suhairat din yarinyar kanwar Hajja ce anti kubura."

Tace."Kace mata kada ta sake zuwar min gida tunda ba alkairi ne yake kawota ba."

Ya danyi shuru yana mamakin maganarta, cikin nutsuwa yace "Kince ba alkairi ke kawota ba sai ki f

ada min abinda ya faru dan na fahimci dama keda ita tuntuni kunsan juna."

Tace."Idan na fada maka abinda ya faru ranka zai 'baci watakila ma ka dauki tsatstsauran mataki akansu har ita anti kuburan, fad'ar maganar bata da amfani tunda ba alkairi ba

n

e, dalili kenan da ya sanya nace ka hanasu shigowa inda nake dan mutukar suka sake zuwa suka zagi iyayena sai na rama.".....Ranshi yaji ya 'baci jin abinda tace Yace."A gaban hajja kukayi wannan shashancin."? Mikewa tayi daga jikinsa tace"Nifa kar kaga lai

fina nasu ne dan bar musu gurin ma nayi saboda abinda ya dameni shi ya dameni."

Yace."Shikkenan tunda bakya so su shigo miki gida zasu daina shikkenan ko?" Babu kunya tace"Eh." Yace."Sauko kici abinci." Tabi ledojin dake gabansa da kallo, a hankali ta sau

ka ta dan mike kafafunta shi kuma ya shiga bude ledojin manya manyan kaji ne gassasu wanda sukaji hadi sosai sai kamshi sukeyi.

A nutse suke ci suna dan hira yana bata labarin irin nasarorin da yake samu ta 'bangaran siyasar shi, yanzu babu local goment d

in da basu kai ziyara ba kuma ko ina sukaje cike da nasara suke dawowa, al'amarin siyasar dai ya dauki zafi sosai da sosai ta inda ko ina ka zaga a fad'in jahar kano zance Amadu Musa ake da fatan Allah ya bashi mulkin jahar kano a hannunsa, pastes dinshi s

ai yawo suke a titi kasuwanni gami da jikin gidajen mutane, gabakidaya al'ummar jahar kano sun gaji da mulki Lawal rabo sauyi kawai suke bukata a jahar tasu.

Sosai taji dad'in irin nasarorin da yake samun ta 'bangaran siyasarsa dan har sai da fuskarta

ta nuna alamun jin dadi ta dinga yi masa addua gami da fatan nasara akan dukanin abinda ya sanya a gaba.........Da kyar ta yunkura ta mike tsaye ya dan bita da kallo lokacin da ta nufi toilet sai ya mai da hankalinshi kan abincin dake gabanshi......brush

tayi ta tsuguna tana fitsari dan yanzu haka takeyi bini bini fitsari kuma idan ta tsuguna ba wani na kirki takeyi ba.?

tana tsarki taji wani abu me yauki na biyo hannunta bata damu ba dan tun da cikinta ya tsufa take ganin abubuwa iri iri, da kyar ta mike

tsaye tana cije baki ji Tayii kasan mararta yayi mata wata irin dam'ka! salati tayi ta dan rike kofar toilet din tana mai da numfashi.

A hankali ta lalla'bo ta fito lokacin baya dakin sai ta kwanta kan bed tana lumshe idonta......Bacci ya soma fizgarta t

aji motsin shigowarsa ya shiga toilet yay brush ya fito ya kashe fitila yaje ya kwanta kusa da ita......Kamar dai zai daure sai ya kasa hannunsa yasa ya dan janyota jikinsa yana shafa bayanta da gashinta

Gabanta ya shiga faduwa tana addua Allah yasa ka

da yace wani abu dan yanda take jin ciwo bata jin zata iya wani abun.....Aikuwa dai abinda yake nufi kenan dan sai kesses yake mata tare da kokarin sabule mata rigar jikinta.

Cikin sanyin murya tace"Dan Allah kayi hakuri yau cikina ciwo yake." A maraira

ice yace."Nayi kokarin yin hakan nakasa ki daure nayi koda sau daya ne hankalina zai kwanta." Shuru tayi masa, ya cigaba da wassaninsa da sassan jikinta yayin da take sake jin ciwo na tsantsanta a gareta ta dinga cije bakinta tana kokarin daurewa, lokacin

da ya shigeta wani irin murd'a da dam'ka mararta tayi ta rirrike damtsansa tana salati! shi kuwa ai baya ma cikin nutsuwarsa dan duk sanda zai jishi cikin wannan gurin yakan manta da hankalinsa.....Jin kamar an 'kara mata ni'ima ya sanya ya kwarkwance ya

dinga buga sambatu yana bugunta sam ya mance lalurar da take tare da ita.

Kuka ta dinga yi tana masa magiya ya rabu da ita, lokacin yake kara kuzari da karfi kukanta na kara ingixashi kan abinda yake yi............nishi ta dinga fitarwa sama-sama yaron

dake cikinta yana dunkulewa guri guda yayinda mararta take mata wata irin dam'ka tana murd'a mata!! "Wayyo Allahna ka kawo min agaji kada na mutu na shiga uku abinda nake gudu sai ya faru."! sambatun surutun da take kenan! ya rufe mata bakinta yana sake b

ugunta da karfi shima yana daf da kawowa ne shiyasa ya rasa nutsuwarsa...........Jikinta ne yayi lakwas duk wani kuxari nata ya kare sai idanunta suka hau lumshewa tana shiga ganin bibbiyu cikin idanunta.

Sai da ya tabbatar da duk ya fitar da abinda ke

mararashi sannan ya hakura, aikuwa yana zare jijiyarshi wani irin jini ya ambulo daga jikinta.......Yaji saukarshi kan cinyarshi, cikin gaggawa ya kunna fitila dakin yay haske kawai sai yaga idanunta suna kafewa tana jawo nunfashi da kyar ga jini sai ambul

owa yake daga

gabanta.

Salati ya sanya a d'imauce ya sauka daga bed din, yay dira dira sai ya dawo bed din a gigice ya dauki jallabiyarsa yasa da gajeran wando.....Hannunsa na kyarma ya dauki wayarsa ya kira Dr Nasir yace gashinan zuwa hospital dinshi

emagency........Garba ya kira a waya yace maza ya fito da mota.......Yay gaggwar maida wayar aljihunsa ya tarairayota jikinsa sai rawa yake yaga tayi lakaf komai nata ya daina aiki! Kawai sai yaji ya tsinke da al'amarin cikin gaggawa ya fita daga dakin ya

kira Hajja a gigice ta fito ita da rashida suka shiga dakin.

Rashida na ganin halin da yar uwarta take sai ta fashe da wani irin kuka tana fad'in "Anti Wasila kada ki mutu ki barni wayyo na shiga ukuna." Rirrike hannunta tayi tana kuka, ita kuwa hajja ba

yarinya bace ganin babu kaya a jikin Wasila ya sanya ta fahimci abinda ke faruwa, wato rashin hakurinsu yasa sun jawowa kansu matsala, na'kuda mai tafe da jini ai hadari ce sosai.

Da sauri ta umarceshi wanda yake tsaye ya rasa yanda zaiyi da ya sani yake

yafi dubu....Tace"Ka dauko mata kayanta ka sa mata muje asibiti." Sai sannan ya dawo hayyacinsa ya nufi wardrobe cikin saurin gaske.

Rashida ce ta sa mata kayan shi kuma ya dauketa a hannunshi suka fita daga dakin........Garba ne ya tukasu zuwa asibiti

n dr nasir yayin da jikin wasila ya sake rikicewa sai salati takeyi tana yin wani irin nishi wanda kana jinsa kasan tana cikin halin ciwo........Amadu addua kawai yake mata hankalinsa duk ya tashi lokacin ita kuma ta dinga rirrike masa hannunsa tana wani

irin murkususu a jikinsa.

Littafin na kudi ne....

Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*BINTA UMAR ABBALE*alliya:

'Yr Bngr Sys

*73*

A mutukar galabaice

aka shiga dakin haihuwa da Wasila, Dr Nasir da wasu narses biyu suka rufu a kanta har sai da suka samu nasarar tsayar da jinin dake zuba daga jikinta, lokacin kuma ta daina duk wani yunkuri da takeyi duk karfinta ya kare bata gane wanda yake kanta, Dr Na

sir ganin halin da take ciki na baraxana da rayuwarta ya sanya ya fita daga dakin da sauri, nan ya iskesu a tsaitsaye Amadu sai zurga zurga yake a gurin hankalinsa a tashe.

Dr yace."Yallabai muje ofis zamuyi magana." Amadu ya juyo yana kallonshi, ganin ya

nayin fuskar dr din ya sanya jikinsa yin sanyi sai kawai yabi bayanshi yana mi'kawa Allah a'lamarin.

Dr Nasir yace"Yallabai yarinyar nan ta galabaita sosai dan duk wani karfinta ya kare, ba zata iya haihuwa da kanta ba kayi hakuri ka sanya hannu yanzu m

u shiga idata tiyata." Wani irin gumi ne ya shiga yanko masa, idanunsa sunyi jawur ya karbi takardar dake hannun Dr din jiki a sanyaye ya sanya hannu ya aje takadar yana me dafe kansa Dr ya mike a hankali yace"Yallabai ka kwantar da hankalinka insha Allah

za'ayi nasara." Kanshi na 'kasa har dr din ya fita daga ofis din bai dago ba dik ya rasa yanda zaiyi yana ganin kamar rashin hakurinsa ne ya janyowa yarinyar shiga wannan matsala........Hannu yasa ya goge gumin fuskarshi ya mike ya fita daga ofis din da s

a'bulallan jiki.....Hajja da rashida na ganin yanayin sa ai duk hankalinsu ya tashi,Rashida kam kuka tasa tana adduar Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login