Showing 15001 words to 18000 words out of 176422 words
'karasa ya fuzge niqab! din ya jefar, tayi saurin kaud
a kanta gefe.
Hannu ya mika yayi kamar zai juyo da fuskarta sai ya fasa yace." Juyo ki kalleni ina son muyi magana dake." Sai da ta dai-dai ta nutsuwarta tukkuna ta juyo tana kallonshi........Sun kai kimanin minti uku suna kallon juna kafin ta dauke kan
ta tana wani ya mutse fuska.
Gyaran mirya yayi a nutse yace."Ina so ki fad'amin nawa aka biya ki kika tsunduma kanki a wannan harka ta jagaliya ki fada mun ko nawa suka baki ni nayi miki al'kawari zan nin ka miki abunda suka baki ko sukayi miki alkawari
n mutukar zaki dawo kiyi harkar ta siyasa mai kyau, da tsari!
Ta mike tana karkad'e hijab d'inta ta kalleshi ido da ido tace"Ni! bana jagaliya siyasa nake tsaftacciya kuma kai baka da kudin da zaka iya biya na kan wannan harkar."
Murmushi ya saki y
ace."Kina bani tausayi yarinya baki san waye Ahamdu ba ko."? Tace"Saninka ba zai amfana min da komai ba tunda nasan anayi siyasa ne da ra'ayi ni bana ra'ayinka kuma baka isa kasa ni na sauka daga a'kida ta ba.''
"God."! yafada yana tafa hannunsa ya ka
lleta da kwantaccen murmushi a fuskarshi yace." Gaskiya kin burgeni yarinya kuma ana siyance ana son mutum mai a'kida ni kaina idan da zan samu abokin tafiya irinki da naji dadin harkar ammafa ni yanda na dauka kin tsunduma kanki wannan harka ne domin cimm
a wata manufa taki.
"Kwarai kuwa akwai manufofi da nake dasu akan wannan harkar wanda ni kadai na barwa kaina su ina so kuma Allah ya cika min burika na."
"Masha Allah shin meye sane kuka daura tuntuninku akaina kuka tsawwala min sai kace ni kadai n
e dan takarar Governor dake takara da governor ku me yasa duk inda nake kuna bibiyata da al'amurana saboda tsabar bin diddigi irin naki har gida kike biyo ni kina kokarin ci min mutunci shin wai me kuka dauki wannan harkar ne."!?
Wasila tayi shiru yace
." Siyasa ba hauka bace! wad'anda suka san abunda sukeyi sunayi ne kan tsari amma ke naga kina so ki wuce gona da iri saboda talauci yayi miki katutu shiyasa kike ganin zaki iya zagin mutum kamar ni wanda yake da shekarun da suka nunka naki sau uku, okey
nasan
babu abunda ke damunki sai jahilci da rashin mafad'i to wannan shine lest winning na 'karshe kada! na sake ganin wad'annan kafafun naki a gidana duk ranar da kika sake kuskuran shigo min gida to a ranar ki kwana da shirin wad'anann kafafun naki ba
naki bane dan sai na sanya an ragargaje su! in yaso sai naga kafafun yawon *Banga* ban hanaki ki zageni ba ko ki jefe ni kije kiyi tayi idan kin cimma burinki nasan zaki bari gidana dai ban lamunce in sake ganin kafafunki a ciki ba."
Maganganunsa sunyi
mata zafi sosai! ta kalleshi tana girgiza kai *"Jagaliya da Banga* yanzu na fara." Tana fadin wannan magana sai tw zuge jakarta ta zaro kudinshi na jiya ta jefa masa "Wannan kudin da ka bawa Mamana da kanwata basu ishemu kallo ba saboda aban bamu wanda ya
f.......... Taji saukar Wani bahagon mari a kumatunta! A razane! ta dafe fuska idanunta yayi jawur! Ya dam'ki! wuyanta ya sha'ke cikin hijab.....Ta dinga kyarma! tana kyafta ido!! Ganin idanunta sun soma shagid'ewa ne ya sanya ya saketa sai ta fad'i a guri
n ragwajab! tana kakari! tare da rike ma'kogwaronta! kanta 'kas!! ya tsugana dai-d'ai kafafunta, A kausashe yace." Har yanzu baki san waye Ahamadu ba ko! ni zaki jefa da kudi! ke! wai shin ma dame kike takama ne.''!!! Wasila tayi shiru bakinta ya mutu ha
r yanzu ma'kogwaronta suya yake mata wai! sauran kadan ta bakunci lahira......"Wallahi wallahi duk ranar da kika sake gangancin aikata min abu makamancin wannan sai kin raina kanki in yaso su wad'anda suke daure miki gindi su same ni da kansu ni bana tso
ron kowa kije ki fada musu basu isa nayi dake ba su zasu zo da kansu mu fafata! mahaukata kawai wadanda suka dauki mulki wata tsiya kije ki fad'a musu ni *Ahamadu* ina jiransu suzo da kansu sa'ko na baki duk ranar da suka sake turo ki to zan huce fushina
a kanki Tausayi da jin kai ya sanya nake kyaleki kina min abunda kike so kuma ina baki damarki a siyance okey tunda ke d'in dabbace! mara kishin kanta zan fara cin ubanki idan kin soma ji a jikinki sai kije ki gyara *BANGAR SIYASAR KI* Tashi! maza ki kwash
e min wannan kudin da kika watsar a kas! dubban mutane nacan suna nema ke kin samu kina zubarwa saboda kina da masu baki....Ki shirya min kudina tsaf! a cikin kyaure kamar yanda suke tunda bakwa so akwai dubunku masu so."
Wasila ta yunkura ta tashi tsay
e idanunta yayi jawur!!! Gefan hijab dinta tasa ta goge gomin goshinta ta ratse shi zata wuce!!! Tare ta yayi da kirjinsa ta dannata a jikin bango (garo) Sai ya zamana ma nuffashi da kyar take futarwa Gaggausan mutum irin wannan ya sanya mata nauyinsa ai
sai Allah...."Ni zaki nunawa zafin kai ko."!? Yafada yana sake matse ta a jikin bango.....Kanta tasa ta daki kirjinsa dashi Yace."Idan kukan jini zakiyi anan gurin sai dai kiyi sai naga karshen tashen balagarki kiyi abinda nace kawai shine mafitarki."
C
ikin 'kunar rai! tace"Ka matsa daga jikina ka matseni a bango domin ka cimma wata manufa taka akaina to Allah ya isa kudi kuma zan tsince dan karan kaina ba dan wani ba."
Ya matsa daga jikinta yana ya mutse fuska.......Bani da wata manufa da zan cimma a
kanki saboda na had'u mata iri iri wad'anda suks fiki komai kazama dake mai zanji a jikinki da kike wannan maganar." Shiru tayi masa ba tace komai ba ta hade masa kudinsa ya sanya hannu ya karba da hannu ya nuna mata 'kofa "Fice min a gida wannan shine kar
o na biyu idan kika kuskura kika sake shigo min gida to kin san abunda zai biyo baya."
Hijab! d'inta ta buge! tayi masa wani irin kallo mai nuna alamun akwai sauran kalubale tayi kwafa ta juya tana tafiya da sauri sauri!!! Hannuwa ya zuba cikin aljihu y
ana kallo ta tsaya ta daura niqab dinta kana ta murda kofa zata futa......Dake a kulle take daga waje, Hadi yazo da sauri ya bude mata ta fice da sauri tamkar zata tureshi.....Can ta hango Camas tsaye jikin wata bishiya ta nufe ta da saurin gaske sam! bat
a damu da kallon da mutanan dake gurin suke mata ba, saboda babbar dama ce ta samu domin cimma manufofinta a kansa.....Suna fita suka samu babur kai tsaye government house suka nufa.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺
romantic love story
🌺
*NA:*
*BINTA U
MAR ABBALE
🍒
*
*
🌍
Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan
katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko
orange_
*Free Pege12*
Sai da sukayi nisa sosai Wasila ta cire niqab din fuskarta tana goge fuska Camas tace"Ammafa matar nan taso ta saka ki a bala'i wallahi dan naga guy ranshi ya 'baci sosai ni na dauka ma zan ga kin fito da fasashen baki! walla
hi."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Bai fasa min baki ba amma ya mareni ya sha'ke min ma'kogwaro har na soma jiyo 'kamshin mutuwa! ammafa bai daki banza sai na kulla masa sharri nifa naji dadi da hakan ta faru wani plan zan shirya a kanshi ke dai kawai mu ba
r maganar sai munje gida tukkuna." Camas tace"Shiyasa naga kin fito a furgice! gaskiya Wasila akwai ki da jarumta wallahi da nice da tuni na karaya da wannan harkar akwai hadari a cikinta......"Camas idan kinga na daina banga to na cimma manufofina ne kawa
i ke dai ki cigaba da take mun baya insha Allahu wannan plan din da zan shirya shine zai janyo min arziki na har abadah."
Camas tace"Allah yasa kawata kice dai mun kusa daina yawo a babur din haya zamu mallaki motar kanmu." Murmushi tayi har fararan hakor
anta suka bayyana tace"Ke dai lokaci Camas! Allah dai ya taimake mu." Camas! ta amsa da "ameen" kana suka cigaba da wata hirar.
Koda suka isa government house din Governor da sauran mukarrabansa suna dakin meeting sai da sukayi xaman awa biyu tukkuna su
ka fito lokacin har magariba tayi duhu ya shigo a gurguje suka gaisa kana Wasila ta fada musu abunda ya faru a gidan Ahamadu tace....Wannan damar tamu itace zata rusa duk wani shirinsa a gaban bainar jama'a al'amarin ya faru saboda haka da
kaina zan shiga
gidan redio in watsa maganar nasan wad'anda abun ya faru a gabansu zasu gazgata kaga da kanan shikkenan magana ta kare."
Governor Lawan Rabo yace."Mutukar wannan magana taki ta rusa shirin Ahamdu to ni Lawan Rabo nayi miki al'kawarin baki kud'in da zas
u gigitaki! zan baki mamaki 'Yar gaske in har wannan plan din da kika shirya kan Ahamdu ya sanya ya janye kudirinsa na zama dan takarar governor a jam'iyyar *CPC."*
"Kar ka damu mai girma governor insha Allahu magana ta 'kare kujerar mulki kam kaine zaka
cigaba da zama a kanta."
Tafada cikin karfafawa kanta gwiwa kuma tana sanya ran insha Allah bukatarta zata biya.
Basu dawo gida ba sai kusan karfe goma na dare dan daukarsu sukayi a mota suka nufi wani kayataccen hotel sukayi ciye ciye kana sukayo guz
irin wasu, har bakin layi Alhaji Tasiu ya kawo su yana so ya fadawa Wasila munufarshi a kanta ya kasa wani irin kwarjini take masa shiyasa har ya yanzu ya kasa tunkararta yana kallon yanda abokansa ke shakawata da mata sam baya sha'awa amma yanzu ganin Wa
sila ya sanya yaji yana sha'awarta kuma ya daura aniya a kanta insha Allahu sai ya dandani zumarta yaji ya take....Dama tuntuni Alhaji ma'aruf ke kwadaita masa harkar yana basarwa sai yanzu kuma yaji yana sha'awar yi da Wasila *'Yar gaske!*
****
Baya
n mako biyu da faruwan al'amarin Ahamd ya sake fita kamfen dashi da mutanansa alhamdullahi anyi an kare lafiya dan har gidajen redio sai da suka sanyo muryarsa yanda take jawabi da irin ayukan da zaiyi idan Allah ya bashi gwamnati a hannunsa.....Ahamdu yag
a masoya ta ko wane bangare dan gurin cika yayi ma'kil! da jama'a 'yan nahiyar birget da kwana hudu, babban abunda zai baka mamaki! shine yanda mata da maza manya da yara suke fitowa suna turmutsutsu da fad'in "Se jam'iyar *CPC* sauyi muke so da *Ahamdu da
n Musa* insha Allahu kano takace."
Wasila na zaune kan tabarma anci kwalliya da wani uban les kunnanta da wuyanta gold ne sai sheki yake yi kawai taji muryarsa na jawabi yanda zai kula da gari da ayyukan da zaiyi mutukar Allah ya bashi iko, ta karo mur
ya tana sauraran jawabin nasa da ba'aji sosai sakamakon hayaniyar da tayi yawa, mamaki take ya akayi har ya fita yayi wannan kamfen din basu sani ba.....Cizan lebe tayi ta dauki tafkekiyar wayarta mai tsadar gaske, Alhaji Tasiu ta kira ya daga wayar da sau
ri tace"Yallabai ka kunna redio kaji abunda ke faruwa mutuminka ya fita kamfen sai alkawarin karya yakeyi jama'ar gari na yi masa ihu.'' Alhaji Tasiu ya kunna redion wayarshi yana saurara......Kiranta ya sakeyi a waya bayan ya gama saurara yace."Yanzu meye
matakin dauka." Kwafa tayi tace"Bari bayan sallahr isha'i kazo ka dauke mu muje gidan redion *Salama* zan musu magana idan Allah ya kaimu gobe su sanar da cewar za'a hira dani *Wasila 'Yar gaske* a filin mu Siyasa." Yace." Hakan yayi dai-dai 'Yar gaske in
sha Allahu zan shigo da wuri sai muje ammafa nima ina da wata bukata da nake nema a tare da ke." Yafada yana wani kashe murya.....Tuntuni ta riga ta gama gane inda ya dosa kawai tana basar dashi ta fahimci yanda yake kulafucinta bai san me cin wannan budur
cin nata ba sai ya shirya ji takeyi dashi domin tasan shine darajarta ta gama yawace yawacen ta dawo tilas tasan zatayi aure kuma shine mutuncinta shiyasa take tattala abinta domin ta mika shi ga
namijin da yayi nasarar auranta......Amsa masa tayi kawai da
shikkenan sai kazo d'in." Alhaji Tasiu ya kashe waya yana me cike da nishadi zai biya bukatarshi gurin Wasila.....A waya ta kira Camas! tace bayan sallahar isha'i ta fito zasuje inguwa. Aikuwa Camas! na idar da sallah tayi kwalliya tayiwa mahaifiyata sall
ama ta nufi gidan su Wasila mahaifinta na zaune kan tabarma yana shan iska yana kallon fitarta baice komai ba wanda inda dane da tuni ya korata gida amma dake yanzu ta toshe masa baki da kudi shiru kakeji wai malam yaci shirwa.
Cikin wata dan'kareriy
ar mota Alhaji Tasi'u yazo daukarsu Wasila matasan unguwa suka dinga zind'en Wasila da Camas! cewar ba harkar siyasa kadai suka tsaya ba harda karuwanci ganin irin manya motocin dake zuwa daukarsu, ganin irin shigar da Wasila tayi ta fito dashi ya sanya s
uka sake gazgata zatonsu a kanta tana sanye da wani material roba roba anyi mata wani irin dinki riga da siket ne sun matseta ga wuyan rigar daga baya a fafake! daga gaba kuma anfutar da gidan nono ya matseta sosai Wasila akwai hips da brest duk sun fito s
un das duk lafiyayyan namijn da ya kalleta a lokacin sai ya d'arsa wani abun a ranshi gashi ta kawo wani siririn mayafi ta rataya a kafadarta hannunta sakale da jakarta mahadin takalminta kana kallonta zaka gane ta soma wankuwa idanunta sun bude tar! tar!
sai taunar cingum takeyi.....Alhaji Tasiu yaji jijiyarsa ta mike ganin tsarin jikin Wasila ashe cika da 'kasaitar yarinyar ya kai haka babu shakka dole xaiyi mata kwance kwance ya dandana zumarta.
Gaban mota ta shiga ta zauna camas ta zauna a baya Kana
Alhaji Tasi'u As na gomna ya tuka motar suka fuce daga layin yara na jifan motar da fad'in"Ba mayi! Kano ta d'an Musa ce wallahi.....Alhaji Tasiu yace."Na lura jama'ar unguwar nan taku basayin wannan gwamnatin tamu shin bakya musu hasafi ne kin san fa do
le ki sake musu kudi sosai saboda ranar za'be! su fito su mara miki baya.
Wasila ta sauke ajiyar zuciya tace"Na rasa abunda mutumin nan yake bawa mutanan jahar nan wallahi in kaga yanda jama'a ke sonsa sai ka rike baki ni kaina wani sa'in idan na fito j
ifana sukeyi sai nayi da gaske tukkuna." Alhaji Tasiu yace."Ai yana da masoya gaskiya dalili kenan da muke so mu dakusar da duk wani shirinsa muna so mu kashe masa gwiwa kan harkar yaji kwata kwata ta fita daga ranshi." Wasila tace."Kar ka damu insha Allah
u bukatarmu zata biya a kanshi.
Alhaji Tasiu ya biya tashar redio *Salama* kudi masu kauri yace."Tun yanzu su soma watsa wa cewar zasuyi hira da *Wasila 'Yar gaske* Yar partyn Lawan Rabo governor mai ci a yanzu." aikuwa kafin ma su bar cikin gidan redio
n sun soma sanarwa kan zasu hira da Wasila 'Yar gaske a filinsu na Siyasarmu da misalin karfe takwas na dare."
Tun a cikin mota Alhaji Tasiu ke yi mata wani irin kallo yana lumshe ido tana hankalce dashi kawai tana basarwa ne babu zato taji saukar ha
nnunsa kan cinyarta....kici kici tayi da fuska tace"Meye haka kuma kar ka kara kuskuran ta'ba jikina duk mutumcin da muke da kai naga zaka keta min martaba ta mutuntaka to zamu raba hanya."
As ya soma yake yana sosa kai yace."Har yanzu baki gane inda na
dosa ba kenan *Yar gaske* ki taimaka min rana daya ki mallaka min kanki." Ta watsa masa wani irin kallo, kankance ido tayi tace"As ina ganin girmanka da mutuncinka muyi harkar data hadamu da kai wato siyasa ni ba yar iska bace bana kuma shiri da mazinaci
saboda haka kada ka kara yi min magana irin wannan duk ranar da ka sake to kam zan fadawa mai girma governor yayi min tsakani dakai ka kyaleni nayi sana'a ta kaje ka nemi 'yar iska kuyi iskancinku amma ni ba wannan na fito ba."
As yaji ciwon magangunta
Wasila butuluce meye bai yi mata ba a rayuwa da girmansa da komai take fada masa irin wannan maganar.....Shiru yayi bai sake tankawa ba Ita taci kunu tana tauna cingum dinta jefi jefi tana amsa waya Camas na baya da tata wayar a hannu tana chating duk tana
jin abunda sukeyi tana ganin idan da itace Wasila da gudu zata amince wallahi ai duk sana'a ce a wannan zamanin samun irinsu As zaiyi wuya kuma ta fahimci mutumin bashi da mugunta iya kudi yana sakar musu ya kaisu su dungo siyayya harda ta banza ya biya
kudin kuma ya basu wasu ita kam idan ya nemeta zata amince masa da gudu.
****
Washe gari gidan redion *Salama* suna bude tasharsu da abunda suka fara kenan "Jama'ar gari da misalin karfe takwas da rabi na dare zamuyi hira da Hajiya Wasila 'Yar gaske
a filinmu na Siyasa kowa ya kasance da redionsa a kusa dashi a dai-dai wannan lokaci domin yaji abunda yake tafe da wannan shahararriyar 'yar siyasar."
Gari ya dauka kowa na jiran lokaci......Labari ya iske Ahamdu ta bakin abokinshi Khalifa wanda yake
mara masa baya ga dukanin harkokinsa tare sukeyi kuma shine a matsayin mataimakin shi idan Allah ya basu mulki a hannunsu.........Sam bai wani damu ba da jin wai zai ai hira da yarinyar a tashar