Showing 150001 words to 153000 words out of 176422 words

Chapter 51 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

/>
a shigo ciki....Wasila ta mi'ke tsaye fuskarta cike da! walwala da farin ciki mara misaltuwa, Tabawa Iya mai waina da Uwani suka nemi guri suka zazzauna a nutse ita kuwa Kuluwa sai kalle kalle take tana ya'ke dafaffun ha'koranta da kyar ta zauna kan kujer

ar tana wani irin abu irin na marasa gaskiya......Hajja ta dinga fadin "Sannuku da zuwa kai masha Allah sannuku Wallahi ko jiya sai da mukayi zancenku ashe kuna tafe." Inna Tabawa tace"Aikuwa dai munata sa rana sai yau Allah ya nufa yau din ma Ai maigidan

nan ne ya tura a ka dauko mu.....Kuluwa tayi saurin kar'be maganar tace"Wallahi kuwa ai rashin kud'in mota duk shine yayi mana cikas da tuni munzo anyi hidimar suna damu ace yarinya ta haihu babu danginta ai da kunya gashi duk muna raye a duniyar."

Wasila

taji kamar ta kwada mata mari jin abinda take fad'a shashashar mace kawai daga zuwanta har ta soma sakin layi....Ita kuwa Hajja murmushi tayi kawai ta mi'ke tana kallon Rashida tace"Kije ki kawo musu abinci tunda Rabe ya fita.'' Rashida ta mi'ke ta nufi k

icin cike da takaicin Kuluwa da haukanta.

Kuluwa sai washe baki take tana kallon baby zahra dake hannunta tace"Yarinyar tubarakallah kyakykyawa gata da jikin girma kamar tayi wata uku kai masha Allah." Uwani ta kalleta tana dan jan tsaki cikin ranta, sh

iyasa fa taki amincewa da zuwansu tuntuni saboda hauka da rashin kamun kai irin na kuluwan

Inna Tabawa ta kar'bi yar tana sanya mata albarka kana ta mi'kawa 'Yar uwarta iya mai wani itama ta sanya mata albarka ta mi'kawa Uwani, kunya ta hana ta 'karbar

yarinyar sai dai tace"Allah ya rayata tafarkin addinin musulunci." Ganin ta kasa kar'bar yarinyar yasa Kuluwa dashare baki tace"Uwani kunya ki keji ne ai dole jikar 'yar fari hahahahaha." ta karashe maganar tana dariya kamar sabuwa

r mahaukaciya sai wan

i mutsu mutsu takeyi......Uwani girgiza kanta tayi tayi mata banza ba tace mata komai ba haka su Inna Tabawa dama suma haushinta sukeji.........Koda Rashida ta jere musu abinci kan daining Kuluwa kasa zama tayi kan kujerar sai kauyanci takeyi duk ta hargit

sa musu guri.....Wasila tace"Rashida ki kwashe abincin daga dainnig din ki shirya musu shi kan daddumar can ta gefe sai sunfi jin dadin hakan."

Da sauri Kuluwa tace"Aikam dan gaskiya zama kan wannan abun ba zaiyi dadin cin abinci ba gwara mutum ya zauna a

'kas yanda abincin zaifi tsirga masa.

Cike da takaicinta tace"Dan Allah Kuluwa ki nutsu mana bafa a aljanna kike ba da kike ta wannan rawar jikin haba! ki daina haka dan Allah idan ba haka ba to ni kada ki sake zuwar min gida dan ba zaki zo ki bani kun

ya ba.'' Kuluwa ta hau ya'ke cike da kunya tace"Yi hakuri 'yar nan al'amarin ya rud'ar dani wallahi ban ta'ba shiga irin wannan daular ba sai yau gaskiya ke d'in 'yar baiwa ce Allah ya samu a danshin ku."

Tsaki kawai Wasila tayi ta bar gurin, Uwani tace"K

uluwa kafin muzo gidan nan fa sai da mukayi magana dake wai me yasa kike hakane kada da mai gidan nan ya shigo ki bamu kunya a gabansa."

Kuluwa tace"Kai jama'a wai ya kuke so nayi ne? to shikkenan bari nayi gum! da bakina na daina sanya albarka tunda dai

itace bakwa so nasa." Rashida tace''Hakan shine yafi alkairi dake." Kuluwa taja bakinta tayi shuru sai dai muzurai kawai takeyi tana gyara zamanta, haka suka ci abinci mai cike da nama da lemuka masu sanyi

Bayan sun gama cin abincin Hajja ta fito daga

daki tana kallon Wasila tace"Yana da kyau ki kira mai gidan a waya yazo su gaisa tunda naji kamar suna cewa yau zasu koma." Ai kafi ma Wasilan tace wani abu Kuluwa tace"A'a ba yau zamu koma ba sai mun kwana biyu tukkuna dan haka malam yace mu zauna mu yaut

a tukkuna." Hajja tace"A'a to masha Allah hakan ma yayi kyau ai babu damuwa." Ita kanta Hajja ta fahimci matar kamar bata da hankali.

Wasila jikinta yay sanyi ganin abin na Kuluwa naso ya wuce gona da iri babu shakka baza ta so zamansu a cikin gidan ba ba

dan komai ba sai dan kada su zauna Kuluwa ta zubar musu da d'an sauran mutuncinsu da suke dashi a idon maigidan dama hakan ma ya aka kaya yana musu wani irin kallo to ballanta kuma yazo yaga irin haukan da Kuluwa takeyi ai raini ne zai sake shiga tsakanin

su......Ke'bewa sukayi da mahaifiyarta Tace"Uwani gaskiya gwara ku tafi ni bana so ku zauna a gidannan saboda waccan matar mara hankali kawai idan Kunyi sallah sai ku tafi."

Uwani tace"Rabu da shashasha, ai dama mu ba zama zamuyi ba sai kace wasu marasa

hankali yau din nan zamu koma tunda Allah yasa mun ganki lafiya da yarinyarki ai anyi barka ita idan zata zauna sai ta nemi guri kwad'ayayyar banza kawai."

Wasila tace"Ai naga alama so takeyi ta zauna min a gida kuma baza ta zauna ba wallahi." Uwani tace

"To yaushe ma ai 'kafarmu 'kafarta." Wasila ta shiga bata labarin irin zaman da sukeyi dashi da kuma dalilin da ya sanya Inna hajara barin gidan.

Uwani tace"To in banda abinshi shikkenan daga an haihu babu wani gyara sai a koma masa ai ba zakiyi daraja a

idonsa ba kada ki yarda ya kusance ki sai kin gyara kanki sannan kin tabbatar wannan d'inkin da akayi miki yayi dai-dai sannan idan kin koma masa a haka yazo yaji wani sauyi ai wulakanci ne zai biyo baya."

Wasila tace"Nima abinda nake so ya fahinta kenan

ya kasa fahinta." Uwani tace"Aikuwa ba zai ta'ba fahimta ba tunda idanunsa sun rufe kiyi kokari kawai ki san yanda zakiyi ki biya masa bukatarsa idan ta taso kuma kada ki dinga yi masa rashin kunya tunda kinga ba sa'anki bane ni da nake mahaifiyarki wataki

la ma ya girme ni." Hawaye ta share tace"Uwani nifa bana mishi rashin kunya sai jiya da yau da safe kuma duk shine ya jawo kin san dama can ni bana shiri da wanda ba zai ga darajar iyayena ba Uwani banta'ba jin kaunarki da tausayinki cikin raina ba sai da

na haihu sannan na tabbatar da cewar Uwa uwace kuma dolene kayi kishinta koda mahaukaciya ce." Uwani tayi murmushi a hankali tace"Ai dama baka ta'bata sanin me duniya take ciki sai ka haihu tukkuna zakayi hankali Allah yay miki albarka, dake da d

uk z

uriar da zaki samu." Wasila ta amsa da ameen tana goge hawaye ta mike a nutse ta shiga janyo manya manyan akwatinan dake gefe a jere

Manya manya atamfofi ta shiga fitowa dasu da mayafai masu kyau da tsada, ta zubesu gaban Uwani tace"Ki za'bi wad'anda suka

yi miki sauran kuma sai ki bawa su Inna mai waina." Uwani ta shiga d'aga atamfofin tana dubawa tace"Masha Allahu mungode sosai Allah yayi miki albarka." ta amsa da ameen tana zuba mata kayan cikin sabuwar akwati.....Wani dan karamin akwati ta dauko ta bud

e kudi masu yawa ne a ciki ta tura gaban Uwanin tace"Ki d'ibi iya yanda kike so wannan kud'in da tarin atamfofin nan na samesu ne a haihuwar da nayi....Uwani ta tsorata da ganin Uban kudin dake cikin akwatin tace" Ki dai bani abinda kikayi niyya Wasila d

uk wannan kudin naki ne."? Girgiza kanta tayi tace"Uwani basu kadai bane ma kinga wad'annan takardun shaidar mallakar rumfuna ne cikin babbar kasuwar dake cikin gari (sabon gari) wanda maigidan ya mallaka min duk saboda ya sameni cikkakiyar budurwa yan

zu haka ban san iya adadin kudin da ake samu ba cikin ko wace rana, yace dai zamuje a bude accont ya dinga sanya min kudin a ciki." Uwani ta fashe da kuka tana kallon 'yar tata tace"Nagode Allah da mazon Allah da Allah be sanya kun d'auki hud'ubata ba kun

zubar da mutuncinku a titi nasan da mutumin nan be sameki cikkakiyar mace ba da ba zai miki wannan halaccin ba, kuma da tuni zamanku Baiyi nisa irin haka ba ('kalube gare ku 'yan mata kuyi tattalin budurcinku domun ku mi'ka shi ga wanda ya dace shine mijin

auranku, koda namiji bai maka kyauta ba to abin alfahari ne ya sameki cikakkiyar mace)

Wasila tace" Kinga dama abinda nake ta so ki gane krnan nima nasan da bai sameni da budurci ba da tuni ya sakeni wallahi." Uwani ta goge hawaye tace"A koda yaushe in

a alfahari dake Wasila kuma kullum cikin shi miki albarka nake shiyasa kike ta samun cigaba a rayuwarki, nasihata zuwa gareki shine kiyi wa mijinki biyayya ku zauna lafiya da juna kada naji kada kuma nagani yanzu wannan mutumin shine uwarki da ubanki kuma

shine gatanki duk wani umarni da zai baki kibi mutukar bai sa'bawa addinin Allah ba." Wasila tace"Insha Allah Uwani zanyi kokari nagode....... Wasila ta irgi kudi kimanin dubu dari biyu ta zuba mata cikin akwatin tace "Uwani gashinan ki siyi waya kiyi san

a'a da sauran ga numbar wayata zan rubuta miki idan kun koma gida sai ki kirani mu dunga gaisawa duk kuma abinda kike so ki siya kici abinda baki dashi kiyi min waya insha Allah zamu zo nida rashida bada jimawa ba." Uwani tace"Kudin da kika bani basuyi y

awa ba kuwa kada na aje Kuluwa ta sace." Wasila tace"Kada ki aje akwatin a gidanta ki kai kayanki kidan Inna Tabawa." Uwani tace"Yawwa to hakan zanyi." Mi'kewa sukayi a tare suka fito palo, suka tarar da Rashida da Kuluwa sai musayar yawu sukeyi Hajja n

a musu dariya Kuluwa da dai taga kowa nayi mata kallon mahaukaciya sai ta shiga taitayinta ta kimtsa kanta sai dai har yanzu ba ta daina mamaki da al'ajabi ba.

Uwani tace"To Hajja mun fito mu zamu tafi." Hajja tace"A'a ba zaku tsaya maigidan yazo ba ku

gaisa." Uwani tace"Ai yamma tayi." Hajja tace"Kuma da naji Kuluwa tace kwana biyu zakuyi." Uwani tace"Haba Hajja kamar wasu marasa hankali ai tunda munga lafiyar yarinya da abinda ta haifa zaman me zamuyi." Kuluwa tayi saurin kallonta tana so tayi magana,

Uwani tayi bala'in shan kunu babu fuska, Kuluwa ta sunkuyar da kanta 'kasa ranta duk a 'bace! lallai idan sun koma gida sai ta shukawa Uwani rashin mutunci tunda tana ba'kin cikin su zauna suyi kwana biyu su dandali arziki.

Hajja tace"To ke Wasila baki k

ira mijin naki a waya ba, ai be dace ba ace su zo baizo sun gaisa ba." Tace."Hajja kina ji fa Inna Tabawa tace shine ya tura aka d'aukosu ai yasan da zuwansu."

Hajja tace"Eh 'kwarai kam amma kika sani ko wani abune ya dauke masa hankali tunda kinga kwan

a biyun nan abubuwa da yawa suna dauke masa hankali, yana da kyau ki sanar masa da zuwan nasu watakila ko mantawa yayi." Tace"Shikkenan Hajja." Daki ta nufa domun kiran wayarshi kamar yanda Hajjan ta umarceta sam bata so suyi ta jayayya da matar.

Suna

tare d

a khalifa yaga kiran wayarta sai ya aje wayar suka cigaba da abinda sukeyi shi da Khalifan wanda har ya shiga mamakin ganin bai daga wayar ba ya sanya yace."Da alama dai 'yan mata da zawaran dake damunka ne tunda naga baka dauki wayar ba.'' ba ta

re da ya bawa maganar mahimanci ba yace."Wasila ce." Khalifa ya kalleshi cike da mamaki yace."Lefi tayi kenan ake hukuntata ta wannan hanyar." Murmushin takaici yay mai tafe da bacin rai yace."Khalifa na ta'ba ganin wanda ya samu damar da wannan yarinyar t

a samu a kaina kuwa."? Khalifa ya girgiza kansa yace."Gaskiya ban ta'ba gani ba nima kana sonta sosai dan duk wasu alamu sun nuna." Ya girgixa kanshi cikin takaici yace."Nima nasan da haka khalifa wannan damar data samu ce ta sanya take takani yanda ranta

yake so yarinya 'kankanuwa ta dinga nuna ni da yatsa tana daga mun murya gurin magana tamkar zata zageni."

Khalifa yace."Subahanallahi! me ya janyo hakan." ?Tsaki yaja yace."Saboda kawai na nemi hakkina shikkenan cibi ya zama 'kari."

Khalifa yace."Ban

gane ba."? A nutse ya kalleshi ya dan gyara zamansa ya soma warware masa abinda yake faruwa tsakaninsu."

Khalifa yace."Kai nifa shiyasa sam bana son wannan zaman jegon wallahi duk daga wannan zaman ake lalata maka mata , yanzu ita wannan matar abinda

tayi shine dai-dai da girmanta da komai ta dinga d'ora yarinya kan turba mara kyau, idan bata sauke maka bukatarka ba gurin wa zakaje tunda kai ba manemin mata bane."

Ya sauke ajiyar zuciya ransa a 'bace yace."Allah Khalifa yarinyar nan tayi wasa sai na '

kara aure bana son hauka da da'ki'kanci wallahi kuma zata gane bata da wayo." Khalifa yace."A'a kayi hakuri dai ka cigaba da rarrashinta kasan yarinya ce."Tsaki yaja yace."Allah ya sawa'ke khalifa bazan kuma zuwa gunta sa wata bukata ba taje ra rike kayant

a nima na rike nawa zan kuma fara neman aure."

Khalifa yace"Yanzu ka sauka daga kan ra'ayinka kenan."?

Yace."Duk wani abu da zanyi itace ta jawowa kanta ni babu ruwana." Khalifa yace."To Allah ya za'ba abinda yafi alkairi." Ya amsa sa ameen." Lokacin ki

ran ta ya sake shigowa wayar tashi yana ganin sunanta ya kashe wayar yana jan tsaki.

Cike da takaici da mugun ba'kin ciki ta fito daga d'akin murya na rawa Tace"Hajja bai dauki wayar ba watakila ko baya kusa da wayar ne." Hajja tace"E to hakan na iya ka

sancewa." Mikewa tayi ta shiga daki tana fad'in "Ku dan jirani na fito."

Uwani dasu Inna Tabawa suka mike Wasila ta jagorace su suka fita Ita Kuluwa zama tayi har sai da Hajja ta fito daga daki ta mi'ka mata karuwar ledar dake hannunta tace"Gashinan turam

an atamfofine da mayafai da sabulai sai ku kasafta a tsakaninku." Kuluwa ta kar'be da sauri jikinta na kyarma sai washe bakinta take tana ta zabga godiya, Hajja tace."Babu komai Kuluwa ku gaida gida mungode."

Suna can parking spece Kuluwa takaraso hamma

tar ta ma'kale da ledar kayan da Hajja ta basu sai murna takeyi tace"To Wasila da Rashida mu mun tafi sai mun sake zuwa ke Wasila idan maigadan nawa ya dawo to ki mi'ka gaisuwata gurinsa tunda dai rowarsa kike mana." Wasila tana daure fuska tace"Zai ji ku

gaida gida ku gaishe da Kawu Madu." Suka dinga amsawa da "ameen." Duk suka shiga cikin motar Garba yaja suka fita daga cikin gidan......Wasila da Rashida suka juya jikinsu a sanyaye suka koma ciki To itama Uwanin dai daurewa kawai takeyi amma zuciyarta bab

u dad'i sam! tana bala'in 'kaunar 'yayanta kamar yanda suke 'kaunarta.

Littafin na kudi ne......!

Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya kema keda Allah Whasap numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*alliya:

'Yr Bngr Sys

*78*

_*Sa'ko na mussaman zuwa gareka Amadu 'kawayen Wasila irin su Mumy Farhan, Bomis Zainab kankara Mrs Aliyu Nafisa Buhari Hauwa Chindo, Sakina Ummee da dai sauransu, sunce kayi hakuri dan Allah karkayiwa Wasila kishiya kayi mata uziri saboda yar

inya ce, idan kuma ka kuskura ka 'kara aure to zaka gane baka da wayo dan duk wacce zaka aura ba zata kama 'kafar Wasila ba, zaka dawo inda kake salati kana kiran sunan Allah

πŸ˜…πŸ€­

babu ruwana Sistar Sakina ce tafad'a

πŸ•ΊπŸ•Ί

sannan Sistar Jamila tace duk wacce

zaka aura sunanta salamatu salam dan ba zata iya da jarabarka ba

πŸ•Ί

babu ruwana! Jamila da Ummee ne suka fad'a ni dai 'yar aike ce......Momyna tace kayi auranka dan ba Wasila ce kadai mace ba, takwara Fatima Yakubu ma haka tafad'a Sai sistar Hadiza Shall it

ama haka tace ka more rayuwarka, Shafa'a S Yari da Bilba sunce kayi aure ka more rayuwarka

πŸ’ƒπŸΌπŸ”₯

ni dai na isar da sa'kona Amadu sai ka yanke shawarar da zata fishe ka, nima nace ba Wasila ce kad'ai autar mat.......

πŸ™ŠπŸ˜Œ

*_

Cikin sanyin jiki suka kom

a cikin gidan Hajja ta gansu duk babu kuzari a tare dasu tace"Ai kam ni kaina naso su zauna su danyi kwana biyu ku samu sakewa da mahaifiyarku amma ace daga zuwa sai su tafi wallahi banji dadin hakan ba sai kace wad'anda ake kora."

Rashida ta goge hawaye

tace"Nima naso su zauna wallahi yanzu anti Wasila yaushe zamuje to." Wasila ta kalleta ranta duk babu dad'i tace."Sai an d'an kwana biyu baby tayi 'kwari zamuje insha Allahu." Hajja tace"Kwarai kuwa hakan yana da kyau, Allah ya kaimu ya bamu lafiya mai amf

ani." Duk suka amsa da "ameen."

To har dai kusan goma da wajan rabi bai shigo gidan ba Hajja na kokarin shiga daki ta kwanta ya shigo da sallama a bakinsa......Dukaninsu suka amsa suna masa sannu da zuwa.

Ya kalli Hajja yace."Ashe baki kwanta ba hajja

ko kema kallon kike."? Tace"Oh!oh kai nake ta jira ka dawo ai." Yace."To Allah yasa lafiya."Ganin yana 'kokarin zama ya sanya ta mi'ke a hankali ta bar gurin, Rashida ma ganin 'yar uwarta ta tashi sai itama tayi yun'kurin mi'kewa yace."Rashida koma kiyi z

amanki ya kina kallo zaki tashi kuma."

Cike da kunya da jin nauyi ta koma ta zauna ta maida hankalinta kan tv.....Hajja tace" Dazu munyi ba'ki a gidanan na sanya Wasila tayi kiranka a waya kazo ku gaisa duk da nasan da cewar kasan da zuwan nasu, bai kamat

a ace suzo har su tafi baka zo kun gaisa da juna ba."

Ya d'an dafe kansa yana girgixa kai ya kai minti uku a haka kafin ya d'ago kansa yana kallon Hajjan yace."Wallahi Hajja na manta shaf! ni da kaina na sanya Garba yaje ya daukosu amma kuma banyi tsamma

nin yau zasu koma ba shiyasa kwata kwata ban mai da hankalina gurin dawowa gida da wuri ba.''

Hajja tace"Aikuwa ko awanni uku basu cika ba suka tafi dan babu yanda banyi dasu su zauna su kwana biyu ba suka ki."

Yace."Ashsha! nima ban so hakan ba naso mu

gaisa dasu wallahi amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login