Showing 168001 words to 171000 words out of 176422 words
sauri yace."Nima nafi tunanin haka."
Dainnig ta nufa ya bita da kallo
cikin sha'awa shi dai ba zai ta'ba gajiya da ita ba a rayuwarsa, Rashida ta kar'be baby zahra dake hannunshi Shi kuma ya wuce dainig domin karyawa
Ko a gurin break din ma sai da sukayi wassanin su iya son ransu sannan sukayi break din cike da farin ciki
gami da annushuwa, da kwata kwata baiyi niyyar fita ba yaso ya zauna gida ya yini tare da iyalinsa to dole ne ya fita saboda akwai babban abinda zai sanya ya fita din, harda kuka da zai fita tana ta shagwaba da dire diren kafafu shi kuma sai biye mata ya
ke yi, da kyar dai ta barshi ya fita daga gidan.
****
Tsaf malam Mai allo ya shirya cikin manya kaya yayi wa matarsa Bitan sallama dama duk abinda ke faruwa ya shaida mata saboda ya yarda da ita da nutsuwarta Bitan macace mai hankali da sanin ya kam
ata, fatan alkairi tayi masa gami da dawowa gida lafiya.
Mai allo bai sha wahala ba gurin zuwa gidan Kawu Madu dake Pataskum dan Wasila tayi masa kwance sosai kuma sai da ya tambayi Madu mai itace ya sake tabbatar da cewa shi d'in ba 'boyayye bane.
Allah ya taimaka Kawu Madu nan bai fita ba yaro ya shiga gidan ya shaida masa yayi ba'ko......Kawu Madu na fitowa yaga fuska irin ta Yahuza me rasuwa.
Yace."Hala dai kaine Yayan Yahuza mijin Uwani mahaifiyarsu Wasila ko."
Mai allo ya washe baki
nsa ya
na mi'ka masa sannu yace."E kwarai nine malam ashe ka shaida ni."
Kawu yace."Haba malam ai duk wanda yaga fuskarka yasan kai dan uwan Yahuza ne ai kuna kama sosai.
Mai allo yace." Masha Allah masha Allah! Kawu madu yace."Bisimillahi malam shigo ciki." Ma
i mai allo yace"Da mun zauna ma a zaure magana ce mai muhimanci nake tafe da ita.
Kawu yace."To babu damuwa bari na dauko abun zama." Yay saurin shiga cikin gidan yana washe bakinsa,
Mai allo ya shiga soron gidan ya tsaya yana jiran fitowarsa.
Sai
da suka sake gaisawa suka nutsu tukkuna kafin Mai allo yay gyaran murya yana fuskantar Kawun yace."Magana ce nake tafe da ita Malam Adamu ina fatan kuma zaka dauki maganar tawa da mahimanci." Kawu Yace."Ina sauraranka Malam Mai allo yace."Nazo nan ne da n
iyyar auran Uwani ina fatan amincewarka.".
Kawu madu yace."Alhamdullhi! kai amma naji dad'i wannan magana da kake tafe da ita dama ko jiya sai da mukayi magana da ita dake nan d'in ma tana samun zawarawa sai nace to ta futar da miji tayi aure sai ta nun
a min duk cikin zawarawan dake sonta babu wanda yay mata a cikinsu, amma jikina na bani kai ba zata watsa maka kasa a ido ba ko banza tasan "yayanta sun samu Uba nagartacce."
Mai allo yace."Nayi istahara dangane da al'marin kuma alhmdullhi Jikina na ban
i akwai alkairi shiyasa nayi gaggawar zuwa domin na sameta mu tattauna kuma ku sani insha Allah gobe zanje in samu Kawunta na can kano idan mun tsaida magana da ita."
Kawu Madu yace."Hakan yayi kyau malam babu shakka idan Al'amarin ya 'kullu ni zanfi kowa
farin cikin hakan.
Mikewa yay ya nufi cikin gidan yana fadin'"Bari na kira maka ita ku tattauna.
Koda Kawu madu ya shaidawa Uwani zuwan Mai allo sai ta shiga mamaki sosai jikinta yay sanyi tun bataji abinda yake tafe dashi ba, hakika yanzu take nadam
a gami da dana sanin abinda ta dinga yi masa a baya.
Ta dauki mayafi kalar atamfar dake jikinta ta yafa a jikinta ta fita zauran.....Cikin nutsuwa take masa barka da zuwa tana sunkuyar da kanta kasa, sosai Mai allo yayi mamakin nutsuwarta, zauran yay sh
uru na minti biyar kafin mai allo yay gyaran murya a hankali yace."Ina fatan Kawu Madu ya fada miki abinda yake tafe dani.''
Uwani ta dago kanta tana kallonsa, haiba da kwarjininsa ya sanya ta sunkuyar da kanta kasa a hankali tace"Bai fada min ba."
Mai a
llo ya sakeyin gyaran murya a karo na biyu yace."Wata magana ce mai muhimanci nake tafe da ita ina fatan idan kikaji zaki aminci da ita.".
Tace."Malam ka fad'i ko wace irin magana ce ina sauraranka."
Mai allo yace."Nazo nan ne da bukatar auranki." Uwani
gabanta ya yanke ya fadi sai ta kasa dago ido ta kalleshi.
Mai allo yace."Nasan zakiyi mamaki ko? to ki sani ba'a mamaki da ikon ubangiji tabbas wannan auran namu akwai albarka a cikinsa a yanzu babu abinda nake bukata daga gareki sai amincewarki."
Uwa
ni ta jima kanta a kasa ta kasa cewa komai dan har Malam din ya cire tsammanin za tayi magana, sai kuma yaji tace"Babu komai malam na amince Ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkairi a ciki, sannan don Allah ka gafarce ni kan abubuwan dana dunga yi maka
a baya.
Mai allo yay murmushi farin ciki ya cika masa zuciya yace."Alhamdullhi Naji dadi sosai da kika aminci kai tsaye ba tare da mun kai ruwa rana ba, ni kuma nayi miki al'kawarin rike ki tsakani da Allah da manzon Allah dik wani abu da kikayi min a ba
ya na yafe miki Allah ya yafe mana baki daya."
Uwani ta amsa da ameen Yace."Sati biyu kacal nake so a daura aure ko ya kika ce."?
Murmushi tayi cike da kunya gami da jin nauyinsa tace"To shikkenan Allah ya nuna mana."
To kafin malam ya tafi sai da suka
tsayar da magana shi da Kawu Madu kan cewa kafin cikar kwanakin da suka d'iba zai kawo sadaki da duk abinda ya sawwa'ka." Kawu Madu yace."Kada ka takura kanta malam kawai ka kawo sadaki a daura aure."
Malam yace."A'a dole sai yayi mata suttura da sauran
abubuwan amfani." Cike da girmama juna sukayi sallama Malam ya wuce ya tafi zuciyarsa wasai yana jin wani irin so da kaunar Uwanin na ratsa jikinsa.
***
Masha Allah Addua bata bar komai ba kuma hausawa nacewa duk abinda hakuri bai baka ba to babu sha
kka rashinsa ba zai baka ba
, alhmdullhi gidan Amadu yayi kyau komai na tafiya dai-dai dukaninsu sun kwantar da hankalinsu suna kula da junansu kamar zasu cinye kansu, mutukar na gida suna daki a kulle suna soyyaya baby Zahra kam har ta saba da Rashida
in ba nono zata sha ba baka ganinta gurin Wasila, al'amarin Zeey kuwa tun ranar data kira waya ta haddasa musu rigima bata sake kira ba saboda sosai taji zafin zagin da Wasila tayi mata, tayi ta tsammanin ko Amadun zai kirata taji shuru bai kirata ba, nan
ta gane ashe itace take haukanta dole tilas ta sanyawa zuciyarta dangana ta rubuta masa text wanda lokacin da ya karanta test din sai da ya tausaya mata so masifa ne, shi kam yana ganin ko ya aureta wuya zata sha ko bakin ciki ya kasheta dan ba zai iya kwa
ntata da Wasila ba, kwata kwata yanzu babu wacce take gabansa sai Wasila da babynta.
Yana tsaye tsakiyar daki yana fesa turare ta shigo dakin tana zum'bura bakinta, taki kallonsa ta wuce taje ta kwanta kan bed tana hawaye, tun jiya suke ta tafka rigi
ma tana so taje su gaisa da Mai allo kana su wuce pataskum amma yayi biris da maganarta idan ta dameshi yace zasuje sai an kwana biyu har yanzu kwana biyun ba tayi ba.
Ganin tana kuka sai yaji babu dadi yazo ya tsaya kanta yana tambayarta menene? cikin
kuka da shagwaba tace"Lokacin da Hajja take nan naji tace maka ka dinga bari muna zuwa gaishe da mahaifanmu amma yanzu nayi nayi da kai ka'ki barinmu, ni wallahi gurinta zan kai 'kararka."
Ya zauna gefan bed din yana dariya dan maganarta dariya ta bashi
yace."Ke! ni zaki kai 'kara."? Tana goge fuska da turo baki tace"To ai kana jin maganarta watakila ita idan tayi maka magana ka amince." Ya sasauta fuskarsa yace."Ba hanaku zuwa nayi ba, kinga Rashida jarrabawa zasu fara ranar Monday kuma tare zakuyi keda
ita shine dalilin da ya sanya na dakata tukkuna kuyi jarrabawar sai muje tare nima ai ina so mu gaisa da Malam d'in."
Ajiyar zuciya ta sauke ta rike hannunsa tana shafawa tace"Shikkenan Allah muna gama jarrabawar nan ko kwana daya baza mu kara ba zamu ta
fi."
Ya d'age mata gira yana dan kashe idonsa yace."Wai idan kin tafi ni ya zakiyi dani kin san dai kin saba min da abubuwa da yawa." dariya tayi mishi tace"Kayi zamanka ka huta dama ai wataran cewa kake na dameka."
Yace."Ba wannan ba, kwana nawa zakiyi
." Da hannunwanta tayi masa alama wai kwana ashirin zatayi."
Yace."Bana jin zan bari ki kwana Madam muje mu dawo a rana daya......Rungumeshi tayi tana cikwikwiya masa shaddar jikinsa tana kuka tace."A'a wallahi ni kwana daya be isheni ba."
Cikin mutuwar
jiki da kasala ya cireta daga jikinsa yana duba jikinsa yace."Duba saboda sangarta nayi adona kin 'bata min jiki, ni dai na gama magana ba zaki kwana ba."
Da gudu ta d'ane jikinsa tana kuka "Wallahi sai ka amince nayi sati daya." Abinda take fada kenan
tana cusa fuskarta a kirjinsa.
Jikinsa ne ya mace suka zube ita dashi kan bed din tayi kwance a saman kirjinsa tana masa dukan wasa sai kuka takeyi, rungumeta yay jikinsa na rawa ya shiga sumbatarta ta ko'ina...
****
Cikin ikon Allah Wasila ta shig
e cikin 'yan mata 'yan ajinsu Rashida ta saje dasu ba zaka ta'ba cewa matar aure ce ba, kuma babu abinda ya gagareta gurin karatun dan dama kafin zuwan ranar jarrabawar yana dan koya mata wasu abubuwan dake kuma tana da saurin fahinta babu wani abu da shig
e mata duhu ko ya daga mata hankali sukayi jarrabawar fita daga secondary skull cikin narasarori masu yawa.
*****
Ana ya gobe zasu tafi Garko Kawu Habibu ya kira wayar Amadu yake shaida masa halin da ake ciki, cewar malam mai allo zai daura aure rana
r juma'a mai zuwa, kuma ba da kowa sai da mahaifiyar matarshi Uwani, Amadu yayi mamaki sosai da maganar Kawu Habibu daga karshe yayi addua gami da fatan alkairi ya kuma tabbatar wa da Kawu Habibun cewa insha Allahu suna tafe kafin zuwan ranar..........Ka
sa hakuri yay ya kirata a waya yace."Akwai albishir din da zan shigo miki dashi, amma meye tukwicina." Tana dariya tace"Ai kaima kasa ni." Yace."Nasan me? kawai ki fad'amin tukwicina." Tace."To zan barka kayi sau goma." Dariya ya 'kyal'kyale da ita yana s
ake rike wayar a hannunshi, yace."Kamar gaske ko?
yarinyar daka amfara zaki hau ihu kina cewa na daina ke zafi kikeji."
Ma'kale wayar tayi sosai ta wani lumshe ido tace"E mana ai kaine kakeyi da 'karfi shiyasa." Yace."To me yasa idan na bari ke kikey
i da 'karfin."? Kunya ce ta rufeta ta hau inda inda! Yace." Ai nagane wannan kukan da kikeyi na sharri ne dan dana bari ke kuma kikeyi da kanki kukan d'adi ne ko."?
Sai ta soma shagwaba da sangarta tana fad'in "Ya bari ita bata so." Yana daiya yace."Na ba
ri shikkenn idan na dawo gida bazan fada miki albishir din ba sai nayi sau goma kamar yanda kika fada kin amince." ? "Umm."! tace" Tana lumshe idonta wannan 'yar wayar da suke tasa gabakid'aya hankalinta ya tashi sha'awa duk ta taso mata......
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys
*84*
Aikuwa da ya dawo gidan ta dameshi kan lallai sai ya fad'a mata albishir d'in s
hi kuwa yay ta ja mata rai, sai da suka gama komai na rayuwarsu sannan yake shaida mata abinda ke faruwa, farin ciki ya lulli'beta tamkar anyi mata albishir da gidan aljanna gaskiya taji dad'i sosai da wannan abu dama itama sam bata son zaman mahaifiyarta
ta a haka tunda dai ba wuce auran tayi ba, koda Rashida ma taji labarin abinda ke faruwa tayi ta murna da farin ciki da 'kyar sukayi bacci a ranar saboda farin cikin da suke ciki.
Gari na waye wa ta tashi da walwala da farin ciki sai shiri takeyi shi
kam yana kwance yana kallonta kwata kwata baya son tayi nesa dashi dan dai bashi da yanda zaiyi ne kawai, ya shirya cikin manya kaya kamar dai yanda ya saba, duk ranshi babu dadi kawai dai yana kokarin daurewa ne amma duk da haka sai da fahimta to itama n
ata bangaran tasan tilas tayi kewarsa amma haka zata hakura dan gaskiya tana so taje ta gaisa da iyayenta sosai.....Kafin su tafi sai da ya fara kaisu gidan Hajja suka gaisa sosai Hajja tayi mamakin girman baby zahra yarinyar tayi wayo sosai sai kace wata
'yar wata biyar.
Hajja ta ke'be da Wasila tace"Dama inata so inzo gidan naku Allah be nufa ba to tinda Allah ya kawoki sai ki tafi da ajiyar da nayi miki."
Wani garin magani ne a cikin wani madaidaicin bokiti tace"Kullum ki dinga sha da madara ko nono d
aga can sakwatto nasa aka hada miki, ita kuma wannan zuma ce kada kiyi wasa da ita kullum kina shan murfi biyu safe da dare, idan kikaji dad'insu nasan da kanki idan sun kare zaki bukaci ayi miki wani." Wasila ta sunkuyar da kanta kunyar Hajja takeji sosai
godiya tayi mata cike da kunya tana kara jin kaunar matar a cikin ranta.
Hajja har mota ta rakosu tana fad'in "Su gaishe da mahaifiyar tasu insha Allah ranar daurin aure tare da ita za'azo."........Garba ne ke driving Rashida na kusa dashi da baby a ha
nnunta....Ita dashi kuma suna bayan mota sai kalamai take mishi wai ya kwantar da hankalinsa insha Allahu sati guda kamar yau ce."
Ya kalleta sosai yace."Ni nace miki sati guda zakiyi."? Ta kalleshi tana marairace fuska a langwabe tace"Hakafa kace dani s
hekaran jiya."
Yace."Takura min kikayi shiyasa na fada miki haka, yau laraba ko."? Ta daga kanta tana kokarin mai da hawaye, yace."Zan iya daurewa kuyi kwana biyu shima dan dai babu yanda zanyi ne! Ranar juma'a idan na shigo daurin aure sai mu tafi."
Mur
ya na rawa tace"To baza muje pataskum din ba." Yace."Wane pataskum kuma Itama Momyn ai nan za'a kawo ta sai ku had'u kawai ku gaisa."
Tace."Ai sai dare za'a kawota kuma lokacin nasan mun tafi." Yace."Ni zanyi magana da Malam d'in kancewa ana daura aure
a tura mota a daukota ke Ni da kaina ma zan tura Garba ya daukota da sauran 'yan uwa sai ku gaisa da juna.'
Shuru tayi masa domun ta fahimci duk dubarar da zatayi masa ba zai amince ba.
Haka suka isa Garko kowa na jin damuwa cikin ranshi mussaman shi Ub
an gayyar da yake fargarbar dare yay yasan kuma shi da bacci sai dai yaga anayi.
Amadu kafin ya tafi babu inda bai je sun gaisa ba cikin dangin Wasila yau kowa yaga mijin da take aure suka zama abun kallo a garin ba'yan uwansu kadai ba harda jama'ar gar
i fitowa suke suna kallonsu mussaman da wani matashin saurayi dake shiga kano sarin kaya ya gane fuskarshi sosai ya dinga watsawa mutane ai shine *Amadu Musa Ba.Iya.ka d'an takarar governor Kano* Aikuwa Jama'ar garin Garko tamkar an musu albishiri da gidan
aljanna! suka fito kwantsinsu da kwarkwartasu suna ihu da fad'in "Allah ya baka mulki jahar kano fari mai farar anyi maliya mai ruwan 'kare kukanka." Ganin yanda Jama'a suka nuna masa 'kauna sukayi dafifi a jikin motarsa ya sanya ya koma cikin motar tashi
ya bude wata ma'ajiya da yake aje kudi ya daukosu dami guda, ya wakilta mutane biyar yace."kowa a bashi abinda ya samu." Aikwa Jama'a sukayi layi suna ihu da 'kara yi masa kirari.....Wannan damar da ya samu ce ya sanya ya Umarci Garba da yayi maza maza y
aja motar su bar gurin dan idan ba haka ba jama'a baza su bari ya tafi ba.
Su Wasila na cikin gidan Malam mata dam'kam tamkar suyi mata sujjada ita abun ma mamaki yake bata sai wani bata girma ake kowa so yake yayi tozali da ita, wato tun mijin nata bai z
ama governor ba har sun soma kiranta da matar governor dariya kawai take musu itama ta fito da kudi daga jakarta ta shiga raba musu......Deluwa sarkin kanzagi tace"Hajiya Wasila ina fatan idan kun samu mulki a Hannuku baza ki manta da Kauyen Garko ba domin
dai nan ne tushenki asalinki Karamar hukumar garko na bukatar hanyoyi masu kyau, na bukatar wuta da ruwa da kuma makarantu gami da asibitoci sannan muna bukatar tallafi domin mu inganta harkokin noma da sauransu."
Wasila dukanin abinda Deluwa ta fad'a s
ai da ta rubuta a wayarta tace"Insha Allahu duk su kwantar da hankalinsu idan mijinta ya samu mulki a hannunsu Wannan karamar hukuma zata zama city za'a gyara sosai yanda kowa zaiyi sha'awarta.
Sai bayan magariba suka samu sassaucin mutane a gidan, Bi
tan ta shigo dakin bayanta goye da zahra tace"Oh! ai shikkenan kuma gidan nan zai zama sansani na jama'a duba dai mutane sun kasa bari ki huta abincin ma sun hana kici cikin nutsuwa."
Wasila tayi dariya tace"Bitan ai haka siyasa take dama zakiga mutum k
wata kwata baida nutsuwa daga zarar na bar garin inace shikkenan kuma." Bitan tace"Aikuwa dai kuna kokari wallahi ga baiwar Allah nan itama an shiga hakkinta." Tafada tana kokarin kwance zahra daga bayanta.
Tace"Ki bata nono tasha Rashida zata shigo muku
da abinci."Yarinyar na ganin mamanta ta soma cilla kafafu tana b'angala dariya.
Bitan tace"Ji ja'aira wai ta san uwarta."
Wasila na dariya tace"Bitan wannan yarinyar wayo ne da ita ai."
Bitan tay dariya tana kokarin fita daga dakin tace"Ai yaran yanzu d
ama da wayonsu ake haifarsu.
Tana fita Inna Hajara ta shigo gidan tare da dan