Showing 102001 words to 105000 words out of 176422 words
tsaya dogon tunani ba ya sanya hannunshi ya kuma bada umarin a daure mat
a mahaifar duk domin samun zaman lafiyar cikin dake kokarin zubewa.
Rashida ta tinga share hawaye Hafsa na rarrashinta, Ita kuwa Wasila idanunta bushewa sukayi 'kamas! hausawa sukace da wata wuyar ai gwara wata ita yanzu wace irin wahalace bata sha ba s
hiyasa sam bata damu ba tana ganin Allah ne mai rayawa da kashewa.
Cikin nasara akayi mata aiki aka fitowa da ita dakin da suke sistar Aliya tace ta zauna ta huta tukkuna sai sai su tafi gida amma kuma ta kafa mata sharad'ai sosai kan dole ta kula da
kanta babu aikace akaice da zurga zurga sannan kuma ta daina zama da yunwa ta kuma nemi magunguna na karin jini."
Bayan fitar Aliya daga dakin, Khalifa ya dinga tausarta yana bata hakuri kana yace tunda haka ta kasance cewar tana da cikin Ahamdu to la
llai zaiyi mishi bayani domin ya sani....Tace"Ni dai bana so ka fada mishi don Allah ka bari duk ranar da Allah ya saukeni lafiya sai ya sani amma bana so yanzu ya san inda ciki a tare dani.....Khalifa yace."Hujjarki zaki fada min da kike cewa bakya so y
a sani? mutum da abinshi, ai ya zama dole ma ya sani idan sanadiyar cikin yasa ya mayar dake dakinki dama haka muke so." Tace"Bana son haka nafi so kowa Allah ya hadashi da dai-dai dashi dama kaddarar wannan cikin ne Allah ya hadani dashi duk sanda na haif
e shi kuma zai bashi abinshi." Khalifa ya girgiza kanshi yana kallon tsananin wauta da rashin wayo a tare da ita.
Hafsa da kanta ta fita bakin asibiti ta shiga wani kanti da suke siyar da dogwayen riguna da hijab ta siyo mata riga kala biyu da hijab b
iyu sai pants da audiga.......Zeey sai jin haushi takeyi tana ganin duk 'yar uwar tata ta 'bata musu lokaci gurin wata shashashar da basu da hadi da ita taji zafi sosai dan ganin yanda Hafsan ke ta rawar jiki kan Wasilan.......Jikinta babu kwari suka fito
daga dakin....Khalifa ya bude musu motarshi suka shiga, duk gabad'ayansu....Yaja motar suka fita daga asibitin
Har cikin gidan ya shiga da motar, Uwani ta fito ta tsaya dama yini tayi cikin fargaba da tashin hankali ganin 'yayan nata sun fita tun saf
e amma yanzu gashi har karfe shida na yamma basu dawo ba dalili kenan da ya sanya hankalinta tashi.......Fitowar Wasila daga motar yasa ta fuskanci da akwai matsala, sai dai tayi kokarin kar'bar su khalifa hannu biyu suka shiga cikin gidan
Khalifa ya sh
aida mata shi din abokin Ahamdu ne ya kuma shaida mata abinda ya faru da Wasilar shine dalilin da ya sanya ma suka dade basu dawo ba, Sai kawai ta tsinci kanta da yi masa godiya har muryarta na rawa, wato ita tanan sake da baki 'yarta zata mutu akan titi
lallai akwai mutanan arziki a duniya.......Khalifa ya shaida mata abinda Dr Aliya tace dangane da ita Wasilan dole sai an kiyaye an kuma sa ido, har sai sanda cikin yayi kwari tukkuna....Uwani tace"Insha Allahu za'a kiyaye....Yace."Insha Allahu zan sanar
da Abokina abinda ke faruwa mybe ma gobe mu shigo dashi ko da daddare nasan yaji labarin cikin nan zai bukaci sanin abinda ke faruwa....Uwani tace E hakan nada kyau sosai dan muma munyi wannan maganar kuma munje can gidan nashi domin mu shaida masa sai da
bamu sami ganinsa haka muka dawo gida." Khalifa yace."In sha Allah zai zo da kafafunshi kar ku damu...Kudi ya basu kimanin dubu ashirin yace su rike a hannunsu tukkuna, kana ya mike Hafsa dw zeey ma suka mike suna musu sallama, Wasila da kyar ta mike tsay
e domin rakasu, godiya kawai takeyi dan ta rasa ma da wace kalma za tayi amfani lallai yau taga ranar d'an adam Khalifa da matarshi nada hali irin na mutanan arziki.
Tun a cikin mota Khalifa da Hafsa suke mamaki ikon Allah kenan! Hafsa tace"Shiyasa ba b
a'a saurin yin saki komai 'bacin ran da mutum yake ciki kafin ya yanke hukunci ya samu nutsuwa, ko ni anan gurin naga wautar governor wallahi duk dai komai kaga ya faru da mutum kaddara ce amma dai rashin hakuri shike jawo wani abun, yarinya karama da ko 2
years bata cika ba take fuskantar kalubale irin wannan Allah Abban Afnan da ba dan zuwana asibitin nan da sai da cikin nan ya zube in ba wani tsananin rabon ba." Khalifa yace."Tun yaushe nake nuna masa gaskiya ya'ki fahinta kin sanshi fa taurin kai gareshi
sai abu ya kwabe yazo yana nadama ni wallahi na yarda da tuban yarinyar nan bana haufi a kanta kuma ina masa sha'awar ya mai da dakinta tunda dai har rabo ya shiga tsakaninsu.........Tace"Aikuwa dai amma ina jin idan yaji labarin tana da dauke da cikinsa
zai sauko zai kuma so ya dawo da ita duk domin cikin jikinta."
Khalifa da Hafsa har suka isa gida suna zancan Cikin wasila da yanda ta basu tausayi Zeey kam dama tun a hanya ta sauka tace zataje gidansu friend dinta sai suka sauketa ta samu abun hawa r
anta a 'bace! sosai take kishin Wasila da ita da abinda ke cikinta.
Duk rashin imani irin na Uwani sai da ta tausayawa 'yar tata ta dinga rarrashinta taci abinci tasha magani sai ta kwanta, Wasila ta dinga mamaki ashe Uwani dama nayi mata irin wannan
son, taji kwalla ta taru a idonta, tana so ta faranta ran uwarta da 'yar uwarta amma babu hali Kudi suna suke magana, gashi kuma ita tayi al'kawarin barin harkar dake kawo mata kudin da suke jin dad'i.
Bayan sallah isha'i Khalifa na shirin zuwa gidan
Abokin nashi motar shi ta shigo gidan......bayan motar ta tsaya Garba yay gaggawar bude masa motar ya fito....Khalifa ya karasa gurinshi tare da mika masa hannu yana fad'in "Fitowar nan da nayi, nayi ta ne da niyar zuwa gidanka sai gaka kazo.'' Yace." Oke
y Allah yasa alkairi ne zai kawo ka." Khalifa yace."Idan kaji ana alkairi d'aya kenan muje ciki." Suka jera a tare suna tafiya domin shiga cikin gidan kai kana kallon yanda suke mu'amula kasan abokai ne masu tsananin zumunci da kaunar junansu.
Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[14/08, 12:04 pm] Farida Books: 'Yr Bngr Sys
*56*
Hafsa ta gansu sun shigo tare sai ta saki fuska
rta sosai tana dariya tace"Sannu da zuwa gwara da Allah bai sa ka bawa mijina wahala ba kazo dama bana so ya fita ya barni ni kaina a gida naji dadin zuwanka." Ya danji wani iri da jin maganar Hafsa!wato shine mara galihu kenan wanda bai da mata mai tatta
lin sa yana yawo da daddare babu me cewa dan me.''?
Kan kujera ya zauna yana jan kafafun Afnan dake kwance kan kujerar tana kokarin yin barci, jin muryarshi yasa ta bude idonta a hankali ta shige jikinshi tana fadin "Dadyna yaushe kazo ina Aunty Amaryat
a."? Rungume ta yay yana shafa kanta yace." Baby Afnan iya rigima baki bacci ba."? Kai ta daga mishi tana lumshe idonta....Hafsa tace"Yanzu nan ta gama rigima ai ta gaji ta kwanta tana son yin bacci 'kiriniya da fitina a gurin Afnan sai a hankali."
Dan
hararata yay yace."Ke waye yasan abinda kikayi kina yarinya gwara nata me sauki ne." Hafsa tasa dariya tare da wucewa daining tana fad'in "Governor da Afnan kenan ai fada a shirya." Shima dariyar yake yana shafa kan Afanan din yana lallabata tayi bacci.
Khalifa ya zauna kusa dashi yana me cire halar kanshi da fad'in"Yau na sha zurga zurga Wallahi da tun safe ban zauna ba."
Yace."Shiyasa nayi ta tsammanin shigowarka naji shiru kasan dai maganar nan ba zata yiwu ta waya dole sai mun tattuna akai , Alha
ji Danliti ya
matsa min da kiran waya kan dole sai mun bashi rancen kudi har miliyan saba'in wai zai shigo da kaya, kudinshi sun yanke kasan sam bana son mu'amula dashi saboda bai da dad'in sha'ani."
Khalifa yace."Mu aje maganar Alhji 'Danliti a gefe g
uda ni muhimiyyar magana ce nake tafe da ita." Ahamdu ya kalleshi a nutse yace."To ina sauraranka."
Khalifa ya dan gyara zamanshi sosai ya mai da hankalin sa kan abokin nashi ya bude bakinsa a nutse yace."Shin kasan matarka da ka saki tana dauka da ciki
n ka har na tsayin watanni uku da sati biyu."
Yaji wani irin shocking a jikinshi ya zubawa khalifa yana kallonshi yana so yayi mishi 'karin bayani. Khalifa ya gyara fuskarsa sosai alamun maganar da zaiyi mai muhimanci ce Yace."Wasila na da ciki kamar y
anda kaji na fada maka da farko, Dazu ina kan hanya ta ta zuwa gidanka Hafsa ta kira ni a waya kan cewa inyi gaggawar zuwa babban asibitin murtala dake cikin gari ga abinda ke faruwa, dalili kenan da ya sanya kaji ni shiru banzo ba............Khalifa ya sh
iga warware masa abunda ya faru da Wasilan da irin sirad'in da ta tsallake dashi kanshi cikin jikinta da yake cikin wasiwasi da 'kila wa 'kala ya kuma tabbatar masa da cewar mutukar ana so cikin ya inganta a kuma haifeshi cikin salama da nutsuwa da kwanciy
ar hankali tilas yarinyar ta samu kulawa mai kyau sannan ne za'a samu dukanin abinda ake so."
Tunda Khalifa yake maganar yake jin wani iri a jikinshi, ya shiga lissafin watannin cikin dai dai lokacin auransu ne dan a hasashen sa ma yana zargin haduwarsu
da yarinyar ta farko ta same shi...........Jikinsa ne yayi sanyi sosai kafatanin hankalinsa ya karkata kan ingantuwar d'anshi da samun xaman lafiyarsa a cikin uwarshi, gabanshi ya dinga faduwa yana addua da godewa Allah da bai sa cikin ya zube a kan hanya
ba! Ji yay wani irin gumi na keto masa, Khalifa ya lura abokin nashi ya shiga rud'u da tashin hankali sai ya dafa kafad'arshi a nutse yace."Yanzu wace shawara ka yanke dangane da yarinyar dashi babyn dake cikin cikinta." ? Ya dan kalli Khalifa cikin yanay
i na damuwa yace."Nama rasa me zanyi wallahi Khalifa nagode kwarai da gaske Allah ya bar abota da zumunci mai amfani yanzu idan da babu kai mybe da tuni na rasa gudan jinina, bana haufi kan cikin yarinyar nan nawa ne Khalifa nasan lokacin da nayi abina." K
halifa yace."Haba babu komai wallahi ni da kai yanzu 'yan uwane mun wuce a kira mu abokai duk abinda nayi maka kaina nayi wa, ina tambayar ka matakin da zaka dauka dangane da yarinyar da abinda ke cikinta babu shakka dukaninsu suna bukatar kulawa mai kyau.
......Yace."Khalifa kasan dai halina idan nayi magana kan abu ko kuma na yanke hukunci kan abu bana ta'ba barin abu daga baya in waiwayeshi, amma tunda haka ta kasance Zan sakata gida in killace ta sannan in hada mata komai na jin dadin rayuwa ta zauna ta
cigaba da kula min da yaro na har sanda Allah zai sa ta haife mun abuna.....Idan ta haihu in taga zata shayar dashi ok idan taga bata da ra'ayin hakan zan nemi mai raino insha Allah amma bana ji sanadiyar wannan yaro ko yarinya na cigaba da zaman aure da
ita.
Khalifa bai so jin haka da gareshi ba amma bashi da magana dama kuma yayi al'kawari kancwa ya bar cewa dashi ya mai da yarinyar, yasan duk sanda ya gane mahimancin ta a gurinsa zai dawo yana neman shawararshi, Sai
kawai yace."Shikkenan hakan yayi
dan gaskiya na fahimci akwai matsatsi da rashin sukuni da rashin abinci mai kyau a tare da ita da Mahaifiyarta da yar uwarta ina ganin idan anyi hakan zasu samu sakewa sosai kai kuma zaka samu lada kuma dan Allah ko bayan ta haihu ka kar'bi d'anka ko 'yar
ka to ka bar musu gidan da komai na ciki su zauna sada'katuljariya zaka samu lada."
Yace."Khalifa a yanzu yarinyar nan zan iya yi mata komai albarkacin gudan jinana da take dauke dashi kasan ni idan nayi kyauta bana waiwaye saboda haka bayan gida ma ni
mai iya mallaka musu wani abun ne kar ka damu da wannan." Khalifa ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Hafsa dake karasowa inda suke......Ta zauna kusa da mijinta a hankali kai da ka gani kasan itama tana cikin damuwa, Wai shin Shi governor wane irin mutum n
e? ace ayi ta abu d'aya haba ai yaci ace ya hakura ya dawo da yarinyar nan, ta lura kamar ma ya fiso yayi ta zama a haka babu aure da shekarunsa da komai shiyasa mutane ke masa kallon mara lafiya da sauransu. Irin abinda take ta fad'a kenan cikin ranta...
.....Ya d'an kalli agogon hannunshi shifa da ba dan dare yaja ba da ya dauki khalifa sunje ya gano yarinyar nan ba wai dan ita zaije ba a'a dan abinda ke cikinta cikin fargaba yake sosai yana ganin kafin gari ya wace cikin zai iya zubewa...... Babu zato kh
alifa yaji yace."Tashi muje nagano yarinyar nan."
Khalifa ya kalleshi cikin mamaki yace."Yanzu da daran nan dubi time fa sha d'aya shaura." Ya d'anja tsaki yana mutsika goshinsa yace."Gabad'aya hankalina ya kasa kwanciya Khalifa ina jin a jikina kafin
safiya cikin nan na iya zubewa ko wani abu ya faru, nasan mutukar banje na ganota ba ba zan iya rintsawa ba." Khalifa ya dinga kallonshi yana jijjiga kai yace."Shin wai ita kake son gani ko kuma abinda take dauke dashi."? Da sauri yace."No ni abinda ke cik
in cikinta nake son gani ba wai ita ba meye gamina da ita." Khalifa yayi wani murmushin takaici yace."To ina me tabbatar maka da cewar ko kaje yanzu wahalar banza xakayi dan nasan tayi bacci kuma ka'idar masu lalurar ciki ba'a tashinsu daga bacci, kuma kan
a maganar ba dan ita zakaje ba to shi cikin naka in kaje ganinsa zakayi ido da ido ko kuwa zaka ce ta d'aga maka riga ne ka gani."? Ya shiga kallon Khalifa yana me nazarin maganarshi, Ya akayi kwakwalwarshi ta toshe ne? shifa a tunaninsa idan yaje yace ta
bud'e masa riga yaga d'anshi! sai kuma yanzu maganar Khalifa ta sanya ya hango kuskuransa, yanzu dai babu aure a tsakaninsa da yarinyar nan yasan ko yaje bashi da hurumin rike mata koda d'an tsaya ballanta yace ta bud'e masa riga yaga d'ansa
Gumi ya shi
ga karyo masa ya ciro hankici yana gogewa ranshi sai 'kuna yake yi yarinyar nan tayi bala'in cutarsa yasan kuma yanzu shi da kwanciyar hankali har sai yaga d'anshi a hannunshi tukkuna
Khalifa yace."Hakuri za kayi gobe idan Allah ya kaimu sai mu je da wu
ri ku gaisa kasan kuma ko kaje babu ruwanka da ita tunda ba muharramarka bace." Sai yaji kamar ya kwad'awa Khalifa mari da jin maganar da ya fad'a Yaja karamin tsaki yana me mikewa tsaye da fad'in "Allah ya kaimu goben zan shigo da wuri muje, kuma a goben
nake son sauya musu gurin zama duk domin samun nutsuwa da kwanciyar hankalina inaji a jikina mahaifiyar yarinyar nan zata iya zubar min da ciki koda kuwa ita yarinyar bata so." Khalifa yace."Kai kake wannan hasashen amma a dazu munyi magana da mahaifitar y
arinyar ta tabbatar min da cewar kwanaki sunzo har gida domin su shaida maka abinda ke faruwa basu sami ganinka ba kaga kuwa idan
hakane to bata da hannu gurin zubewar cikin ka." Yayi shiru yana nazarin khalifan kafin ya kad'a kanshi yana fad'in"Koma dai m
enene ni bazan ta'ba aminta dasu ba tunda sun shani na warke Allah ya kaimu goben kawai." yana gama maganarshi ya nufi hanyar fita, Khalifan ya mike yabi bayanshi.....Hafsa kam dama tuntuni tayi shigewarta d'akin Governor bai ta'ba 'bata mata rai irin yau
ba mutum sai kace fir'auna zuciya kullum babu kyau ace kayi ta ri'kon mutum a ranka.
Yanda yaga dare haka yaga rana ya kwana yana juye juye da zumud'in son gari ya waye duk domin zuwa ganin gudan jininshi dake kwance cikin mahaifar Wasila......Asuba
r fari ya mike ya shiga toilet wanka ya soma yi kana ya dauro alwala ya fito ya shirya tsaf ya nufi masjid, ya kasance mutum na farko bayan liman da ya fara isa masalacin, sai ya zauna cikin nutsuwa ya fara jan carbi kafin liman ya tada sallah.
Misalin 'karfe takwas sun shirya tsaf! sun fito da jakkunansu, da duk abinda suka san nasu ne a cikin gidan, suka fito tare Uwani da Rashida suke jan akwatinan kayansu yayin da Wasila ke bin bayansu cikin sanyin jikinta, wani irin yanayi mara dad'i takeji
a cikin zuciyarta.....Bakin gate suka nufa, Wasila ta fito da keys din gidan ta mi'kawa d'aya daga cikin masu gadi tace"Idan As yazo su bashi. masu gadin gidan kamar zasuyi magana sai kuma sukaja bakinsu sukayi shiru suna kallonsu suka fice daga gidan da
akwatinan kayansu.......A jigaje ta 'karisa bakin babban titi dan wannan tafiyar da sukayi ya sanya ta haki! dan har sai da suka samu guri suka zauna ta huta tukkuna kafin su cigaba da tafiya.......Babur din a dai-dai sahu suka samu ya daukeshi zuwa tashar
kabuga.
"Wai wannan wane irin wulakanci ne ? na shigo gidanka tun safe ka shanya ni a palo sai kace yaronka ina ta fama zaman jiranka kai kana can kanayin abinda ya dameka, idan ba zaka fito ba zanyi tafiyata ba wai ban san gidan bane."!!! Ahamdu
yake waya da khalifa lokacin da yake kai komo a tsakiyar palon nashi......Khalifa ya fito daga bedroom d'insu kunnanshi ma'kale da waya yayin da Hafsa ke biye da bayansa hannunta rike da turare da kuma hularshi tana gyarawa.
Ahamadu ya dinga watsa musu
harara kamar idonsa zai fad'o 'kas! Yace." Ga d'an iska kun bari yana muku jiran gida kun shigo ciki wai me yasa bakwa gajiya da