Showing 123001 words to 126000 words out of 176422 words
ance masa yana son yarinyar sai yace ba hakaba gashi lokaci 'kan'kani duk ya wani susuce a cikin mota.
Kuluwa ta fito daga cikin d'akinta hannunta rike da wani 'kullin kaya, wanda zanin da aka d'aure kayan y
ayi da'kal-da'kal da daud'a, ta nufi inda Uwani ke sunkuye da wata 'katon baho a gabanta, wacce ta cika ta da kayan wanki ta zuba klin da sabulu a hannunta tana cud'awa! Kuluwa ta dire 'kullin kayan dake hannunta tace"Uwani idan kin gama wankin dan Allah k
i d'an sa'be wa 'kananan yaran nan kayansu tuntuni nake so nayi wanki bani da sabulu kina dai kallo kwana biyu gidan sai a hankali yanzu Kawunki baya fita komai ya rinca'be mana." Uwani ta d'ago kanta cikin tsananin wahala da gajiya tace"Kuluwa kinga dai s
abulun nan banawa bane na mutane ne dan Allah ki bari a wankewa mutane kayansu ya fita wai me yasa duk sanda zanyi wanki sai ki kwaso min kayan yara kice na wanke alhalin kin san sabulu da omo ba nawa bane nima aikatau nakeyi a biyani."
Da jin abinda Uwan
i ke fada sai Kuluwa ta fusata ta soma sirfa mata masifa da fad'in wallahi duk sanda ta sake yi mata musu kan abinda ta umarce ta dashi to sai ta bar mata gidanta." Uwani dai ta cigaba da gurxar wankinta bakin ciki duniya kamar ya kasheta, tun safe take wa
nkin jama'a har yanzu bata karya kummalo ba, ko da yake sai ta g
ama wankin ta kai sannan zata samu kudin da zata siyi abin karin dashi dan tuntuni Kuluwa ta daina bata abin kari a gidan, da daddare kawai take bata abinci shima d'an mitsitsi idan towo n
e kuwa sai ta lakata mata 'karshen kwasa cikin kwano wanda yaro 'karami ma yaci ba zai isheshi ba.
Tana gurxar wanki hawaye na 'kokarin su'bce mata, wannan wace iriyar masifa ce take cikinta? tayi dana sani tayi nadama tayi da ace abinda ya wuce zai dawo
baya data yi gaggawar gyara kuskuranta, wannan wuya da take sha tasan duk itace ta jawowa kanta, Allah ya kawo musu dauki ita da 'yarta ya had'ata aure da mai kudi mai mu'kami amma sabida hange da mummunar kaddara ta dinga zugar 'yar tata ta kashe auranta
, yanzu wa gari ya waya? wahalar da take ciki a yanzu ta wuce wacce taci a baya, a gidan Kawunta ana bata abinci taci ta koshi anan kuwa sai dai ta nema ta ciyar da kanta, Kawu Madu sallamamman namiji ne mijin tace sai abinda kuluwa tace ayi a gidan yake y
i shiyasa duk abinda yake faruwa da rayuwarta baya tofawa, tun bayan tafiyarsu Wasila da kwana uku Kuluwa ta soma gallaza mata kyara! da hantara! da masifa! da kuma horan yunwa! ganin hakane ya sanya Ta nemi Inna Tabawa tana kuka take shaida mata halin da
take ciki, itama Tabawar ta tausaya mata sosai sai da bata da yanda za tayi tunda itama talakace, sai kawai ta bata shawarar kan cewar ta kama sana'a sai ta rike kanta, saboda ba komai ne yake sanya Kuluwa nayi mata rashin mutunci ba saboda tana bata abin
ci ne." Uwani tace"Dama can baya nayi sana'ar wanki indai zan samu anan to wallahi zanyi na rufawa kaina asiri." Tabawa tace"Kada ki damu idan Allah ya kaimu gobe kizo gidana mu
tafi cikin gari Unguwar amare zamu mubi gidajen mutane idan suna da wankau su
bamu." Uwani tace"To shikkenan."
Aikuwa gari na waye wa Ta shirya ta tafi gidan tabawa, suka dauki hanyar cikin gari.......gida biyar suka samu wanki aikuwa Uwani ta zage ta wanke musu kayansu ta shanya musu tsaf suka biyata kudinta, ranar sai yamma
suka dawo gida, Uwani ta bawa Tabawa kudi cikin kudin da samo ta 'boye sauran a jikinta......Tun daga sannan Uwani ke zuwa unguwar amare tana musu wanki watarana kuma ta d'oro kayan saman kanta ta tawo dashi gida sai ta wanke su bushe tsaf sai ta kai musu
su bata kudinta.
Da 'kyar Rashida ta iya gane hanyar gidan ta dinga nunawa Garba hanya yana bu ta cikin kunyar gonakin mutane gwajab gwajab din da motar take ya sanya ta bud'e idanunta tana d'an motsawa, sai kawai taga duk rabin jikinta a jikinshi, ya
yin da shi kuma yayi wani irin zama a cikin motar kamar wanda zai kwanta yayi hakan ne domun taji dadin yin baccin a jikinsa........Da sauri ta mike zaune tana gyara xamanta had'e da gyara mayafinta ta d'ora saman kanta.......Ya mi'ke zaune sosai yana ya m
utsa fuskarsa, hakuri kawai yake yi amma wannan kwanciyar da tayi a jikinsa ta ya mutsa shi, sosai ya d'an saci kallonta sai yaga tana hamma! da alamun baccin bai isheta ba, sai kuma ya mutsa fuska takeyi cikinta ne ya soma 'kullewa yunwa na sasakarta dama
'ka'ida ne idan tayi bacci ko yayane ta farka sai taci abinci.......Jikinta ne ya soma rawa, ta dinga zare ido tana mutsu mutsu ta rasa ya za tayi a yaron dake cikinta yana mata wani irin motsi da zillo tare danno mararta kamar me shirin fitowa waje,
cikin rawar murya tace"Rashida ina kayanmu suke."? Rashida tayi saurin juyawa tana kallonta ganin yanda idanunta suka kad'a ne ya sanya ta gane yunwa takeji da sauri tace" Suna bayan mota." Still murya na rawa tace"To sai kizo ki dauko min kin san dai ce
wa nayi ki rike min a hannunki saboda zan iya bukatarshi cikin ko wane irin yanayi me zai sanya kisa a cikin akwati.'' Rashida tace."Yi hakuri anti Wasila ai mun kusa sauka." Tsaki taja tana motsa bakinta.....Ya kalli Rashida cike da kulawa yace."Menene."?
Tace." 'kwai dafaffe ne Bitan ta bata shine tace na ri'ke mata a hannu na ni kuma wallahi na manta nasa a cikin jakar kayanmu gatacan a bayan motar." Shiru yayi kawai ya juya bayanshi da kanshi ya kinkimo jakar kayan nasu ya d'ora saman cinyarshi ya zuge
zif din jakar ya soma dubawa.....Nan ya d'auko daurin leda yaluwa da dafa
ffan 'kwai a ciki kusan guda ashirin, a jikinta ya d'ora ledar ya mai da zif din jakar ya zuge kana ya maida ita inda take ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Gashinan
karkiyi kuka gama naga shi kike shirin yi." Shiru tayi masa ta cigaba da kokarin kwance ledar.......Kar'ba yay ya kwance mata ya d'auko d'aya ya soma 'bare mata , ya mi'ka mata ta kar'ba da sauri gutsira biyu tayi masa ta cinye.....Tana kallon hannunshi da
ke kokarin 'bare mata wani, Haka dai yayi ta aikin 'bare mata kwai tana taunewa sai da taci guda tara sannan ta hakura ya mi'ka mata ragowar ruwan swan din da yasha d'azu ta 'karba tana sha tana lumshe idonta sai yanzu taji dama dama a jikinta.
Uwani na
tsaka da shanya kan katanga taji tsayuwar mota, dake katangar bata da tsayi sosai ana hange na waje kafin ta ankara taga Rashida ta fito daga cikin motar Wasila ma ta fito da sauri ta ajiye rigar dake hannunta ta nufi cikin dakin da take kwana mayafi ta
dauko tayi hanyar
fita tana kokarin yafawa a jikinta, a soro sukayi kicibus da Rashida sai ta rungumeta tana fad'in "Rashida sai yau kuka tunani dani ko? ke da waye a cikin mota ina Wasila ya jikin nata."? Rashida ta dinga kallon mahaifiyarta ta ganinta ga
je gaje yayi masifar daga mata hankali, Wasila ta shigo ta gansu sai itama ta shiga bin Uwanin da kallo jikinta sharkaf da ruwa......Gashi duk tayi wani wujuga wujuga da ita. Uwani ta rumgume Wasila tana hawaye tace" Yarinyar nan kullum dake nake kwana nak
e tashi a raina Alhamudullihi jiki yayi kyau masha Allahu ga cikin ki ya girma dama ai nasan mutukar kun koma gaban mai allo zai kula daku mutum ne shi mai tausayi kuma yana kaunarku." Wasila da Rashida suka shiga binta da kallo jin abinda take fad'a kan m
ai allo wai yau Uwani ce ke yabon mai allo lallai duniya.
Gidan suka shiga gabad'ayansu, Wasila ta dinga bin gidan da kallo ko ina kaca kaca da kazanta iri iri ga wani wari na tashi da alama shaddar gidan ta cika tana bukatar agaji warin yayi yawa.....T
a dinga bin mahaifiyarta da wani irin kallo na tsantsar tausayi da jin kai. a hankali tace"Uwani wannan wane irin 'kuraje ne a jikinki? dubi yanda fatar jikinki ta kod'e kinyi wani iri duk kin rame."! 'Kwallah ta cika kwarmin idon Uwani tace"Ku mu shiga ci
ki babu komai." Bin bayanta sukayi suna mamaki tabbal akwai abunda ke faruwa da mahaifiyar tasu.........Kuluwa ta fito daga dakinta kirjinta daure da dadd'aud'an zani!!! kanta babu d'ankwali tamkar hammatar d'an iska yayi wani cibiri cibiri dashi dan sabod
a tsabar dauda gashin kan nata har ya soma d'aukewa da kanshi wani guri da a kwai wani gurin babu.....Ganinsu Wasila yasa tasha kunnu tana fad'in "Ku kuma yaushe kuka zo."? Wasila tayi saurin kauda kanta daga kallonta dan ji tayi tsigar jikinta na tashi k
allon gashin kanta ya sanya mata tashin hankali amai na taso mata....Rashida tace" Yanzu muka zo Baba mun same ku lafiya."? Kuluwa tace "Lafiya lau ina fata dai yau zaku juya domin dai muma bamu da abinda zamu baku koda yake dai ga uwarku nan na neman kudi
zata iya daukar dawainiyarku." Babu wanda yace mata ta tafasa ballanta ta sauke suka shige dakin ina Uwani ke zaune tana jiran shigowarsu......Nan suka tarar da ita a zaune a gefen wata guntuwar tabarma ta zabfa tagumi! Wasila ta dinga bin dakin da kallo
daki sai kace zai rufta ya durkushe gashi babu labule babu ledar kasa sai wata guntuwar tabarma wacce take nuni da cewar nan ne makwancin mahaifitar tasu.....Kwallah ta zubo mata murya na rawa tace"Uwani wannan wace irin rayuwa kike ma'kaskanciya, wannan
d'akin da kike ciki ya ru'be wallahi saura kad'an ya rufta bakya tsoro watarana ya rufta dake."
Uwani na hawaye tace"Ya zanyi Wasila! Ya zanyi? nice na cuci kaina na kuma cutar daku na tabbata da kina gidan Alhaji Ahmadu da duk wannan wahalar bamu shige
ta ba, nasan da tuni munfi karfin gurin zama da ci da sha da suttura, na cuci kaina na cutar daku Ubangiji Allah ya yaye mana wannan masifa."!!! Ganin tana kuka sai suma suka fara kuka ta goge hawayenta tana fad'in "Idan dan kunga ina kuka kuma kukeyi to
na daina yi sai kuyi shuru." Wasila ta goge fuskarta tana kallonta.....Uwani a nutse
ta soma basu labarin wahalar da takesha a gidan da yanda kullum take cin ruwa sai kace agwagwa.
Wasila tace"Ai dole sanyi ya kamaki Uwani wannan wace irin masifa ce
ace kullum mutum na cikin ruwa dubi fatar jikinki ta kod'e ta bushe ga wasu kuraje marasa kyawun gani sun feso miki a jiki.
Uwani tace"Wai sunanan ina sha musu magani da ai sunfi haka yawa a jikina." Wasila ta shiga girgixa kanta tana tunanin yanda za
tayi ta kubutar da mahaifiyarta daga wannan ukuba.
Uwani ta kalli Rashida tace"Wai waye ya kawo ku a mota ne."? Rashida tace"Alhaji Ahamadu ne mijin aunti Wasila." Da sauri ta kalli Wasilan tana neman karin bayani......Rashida itace ta shiga fada mata y
anda al'amura suka faru.....Uwani ta dinga washe bakinta tana fad'in "Alhamdullhi Allah nagode maka daka amsa adduata kullum.burina mutumin nan ya dawo garemu naji dadin wannan zuwan naku kuma yau zanyi bacci harda munshari." Wasila tace"To sai ki sauya ka
ya kije soro ku gaisa dan da kunya a shigo dasu wannan 'kazamin gidan." Uwani ta mike da sauri ta bude jakar kayanta ta dauko atamfar data rage mata dan duk kayan da tazo dasu Kuluwa ta sace taje ta siyar, sai dai kawai in ta fita taga kayanta a jikin muta
ne idan ta tambayesu sai suce kuluwa ce ta siyar musu shaddar wasila ma data sace gidan ma gari ta kai suka siya.........Suna kokarin fita daga cikin gidan Kawu Madu ya shigo gidan yana washe bakinsa hannunsa rike da kud'i sabbin 'yan dubu dubu kar kar da
su......Kuluwa yake kwad'awa kira ta fito daga d'aki da saurin gaske dan har zaninta na 'kokarin fad'uwa ta rike da kyau! tana fad'in "Malam ya akayi ne." Yace."Ki fito kizo ki dangwali arziki ki barshi ashe yarinyar nan Wasila matar babban mutum ce, ikon
Allah yafi gaban wasa! Kuluwa kinga uban kudin da mijinta ya bani yana waje shi da abokinsa sunzo cikin wata 'karuwar mota kamar jirgin sama."! A d'amauce! Kuluwa tayi hanyar waje tana tafiya kamar zata kifa 'kasa saboda sauri! Kwata kwata ta manta a halin
da take ciki babu dankwali da riga daga ita sai daurin kirji.....
Littafin na kudi ne....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah What'spp numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*64*
Da sauri Uwani ta tare bakin 'kofar fita tana kallon Kuluwan cikin mamaki tace"Haba Kuluwa dubi yanayin da kike ciki babu suttura a jikinki kanki babu dankwali sannan kuma kike 'kokarin fita haka gaban siriki karfa ki manta mutumin nan babban mutum n
e kamar yanda Kawu ya fada miki idan kin fita haka ai kin zubar mana da kima da mutunci ." Kuluwa ta hau ya'ke tana washe baki tace"Wallahi duk na manta babu riga a jikina Uban kudin dana gani hannun Malam su suka gigitani amma bari inje in sanyo riga ku j
irani dan Allah." Da sauri ta koma cikin gidan jikinta sai rawa yake.....Wasila da Rashida suka bita da kallon mamaki matar mayyar kudi ce duk ta fita daga hayyacinta.....Kawu Madu kuwa na tsaye sai dariya yake yana ta dangwalar miyau a hannunshi yana lis
safa kudin hannunshi, kamar zautacce ya kalli Uwani yace."Uwani kudin nan dubu hamsin ne wallahi! kai masha Allahu gaskiya naji dad'in zuwan mutumin nan Uwani ashe haka Allah yayi wa 'yar arziki amma saboda baki da hankali kika
kashe mata aure, saboda kina
mata bakin ciki, waye ya fada miki yanxu ana wasa da auran irin wad'annan mutanan? ai duk abinda ya faru ya fad'a min yanzu kafin na shigo sai ku godewa Allah da Allah yasa ya mai da auran dan da bai mayar da auran ba to da kun cutar damu wallahi dan wan
nan arzikin sai da mugani a nesa amma yanzu ko banza nasan zamu dinga samun zakka a kai a kai! idan Allah ya nufa ma wataran sai da kawai naji ance na fito an biya min kujerar makkah." Kawu Ya 'kare maganar tashi yana dariya had'e da gyara babbar rigarshi
yana sake gyara xaman kudinshi a aljihu........Kuluwa ta karaso cikin wata kod'ad'diyar atamfa da wani ya mushashshen mayafi da duk ya tattare saboda tsabar yaga jiya da yau wai nan sune karshen adakarta, sai wani washe baki take ta kalli Uwani tace"Ai ha
ka yayi ko."? Uwani dai shiru tayi dan bata da abince wa sam ma bata so Kuluwa ta bisu gani take zata iya yin wani abun na rashin hankali ita kuma bata so yanzu mutuncinsu a zube a gurin Ahmadu......Kawu ne yay gaba suka biyo bayanshi
A babban soron gid
an suka tsaya Kuluwa sai l'eken kofar gidan take dan Kawu cewa yayi su tsaya anan zai shigo dashi Kuluwa duk ta 'kago sai d'aga kai takeyi tana lekawa.....Wasila taji tamkar ta gaura mata mari shin wai ita wannan matar wace irin mata ce mara kintsi da kam
un kai.? 'Kamshin turaranshi ne ya bakuncin hancinsu gabad'aya, Uwani ta gyarq lullubinta hade da sunkuyar da kanta 'kasa kunyar hada ido take dashi sosai, Ita kam kuluwa fad'i take "Sannunku da zuwa Alhaji sannuku." Ahmadu da Khalifa suka samu gefe suk
a tsuguna a nutse aka fara gaishe gaishe, Ahmadu ya kasa tantance mahaifiyar matar tashi duk da ya ta'ba ganinta sau d'aya amma dai baya tunanin Kuluwa itace saboda yanda ta za'ke da yawa sai banbad'anci takeyi tana musu hirarraki Mikewa sukayi a tare Kha
lifa ne ya fara yin gaba shi kuma ya tsaya yana gyara rigarshi, kuluwa ta tsura mishi ido Kudi ya fito dasu daure a kyaure ya mi'kawa Wasila dake gefanshi a hankali yace."Ki bawa Momy ko." 'Kin 'karba tayi Kuluwa tayi wuf ta kar'be kudin tana washe baki d
a fad'in "Ai kunya ba zata bari ta kar'ba Alhaji Mungode kwarai Allah ya tabbatar da alkairi ya baku xaman lafiya." Uwani da Wasila ba suji dadin Abinda Kuluwa take ba, sai basu da yanda za suyi da ita......... Kuluwa da Kawu har bakin mota suka rakosu sun
a musu godiya da fatan alkairi, jama'ar garin sun taru suna mamakin irin bakin da Kawu Madu yayi, sai bayan motarsu ta 'bace daga gurin ne Kawu ya shiga yi musu bayani cewar Ai sirikin sa ne mutumin dake auran 'yar gidan Uwani 'yar 'kanwarshi.....
Uwani c
ikin gidan ta koma ta shiga daki ta had'a tagumi hawaye takeyi sosai takejin kewayar 'yayan nata amma ko babu komai zamansu a gidan Ahmadun sai yafi mata kwanciyar hankali fiye da su zauna a wani guri itama ta yarda mutumin nason 'yarta dan da baya sonta d
a bazai mayar da ita ba duk da tarin laifin da tayi masa.
Bayan azuhur suka sauka gajiya gami da jiri da zaman mota suka taru sukayi mata yawa, dan da kyar ma ta iya fitowa daga motar kafafunta duk sun sage sunyi tsami! Tana dan ya mutse fuska t
a r
ike hannun Rashida tana kokarin zama gefan shuke shuke! Ya fito daga cikin motar hannunshi rike da babbar rigarshi, Garba ya kar'bi rigar da wayoyinshi, hankalinshi na kansu yaga tana matse fuska cike da kulawa yace."Lafiya menene."? Shiru tayi mishi." Ya
kalli Rashida yace."Ku shiga ciki mana karki bari ta zauna anan." Rashida ta kama hannunta suka soma tafiya, 'kafarta ta dama ce ta ri'ke ta kasa takuwa,