Showing 105001 words to 108000 words out of 176422 words
abu guda ne."!! A zafafe yake maganar......Hafaa ta gumtse dariya kanta a 'kas tana sanyawa mijin nata links din hannunshi ta
ce"Allah ya huce zuciyar governor ba wai abinda kake tunani muke ba, lokacin da kazo gidan bamu dad'e da tashi ba shiyasa."
Ya maka mata harara yace."Ke kika san wannan ni a gurina karfe shida na safe ba safiya bace lokacin duk wani me himma yake tashi
domin gudanar da harkokinsa na yau da gobe ke kuma a lokacin kike sake ma'kalewa wai ke gaki wacce ta iya soyayya."
Khalifa yace."Wai meye laifina nan ne? tayi fa 'kokari sosai kawai kazo mata gida da asuba kuma kace sai kaga yanda kake so ba zai yuwu b
a lokacin da kazo ma ni ko tashi banyi ba wayarka ce ta tasheni." Yace." Dan Allah ni muje dubi time kun 'batawa mutane lokaci mtsss!. Duk suka bishi da kallo cikin mamaki masifa yake musu sai kace sune suka sashi ya aikata abinda ya aikata shine kuma zai
zo ya d'aga musu hankali basuji ba basu gani ba...
A mota ma sai mita yakewa Khalifa, wanda tun baya ramawa har ya shiga ramawa ya dinga yi masa shagu'be duk domin ya fahimci cewar shifa d'an taimako dan haka ba zai zo ya dinga d'aga mishi hankali ba
idan yana so ya cigaba da samun nutsuwa da kwanciyar hankali to yayi gaggawar dawo da iyalinshi gabansa, To
wannan magana da khalifa yayi itace ta kashe masa baki yayi shiru sai dai jefe jefi yakan ja tsaki ya duba agogon dake daure a hannunsa.
Dai-
dai gate din gidan khalifa yay parking ya shiga horn da sauri daya da sauri mai gadi ya bude gate din dan duk sun dauka As ne sai bayan motar ta shiga cikin gidan ne suka gane cewar bashi bane..........Shine ya fara fitowa kafin Khalifan ya fito.......Dake
masu gadin biyu ne daya sai ya tsaya bakin gate din daya kuma ya nufi in da suke....Gaishesu ya shiga yi yana so yayi magana amma be san me zaice ba yaso dai ya shaida fuskokinsu mussaman Khalifa da shine yayi zuwan karshe cikin gidan.......Shine ya fara
yin gaba da nufin shiga cikin gidan sosai Kafin Khalifa yace."Ka d'an dakata na kira wayarsu naji ko." Dan tsayawa yayi yana ya mutsa fuska, Khalifa ya kira numbar wayar Rashida dan itace me waya kuma numbar ta ya kar'ba, Wayar na hannunta tayi saurin d'ag
awa tana kara wayar a kunnanta lokacin suna tsakiyar tasha suna ciku cikun hawa mota........Tayi ta fadin "hello " hello "hello network da hayaniya sun hanata jin muryar Khalifa inda shi kuma nashi 'bangaran yana jin muryar ta rad'au! sai dai dik inda take
tana cikin hayaniyar jama'a da ababen hawa! Fad'i yake " Rashida kina jina? kina jina." Da karshe ma sai wayar ta tsinke yay gaggwar cirota daga kunnanshi yana dubawa.....Mai gadin dake tsaye yace."Yallabai mutanan gidan fa basa nan dan tun sassafe suka f
ita da akwatinan kayansu da alama sunyi balaguro ne."! Ya wani juyo a sukwane! yana kallon gate man d'in bakinsa na motsi......Mai gadin yace."Amma dai ina kyautata zaton yanzu basu isa tasha ba ko sun isa baici ace sun tashi ba tunda kasan dole kafin mo
ta ta tashi sai tayi lodi sai dai kuma muma bamu san inda suka nufa ba."
Jikinsa ya soma wani irin rawa! yana kyarma! kafafunsa suka shiga kyarma Cikin tsawa da d'aga mirya Yace ."Wane irin wawanta ne wannan!? Wane irin sakarci da hauka ne yasa zaku b
arsu su fita! meye amfaninku a gidan!? waye ya basu izinin fita da jakkunan kayansu!? ina kuma suka tafi? Ina zasuje! min da gudan jinana? sai muryarshi ta shiga rawa yana wa tsawa masu gadin mugun kallo babu marasa tunani da kwakwalwa kamarsu da har suk
a barsu suka fita daga gidan sun riga sun cutar dashi mutukar sukayi sanadiyar zubewar cikinsa dama tun jiya yake ji ajikinsa akwai abinda zai faru, Ya kalli khalifa yana tsuma!!! Yace." Ko ina suka nufa sai na lalubosu! dan basu isa su yanke min
wannan
hukuncin ba, kawai ka shiga mota muje." Yana maganar ne a sanda yake nufar motar tasu cikin gaggawa da kuma saurin gaske ya bude motar ya shiga
khalifan dake tsaye cikin mamaki! ya rasa ma tunanin da zaiyi ashe wasila bata da hankali dama? tanajin abi
nda likita tace dangane da lafiyarta da babynta amma zata dauki jiki suyi tafiya mai nisa cikin mota mai kwajab kwagab! babu sakarkaru sai masu gadin gidan da suka barsu suka fita daga gidan........Da saurin gaske yabi bayan abokin nashi ya shiga motar da
gaggawa ya mayar da murfin ya rufe Ahamdun yaja motar da karfin gaske, ya nufi kofar fita daga gidan cikin sauri wanda yake bakin gate din ya matsa gefe guda yana zazzare idonsa.
Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book keda Allah! Ki
ka karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap Numbar
*07084653262*[14/08, 12:04 pm] Farida Books: 'Yr Bngr Sys
*57*
Zaman motar ne ya isheta ta dinga ya mutse fuskarta tana dan tsartar da yawu ta tagar motar kanta ne ke sarawa tana jin wani irin amai n
a taso mata, hayaniya ta mutane duk ta cika mata kunne ga warin fetur da tsamin hammatar wata mata dake kusa da ita d'aga rigarta ta fito da nono ko kunya ba taji tana shayar da yaronta alhalin motar da akwai maza a cikinta, haushin matar ya sanya ta ding
a dauke kanta tana jan tsaki wasu matan sam babu kintsi da kamun kai cikin motar haya mai dauke da mazan da ba muharraman ta ta fito da nono kowa nagani gashi da ta motsa warin hammatar ta zai buga......Mutum biyu kacal ake jira motar ta tashi Wasila duk t
a kosa su tafi ko ta sha'ki iska mai dad'i bayan warin hammatar matar ma mazan dake ciki wasun sy wari sukeyi abinka da wanda rana ta daka....Uwani da rashida kam hira sukeyi suna cin awara da suka siya kafin su shiga motar...Kira ya shigo wayar rashida da
ke kan cinyarta. Da sauri ta kalli Wasila dake zura kanta tagar motar tana shakar iska tace"Anti Wasila kinga Khalifanan ya sake kira." Tace"Ki daga mana to." Rashida ta d'aga wayar tare da fad'in "Hello." Khalifa dake driving yay sauri mika mishi wayar y
a kar'ba da sauri yana kokarin kara wayar a kunnensa ta fad'i 'kasan site sakamakon rawar da hannunsa yake yi....Kasancewar wayar ta bugu da karfi yasa ta mutu ya dauko da sauri ya kunna ta bude, ya lalubi numbar yana sake kira, A dai-dai lokacin ne kuma w
asu matasa suka shigo motar direban motar ya Umarci rashida ta gyara sosai domin su samu gurin zama garin gyarawa wayar dake cinyarta ta fad'i kasan motar ba tare da ta sani ba....Aikuwa shi wanda zai zauna kusa da ita ya sanya hannunsa ya dafe ta, a take
yay dubarar cire sim din lokacin da Rashidan ta juya suna magana da Wasila ya jefa wayar karkashin kayanshi, Rashida matsatsi da xafin mota ya sanya ta manta da wayarta burinta kawai su tashi saboda zafin ya isa.....Aikuwa sai da direba ya cika motarsa tsa
f sannan ya shiga ya zauna maxauninsa ya tashi motar suka fita daga cikin tashar suka dauki hanya
Abin kamar al'mara kiran wayar yake ana ce masa a kashe take, ya kira ya kai sau ashirin maganar dai daya ce wayar a kashe take! Ya d'ago kanshi
yana wat
a irin zufa bakinsa na rawa yace."Khalifa wai meke faruwa ne? Wayar nan fa ta'ki shiga kana ji da kunnanka a kashe take Why! Wad'annan yaran naso su sanya zuciyata ta buga!!!!!!! Khalifa tsorona Allah tsorona Annabi kar cikin nan ya zube, ko a samu wata m
atsalar nasa raina akanshi."Ya 'kareshe maganar cikin rauni da sarewa da al'amarin.
Sosai ya bawa Khalifa tausayi yace."Ni ina tunanin network ne matsalar Amma kar ka damu abokina insha Allah cikin nan ba zai samu matsala ba muje tashar kabuga insha All
ah xamu samesu idan ma motarsu ta tashi ai mun san inda suka nufa kai tsaye sai mu wuce can garkon ni da kaina zanyi wa mai allo bayanin komai."
Hularshi ya cire ya ciro hankici ya goge fuskarshi da saman kanshi, Yana jin wata irin fargaba na kamashi ya
nzu da wane ido zai kalli mai allo to me ma zaice masa idan sunje? Yace"Khalifa bani da wani bayani da zan iya yiwa mutumin nan saboda ina jin kunya wallahi in ce masa saboda d'ana ko 'yata dake cin Wasilan zan dauketa kasan da akwai nauyi." Khalifa yace."
Kar ka damu zanyi mishi bayani."
Ya shiga girgiza kanshi yana fad'in "Kamar nasan abinda zai faru shiyasa jiya nace maka muje inda suke da yanzu duk hakan bata faru." Khalifa yace."Ni nayi mamaki wallahi saboda jiya lafiyar Allah muka rabu dasu ko da was
a basu shaida min cewar zasu tafi wani gurin ba amma basu kyauta ba wallahi kuma Wasila tayi wautar gaske."
Girgixa kanshi kawai yake yana adduar Allah yasa su samesu a tasha don shi kam yana bala'in jin kunyar had'a ido da mai allo.
Khalifa ne kawa
i ya iya fitowa daga motar bayan shigarsu tashar ya kutsa cikin mutane direbobin motoci yana dube duben motocin mutane, ko kusa ko alama bai hango koda kyallin mayafin wata daga cikinsu ba, haka ya gaji ya nufi inda motar su ke fake.....Shi kuwa uban gayya
r tamkar wani zautacce ko kuma mara kunne yana ri'ke da waya a hannunshi sai kiran numbar Rashida yake tamkar mai kunnan 'kashi ko kuma kurma yana jin abinda matar nan ke fad'a masa cewar wayar a kashe take amma ya kasa daina kiran wayar.......Ganin Khalif
a ya doso motar tasu cikin sanyi jiki ya sanya shi rarraba ido yana jiran karasowarsa...
Khalifa yace."Babu fa alamun yaran nan cikin tashar nan kawai shiga mota muje." Jiki a mace ya bud'e mota ya shiga duk yayi wani laushi kamar mara lafiya....Khalifa y
aja motar suka fita daga tashar duk rayukansu babu dad'i.......Sai da suka hau kwalta sosai kana ya sauke numfashi yana huci! yace."Khalifa Allah banta'ba ganin sukuwar uwa irin uwar wad'annan yaran ba, ni yanzu ma ita nake jin haushi wallahi." Khalifa yac
e."Gaskiya tayi wauta itama data d'auki yarinyar nan da wannan lalurar suka dauki hanya bayan sai da na fad'a mata dokar da likita ta kafa kan 'yar tata shiyasa wallahi mace komai shekarunta watarana ta tafka maka wani abun haushin sai kaji kamar ka d'ora
hannunka akanka.
Yace."Nifa babu ruwana Allah cikina ya samu wata matsala sai na dauki mataki kanta da ita da uwar tata." Khalifa yace."Ai kaji irinta wai kai me yasa kake hakane? Matar nan fa ta tabbatar min da cewar sunzo har gidanka da maganar cikin
basu samu damar ganinka ba suka hakura suka koma kan me yasa za kaga laifinta anan bayan tayi kokarin ganin an fita hakkina."
Tsaki! yay yaja bakinsa yayi shiru yana muzurai! da ya tuno wani abu sai gabanshi ya fad'i! gaskiya yana bala'in son cikin nan na
shi a yanzu ji yake zai iya hakura da komai na rayuwa mutukar cikinsa zai tsira.
Tafiya suke mota na gwajab gwajab yayinda ciwon ciki da mara ya tsananta a gareta ta! ta dinga sunkuyar da kanta tana zufa da kiran sunan Allah gumi ko ta ina d'iga y
ake a jikinta, tsabar yanda take jin jiki sunan Allah kawai take kira tana jin wani irin imani na ziryartar ta anya kuwa wannan cikin bashi ne ajalinta ba? abinda take fad'a kenan cikin zuciyarta.
Sun isa garin Garko Lafiya sai da kuma lokacin mai all
o ya jima da fita tsangaya, Tanimu ne yay musu jagora har makarantar tashi.....Mai allo na tsakiyar al'majiransa ya hango zuwansu sai ya mike a nutse yana fara'a yana musu barka da zuwa......Cikin wata rumfar kwano da babu kowa a jiki suka nufa. Ma allo da
kanshi ya karkade musu tabarma suka zauna sai aka shiga gaishe gaishe, Ahamdu sai sunkuyar da kanshi yake duk kunya ta dabaibayeshi sai yanzu yake jin kunyar dattajon yaga shi kuwa sai fara'a yake yana tambayarsa gida da harkokin yau da kullum. Khalifa ya
ce."Alhamudllhi malam komai na tafiya yanda akeso sai da aita tayamu da addua." Mai allo yace."Addua munanan munayi har sai da numfashin mu ya dauke."
Khalifa ya ja gwaron numfashi kafin ya gyara zamanshi a nutse yace."Allah shi gafarta malam dama mun b
iyo sahun yaran nan ne wato ina nufin Wasila da 'kanwarta da kuma mahaifiyarsu, domin muji shin sun iso lafiya! sannan kuma muna da tabbacin cewa nan suka nufo dalili basu da wani gurin in ba nan d'in ba, Allah shi gafarta malam babu maganar rufe rufe ci
kin maganar nan Yarinyar nan Wasila na dauke da ciki har na tsayin watanni uku da satika kuma akwai matsala mai girma tattare da ita da d'an dake jikinta wannan shine babban dalilin ma da ya sanya shi Abokin nawa yace."Lallai ilallah sai munzo domin mu tab
bar da zuwan nasu cikin 'koshin lafiya."
Mai allo ya dinga kallon Khalifa cikin mamaki da kad'uwa ya d'an gyara zamanshi kafin yace."To Idan na fahimci inda maganarka ta dosa anan shine kana so ka sanar dani cewar kun biyo sahun su Wasila domin kuna tu
nani ko nan suka zo kamar yanda ka fad'a hakane ko? Khalifa yace."Hake Malam." Mai allo yace."To a gaskiya ni dai har na fito daga gida banga zuwansu amma ban sani ba ko bayan na fito suka iso bari nasa yaro yaje ya duba a gida." Ya mike ya fita daga ind
a suke.
Ahamdu ya kalli Khalifa cikin sarewa da tsananin damuwa yace."Anya Khalifa anya yaran nan suna nan kuwa? jikina na bani ba nan suka zo ba." Khalifa yace."Ka dai bari tukkuna mybe bayan ya fito daga gidan suka sauka garin kamar yanda ya fad'a d'i
n in banda abinka idan ba nan suka zo ina zasuje da yafi nan d'in." Yay shiru yana jin wata irin zufa na karyo masa, mikewa yay ya fito daga rumfar kwanon ya kama kallon hanya sai kace wani zautacce ga rana sai kwalle masa ido take.
****
Misalin 'Kar
fe biyu da rabi na rana suka sauka garin Fataskum, bayan sun sauka daga mota Uwani ta dinga rarraba ido tana dube dube hanya dan garin gabad'aya ya sauya mata yau kusan shekaru goma sha biyu da rabonta da garin, tin tana goyon Rashida lokacin Yahuza na dan
da mutuwa tunda tayi wannan zuwan bata sake waiwayar garin ba, dama mutum hud'u ne suka rage musu a dangi Babban yayansu mahaifiyarta da suke kira da Kawu Madu sai Mai binshi Kawu Isa sai kuma Iya mai waina da Tabawa dama su biyar iyayensu suka haifa mah
aifiyarta itace ta uku ita ke bin Kawu Isa sai Iya mai waina sai kuma Tabawa! Mahaifiyarta itace kawai tayi aure a wani gari, amma dukaninsu cikin garin Fatskum suke tare da iyalinsu mutukar sun fita daka garin to sunje wani garin ziyara.....Tun bayan rasu
war mahaifiyar Uwani Kawu yaso daukarta domin su dinga kallonta a matsayin 'yar uwarsu, mahaifinta ya'ki lamince masa haka suka hakura suka bar mishi 'yarshi, gashi bashi da cikakkiyar lafiya shima a lokacin ya hana a tafi da itane domin ya dinga kallonta
tana d'ebe masa kewar mahaifiyarta.......Sai da cutar ajali ta kamashi ne 'kaninshi ya daukeshi ya kaishi gidanshi dake akwai shago a wajen gidan nan ya ajeshi yake kula dashi, to shine fa tun daga lokacin Uwani ta soma shan wahalar rayuwa gidan Kawun nata
har mahaifinta ya kwanta dama, a lokacin ta 'kara shiga tsaka mai wuya ga wuya ga maraici ga tsananin azabah! Saboda zalinci irin na Kawun ya siyar mata da gidan da ya zama gadonta ya sanya kudin a aljihunsa ya cinye matansa na zugashi da fad'in Ai idan y
aci Allah ba zai tuhume shi ba tunda dai shima yana ciyar da ita...........Sai da sukayi aure da Ayuba ya jagorance da kanshi sukaje can Fatsukum din dangin mahaifiyarta da kwatance, to tun daga sannan ta gane hanya........Saboda matsatsi da talauci da kum
a rashin kudin mota ya sanya bata zuwa garin a kai a kai, sai ta dauki shekaru masu yawa kafin taje to wannan karon dai shekarun data dauka ba taje ba sun fi na baya.......Da tambaya suka iske gidan Kawu Madu dake shi d'in ba 'boyayyen mutum bane a gari
n yasa basu sha wahala ba,
Suna zaune kan katuwar tabarma shida abokanansa gabansu katon farantin silba ne jere da kwanuka, da jug jug na ruwa da alama abinci suke shirin ci ya hangosu, Sai ya shiga wasiwasi da tunani to sai da suka iso inda suke ya ta
bbatar da cewa su d'in ne Yace."Uwani ko ba ita bace."? Tace."Nice Kawu."! Sai ya washe bakinsa yana fad'in "Kece kike tafe da ranar nan babu shakka yau an tuna damu kenan gaki ga zuriarki lallai yau patskum nada manya 'baki sannuku da zuwa." Mi'kewa yay y
ana 'kwalawa yaran dake wasan langa langa a 'kofar gidanshi kira.....Suka rugu a guje yace."Maza ku kwashi kayan nan ku shida dasu gida.....Yaran suka dinga ihu! suna fad'in "Yeeee! munyi 'baki daga birni da gudu suka runtuma cikin gidan suna jan akwatinan
kayan nasu
****
Can ya hango yaron da aka tura gidan ya fito daga wata hanya yaji tamkar yaje ya tareshi ya tambayeshi, sai dai kawai ya daure ya bi yaron da kallo har ya isa inda mai allo yake ya tsuguna yana masa magana." mai allo ya Umarceshi da ya
koma gurin zamanshi kana ya mike daga kan kujerarshi Ya nufo inda yake tsaye babu yabo babu fallasa a tare dashi, tun kafin ya karasa inda Ahamdun yake ya hango damuwa da tashin hankali a tare dashi, sosai ya shiga mamaki yana tunanin