Showing 117001 words to 120000 words out of 176422 words

Chapter 40 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

sa takalminta da lullubin mayafin ta da ya sauka kafadarta........Rashida ta karaso gurin cike da nauyi da jin kunya take musu barka da zuwa! Ya dinga amsawa da sakakkiyar fuska kamar bashi ba sai wani dariya yake yana godewa Allah lallai Khal

ifa Waliyi ne ashe dai da gaske a maganarshi , ya tabbata tunda yaga 'yar uwarta itama tana ciki........Ya kalleta a nutse yace."Ina fata mai allo na nan." Tace."Eh yana nan yau bai fita da wuri ba ya tsaya yiwa anti Wasila rubuta." Da jin maganarta sai y

aji tamkar an tsiyaya mishi ruwan sanyi mai madara a ranshi yaji duk wani kunci da tashin hankalinsa ya kau! sai ya dinga zumud'in shiga gidan, yana fad'in "To kije ki shaida mishi cewar mune muke tafe." Da sauri Rashida ta nufi cikin gidan cikin murna da

farin ciki sai kace wacce akace ga mahaifinta ya dawo duniya......... Lokacin da shiga gidan Wasila ta tashi hakanan Bitan ma tana kicin tana gyara tukunya, ta zube a gabanshi da walwala a fuskarta tace"Kawu ga Alhaji Ahamdu mijin anti Wasila nan shida m

ahaifiyarshi yace a sanar maka da zuwansu." Mai allo ya jinge allon dake hannunshi yana kallonta Yace."To Masha Allah sune suke tafe cikin wannan ranar? maza karkade tabarmar nan ki gyara musu guri bari na shigo dasu Allah yasa ma ban fita ba da munyi sa'

bani." Rashida ta shiga karkad"e tabarma tana sake share gurin da marmatsar da abubuwan dake kan hanya.....Mai allo ya sanya takalmansa a nutse ya fita daga gidan.........Tana 'kokarin fitowa daga band'akin ne hancinta ya sha'ko mata masifaffen 'kamshin t

uraransa da ba zata ta'ba mancewa dashi ba......Gabanta ya yanke ya fad'i lokacin da ta tsinkayi muryarshi yana sallama a gidan ta kuma tsinkayi muryar mai allo yana fad'in "Sannunku da zuwa Alhaji sannu kun d'auko rana Hajiya sannu da hanya, ku shigo

ciki

......'Kyauran band'akin ta ri'ke gam! jikinta na kyarma! ta dinga fad'in innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! me ya kawo shi? me yazo yayi mana? me yake nema kuma? babu wanda zai bata amsa, ta cigaba da rike kyaure tana rawar jiki tana kuma juyo muryoyinsu

a lokacin da suke gaisawa da juna. Jikinta ta duba daga ita sai zanin atamfa dan da zafi ya isheta bayan fitar rashida ruwa ta cika a bokiti taje ta kwara a jikinta wai ko ta samu sassauci babu abinda ke jikinta sai zanin atamfar da dankwalinshi, kamar z

a tayi kuka yanzu ni ya zanyi na fito ga mutane gashi ba suttura a jikina? tunanin da take kenan ta juyo muryar Mai allo na fad'in " Rashida shiga ki kira 'yar uwarki mana ni kaina a 'kasa ina rubutu ban san sanda ta tashi daga gurin nan da tana kwance a g

urin nan da kake zaune." Yafad'a yana nuna masa inda yake zaune, sai ya shiga bin gurin da kallo kamar zai ganta a gurin......Rashida ta duba dakin bata ciki, Bitan dake kokarin fitowa daga d'aki tace"Ai inajin tana band'aki wanka take kasan dama yini take

watsa ruwa bata son zafi ai." Mai allo yace."To to koda naji." Ahmadu kuwa jin abinda Bitan tace sai kawai ya shiga rarraba idanunsa a cikin gidan yana laluben ta ina zata fito......Aikuwa sai yaji motsin 'kyaure a wani 'bangare da sauri ya mai da idanun

shi gurin......Ta fito a hankali kamar wacce 'kwai ya fashewa a ciki take tafiya, zanin jikinta ya d'angale saboda daurin kirji da tayi sai tayi amfani da dankwalin gurin kare kirjinta da fuskarta.......Gogon ya wani susuce a gurin ya dinga kallonta tin da

ga kafafunta har zuwa kanta, jikinsa yay wani bala'in sanyi lokacin da ya hango tudun cikinsa dake jikinta, rintse idonsa yayi yana tasbihi ga Allah ya sauke wata gawurtacciyar ajiyar zuciya, Ya bud'e idanunsa da sauri a dai-dai lokacin da take 'kokarin

shiga d'akinsu santsin takalmin dake kafarta ya kusa kayar da ita, tayi axamar rike kyauran d'akin tana salati zubewa tayi bakin kofar lokaci guda zanin jikinta ya kusa sa'bulewa dankwalin da ta rufe kanta da kirjinta tuni yayi nashi guri, wani irin 'kulle

wa marar tayi tana murd'a mata.........kawai ganinsa tayi tsaye a kanta ya wani gigice yana sa'be babbar riga dama manyan kaya ya saka tunda duk sanda zaije gurin mai allo baya zuwa da tazarce na shadda ko yadi riga da wando da malin malin yake sanya......

..Shine yay bake bake a gurin yana fad'in "Subahanallahi! Kafin ta juyo miryar Bitan na fad'in " Haba Wasila sai da fa na hanaki saka takalmin nan saboda santsin sa sau nawa yana kokarin kayar dake dan dai kawai Allah na kiyayewa ne, kinga ni dai yau ga ab

inda ya ja miki." Bitan ta 'karashe maganar tana kokarin mikar da ita! Rintse idonta tayi tana fad'in "Wayyo cikina mara ta ciwo Bitan Ya Allah."!!!! Da sauri yay nufi shiga dakin zufa na karyo mishi Hajjah ta dakatar dashi tana hararshi, ita ta shiga dak

in suka kama Wasilan suka janye ta daga bakin kofa! Shi kuma ya cire hularshi yana fifita da ita! Wannan wane irin tsautsayi ne? daga zuwanshi yana murna Allah dai ka taimake ni."! Abinda yake fad'a kenan ya koma ya zauna yana cigaba da fifita da hulars

hi fargaba duk ta cika masa zuciya......Mai allo ya kalleshi cikin naxari sai kawai ya girgiza kanshi yana murmushi a cikin zuciyarshi ya cigaba da d'auraye rubutun dake jikin allon hannunshi, Yace." Tuntuni naji Bitan nayi mata magana kan ta daina saka ta

kalmin nan saboda rashin ji ta'ki dainawa, gashi yana so ya cutar da ita, tunda abin ya kasance da haka da kaina zan dauke takalman na fita dashi.''

Ya aje hular dake hannunshi a gefe yana fuskantar mai allon sosai, Yace."Shine babban damuwar dama, ak

wai kuruciya da rashin sanin ciwon kai a tare da ita shiyasa take aikata komai yanzu daba dan Allah ya takaita ba da mummunar faduwa za tayi." Mai allo yace."Allah dai ya kikeye."

Mikewa yay hannunshi rike da rubutun ya nufi dakin......Binsa yay da kallo y

ana ji kamar yabi bayanshi sai dai kallon da Hajjah tayi mishi a d'azu yake tunawa.

Mai allo ya tsaya bakin 'kofar dakin yana mikawa Bitan rubutun hannunshi da fad'in "Bata tasha kana kuma ki shafe mata jikinta dashi, za taji sassauci rashin jin magana

ne irin na mutan yau, takalma zan daukesu yanzu in fita dasu idan ya kasance ta shiga bandakin babu takalmi sai ta shiga haka ai lalurace tunda shi takalmin na baraxana da lafiyarta" Hajjah babah tace"Kwarai kuwa malam ka kwashe takalman a fita dasu tunda

suna neman cutar da ita kuma mutukar tana ganinsu to ba zata daina sakawa ba."

Mai allo ya sunkuya bakin kofar ya kwashe sabbin takalman 'yan madina ya samu leda ya zuba a ciki ya daure ya rataye jikin wata kusa dake bangon gidan yana fad'in "Anjima i

dan zan fita zan fita dasu in bawa yara sayi amfani dashi."

Yana zaune yana kallon mai allon duk ya rasa abinda ke damunshi hankalinshi na cikin dakin burinshi ya sake tozali da ita da cikin jikinta, jikinsa ne yay sanyi ganin babu wata sakewa irin tada

a tare da mai allon yasan dai sun gaisa cikin girma da mutunci amma duk wannan rawar jikin da mai allon keyi masa ya daina magana ma ba sosai sukeyi ba......Hajjah babbah da Bitan suka fito daga dakin, Hajja na fad'in "Ciki fari dama ai kyaga wauta iri ir

i Allah dai ya rabasu lafiya.'' Duk suka amsa da " ameen." Har dashi gogan da yabi ya zubawa hajja ido yana so yayi magana sai dai yayi shiru ya sunkuyar da kanshi 'kasa, tunda khalifa baya gurin to yanzu hajja itace garkuwa a gurinshi amma shi kanshi yanz

u ya gane ya tafka babban kuskure sosai mugun kunyar mai allon ne ma ya rufeshi yanzu da wane ido xai kalleshi yayi mishi bayani dangane da abinda yake tafe dashi.

Hajjah ta gyara zamanta a nutse tace"Malam gurinka nazo domin magana mai muhimanci nake

tafe da ita.'' mai allo ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Hajiya ina sauraranki." Hajja tace"Malam da farko dai ina me baka hakuri a bisa abinda ya faru, nasan dole rayukan ku su 'baci saboda duk mutumin da akece an saki d'anshi dole ne ranshi

ya 'baci mussaman idan anyi bunkice an duba anga babu 'kwakkwaran dalilin da ya sanya aka aikata sakin kamar dai yanda al'amarin nan faru, yarinyar nan wasila an saketa ba tare da wani dalili me karfi ba, tabbas an shiga hakkinta mutuka!! kuma irin wanna

n sakin shine ubangji baya so.....To amma nasan dai kai mai ilimi ne kuma kasan kaddara dai- dai gwargwado kasan cewar duk abinda Allah ya kaddara sai ya faru a kan bawanshi to sai ya faru, saboda haka ina so dukaninmu mu dauki wannan abun a matsayin kadda

ra wacce ta riga fata......Kuma hakika naji dad'i sosai da ya kasance cewa sakin an aikata irin wanda musulunci yake so, akwai sauran dama a halin yanzu, dan haka muke ro'ko ayi hakuri yarinyar nan ta koma d'akinta."

Mai allo ya sauke ajiyar zuciya mai

'karfi! yana kallon matar.....Hakika matar nada mutunci da kima da kuma sanin ya kamata ko ga yanayin kalamanta, baya jin zai iya wani ja'inja kan maganarta mutukar shi Ahmadu da yarjewarsa take masa bikon matarshi, zai amince da maganarta, sam baya so a z

o ayi abu irin na baya ma'ana a koma gidan jiya, Ahamdu ne me aure ba Hajjah ba kuma shi ake so ya furta da bakinshi kan cewar ni wane na

janye sakin da nayi wa mata wance na mayar da ita dakinta yanzu tana matsayin matata kamar yanda addinin musulunci ya

tanada, to mutukar yaji wad'annan kalmomi daga bakinshi, bashi da tace addini ya riga ya halasta masa matarshi tunda dama ba tayi iddah ba." Yace."To masha Allah Hajiya, ai dukanin abinda kikaga ya faru dama da sanin Allah duniya babu wanda ya isa ya tsar

awa kanshi rayuwa face wacce Allah ya tsara masa, auran Ahamdu da Wasila ya 'kare a lokacin da Allah yake so, kuma a sanda yake so zai iya sanyawa su koma su cigaba da zama mutukar rabo bai 'kare a tsakaninsu ba, Ni bani da tacewa anan gurin hakanan itama

yarinya bata da magana, tunda a yanzu addinin musulunci ya bashi dama a hannunshi, zai iya yankewa kanshi hukunci, ina nufin ya d'auki aniya a zuciyarshi kancewa ya mayar da matarshi ko kuma akasin hakan duk wannan damar yanzu a hannunsa take, Yanzu ni shi

nake jira ya furta min da bakinshi cewar ya amince yarinyar nan ta cigaba da zama matarshi ko A'a."? Mai allo ya 'kare maganarshi hankalinshi a kwance.

Hajjah babba tace"Eh gaskiya ne malam maganar ka na kan hanya a yanxu magana na bakinsa dani da kai

duka 'yan fatan alkairi ne domin dukaninmu ba zamu haramanta abinda ya halasta ba saboda haka magana yanzu tana gurunka kai muke sauraro." Hajja ta'kare maganarta tana me zuba masa idanunta.........A nutse ya d'ago kanshi zaiyi magana kenan, Ta fito daga

dakinsu, sai duk suka zuba mata ido har ta tattako a hankali ta 'karaso inda suke zaune! gaban mai allo ta dur'kusa tana hawaye da rike masa hannuwa tace"Kawu kaine fa kace ba zaka sake takurani ba! Kawu ashe ka manta al'kawarin da kayi min ranar da muka z

o garinan kace ba zaka sake yi min tilas ba, zaka barni da kaina na za'bi miji wanda yayi dai-dai da rayuwata na aura." Da sauri! ya d'ago kanshi yana kallonta jin abinda take fad'a! da cikinsa za take tunanin yin aure? Kafin ya gama tunani ya juyo muryart

a na shashshe'ka tana fad'in "Kawu ni daina bana son na koma gidanshi, sabida ba zan iya rayuwar da nayi dashi a baya ba, Zargina yakeyi Kawu nasan kasan aure da zargi a musulunci ya haramta ni kawai a kyaleni na haifu lafiya sai a bashi d'anshi." Cikin k

uka da yanayi na damuwa take maganar gashi ta ruk'e hannun Kawunta katamau!

Dukaninsu suka bita da kallo mussaman gogon da duk jikinsa yayi sanyi ya dinga kallonta yana hango tsabagen 'kiyaysrshi a cikin kwayar idanunta......Sai yaji wani irin ba'kin ci

ki da takaici ya turnu'keshi! wato har wani kuka take tana nadama da fad'in ba zata koma gidanshi ba, to me yake mata da za tace ba zata koma gidanshi ta cigaba da yin rayuwar da tayi a baya ba? shin tun da suke yaushe yayi zarginta? shine zai fad'awa kowa

cewa ita d'in kamila ce kuma nitsatstsiya tunda ta kawo mishi burducinta! bai ta'ba zarginta ba sai sanda wannan al'amarin ya faru!!!! 'Kwafa yay cikin ranshi, ai magana a hannunshi take ba'a hannun wani ba, malam mai allo na shirin yayi magana, Ya rigash

i da gyaran murya kafin yace."Ai maganar saki tuntuni na janyeta malam yarinyar yanzu haka a matsayin matata take, wannan dalilin ne ma ya sanya ni dauko Hajja domin tazo ta baka hakuri a bisa abinda ya faru tsautsayi ne da kaddara amma insha Allah hakan b

a zata sake faruwa ba." Mai allo ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace."To madallah Alhaji naji dad'in wannan kalmar taka kuma Wasila zata koma gidanka insha Allahu amma ina so in baka shawara ko kuma in tunasar dakai duk da cewar ka sani, Allah da kanshi

ya hallata saki amma kuma baya so a akaita shi, kayi kuskure a lokacin daka yanke hukunci, bance yarinyar ba tayi maka laifi ba tabbas tayi laifi wanda ya dace ka dauki ko wane irin mataki a kanta, amma banda saki, ni a ganina

ba tayi abinda za'a saketa b

a, saboda ita mace komai girmanta da shekarunta abar tausayi ce ballanta yarinya 'karama irin wannan!? Ka saketa tana da ciki, abinda ba'aso sannan ta amshi laifinta ta nemi afuwarka ka koreta daga gidanka, bazan 'boye maka Alhaji yarinyar nan ta wuya da w

annan cikin na jiki kafin su zo nan kenan, sai bayan zuwansu, dana tsananta gurin yi mata tofi da rubutu sannan ta samu lafiya har kazo ka ganta haka, ina fad'a maka da can kwanakin baya kazo da sai ka tausaya mata mutuka dan abincin kirki bata iyaci sai y

ame yame irin nasu, to Alhamdullhi yanzu lafiya ta samu tana iya cin komai ta zauna lafiya, saboda haka nake baka shawara da kuma tunasarwa kan cewar duk wani abu da matarka za tayi maka na kuskure to ka dinga sanya hankali da nutsuwa kafin ka yanke hukunc

i akai dan saurin saki bashi ne hukunci ba, wallahi Alhaji da kazo bayan yarinyar nan ta haihu to banga dalilin da zai sanya in tilas ta mata cewar sai ta cigaba da zama da kai ba, zan dai baka dama ka shiga cikin zawarawanta idan har kana da muradin hak

an."

Ya dinga kallon mai allo cike da d'umbin mamaki! wato shine ma zaibi layin zawarawa sai kace wani shashasha! tsaki yaja cikin ranshi mai allo bai ta'ba 'bata masa rai ba irin yau! amma sai ya shanye ya dake! ya hakura tunda dai magana ta'kare ai shi

kkenan........A nutse yace."Arrama insha Allahu hakan ba zata sake faruwa dukanin abinda ka fad'a gaskiya ne tsautsayi da 'kaddara basa wuce kan kowa, saboda haka insha Allahu magana ta wuce a gurina zan rike yarinyar nan tsakani da Allah da manzonsa, Sabo

da haka yanzu sai su shirya kayansu ita da 'yar uwar tata mu tafi in yaso sai ta dinga d'an d'ebe mata kewa har Allah ya sauketa lafiya"...............Da jin maganar dake fitowa daga bakinshi yasa ta mike da sauri ta shige d'akinsu tana wani irin kuk

a mai cin rai!!? Ta sanya hannuwanta duka ta dunga dukan katifar dake shimfid'e a tsakar d'akin.

Littafin na kudi ne.....!

Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whsap numbar

*07084653262*alliya:

'Yr Bng

r Sys

*62*

Rashida ce ta shiga dakin ta tsaya kanta tana kiran sunanta, "Anti Wasila dan Allah ki daina kuka ni wallahi banga abin kuka da damuwa anan ba,Allah na yarda da nadamar mutumin nan yanzu kuma yana sonki dan da baya sonki ba zai tayar da hankal

inshi a kanki ba, kawai ki hakura ki koma dakin ki shine mutuncinki damu gabakid'aya." Idanunta jaga-jaga da hawaye ta dago tana kallon 'yar uwar tata dake durkushe kusa da ita, "Rashida nifa bazan koma yanzu ba sai na haihu haka kurrum kai tsaye zaizi yac

e ya mai dani sai kuma na kwashi jiki na bishi babu wani shiri da da yanxu ba d'aya bane yanzu nasan ciwon kaina." Rashida tace"Eh gaskiya kuma hakane to da zai bari ki haihu shikkenan yafi sauki hakan amma yanzu ku kin koma nasan hankalinsu mai allo ba za

i kwanta ba.

To a can tsakar gida kuma sai fafatawa ake tsakanin mai allo da Ahamdu da kuma Hajjah inda mai allo ya kafe kai da fata yace Wasila ba zata koma ba sai ta haihu sannan Ahamdu da Hajjah sai rarrashinsa suke da kawo masa

misalai wanda suke

nuni da cewar in ta koma d'in ai babu matsala insha Allah zasu kula da ita da kyau dan har hajja tayi al'kawarin zama tare da ita har sai ta haihu tayi ar'bain tukkuna sannan ta tafi gidanta, Malam mai allo yayi shiru yana nazarin maganarsu, shi dai hanka

linsa yafi kwanciya da zaman yarinyar a gabanshi to amma bashi da yanda zaiyi dole ya hakura ya basu tinda yanzu suke iko da ita, Yana mutukar ganin girman hajja sabida matar tasan abinda takeyi sosai.....Yace."To shikkenan ai tunda kun rinjayeni na bar mu

ku amma kuyi hakuri ku barmin rashida dan naji kana cewa tare zaku tafi da ita." Ahmadu ya marairaice sosai yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login