Showing 147001 words to 150000 words out of 176422 words
maganar cikin 'ka
s'kantar da kanta.......Uwani ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Kuluwan kamar ba itaba wai yau an wayi gari Kuluwa nayi mata magana cikin kalami mai dad'i lallai duniya kenan.
Tace"Kuluwa ba wai bana so muje bane gaskiya bana so muje gidanan kiyi wani
abu da zai sanya kima da mutuncinmu ya zube mutumin nan ba karamin mutum bane kuma kinga mu sirikai ne dole mu kama girmanmu ke kuma kuluwa baki da girma sai na jiki idan kin amince cewar xaki kiyaye kuma zaki nutsu sosai to shikkenan sai mu shirya idan Al
lah ya kaimu dani dake da Kawu da kuma su Inna mai waina muje muga abinda yarinyar ta haifa."
Cikin kwantar da kai Kuluwa tace"Haba Uwani wallahi bazan aikata abin kunya ba zan kula sosai bazan baki kunya ba insha Allahu." Uwani tace"Shikkenan to yanzu za
n tashi na shirya na nufi gidan Inna Tabawa domin na shaida mata halin da ake ciki." Kuluwa tace"To hakan yayi bari idan na sauke abinci sai na d'an d'umamaki ruwan wanka kafin ki tafi kiyi sai kinfi jin dad'i." Mikewa tayi ta nufi kicin........Uwani tabi
ta da kallo cike da mamaki.
Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*76*
Koda Rashida ta dawo ta tarar Inna hajara
ta tafi itama sai da taji rashin dad'i tayi ta tambayar Wasila dalili, kunya ta hanata fad'a mata kawai sai tace"Rashida kin san dai rigimar Inna hajara dama da kyar na samu ma ta zauna tayi wad'annan kwanakin amma babu wani abu da akayi mata wanda zai sa
nya ta tafiya kawai dai dama tayi ra'ayi ne." Rashida ta amince da maganar Wasila suka zauna suna jimamin tafiyar Innar tasu.
To can 'bangaran su mai girma governor Lawan Rabo sun tada aiki sosai shida mu'karrabansa duk dan ganin yanda al'ummar jahar s
uka tashi hankalinsu gurin ganin sun rusa tafiyarshi da kuma jam'iyyar da yake ciki gabakid'aya jamiyyar da yake ciki dashi kansa sun daina power gabakidaya jama'a nata komawa jam'iyyar *CPC* jam'iyyar su Amadu kenan duk ta doke sauran jam'iyyun da suke
adawa da junansu......Hankali mai girma governor yayi masifar tashi, babu shakka idan ya tsaya kallon ruwa to kuwa kwad'o zaiyi masa 'kafa, tuni ya kira 'yan fadarshi irin su As da mataimakinsa suka zauna zaman meeting inda suka yanke shawarwarin da suke
ganin zasu taimaka musu gurin campaig, governor ya fitar da miliyoyin kudi ya rabawa 'yan gwangila irinsu As yace aje ayi duk abinda ya kamata a cikin jahar domin a jawo hankalin jama'a jam'iyyarsu........As suka fara aiki gadan gadan inda suka fara rushe
rushen gidajan jama'a da masana'antu wai zasuyi babban titin da jirgin 'kasa zai dinga wucewa, jama'a da yawa suka shiga halin damuwa an rushe musu muhalli ba'a basu diya ba masu sana'oi suma an rugaza musu guri ba'a biyasu ba, a mai dasu gida an tsuganar,
takaici ya ishesu sai kawai suka soma shiga gidan redio suna zage zage da fad'in Allah sai ya saka musu wannan zalincin da ake musu.....Mai girma governor ya tafi katsina gurin abokinsa ya samu labarin abinda yake faruwa a jahar tashi, a take ya kira As
yace ya shirya da kanshi ya shiga gidan redio yayi bayani wanda zai dauki hankalin jama'ar gari su amince da manufarsu.
As ya shiga gidan redio na salama ya dinga zabga 'karya da 'karairayi kan cewar mutukar jama'ar gari sun sake za'bar lawan rabo to babu
shakka zasuji dad'i a wannan karon komai zaiyi sauki za'a samu sauyi na rayuwa sannan yace."Duk wanda aka rushe masa gida da gurin sana'arshi a gurin aikin titin da sukeyi to duk su kwantar da hankalinsu za'a biya su hakkinsu......Ashe jama'ar gari sunyi
dafifi a wajen gidan redion koda su As suka fito dashi da 'yan rakiyarsa da 'kyar suka sha dan ma da akwai security a tare dasu amma dai dik da haka sai da sukayi raga raga da gilashin motocinsu suna tafad'in "bamayi! kano ta d'an musa ce."
Ranar Amadu
da Khalifa sun sha dariya hankalinsu kuma ya kwanta sosai ganin suna samun nasara a cikin tafiyar tasu kullum 'kara samun masoya sukeyi ta ko wane fanni.
Tun ranar da Inna hajara ta bar gidan a tsakaninsu suka daina samun jituwa wanda gaisuwa ce kawa
i take had'asu daga haka shikkenan zai fice harkokinsa, kuma koda ya dawo gidan yaga bai ga Inna Hajara baice mata komai ba itama ba tace masa komai ba, dukaninsu sun shiga cikin damuwa mai tsanani babu kamar ya ita kullum sai tayi kuka, ita bata ga abin f
ushi da daukar gaba ba ta lura yana da hakuri sosai amma bai iya fushi ba dan haka sai ta yanke shawarar tunkararsa ta bashi hakuri idan ya hakura shikkenan idan bai hakura ba zata rabu dashi duk ranar da ya gaji ya sauko dan kanshi.............Yau da wuri
ya shigo gidan dan goma ma ba tayi ba, sai da ta bari Hajja da Rashida sun bar palon tukkuna ta fito daga dakinta tayi kwalliya sosai sai 'kamshin turare take.
Murd'a kofar dakin tayi ta shiga da sallama a bakinta.....Babu kowa sai dai tana jin alamun mo
tsi a toilet dinshi ta dan zauna gefan gadon tana bin dakin da kallo yaushe rabonta da shigowa tun ranar suna gashi yau kwananta talatin da bakwai da haihuwa saura kwana uku tayi ar'bain......Tana zaune tana sa'ke-sa'ke ya fito daga toilet d'in 'kungunsa d
aure da towel da karami a hannunsa.
Had'a ido sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa.....Kadaran kadahan ya kalleta ba tare da yace komai ba ya 'karasa bakin mirror ya dan tsaya yana sake
goge fuskarsa.....A sanyaye ta mi'ke ta isa i
nda yake tsaye ta 'karbi towel din hannunsa tana so ta goge masa jikinsa, sai kawai ya bar mata gurin, Ta bishi da kallon mamaki yaje ya nemi guri ya zauna gefan gado yana shafa vasillin a jikinsa, ba tayi zuciya ba ta isa inda yake a hankali ta sanya han
nunta ta 'karbu vasilin d'in tana marairaicewa, Ya mi'ke kawai ya barta a gurin........Wardrobe ya nufa domin daukar jallabiyarsa, da gudu taje ta rungume faffad'an bayansa tana shashshekar kuka tace"Kayi hakuri kaji." Ajiyar zuciya ya sauke yana dan jin
sassauci cikin zuciyarsa, shima dik abinda yake daurewa kawai yake yi yana dai so ya nuna mata kuranta ne, amma ba dan ya cuzguna mata ba, idan da ta kwantar da hankalinta shima ai yasan abinda yake yi ba zai ta'ba cutar da ita ba, amma ranar nan ya kwadai
tu da ita mutu'ka ya kuma nemi ta a gaza masa ta'ki! dashi d'in manemin matane to babu shakka a ranar sai yaje ya biyawa kansa bukata amma haka ya hakura ya cireta daga cikin ranshi duk dan ya nuna mata kuskuranta
A nutse ya jiyo da ita suna fuskantar
junansu, kasa hada ido tayi dashi ta sunkuyar da kanta 'kasa tana goge fuskarta, a hankali ya sanya hannunshi ya goge mata hawayen fuskarta ya tallafo fuskarta sosai cikin tafin hannuwansa ya kallonta.
Takasa d'aga kanta ta kalleshi saboda kunya da kuma t
sabar kwarjin da Allah yayi masa.
Murya a kasa kasa yace."Me kikayi min kike bani hakuri."? Sai ta dago fuskarta tana kallonsa.
Ya sanya d'an yatsansa saman le'banta na 'kasa yana shafawa a hankali a hankali shi dai yana masifar son le'bunanta.
Kasa
cewa tayi komai ta maida kanta 'kasa tasan yana sane yake tambayar ta yafi kowa sanin kan abinda yasa take bashi hakuri.
Murmushi yayi a hankali ya cika fuskarta ya juya ya dauko jallabiya cikin wardrobe yana fad'in "Ina momyna ko tayi bacci."? A hankali
ta d'aga kanta tace" Yanzu nan na lalla'bata ta kwanta.....Hannunta ya ri'ke yace."Muje parlo yau ke zaki bani abinci a gajiye nake."
Taji dad'in yanda ya saki jikinsa sosai wannan ya sake tabbatar mata da cewar ya hakura da fushi da ita kuma ta lura
dama kamar daurewa kawai yakeyi yana hakuri.
Ya zauna kan kujera yana dan dubawa babbar wayarshi yace."Ki had'o abincin ki kawo min nan zanci." Da sauri ta nufi daining din ta had'a mishi abincin komai da komai ta kawo gabanshi ta ajiye......'Kasa ya s
auko hankalinsa na kan wayarshi yana dan juya abincin da cokali, sai ta kar'bi cokalin ta fara d'ebo abincin tana sa masa a bakinsa.......Kar'ba ya din gayi ba tare da ya kalleta ba hankalinsa gabakidaya yana kan wani text da Zeey tayi mishi.
Kafin ma ya
gama karanta text din kiran wayarta ya shigo wayar tashi.
Dama tuntuni ya goge number ta cikin test dinta ma dan tasa sunanta ne ya ganeta.
Ganin numbarta tace ya sanya shi daga wayar a nutse yay sallama dake hands free ya bud'e Wasila najin muryar Zeey
tana fada'in "Ranka ya dad'e barka da dare yau dai naci sa'a an d'auki wayata."
Gabanta ne ya shiga fad'uwa sai hannnta ya soma rawa tana kokarin sanya masa a bacin a baki cokalin ya su'buce daga hannunta abincin ya zube a jikinsa sa kasan gurin.
Dan dub
anta yay yana dan gyarawa hankalinsa nakan maganar da zeey ke masa yace."Zainab ya kike ya gida ya kwana biyu."
Zeey tace"Alhamdullhi yallabai Wallahi kwanaki nayi ta kiran wayarka domin nayi maka Allah ya raya baka dauka ba nace to ko wani laifin nayi.'"
?
Murmushi yay a hankali ya dan koma saman kujera yace." Ai ke bakya laifi Zainab mybe lokotan da kike kiran wayar ina da uziri ne shiyasa amma nagode kwarai kuma naji dadi da kulawarki."
Zeey tace"Ai har taron suna nazo sai dai ban dad'e ba na tafi domi
n a ranar ana bikin wata friend dina ne." Yace."Masha Allah kema ai yana da kyau ki futar da miji kiyi aure Zeey kin kwana biyu fa."
Zeey tayi dariya me shashshe'ka tace"Yalla'bai kenan aini da aure sai dai inga anayi namiji daya nake so a duniya amma ya'
ki aurana."
Yasan inda maganarta ta dosa sai ya nuna bai gane komai ba, Yace."Zeey meye abunki? kina da ilimi sosai kana kina da kyau dai-dai gwargwado me kuma ake nema."?
Murmushin takaici Zeey tayi tace"Duk da ina da abubuwan da ka
fad'a yanzu to s
hi banyi masa ba."
Dariya yasa yana d'an sosa gemunsa yace."Haba dai sai kace makaho ni da ba dan nayi aure ba da kawai na shigo anyi dani." Zeey tayi wata dariya me shashsheka tana sake ma'kale murya tace"Ashe kasan inda maganata ta dosa tunda naga ka d'
auko hanya, Yallabai ko yau kazo ni a shirye nake dama ai Ubangiji cewa yay kuyi Hud'u mutukar zakuyi adalci." Ya bud'e bakinsa zaiyi magana yaga ta jefar da cokalin hannunta ta mi'ke rai a 'bace ta bar gurun......Ya bita da kallo har ta bude daki ta shiga
ta bugo kofar da karfin gaske.....sai kawai ya girgiza kansa ya cigaba da hira da Zeey inda take ta tsara masa kalamai ita dole sai ta samu shiga a gurinsa........Yace."Ki bari zan duba maganarki a tsanake zan kira ki a waya." Cike da farin ciki da jin da
di Zeey tace"Shikkenan Yallabai ina sauraranka." Kashe wayar yay ya ajiye ta kusa dashi ya gyara zamansa sosai ya cigaba da cin abincinsa.
Koda ta shiga dakin kwanciya tayi kan bed taci kukanta ta koshi ta kuma dauki al'kawarin yi masa rashin mutunci
tunda dai shi bai san hakkin d'an adam ba in bansa wulakanci da rashin mutunci ya rasa ma a inda zaiyi hira da budurwarsa sai gidanshi kuma a gabanta lallai zata nuna masa cewar ta san abinda takeyi duk da take jahila to tasan ciwon kanta.
Sai da ya k
ammala cin abincinsa a tsanake tukkuna ya bita dakin, lokaci har tayi wanka ta kwanta tana bawa baby zahra nono ta tashi daga bacci, yazo ya tsaya kansu yana kallonsu, ganin yanda tayi bala'in shan kunu ne ya sanya ya kasa cewa da ita komai sai kawai ya ts
uguna ya mannawa 'yarshi sumba a saman goshinta ya mi'ke ya fita daga d'akin.
Da 'kyar bacci ya dauketa saboda tsabar bakin ciki da takaici, ta tashi da safe cikin rashin walwala har Hajja ta shigo dakin suka gaisa ta shirya zahra har taso ta fahimci
wani abu amma dai ba tace mata komai ba itama so take ta cika ar'bain ta tafi ai tayi abinda tayi, Hajja na fita da Zahra ita kuma ta shiga toilet domin yin nata wankan.
Kafin ta fara wankan sai da ta shiga cikin ruwan d'umi tayi minti goma sha biyar san
nan ta fito tayi wankanta da sabulai masu kyau da kamshi ta fito daure da karamin towel iya cinyarta.........Ashe yana zaune a dakin ya shigo tana toliet sai ya zauna zaman jiran fitowarta.......Ganin ta a haka fatar jikinta na wani irin she'ki da sul'bi g
a santala santalan cinyoyinta a waje dik sai ya rasa nutsuwarsa ya dinga binta da wani mayen kallo har ta wuceshi ta nufi mirror tana zum'buro bakinta tare da sauya salon tafiyarta.
Kasa daurewa yay ya mi'ke ya nufi inda take......Tana sane ta bude towel
din wai zata sake d'aurawa aikuwa ya hangota ta madubi hankali a tashe yaje ya ri'ke towel din yana kokarin fuzgewa daga hannunta.
Ta dan tureshi kadan ta bar masa gurin......Matseta yay jikin wardorbe yana rarraba idanunsa a jikinta..........Ta dinga tu
re kirjinsa tana son yin kuka amma dai ta daure saboda bata so ya dinga raina mata hankali....."Wai dan Allah meye haka bafa girmanka bane hakan da kakeyi ka kyaleni ni nasa kayana, kuma gidan nan dole ne ma na barshi dan ba zan zauna a inda ba'a bukatar d
angina ba.'' A kausashe take maganar tana tuttureshi daga jikinta
Muryarshi ba sosai take fita ba yace."Wace irin magana kikeyi ne waye baya kaunar dangin ki da har kike ikirarin barin gidan auranki."
Sai ta fashe da kuka tana wani irin bubbuga 'kafafunt
a ta tureshi da 'karfi tana haki ta matsa gefe tana kallonshi tace"Eh dama zaka fad'i haka mana yau kwanan Inna Hajara nawa da tafiya ka ta'ba tambayata dalilin tafiyar ta!? Sannan yau kwanana nawa da haihuwa me yasa baka ta'ba tunani koda sau d'aya ne kac
e bari ka tura d'aya daga cikin yaranka domin yaje ya dauko mahaifiyata kan tazo taga abinda na haifa, na sani dama tuntuni na san da cewar baka dauki Uwata a matsayin komai ba dan da ka dauketa da daraja to da duk inda take kaje ka gaisheta da kanka kuma
ka shaida mata na haihu da abinda na haifa.....To nagaji ni ba shashasha bace nasan kuma inda ke min ciwo zanyi tafiyata in yaso sai ka auro wacce kake ganin Iyayenta sune dai-dai da kai da kimarka."
Tana gama maganarta ta bude wardorbe ta duba kayanta t
a dauki riga da sket na wani had'addan swiss less ta shirya jikinta duk yana tsaye kamar gunki yana kallonta da mamakin kalamanta, bude kofar dakin ce ta sanya shi dawowa hayyacinsa, yay gaggawar kallon bakin kofar sai ya hango ficewarta daga dakin tare
da jan kofar da karfin gaske.
Littafin na kudi ne!
Idan kika futar min da book keda Allah! Idan kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*77*
Ya jima a tsaye a tsaki
yar d'akin yana mamakin irin maganganun da yarinyar ta watsa masa, ransa yayi masifar 'baci sosai ashe raini har ya soma shiga tsakaninsu tunda har zata iya d'aga masa murya! gurin magana tana fad'a masa duk maganar da tazo bakinta tana d'aga masa harshe
kamar zata zageshi Idan tana so ta nusar dashi abinda ke zuciyarta ai sai tayi masa bayani cikin fahimta ba da irin wannan sigar ba, dole ne ma ya dauki tsatstsauran mataki a kanta, idan dan wannan abun na jikinta take kokarin zaginsa to taje ta ri'ke kay
anta zai nuna mata shi d'an halak ne.
Koda ya fito daga 'dakin bai kalli inda suke zaune ba ya wuce bedroom dinsa ransa duk a jagule.
Wasila kuwa jin zuciyarta take wasai tunda ta samu ta fad'i abinda ke cikin ranta shikkenan itama ta dauki al'kwarin
akan ba zata sake zama ya dinga raina ta ba ballanta har ya dinga d'aga wayar 'yan matansa a gabanta sai ta nuna masa itama macace wacce tasan abinda takeyi.
A shirye ya fito da shirin fita, ya tsaya suna magana da Hajja, Hajja tace"Nima fa na kusa t
afiya tunda dai Allah yasa ta haihu lafiya shikkenan zan koma gida." Yace."Kiyi hakuri kiyi zamanki tare damu." Tace"A'a dai gwara na kuma gidana bana dinga zama cikin yara ba." Yace."Hajja ai zaman naki cikin Yara gyara kike ba 'barna ba." Wasila da kanta
yake sunkuye tayi saurin dago kanta tana kallonsa, sai taga kamar magana yake fad'a mata kan Inna Hajara oh! wannan mutum baya barin takwana! wato Yana nufin Inna Hajara itake aikata 'barna kenan......Mi'kewa tayi ta bar musu gurin ba tare da tayi kuskura
n kallonshi ba, Hajja ce ta bita da kallo sosai ta fuskanci akwai matsala a tsakaninsu amma kuma ba za tayi masu magana ba sai ranar da zata tafi tukkuna idan kuma sun dai-daita kansu shikkenan.
Yana fita Garba ya daukeshi a mota kafin ya ajeshi cikin m
a'aikatarshi yake Umartarshi da cewar idan ya saukeshi ya nufi can garin su Uwani Patskum yaje ya sanar musu da cewar Wasilan ta haihu idan da me ra'ayi zuwa yaga abinda ta haifa sai ya dauko shi yazo dashi.....Hakan ce ta kasance Garba na saukeshi sai ya
dauki hanya kamar yanda ya umarceshi.
Suna zaune a palo bayan azahar dan uku ma ta kusa Rashida ma ta dawo daga makaranta, kawai sai sukaji sallamarsu su Uwani da Kuluwa dasu Inna Tabawa........Rashida ta mi'ke a guje taje ta bude musu kofar falon suk