Showing 30001 words to 33000 words out of 176422 words
motar....Ta sanya hannunta ta kare fuskarta t
ana jan tsaki!!!
Ahamdu dake gaban motar gabanshi ya fad'i Allah yasa dai idonshi ba gizo yake masa ba, sai da suka zo daf da ita ya tabbatar da zarginsa Itace! ma'kale a jikin bango tana jira su wuce! sai ya shiga tambayar kansa, Yarinyar nan daga ina
take a cikin wannan daran? shin ita da waye? kuma meye ya fito da ita daga gida. Bashi da me bashi amsa dole sai ita, da sauri ya sanya Garba ya tsayar da motar ya bude motar da zama ya fito ya iske inda take ma'kure!
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺
roma
ntic love story
🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE
🍒
*
*
🌍
Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.05423821
24.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars......
.90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*Free Pege19*
Saboda yanayin hasken gurun ya sanya tun kafin ya karaso kusa da ita ta ganeshi gabanta ne yayi wata mummanar faduwa da azama! tayi kokarin barin gurin.....Taku biyu yayi ya cafki hannunta guda
.....Cak! taja ta tsaya tana mai da nuffashi domin ganinsa ya sanya jikinta kyarma wanda shi kanshi sai da yaji a jikinsa sakamakon rike hannunta da yayi, Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta juyo fuska a had'e! Suka hada ido dashi yana tsaye shima tashi
fuskar babu alamun wasa....Kafin tace"Komai ya mangantu.....'Karfe goma sha biyu na dare kina waje a matsayinki na 'ya mace mai daraja kin watsar da wannan 'kimar da Allah ya baki kin mai da kanki tamkar tunkiya kiyi nan kiyi can cikin dare saboda rashin s
annin ciwon kai kin mai da kanki tamkar namiji namijin ma irin wanda bai san darajar kanshi ba."
murmushi tayi mai ciwo tace."
Idan hakane kai ma
Ashe kana d'aya daga cikin jinsin irin mazan da ka fad'a yanzu, Kai ma me ya fito da kai da daddare idan k
a yarda da kanka? kana kirana tinkiya kai kuma sai ka kira kanka da bunsur......! kamar ya sanan sunan da zata kirashi dashi yayi saurin kife ta da mari! jikinsa na kyarma! yace."Ahir!! d'inki ki kirani da wannan suna! na kira da tinkiya din domin sunan
da ya dace a kira ki dashi kenan, dube ki don Allah wai ke kinyi kwalliya kina yawo sa'ko da loko kina rabawa jama'a jikinki a banza job wane wawa ya jaki ya jaki ki bishi saboda rashin martaba kai ya jama'a ba zasu kira ki da sunanan tinkinya ba."!?
Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata a kumatu idan ta fahimci maganarsa anan shima yanayi mata kallon karuwa kenan? wai shin mai yasa mutane basa yi mata adalci ne a duniya ta tsani a kira ta da wannan suna, sunan tinkiya na nufin mace mara hankali
mara ilimi mara nutsuwa da kamun kai....Tunda suke karawa da guy din bai ta'ba 'kona mata rai irin yau! ba su kansu hawayen dake zuba a fuskarta ta bata san sanda suka zuba ba, da budurcinta da komai yake kiranta da tunkiya.....Hannunta da cikin nasa ta f
uxge! ta bar gurin a gaggauce!!! bayanta yabi ya sake ruke hannunta ta sanya karfi ta tureshi kuka take hai'kan! tsabar kalmar daya kira ta da ita tayi mata ciwo tana ji ma tamkar ta hadiyi zuciya ta mutu.......Yayi saurin tatar gabanta rai a bace yace."Id
an baki tsaya ba wallahi yanzu a gurin nan zan tu'be ki na kwashi rabona duk da hakan ba halayyata bace zanyi miki hakane dan in nunawa duniya halinki....Gwara kawai ki tsaya ki daina sauri."
Hawayen fuskarta ta goge tace"Kai baka isa ka tu'be ni ba w
allahi sai dai na tu'beka! kuma sai nayi maka sintir! zaka san wanda ka mara." murmushi ya saki hakika dauriya da jarumatar yarinyar na burgeshi, yace."Idan kin isa ke mara kunya ce ki 'kara taku d'aya anan gurin wallahi sai na baki mamaki! sai na tu'beki
! kuma na gudu da kayanki ki 'kara taku daya ki gani."
Wasila ta kalli fuskarsa taga babu alamun wasa a ciki sai gabanta ya fadi tabbas zai aikata abunda ya fada bari kawai ta lallabashi su rabu lafiya amma sai ra rama abunda yayi mata.
Tsayuwa ta gy
ara tace"Wai shin yanzu da ka tare min hanya me kake nufi dani.'" Yace."Abubuwan da nake nufi dake suna daya wa saboda haka shige muje ki shiga mota muje."
Ta kalleshi she'keke! tana gyada kai! "Ko da kudi ba zan shiga motarka ba nasan idan na futa bab
ban titi ba zan rasa abun hawa ba kawai ka fada mun dalilin da ya sanya ka tsare min hanya."
"Kin san ke mai laifi ce a gurina ko? so bana son jayayya kiyi abunda nace dake idan ba hakaba zan kira Yarana a waya so zu su baki mamaki! duk yawansu sai sun
kwanta dake sunyi miki fata fata!!!!!! Tsorata tayi dajin maganarsa mussaman da taga yayi kici kici da fuska yana kokarin dauko wayarsa,, sai ta sassauta murya a hankali tace" Dan Allah kar ka kira su muje motar nayi alkawarin kome kake so zanyi maka amm
a kar ka kira yaranka su wulakanta ni."
Yace."Wuce muje." Gaba tayi da cokalalen takalminta har tana gord'ewa sai waiwaye take ko zata samu mafakar da zata arce babu gida gaba babu gida a baya.....Da kanshi ya bude mata mota ta shiga ya zauna kusa da i
ta fukarsa babu wasa, gabanta sai masifar faduwa yake shikkenan yau ta fada komar Ahamdu sai Allah kuma tsinewa babu irin wacce ba tayi wa As ba shine silar fitowarta da wannan daran da bai fito ba da tuni ta gida tare da mahaifiyarta da 'yar uwarta.
'K
asa tayi da kanta hawaye na d'iga ta dinga sanya gefan lifayar tana gogewa sam! ba taso ya ga gazawarta a kansa amma inaa ta kasa tsayar da hawayen dake zubar mata mutukar ta tuna kalmar da ya kira ta da ita sai taji zuciyarta ta karye *Tinkiya* wannan kal
ma tayi masifar ragargaxa mata jikinta da duk wani kuzarinta da kwanjinta a kanshi....... Gani tayi mai gadi na bude tangameman gate din gidanshi, tayi saurin dagowa tana kallonshi taga yayi masifar 'bata fuska, yana magana da securities din dake bakin ga
te din....Tsumu! tayi hankalinta a tashe kar dai guy nan ya kawo ta gidanshi ne domin ya keta mata haddi innalilihi wa ina ilahi raji'un! yanzu meye mafita....
Taga ya bude mota ya fita sai tayi yunkurin fitowa itama, da sauri ya mayar da murfin motar ya
rufe da karfi dan har yana had'awa da hannunta, cije baki tayi tana duba ya tsanta, tunaninta kaf yanzu ya ta'alla'ka ne akan yanda za'ayi ta ku'butar da kanta daga hannunsa.
Can ta hango sun nufi bakin gate tayi saurin mikewa kan site tana le'kansa t
aga yana magana da securities akwai ta zata sosai parking spece da kuma bakin gate din ba tajin abunda yake cewa amma yanda ta lura da fuskarsa babu wasa yana musu magana mai muhimanci.....Juyowa tayi ta fara kokarin bude motar gam! take da mukulli ko wane
murfi a rufe.....Hawaye ya tsinke mata, Innalillhi wa'ina ilaihi raji'un! Sake mikewa tayi tana le'kensa, Can ta hangoshi ya durfafo inda take tayi saurin zaunawa! jikinta na kyarma, yana bud'e motar hankalinta a kai tayi wuf!! ta fito fit! har sai da t
a tureshi yayi saurin tsayuwa cikin zafin nama ya cafki 'kugunta ya rike tam! ya had'e bayanta da 'kirjinsa! Jini hannunsa kan
kirjinta ya sanya tayi masa wata wawar bangaza ta sanya tsinin takalminta ta daki gwiwarsa guda! yayi gaggawar juyo da ita mari y
a kifa mata!!!!! ya rike fuskarta da hannuwansa suka tsirawa juna ido.....Numfashi take saukewa mai zafi !! tana hura hanci! ga idanunta yayi jawur! Tsananin tashin hankali da fargaba ya gani cikin 'kwayar idonta, Ya gyada kanshi cikin jajurcewa yace."Ki s
higa taitayinki ki kuma nutsu wannan haukan da kikeyi babu inda zai kai ki a gurina muje ciki in fad'a miki wani abun al'ajabi."!!
"Ba zan shiga gidanka saboda ni ba 'yar iska bace ka daukoni ne dan ka biya bukatarka ni nafi karfin ka idan kuma ka tsa
nanta to za'ayi mutuwar kasko dani da kai a gidanan, dan nayi rantsuwa da Allah babu wani d'an iska da ya isa ya rabani da budurcina akan hakan zan iya aikata komai."
Ya jima yana kallonta kafin yace."Ke! kina nufin kina sa budurci a yanzu, da har kike
wani tada jijiyar wuya! okey to kar ki damu ba wannan bane manufata a kanki kawai dai yanzu na baki umarni kan ki nutsu kana kuma muje ciki na sanar miki da abun al'ajabin da ya faru dake."
Taji wani irin shocking ya kama jikinta shin wai wannan wane
irin abun al'ajabi yake so ya fad'a mata ne? Ji tayi wata jarumta tazo mata a take tace"Muje amma akwai sharad'i idan ka kusance ni sai nayi maka illah." Yace."Na yarda." Gaba tayi tana gurd'ewa ga lifayar tsabar wahala duk ta warware sai silmiyowa takeyi
tana gyarawa gashin kanta duk ya baje a kafadarta ribbon din ya fad'i a bakin mota......Bayanta yake bi cikin nutsuwa yake 'kare mata kallo warwarewar lifayar ya sanya ya fahimci kayan dake jikinta t_shart ce mai karami hannu sai dogon wando na jins amma y
a da'me ta d'am-d'am! ya fito mata da mazaunai tamkar suyi magana....Dauke kanshi kawai tayi yai saurin wuce ta yaje ya bud'e kofar palon....Yana tsaye ta 'karaso da hannu yayi mata alama ta shiga ta tsuguna tana kwance takalminta dake mai igiya ne... Nan
ma kasa tsayuwa yayi saboda yanda ya hango brest dinta sun bullotso ta saman d'amammiyar rigar dake jikinta sai ya shige palon ya tsaya...Ta shiga ya mai da kofa ya rufe da key.
Had'uwar palon da 'kayatuwarsa sam! bashi ne a gabanta ba burinta kawai ya
fad'a mata abun al'ajabin ko ya nuna mata ta zuba masa furgitattun idanunta
Cikin wani irin taku iske inda take tsaye ya zura hannunsa cikin aljihu dubu biyar d'in sadakinta ya zaro ya kama hannunta ya sanya mata kana ya kalleta ido da ido yace."Ri'ke s
adakin auranki da kyau!! Yau! ni *Ahamdu Musa* na cika d'an halak na tashi daga sunan gwauro na 'yantu na cika cikakken namiji inda nayi tattaki 'kafa da 'kafa na iske har Garkin Gargo na d'aura aure da Wasilatu 'Yar gaske Kawunki Malam mai allo yace na b
aki sadakin ki a hannunki ki lissafa su dubu biyar ne."!
Yana gama maganarshi ya sakar mata hannunta kud'in suka watse a kasan palon.....Bai damu ba ya nufi bedroom dinshi hankalinsa kwance.......Da wani irin mamaki take kallonsa har ya bude dakinsa ya
shiga tana kallonsa tana jinn sautin miryarsa na amsa kuwwa a kunnanta *"Wannan shine sadakin auraki Ni Ahamdu Musa nayi tattaki kafa da kafa na iske garin Garko na daura aure da Wasilatu 'yar gaske na tashi daga sunan gwauro na 'yantu Kawun ki Malam mai
allo yace na baki sadakin ki da hannuna."* Wannan
maganganun kawai takeji a cikin kunnanta kamar yanzu yake fada mata idanunta tsaye a kofar dakinshi.......Kimanin minti goma tana tsaye a gurin tana jajanta maganar gani take ma kamar mafarki take sai da ta
kai idanunta kan kudin da suke watse kasan kafet, sannan gabanta ta sake faduwa ta tsuguna kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta dinga daukar kudin tana hadawa guri guda tsaf! ta lissafa su dubu biyar.......
*"Ni Wasilatu ni aka daurawa aure da sadaki du
bu biyar sai kace bazawara!! Bazawarar ma mara gata da galihu tir'kashi!!!! A fusace! ta mike! ''Karye ne wallahi! Ni Wasilatu nafi karfin ayi min wannan wulakancin Ni za'a daurawa aure ban sani ba Wallahi wannan auran dashi da babu duk d'aya a gurina."!!!
Sai ta nufi kofar dakin nasa gadan gadan!! hannunta rike da 'kudin sadakin auran na ta."*
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺
romantic love story
🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE
🍒
*
*
🌍
Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai
na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*NA SADAUKAR MUKU DA WANNAN PEGE 'DIN*
Rahima Aliyu
Hauwwa Saudia
H.Rabi 'ko
far bai
Fatima Yakubu
Nafisat Ahamad
Zahra Kaduna
Fatima Binta
Jamila Abubukar
Mum Basma
Maimuna bichi
Ummu Yusif
Atou Tabalak
Anty Zeey Kazaure
Zainan Khabir Ishak
Jamila Yusha'u
JiddatulKhairi
_*Kuna da yawa sosai masoya wanda baiji sunan
shi ba afuwa zamu hadu a gaba ina mutukar alfahari daku masoya Ubangiji Allah ya 'kara 'kauna ta gaskiya*_
~~~~~~~~~~~~~
*Free Pege20*
Lest Free Pege
A fusace! ta buga 'kofar d'akin ta shiga, yayi hanzarin juyowa jikinsa sanye da rigar wanka da alama
yayi shiri tsaf wanka zai shiga dan yana daf da bakin toilet din....Idanunta a rufe ta durfafo inda yake tsaye yana kallonta ga mamakin sa sai yaga ta d'aga hannunta dake ri'ke da kud'in zata watsa masa yayi hanzarin ri'ke hannun! suka tsaya suna kallon j
unansu.....Sai yanzu ta lura da irin kayan dake jikinsa, rigar wanka ce mai bud'ad'addan gaba kuma bai daure ba ya sake ta faffad'an kirjinsa mai cike da yalwar gashi yana a bayyane kuma karamin wando ne a jikinsa wanda da ya d'ameshi.
da sauri ta sunk
uyar da kanta 'kas! gabanta na masifar fad'uwa Ganin yanda wandon jikinsa ya masifar matse shi ba ta ta'ba ganin zahirin namiji ba sai yau! Har yanzu hannunsa na rike da nata wanda kudin ke ciki yana watsa mata wani irin kallo yace."Kar ki kuskura kiyi mi
n watsi da kudi a d'aki idan kikayi sai ranki ya 'baci! hakkin ki ne kije dasu duk wanda ki kaga damar bawa ki bashi wannan bai dami kowa ba." Hannunta ya saki ya kama hanya zai shiga toilet d'in! aikuwa ta watsar da kud'in kasan dakin tana fadin "Wallahi
wannnan auran dashi da babu duk daya suke a gurina ka kwashi kudin sadakin ka bana sonka bana ra'ayin auran mutum irinka da har zakaje har mahaifata kasa a dauro maka aure dani to yanzu ba gobe ba sai ka sake ni dan wannan budurcin nawa na mai rabo ne." D
a jarumta take maganarta kuma tsakaninta da Allah take....Ya juyo cikin wani irin yanayi yana bin kudin da ta watsar a 'kas! wato dai sai da ta watsar masa da kudi a d'aki saboda taurin kai!! Nufar ta yayi cikin tsanani na 'bacin rai!!
Sosai ta tsorata!
da ganin yanayinsa sai ta soma ja da baya yana sake tunkarar ta tana sake matsawa gabanta sai duka yake yana daka haka suka dinga yi har sai da suka dangane da jikin bango. (Garu) d'aga hannu yayi kamar zai mareta! sai tayi saurin kauda fuskarta ta sanya d
ukanin hannunwanta ta kare tana sakin 'karamin ihu!! Shiru taji ta bud'e idonta a hankali tana kallonshi ta kafar hannunta yana tsaye daf da ita ya dafa hannunsa guda a jikin bango ya tokare ta sannan faffadan kirjinsa dake bud'e yana gogar hannayenta, 'Da
s!d'as gabanta yake fad'uwa lokaci guda ta rasa miyau! a bakinta ya bushe kamas!!! Sai zare ido takeyi wani irin tsoronsa ne ya shige ta mussaman yanda taga zahirin hallitarshi sai ta ganta wata 'yar ficika a tsakaninsa ya za tayi idan wannan 'katon mutumi
n ya hau ta duka.
"Ashe rashin kunyarki ta banza ce! tunda har kika razana tin kafin nayi miki hukunci." Shiru ya dan yi yana kallonta yanda take kyarma! sai uban gumi take hadawa Murmushi ya saki mara sauti ya girgiza kansa kana yace." karki kuskura na
yi sabo da dukan ki ko marin ki zaki sha wahala, aure ni nayi ra'ayin na aureki saboda na karya al'kadarinki kin shiga gidan redio kin zageni kin aibatani kinyi min kazafin na zina kawai saboda ki bata min suna a idon mutune to bukatarku bata biya har yanz
u da mutuncina a idon mutane na aureki da mummunar niya ba zan munafurce ki ba amma kuma mutunci da 'kimar wannan dattijon ya sanya na janye kudirina a kanki! karyi tunanin ko zanyi wata mu'amular aure dake domin naji baki da wani zance da magana sai na bu
durci ki sani da budurcinki da babu duk daya suke a gurina domin bashi ne a gabana ba, zan killace a cikin gidana ne domin na taimake ki da wannan yawace yawacen da kikeyi kinga ke idan 'yar halak ce godiya ce zata biyo baya a tsakaninmu dalili kuwa na 'ya
n taki na aureki tare da killace ki guri guda, magana ta karshe da zanyi miki
itace maza ki kwashe kudinki da kika watsar min 'kasan d'aki! ruwanki ne kiyi amfani dashi da kanki ruwanki ne ki bayar sadaka bai dami Ahamdu ba."
Bakinta mutuwa yayi murus! sa
i dai Ubab hawayen dake ambaliya a fuskarta, tayi tayi ta d'ago fuskarta ta kasa saboda yanda taji duk wani alkadari nata ya karye amma Ahamdu yayi mata wulakancin da ba zata ta'ba mantawa dashi ba....Cikin tsawa yace."Kin kwashe kudin ko kuwa."! Hucin mag
anarshi ya daki fuskarta tunda har yanzu yana kusa da ita ta ina zata wuce ya babbake hanya.....Idonta ta zuba masa tana