Showing 111001 words to 114000 words out of 176422 words

Chapter 38 - YAR BANGAR SIYASA COMPLETE

rashida sai ta diriri ce ta hau ya'ke...."Am...dama ai nace bari na gyara

muku kayan naku in adana muku su guru guda." abinda tace kenan tana sosa kanta....Rashida bata ce komai ta dauki zannuwa uku na atamfa ta fito daga dakin....Ita kuluwa tana

ganin rashida ta fita daga dakin sai ta cigaba da bincika kayan ta dauko manya many

an shaddodin Wasila masu uban stone work ta d'aga 'kasan katifarta ta sanya ta mai da katifar......Da sauri ta gyara jakkunan kayan ta fito daga dakin tana zare ido.

Wasila kudindine jikinta tayi. ita kadai kwal a katon tsakar gidan ko tsoro bataji gari

yayi shiru sai kukan tsintsaye kawai ke tashi.......... Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauketa ta dalilin magungunan da takesha

Fitowar Kawu Madu daga dakinsa ne ya tayar da ita Sai taji ana kiran sallah da alama asuba tayi, Kawu Madu ya kalleta y

ana mamaki yace." Ke anan kika kwanta." Sunkuyar da kanta tayi kawai sai ya girgiza kanshi ya nufi bandaki da buta a hannunsa........Yana fitowa ya daura alwala ya nufi masalaci,

Kasa shiga bandakin tayi sai kawai tayi gaggwar tsugunawa a bakin rariyar t

ayi fitsarinta ta kwara ruwa, kana ta matsa gefe guda ta daura alwala ta bar gurin.

Shimfidar data kwanta ta dauke ta cire dankwalin kanta ta gyara hijab dinta ta tada sallah......Uwani da rashida suka fito a tare suma alwalar suka daura nan tsakar gida

n sukayi sallah domin dai cikin rumfar babu guri bayan haka kuma ko ina kasa 'kafarka fitsari ne.

Suna zaune a tsakar gidan gari yayi haske Kuluwa ta fito tayi alwala ta goge bakinta da gawayi kana ta shiga kichin ta kunna wuta ta dora ruwan kunu s

annan ta nufi daki domin yin sallah.



Yaran dake dakin suka soma fitowa su kusan bakwai wasu jikinsu da fitsari wasu babu ba tare da sunyi alwala ba suka soma wasa a tsakar gidan wasu kuma tuni sun fice waje da abubuwan wasan su......Su Wasila suka ding

a mamakin wannan rayuwa....Nan rashida take shaida musu abinda taga kuluwa nayi musu da kayansu....Fitowarta yasa tayi saurin yin shiru to itama Kuluwar a kunyance take dan haka sai tayi saurin fadawa kichin tana sosa kai! Wasila abin dariya ya bata sai ta

shiga girgiza kai tana fad'in ''Ni dariya ma take bani wallahi." Rashida tayi dariya kasa kasa tana kallon kicin din.

Wani tsalan kunu ta kawo musu cikin kwanon sha da kufuna guda uku sai 'kullin sikari akai....Uwani ta gaisheta tanayi mata sannu suma

suka gaisheta Ita kuwa ta kasa tsayawa a gurin kunyar hada ido da rashida take......Tana shiga kicin Wasila ta saka fuskarta cikin hijab taci dariyarta ta koshi, kai mara gaskiya dai ko a ruwa gumi yake.

Fitowa tayi daga kicin din da katon farantin silb

a da narkeken d'umamen towo an yanyanka shi sai miya tsululu towon sai iyo yake cikin miyar....Ta kalli rashida tana fad'in 'kawata ga d'umame nan idan kunsha kunun sai kuci kwaji dad'in tafiya da karfinku." Rashida tace"Mungode Kuluwa." Da sauri ta bar gu

rin tana kwalawa yaranta kira wai suzo su dauki kununsu da duk ta zuba musu a kufuna 'kudaje sai bin bakin kufunan

sukeyi.....aikuwa da d'ai- da d'ai yaran suka dinga shigowa suna daukar kufonan kunun suna sha ba tare da sun wanke bakinsu ba.

Kawu Madu

ne ya shigo da sauri yana fad'in "Ina Wasila da Rashida." Sukace gamu Kawu Yace." To maza ku fito ga motar abokina ya kawo ice yanzu zai fita cikin gari sai yaje ku a tasha ku shiga mota." Suka mike da sauri Rashida ta shiga dakin domin dauko musu jakar ka

yansu, dama tasu daya ce ta uwani daya.

Uwani ta mike tana yakar zuciyarta hawaye ne yake so ya 'balle mata tana mayar dashi, suka je bakin kichin din da Kuluwa ke ciki tana zaune dirshan gabanta da karon bokintin da ta dama kunu tana katsewa gefanta ku

ma tukunyar miya ca bude ga ludayi a kasa....Uwani tace"Zasu tafi." Sai ta hau washe baki tana fadin"Bari na taso inyi rakiya ni kuwa me zan baku. 'Yayan nan."? Fitowa tay ta shiga dakinta da sauri ta dauko wata yar takarda fara ta mikawa rashida tana fad'

in 'Kawata ga yariruka kwa sanya ku gaishe da kawunan naku." Rashida ta karba tana godiya tabi bayan Wasila da Uwani da suka riga sukayi gaba.

Littafin na kudi ne.....!

Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah

Whasap numbar

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*BINTA UMAR ABBALE*alliya:

'Yr Bngr Sys

*59*

Tun a mota yake jin alamun zazzabi zazzabi a jikinsa yasan kuma ba komai ne ya jawo mishi faruwar hakan ba sai alhini da damuwar da yake ciki idanunsa sun k

ad'a sunyi jawur! jijiyar kanshi ma ta tashi, yanda le'bunanshi suke a bushe haka ma'kogwaron shi yake dan rabonshi da ruwa ko abinci tun jiya da daddare da yasha coffee kafin ya kwanta, sam ya ma manta da wani abinci saboda tsananin damuwar da yake ciki..

..Yana kallon khalifa na tu'ki yana kur'bar lemo amma shi sha'awa ma baya bashi bakinsa duk ya bushe yana jin wani irin abu ya tokare masa a ma'kogwaronsa.

Ganin tashin hankali murarar a tartare da abokin nasa yasa ya d'an kalleshi bayan yayi parking din

motar cikin gidanshi, Yace."Kayi hakuri abinda zan iya cewa da kai kenan! ka cigaba da addua kawai kan Allah ya tsare maka cikinka da ita kanta yarinyar wannan damuwar duk ba ita mafita ba, tunda dai Allah ya raba ganawa sai ka bar mishi ikonshi, ni munyi

magana da ita a jiya ta kuma shaida min cewar mutukar ta haihu to zata kawo ma'ka d'anka har inda kake." Saurin kallonsa yayi yace."Okey ashe da sa hannunka ta gudu kenan." ? Khalifa yay saurin girgiza kanshi yana fad'in" No ka fahimce ni mana! Jiya nake

fad'a mata cewa dole sai na sanar maka da maganar cikin ta nuna bata so nace mata ai tilas ka sai ka sani shine tace ko anfad'a maka ko ba a fad'a maka ba in ta haihu zata kawo maka d'anka kaji dalilin da ya sanya nayi maka wannan maganar amma wai maganar

da sanya hannuna a cikin guduwarsu bata taso ba."

Girgixa kanshi ya shiga yi yace."Ban san a ina zanga 'kawarta ba mybe a samu wani labari a gurinta." Khalifa yace."Eh to ai kuma inda za'a sameta ne aiki." Yace."Zan duba wayarta baza'a rasa numbar ta

ba." Khalifa yace."Yawwa hakan yayi kyau Allah yasa a dace yanzu dai ka kwantar da hankalinka mu shiga ciki kaci abinci ka huta tukkuna insha Allahu komai zaizo da sauki."

Girgiza kai kawai yay yace."Khalifa hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba sai naga

yarinyar nan, na 'kwallafa raina kan cikin jikinta burina kawai in ganta kuma in tabbatar lafiyar abinda ke cikinta." Khalifa yace." Shine ai nace damuwa da tashin hankali bashi ne mafita ba addua itace mafita kawai ka kwntar da hankalinka ka cigaba da add

ua.''

Murmushi mai ciwo yay khalifa bai san yanda yake ji a zuciyarsa ba shiyasa yake cewa ya kwantar da hankalinsa a maganar kwanciyar hankali ta 'kare a gurinsa yanzu mutukar ba ganin yarinyar nan yayi ba. A

Tare suka fito daga motar tamkar wanda 'kw

ai ya fashe musu a ciki suka nufi cikin gidan. ga gajiya ga rashin samun nasara.

****

Dake akwai tafiyar 'kafa tsakanin bakin titi da cikin 'kauye yasa suka samu babur irin na (kafu-kafu) ya shiga dasu ciki har 'kofar gidan Mai allo aka ajesu, kana

suka biyasu hakkinsu.....Suna kokarin shiga gidan ya fito da cazbaha a hannunshi, kawai sai yay tozali dasu. Ya bude baki yana kallonsu cike da mamaki.

Idanun Wasila ya kawo ruwa rau-rau! ranar naka sai naka! Wai itace tazo garin Garko da 'kafafunta! Hawa

ye suka zubo mata a kumatu, kai a 'kasa suka isa inda yake suka zube gwiwa bibbiyu suna kuka! Tausayinsu ya kamashi da sauri yace."Ku tashi mu shiga ciki.'' Jikinsu a sanyaye suka mi'ke rashida taja akwatin kayan nasu suka bi bayansa.

Kamar dai koda yau

she Bitan na zaune a tsakar gida tsaf da ita jikinta sai kyallin mai yake da alama bata jima da yin wanka ba tana sanye da wani leshi ruwan ganye(kore) irin nada ta d'aure kanta tamau! da dankwalin leshin, cinyar ta farantin shinkafa ne tana tsincewa sai k

awai ta tsinkayi muryar mijin nata yayi sallama, Da sauri ta d'ago kanta tana kallon bakin 'kofa, Yanzu yanzu ya fita ko mantuwa yay abinda take ayyana cikin ranta, sai kuma taga su Wasila a bayanshi.

Tace"A'a malam su wa nake gani a bayanka yau.''? Yac

e."Gasunan nima fita ta na hango zuwan su Wasila ce da Rashida." Bitan! ta ri'ke ha'ba babu yabo babu fallasa a fuskarta tace"To masha Allah sannunku kuzo ku zauna ga gurin zama." Mai allo yace."Kuje ku zauna." Sukaje suka zauna kusa da ita sai sunkuyar da

kai suke mussaman Wasila dama itace akuyarta tayi kuka a garin.....Mirya na rawa tace"Kawu ina wu

ni mun sameku lafiya." ? Yana daga tsaye yake amsawa yana nazarinsu....Rashida ma ta gaishi ya amsa, kana suka shiga gaishe da bitan itama ta amsa cikin k

ulawa kafin ta mike a nutse ta nufi kicin....Mai allo ya dinga kallonsu zuciyarsa na karyewa 'yayan Yahuxa tamkar 'yayan cikinsa suke, duk yanayin da ya gansu na dad'i ko na rashin d'ad'i dole ya shiga damuwa, kallon farko da yay musu ya fahimci akwai dam

uwa da firgici a tartare dasu mussaman Wasilan da tayi firgai firgai da ita kamar ma mara 'koshin lafiya. Bitan ta fito daga kicin

hannunta rike da samira mai hannun roba, ta aje a gabansu ta koma kicin din da sauri ta fito hannunta rike da wani farin jug

ta bude randa ta debo musu ruwa ta aje a gabansu ta zauna tana fad'in" Kuci abinci kunji ko ku daina kuka da damuwa rayuwar nan kowa hakuri yake da ita."

Malam yay gyara murya yana kallon matar tashi yace."Zan fita kamar yanda na niyyata idan Allah ya

sa na dawo sai na zauna dasu, Insha Allah." Bitan tace"To malam ubangiji Allah ya tsare a dawo lafiya." ya amsa yana kokarin fita, Wasila da Rashida har rige rige suke gurin yi masa adduar dawowa lafiya ya amsa musu a lokacin da yake kokarin fita daga gida

n.

Bitan taga sun kasa cin abincin tace"Ku saki jikinku fa kuci abinci insha Allahu ba zaku samu wata matsala dani ba, ni dama tuntuni ina tausayawa rayuwarku mutukar kun gane gaskiya kuma kun gana mahimacin Kawunan ku a gurin ku , ai magana ta wuce s

uma kansu Kawunan naku hankalinsu a tashe yake, amma nasan yanzu hankalinsu zai kwanta tunda kun dawo garesu."

Sai suka sake jin kwarin gwiwa a tare dasu, Rashida ta bude samirar abincin dake gabansu, burabusko ne (biski) yayi shar shar dashi sai kamsh

in man'kuli zuryan yake, ga maggi star guda biyu a gefe da yaji....Wasila taji yawunta ya tsinke sosai taji sha'awar cin burabuskon ta mike a nutse ta wanko hannunta, ta dawo ta zauna Rashida ma mikewa tayi taje ta wanke hannunta sukayi bisimillah tare da

fara cin abincin.

Bitan ta mike a nutse ta shiga kicin ta kunna wuta, Girgi zata dora musu na mussaman, sabida yaran sun bata tausayi sosai da sosai sam basuyi sa'ar uwa ba duk wata wahala da suka shiga mahaifiyarsu itace sila shiyasa kwata kwata basa s

hiri da ita sabida munanan haleyenta gashi tayi ta zagin mijinta a gabanta, duk abinda za tayi wa yaran za tayi musu ne saboda Allah da kuma maraicinsu, ba dan halin Uwarsu ba..

Tas suka cinye burabuskon basu rage komai ba, Wasila tafi rashida ci dan dag

a karshe ma rashidan cire hannunta tayi ta bar mata ta 'karasa cinye tayi gatsa tana hamdala hankalinta ya kwanta sosai da tsabtar Bitan shiyasa kome ta girka ta bata zata iya ci......Bitan ta fito daga kicin hannunta rike da wani ma dai-dai cin kwando daf

affan 'kwai ne a ciki da yawa ta aje a gabansu tace ku 'kara da wannan yanzu zansa yara sunyi min cefene na sake dafa muku abinci. "Wasila tayi murmushi tana fad'in " Bitan mungode Allah ya saka miki da alkairi." Murmushi kawai tayi ta koma kicin tana cig

aba da aike aikenta.

Hajara ce tayi sallama ta shigo gidan tare da d'an autanta Lamir yana biye a bayanta.......Tsayawa tayi bakin kofa tana kallonsu, Sunkuyar da kai sukayi kamar munafukai. Bitan ta fito daga kicin taganta tsaye a bakin kofa tace"Ki sh

igo mana ai ba abin mamaki bane addua bata fad'uwa 'kasa banza." Hajara tace"Ai dole nayi mamaki Bitan! Yaushe suka zo kuma."? Bitan tace"Ke dai shigo ki zauna." Hajara ta karasa kan tabarmar ta samu guri ta zauna idanunta a kansu Wasila ta dinga tunano r

igimarsu da Hajaran tana shan duka a gurinta a duk lokacin da sukazo garin, dan kwata kwata basa shiri sunfi shiri da Rashida......Cikin jin nauyi suka gaisheta ta amsa tana fad'in "Kunga uwar bari kenan."!? Sukayi 'kus! kansu a 'kasa, Hajara zata fara sab

abi! Bitan ta dakatar da ita da fad'in " Haba Hajara wannan ba kana bane! Kullum fa addua kuke kan Allah ya karkato da hankalin yaran nan gareku Allah kuma ya amsa adduarku sannan

kice wani abu, don Allah kar ki fad'i wata mummunar magana kan yaran nan ki

kyalesu ma suji da abinda ya damesu.

Hajara ta fashe da kuka tana fad'in "Haba Bitan! al'amarin nan fa akwai dam

uwa da ba'cin rai wallahi yaran nan sun sanya mu a fargaba da tashin hankali mussaman waccan mai 'katon kan tana sunkuyar da kai munafuka

kawai Ai dama nace duk sanda kika kwaso kafafunki kika zo sai na ci miki mutunc.......Bitan tace" Ashe bakiji maganata ba kenan haba hajara."? Hajara ta kwance bakin zaninta ta goge hawayen fuskarta tana fad'in "Allah ya ji'kan ka Yahuza." Ai sai Wasila d

a Rashida suka sa kuka! Suna bata hakuri! Takaicin duniya ya ishi bitan Hajara tazo ta dagula al'amari ta tayarwa da yara hankali sai koke koke sukeyi......To itama hajaran da taga sun ki su daina kukan sai ta shiga rarrashinmu itama ba yin kanta bane tun

awa tayi da d'an uwanta....Rashida da Wasila suka dinga bata hakuri da fad'in "Insha Allahu baxa su sake guje musu ba tunda sun gane basu da kowa a duniya da wuce su......Hajara taji dad'in wannan magana tasu sai tace " Komai ya wuce insha Allahu.

Haj

ara bata koma gidanta ba har sai da malam mai allo ya dawo suka gana da juna sannan tayi musu sallama ta tafi gidanta da al'kwarin dawowa gobe idan Allah ya kaimu.

Bayan sallahr isha'i mai allo ya samu nutsuwa duk suna zaune a tsakar gida bayan sun gama

cin abinci, mai allo ya gyara zamanshi kan buzunsa yana kallonsu a nutse yace."Naji da dadi kuma nayi farin ciki da har kuka gane mahimancinmu a gurinku, yanzu kun gane cewar baku da wani gata a duniya da wuce Allah da ma'aiki da kuma ni da 'yan uwana, M

ahaifiyarku ta dauke ku ta kai ku can cikin danginta, sun nuna muku cewar su basu da ala'ka daku , kamar yanda kuka fad'a min cewar da kyar ma suka bari kukayi kwana a guda a gurinsu, ni a ganina ba suyi lefi ba kamar yanda kuke tunani sun nuna muku mahim

cin danginku ne, me yasa basu kori ita mahaifiyar taku ba? saboda sun san tasu ce kuma bata da wani guri da za taje idan ba gurinsu ba, naji dadi da faruwar hakan, na kuma tabbatar da cewar hakan zai sake sanyawa ku shiga cikin hankalinku ku gane meye ra

yuwa, alhamdullhi, Allah ne abin godiya a garun mu baki d'aya." Shuru yayi yana sauke numfashi kafin ya cigaba da magana yana me kallon inda Wasila take zaune, Yace."Jiya mijinki yazo garinan cikin tsananin rud'ani da tashin hankali yana shaida min cewar w

ai kina dauke da cikinsa a jikinki shin hakane ko ba haka bane? tunda dai ni kafin wannan zuwan nashi wattani uku da suka wuce yazo har nan ya shaida min cewar ya sake ki saki d'aya wanda a lokacin mukayi ta tsammanin zuwanki baki zo ba sai yanzu.

Tun

lokacin da mai allo ya firta maganar mijinta yazo taji duk wani kuzari nata ya dauke yawun bakinta ya tsinke gabanta ya shiga fad'uwa da 'karfi da 'karfi sai kawai ta soma fad'in kalmar innalilihi cikin zuciyarta, muryar mai allo ce ta dawo da ita hayyacin

ta yace."Ke nake sauraro Wasila." Ta d'ago kanta idanunta cike da 'kwalla tace"Eh Kawu in da ciki." Yayi jim! kafin yace."To masha Allahu, yanzu akwai aure a tsakaninku kenan? ko ku kuma bayan rabuwarku dashi cikin ya bayyana kanshi."? Ta goge hawayen dake

kuncinta tace"Bayan mun rabu cikin ya

fito.'' Shiru yayi yana girgiza kanshi kafin yace."Gaskiya mana, yazo nan hankali a tashe a jiyan ni har na soma tunanin ko da akwai aure a tsakaninku ashe shi saboda cikinsa ya biyo bayanki, to babu lefi ai idan All

ah yasa Habibu ya dawo daga tafiya, tunda shine yake da numbar wayarshi sai ya kirashi ya shaida masa abinda ke da akwai, amma maganar zai daukeki ya killace ki kiyi mishi rainon ciki duk bata taso ba, anan ma zaki raini ciki ki kuma haife lafiya ba tare

da wata matsala ba insha Allahu, wannan dai hakkinsa ne dole a fad'a mishi halin da kike ciki duk saboda jininsa da kike dauke dashi a jikinki." Kuka tasa tana fad'in "Dan Allah Kawu kar a fad'a masa bana so kawai a bari idan na haihu sai a bashi d'anshi N

i bana so yazo inda nake." malam ya shiga kallonta yana mamakin gursheken kukan da take.

Littafin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login