Showing 36001 words to 39000 words out of 108953 words

Chapter 13 - Samarin-Bana-Complete

08 Sep 2026

37



Ananan ananan wata rana yaje saudiya dan sauke farali

Anan ya ha'du da Khamsa'u balarabiyar qasar Harif

Kallo '

daya sukama juna sukasan sun kamu da qaunar juna

Dake wayayyune anan kowa yabaiyana kansa ga 'dan uwansa

Khamsa'u dai 'yar Sarkin garin harif ce

Ita ka'dai Allah ya bashi

Baqamin so mahaifinta yake mata ba

Saidai yanada burin samun 'da namiji



Mahaifiyarta mah 'yar sarauta CE kuma itama ita ka'dai agun iyayanta

Lokacin da tasamu Cikin Khamsa'u alokacin ne iyayanta suka mutu sakamakwan wata cuta da tashiga garin iyayan nata wanda takashe rayuka da dama

Hakan yasa dukkan wata dukiyar mahaif

anta tadawo hannunta

Ta haifi 'yarta Khamsa'u suka raini abinsu har girmanta Wanda ayanxu take shekara ishirin da uku

Sunxo sauke faraline saudiya shine Jabiru yaga Khamsa'u suka fa'da qaunar juna

Tun aranar iyayan Khamsa'u suka San da Jabiru

Da

sun qita dashi Amma ta bijiremusu Sam

Haka suka rabu da ita bayanda suka iya



Soyayya tayi qarfi tsakaninta da jabiru har magana tayi xafi iyaye suka shiga xancan

Dan koyaushe Jabiru yana hanyar garinsu Harif

Daqar magana tayi qarfi har All

ah yasa Khamsa'u taxama mata ga Jabiru

Iyayanta sukace baxai kawo musu 'ya Nigeria ba Saidai ya xauna da ita a qasar Saudi dan tafi kusa da qasarsu

Dake Jabiru ya mutu kan Santa haka ya yarda yasai gida aqasar saudiya suka tare da Amaryar tasa.

Tund

a Jibiril yaje yaga maxaunin qanin nasa Jabiru yaga sai hankalinsa ya tashi maqin cikinsa yaci karfinsa nan yafara tunanin Hanyar da xaiyi ya kashe Jabiru danya mallaki dukiyarsa

Lokacin ko idan Jabiru yaqara wayewa dan shiga qasashe da yakeyi shida ma

tarsa Khamsa'u

Nan yasa hannun jarinsa a qasar Kuwait yasaka a England yasaka a American

Wa'yannan qasashe uku dayasa hannun jarinsa sune silar qara ha66akar axxiqinsa

Mutum ne me San temako me ibada da San Allah da Manzansa

Hakance tasa yaware kas

u mafi tsoka daga dukiyarsa yaba yayun nasa

Naziru da Auwal ne kawai sukayi farin ciki da kyautar suka dinga murna dasama qanin nasu albarka

Jibiril najinsu yajah tsaki Yace wai murnar mesukeyi dan yabasu 'yan ku'din dabai taka kara ya karya bah

Duk

da kallan mamaki suka bishi dashi kana suka hango tarin baqin ciki da hassadace take damun yayan nasu

Wata rana iyayan Khamsa'u suka shirya kawo mata xiyara.

Sai dai basuxo gareta ba jinginsu yasami matsala sukayi mummunan hatsari Wanda duk nacikin

jirgin yarasa ransa dan babbakewa sukayi

Sanda Khamsa'u tayi shekara kafin mutuwar tasaketa

Alokacin ne kuma tasamu ciki.....

Wai xokuga murna gun Jabiru

Kowa ya tayashi murna da samun wannan cikin musamman da akayi scanning aka gano 'yan biyu k

uma Dukka maxa

Lokacin Naziru yana da 'yarsa Saudat

Auwal kuwa Saida cikin Khamsa'u yakai wata hu'du Matarsa tasamu ciki

Hmmmm

Jibiril yasamu qannansa Naziru da Auwal Yace yanaso subashi ha'din kai su kashe Jabiru da matarsa Khamsa'u dan Su m

allaki dukiyarsu

Idan suka mallaki dukiyarsu ya tabbatar wani ikwan Allah ne xaisa suyi talauci arayuwarsu

Sam Naziru da Auwal sukaqi yarda da hakan dan sunasan Jabiru abin duniyarsa bai rufe musu ido bah

Yace toh shikenan shi xai aikata kuma Wlh

i suka fidda wannan xance saiya hallakasu suma

Naziru Yace ai Yaya bame harnakawa sai Allah haka kuma baxai baka damar cin galaba akansu ba

Auwal Yace hakane kam

Murmushin mugunta Jibiril yayi Yace xaku gani

Da ido suka bishi Suna mai addu'ar Allah

yayaye mishi Baqin ciki

Ana saura wata 'daya Khamsa'u ta aihu tadanqama mijinta Jabiru dukiyarta me tarin yawa Tace yajuya mata

Wata qanwar babanta Amme Salima wacce take Aure anan qasar saudiya da Naziru da Auwal Yayun shi jabiru sune suke da shaida

akan mallaka mishi dukiyar tata da tayi

Nan yasa mata Su a hannun jari na qasashen da yake harda

Kuma duk dukiyar tashi da tata yasaka musu Suna 'daya dashi ne mutum yake da damar mallakar wannan dukiyoyin ko bayan ransu

Wato wannan sunan shine suna

nta Wato ( *Khamsa'u* )

Indai bada wannan sunan kayi amfani ba kaje kar6ar wani ku'di a American England Kuwait toko in aka kamaka 'daurin rai-rai ne dan ansan ba naka bane

Toh Jabiru ya ke6e da 'yan uwansa biyu wa'yanda ya da'de da sanin SOYAYYAR gas

kiya suke masa Wato Naziru da Auwal

Dan haka yagaya Komai akan dukiyarsa data matarsa

Sun jinjina masa kuma suntabbatar masa bamaijin wannan sirrin nasa

.

Ranar ta kasance Asabar mummunar ranah ga masoyan Khamsa'u da Jabiru

Dan Jibi

ril ya samu nasarar harbe Jabiru qiri qiri acikin gidansa lokacin Khamsa'u tafuta tirenin 'din masu cika nan kusa da gidanta

Aiko tana dawowa taga gawar mijinta alamar kasheshi akayi.

Nan tashin hankali ya sata na'kudar dole

'Yan aikin gidannane suka

kaita asibiti

Annan ta haifi RAMADAN da RAMADAN junior

Bayan aihuwarsu da tayi da minti biyu tace ga garinmu nan. Rai yayi halinsa

Kuka Sosai Naziru da Auwal sukayi ganin gawar 'dan uwan nasu da matarsa

Abin takaici Jibiril ya tabbatar musu da

cewa shiya kashe Jabiru

Basuyi mamaki ba dan sunsan dama tunda Yace saiya kasheshi ikwan Allah ne xai hanashi aikatawa

Amme Salima tanemi da Jibiril da Auwal Naziru subata 'yan biyun nan Amma sukaqi musamman Auwal dayace shixai 'dau 'daya shi kuma Na

ziru ya 'dau 'daya

Haka tanaji tana gani suka qi batasu Amma sun bata tabbacin xasu dinga kawo mata Su tana Ganinsu

Tayarda da hakan

Bayan sun rabu ne akan hakan Jibiril ya bu'de musu wutta akan Saidai subashi yaran

Sukuma suka mishi Jan wiya aka

n baxasu bashi suba ya kashesu

Daqar yasamu kansu suka bashi 'daya bayan yayi musu rantsuwa akan baixai cutar da yaran ba

Su temaka mishi xaisamu me shayarwa ta shayar dasu

Sam sukaqi

Daga baya dai suka bashi 'daya Wato junior RAMADAN qaramin ciki k

enan

Yaran sunci suna kamar haka

Muhammad da Sadeeq

Muhammad shine RAMADAN 'din SAILUBAH

Sadeeq kuma shine RAMADAN junior

Sai Naziru ya 'dauki RAMADAN nasa ya ha'da shi da 'yarsa Saudat

Daga baya yasamu khairat

Jibiril dama bashi

da niyar kuma kashe junior RAMADAN dan Hakka kawai Allah ya jarrabeshi dasan yaran

Abinda yakeso dai yasamu

Danya samu dukiyar Jabiru

Dangin Su gidajan da filiyan da yasiya a nan gida Nigeria sudai ya samu

Dan baisan da wancan hannun jarin da Jabi

ru yake dashi a American England Kuwait ba

Tafiya tai tafiya har ya cinye komai. To dama hakkin marayuu ina xai kaisa

Ganin haka yasa yayi wani rikakken 'dan fashi

Anan ya shige harkar

Aikowa yaxama wani Babba a harkar

Tunda ya kar6i junior

RAMADAN bai ta6a kawoshi kano ba

Haka 'yan uwansa Auwal da Naziru suke mishi nacin ya kawo musu shi Kullun saidai yadinga turo musu da hotansa

Wata ranah Amme Salima taje gidan Jabiru dan tunawa da 'Yar 'dan uwan nata

Tana binciken kayanta sai k

awai taga diarys biyu nan ta karanta na farko taga na Khamsa'u ne

Ta karanta nabiyu saitaga na Jabiru ne

Dan haka saita kaima Alhaji Jibiril har garin Abujah Tace ya ajiyema Su RAMADAN xai musu amfani wata ranah

Toh tunda ya kar6a ya bai ta6a tsaya

wa ya dubawa ya karanta bah

Saidai yana ankare dasu dan yalura junior RAMADAN 'din yanasan karantawa

Gashi kuma yanasan rigashi karantawa shiyasa Sam yake hanashi 'dauko idan yaxo 'dauka

Shima yana mamakin yanda akayi yakasa tsayawa ya karanta kuma

xuciyarshi tahanashi barin junior RAMADAN ya karanta

Alhaji Jibiril ya sakama junior RAMADAN sunan RAMADAN 'din SAILUBAH ne dan in rana ta6aci masa a Nigeria aka gano fashin 'dan nasa yabar garin Abujah Sannan ya rubuta leta mah jami'an tsoro ajan

suje garin kano wanda suke nema yanacan

Toh sai Allah ya 6abunta al'amarin

Yabama junior RAMADAN ilimi da kulawa shiyasa Sam junior RAMADAN yataso a shagwa6e saidai akwai aiki da hankali da ilimi

Yana karatu a qasar England inda yakesan xama cika

kken doctor

Duk lokacin dayaxo hutune Alhaji Jibiril yake turashi yin fashi da makami

Dan ayanxu mah hutune ya kawoshi Abujah shine Alhaji Jibiril "din ya turashi fashi gidan Dadyn shahuda.

👯👯👯👯👯

*SAMAREEN BANAH*

👯👯👯👯👯👯

*TASU S

ALAN SOYAYYAR*

Junior RAMADAN yaja numfashi dan kammala karanta diaries 'din da yayi

Kanshi ya 'dau caji yagano tabbas mahaifinsu ba mutuwar Allah da Annabi yayi Bah.

Kasheshi akayi.....

Kuma yana xargin Alhaji Jibiril da kisan

Dan rubutun mah

aifin nasu yatsaya mai a inda ya gayama yayunsa biyu akan hannun jarin da yasa a qasashe uku

sukace bawanda xaiji wannan sirri nasa

Ya qara jan numfashi yana San sanin ya akayi mahaifunsu ya mutu da mahaifiyarsu

Dole yaje ga Dadyn brother 'dinnan n

asa yaji ya abin ya kasance

Wanka yayi yayi. Sallah kana yabi lafiyar gado da tunanin Yayan nasa RAMADAN ko yanxu an sake shi ko ba'a sakeshi ba oho

Koma miye yabarma awa 'daya kacal...

👌🏻



Idan yatashi yaji komai.....

By Hajju

[20/03, 17:09]

80k: [8:27PM, 01/12/2016] Rahamat Nalele

👯

:

👯👯👯👯👯

*SAMAREEN*

*

👯

BANAH*



👯👯👯👯

*

👯

TASU SALAN SOYAYYAR*

👯

*Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele*

*Bismillahir*-

*rahmanurrahim*

*PART 82*

Fa'di shahuda take Wlhi na sanshi Dady

Wlhi na sanshi

Ya daka mata tsawa da cewa in baki rufemin baki ba saina dan daqaki Wlhi

Tayi shuru

Shima shurun yayi ya tashi yana safah da Marwa......

Can Yace nasan Wanda ya turoshi hmmm xamu ha'du dan ba abin da xai hanani ramawa

Momynta Tace w

ai har yaushe zaku dena irin wannan abinne

Cikin fusata yace ban sani bah.

Kina kallan uban dukiyar da suka tafi da ita Amma kina San cewa in bari

Tace hmm Allah ya baka hakuri ya kuma ganar daku Yace Amiien

Shahuda tabisu da kallo tanasan fahimtar

wani.........

Yusra CE ta shigo 'dakin da RAMADAN yake tana tafiya ahankali ahankali har taxo gareshi

Dake ya juya mata baya Sam baisan da shigowarta ba

Sanda yaji qashin turare ya doki hancinsa yayi Murmushi dan yasan Yusran CE

Yace Wlcm my q

anwa

Tayi dariya Tace naso na baka tsoro Yace ahaa

Me ya kawoki da wannan lokacin 10:37pm

Tace gani nayi Ya Amar yana can ga budurwarshi kai kuma ya barka kanata aikin tunani. Shine Nace bara naxo na tayaka hira

Yayi Murmushi Yace hmm qanwata kenan

Ai baije ko ina ba yana toilet

Yama xa'ayi yabarni ni 'daya haka...

Tayi saurin rufe bakinta tana dariya Tace Allah naxata ya tafi garetane Kasan fah ba qaramin Santa yake ba

Banyi tunanin xai iya in xuwa gareta yau ba.

Kan RAMADAN yayi magana Amar

ya fitoh daga toilet Yace toh munafuka brother yafimin ita....

Xan iya hakurin ganin har tsawan lokacin daxai tafi

Tace La......

Ya katseta da fa'din. Jeki pls kafin im mangareki

Yusra sanin halin yayan nata yatasa kallan RAMADAN Tace sai da safe

Da

murmushi Yace mutashi lpy my qanwa

Nanfa ta fucce

Amar ya kalli RAMADAN Yace brother naga kamar kanada damuwa

Yace kabari kawai. Ina neman wata mafutace tun 'daxo

Yace koxan iya sanin matsalar

Yace gidan Auntyna nakesan shiga Saidai megidan nat

a 'dan group ne

Tunda akayi Auran ya rabata da wayanta bayasan kowa yaje gareta dan yasan tasan sirrinsa meyake yi

Ina fatan kagane yaran nawa ka fahimceni

Amar yayi Murmushi Yace hmm na fahimceka man. Ina garin nan ban fahimci wannan yaranba ai banyi

ba

tashiga hannun 'dan iska

Dan agarin nan kam irinsu Su kukafi Yawa

Ko ina kashiga Wlhi sune.

Sunfi masu gaskiyan yawa

RAMADAN Yace mafuta.....

Amar ya tashi Yace 'daya CE

Shine kafara siye me gadin gidan da maqudan ku'da'de

RAMADAN yatash

i Yace eh nima nayi tunanin hakan

Shiyasa dana tashi xuwa ban dawo da ku'di ka'dan ba

Amar Yace idan basuyi ba akwaisu guna

RAMADAN yayi Murmushi Yace xama suyi........

😰😰😰

Washe gari?

SAILUBAH tana kwance afalanta sai saqa da warwara take

tasan tunda RAMADAN Yace mata xaixo toko insha Allah xata gansa ko dako xata qara kwana 'Dari tasan duk inda hankalinsa yake yana kanta

Sai dai gabanta na fa'duwa idan ta'daga kanta takalli makeken gidan nata da kuma masu tsaran nasa.

sai taji gabanta ya

fa'di. Takuma shiga tunanin ta'ina xai shigo har tafi da ita batare da an'ankare dasu ba.

Tun shekaran jiya rabanta da wanka. Dan afurgice take da Komai.

Tayi nadamar burinta nasan Auran Alhazawan garin Abujah. Masu ku'di meyawan gaske

Ashe kallan

su kawai takeyi dan yanke kan mutane suke susha jini. Ku'din bana Allah da Annabi bane

Duk saitaji tatsani kanta da duk wani 'dan garin Abujah

(SAILUBAH kenan ba dukka bane aka ha'du aka xama)

Da qar dai yanxu Tatashi tayi wanka tagyara kanta

Jirin

e yake ibanta dan tamanta rabanta da abinci

Duk Komai na gidan tsanarsu ta dirshi aranta

Da kanta tashiga kitchen tayi farfesun kifi ha'de da indomie

Tabaje taci taqoshi kana tadinga kiran sunan Allah da salati ga manxansa manxanmu.....

Da qarfe

biyu RAMADAN yanufi gidan Auntyn tashi batare da 'dan rakiya bah

Cikin sa'a yaga megadin gidan ya fitoh yana Alwala akofar gidan

Cikin girmamawa RAMADAN ya gaisheshi dayin yunqurin shiga gidan...

Amma sai megadin ya katseshi da fa'din samaree wa ka

ke nema

RAMADAN ya dawo gareshi Yace gun YAYATA naxo

Yace me sunanta Yace SAILUBAH

Shuru me gadin yayi da tsaida Alwalar tasa can Yace kayi hakuri samaree banan bane

Cikin damuwa RAMADAN ya kalli gidan xuciyarshi tana gaya mishi Wlhi gidan ne kuma

Auntyn shi na ciki

Yace dan Allah BABAH kamin rai inganta....

Da sauri me gadin ya katseshi da fa'din baxan maka qaryaba samaree kaje gidan gaba qila shine

RAMADAN ya rausayar da kai yanemi guri kusa dame gadin ya xauna Yace xan baka tsabar ku'di daga

naira 'daya har million indai xakamin hanyar daxan ganta

Megadin ya waro ido Yace million

😳

RAMADAN ya gya'da mishi kai

Cikin sanyin yanayi Yace axahirin Gaskiya samaree nan ne gidan. Saidai baxan iya temakwanka ba. Gashi naji kwa'dayin ku'din daka a

mbata baxan 6oye maka ba

RAMADAN Yace me yasa baxaka iya temako na ba

Megadin ya numfasa Yace xan gaya maka ne dan naji qaunarka araina

RAMADAN ya gyara xama Yace ina jinka baba

Megadin Yace megidan nan Alhaji Aminu ya garga'di duk Wanda yake cik

in wannan gidan akan duk wanda yaxo akan dangin Matarsa ne SAILUBAH kar'a barshi ya shiga dan tagano koshi Waye

Duk wanda ko yayi gangancin barin wani nata yashigar masa gida toko Wlhi saiya kashe shi

In yana da iyali takansu xai fara

Kagako samaree

ni inada mata da yara aqauye inajin da'din aiki dashi dan baya tauyemin hakkina. Kaga ya dace in barka kashiga

RAMADAN ya girgixa kai

Yace Gaskiya bai dace kabarni ba

Amma inaso kamin temako 'daya shine ga wannan.....

Ya miqa mishi wata takadda yaci

gaba da fa'din

kasan yanda xakayi ka bata dan Allah

Cikin tsoro megadin Yace baxan kar6aba samaree dan duk abinda xai jawomin matsala da me gidana bana san kusantarshi

RAMADAN ya karkace ya xaro mishi bandin 'din 'yan dubu dubu guda 'daya ya dire mis

hi kan cinyarsa Yace kamin rai babah itace farin ciki na

Cikin sauri me gadin ya saka ku'din a ajjihu da kar6ar takaddar ya saka ta a ajjihun itama Yace jirani yanxu xan kai mata in dawo....

Bai jira cewar RAMADAN ba yashige cikin gidan da turo qofar

da qarfi

RAMADAN yayi Murmushi abayyane Yace shegu masu gadi....

Wata motace tayi parking a gaban RAMADAN

Wani saurayi ya fito yana Sosa qeya Cikin girmamawa Yace Allah yajah da xamaninka oga

👏🏻

Me kakeyi anan

Abin yaba RAMADAN mamaki dan baisan

saurayin bah

Cikin tuhuma Yace kai Waye a ina kasanni

Saurayin ya kallesa da sauri Yace nine isma'il fah

😳



Cikin raini RAMADAN Yace da xaka shiga motarka kaqara gaba da kayima kanka gata.

Ba musu saurayin yashige motar tasa yanata kallan RAMADAN

harya tada motar ya tafi

Acikin gidan ko

Megadi yayi nasarar yin shashin SAILUBAH batare da wani ya gansa ba

Yayi mamakin hakan dan yasan mutum sunfi goma wa'yanda suke tsaranta

Ahankali ya bu'de kofar falan yashiga

ananko ya tarar da ita tay

i cikin tagumi tabishi da kallo

Yayi saurin durqusawa Yace Allah ya temakeki wani ne ya bani wannan nabaki yana....

Kan ya qarasa SAILUBAH ta kar6i takaddan. Cikin sauri tabu'de kuwa

_Ameenci ya tabbata agareki ya Auntyna. Da fatan kinci abinci dan s

hine abinda yafi damuna_

_Nasan bai ta6amin lafiyarki bah_

_Dan haka kicire damuwa dan har'abada bawanda xai ta6amin lafiyarki_

_ina tabbatar miki xan fitoh dake daga wannan qaxamin gidan_

_Ki sake kiyi warwalarki dan banaso nayi toxali dake arame ci

kin damuwa. *Den I Luv u my Aunty*_

Cikin murna SAILUBAH Tace a'ina xan samu bairo megadi

Yace kifa'di Komai da baki dan xuciyata tafara bugawa kar aganoni

SAILUBAH tayi Murmushi Tace toh kace mai inyana Son ya ganni cikin walwala batare da na rame

ba. toya gaggauta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login