Showing 42001 words to 45000 words out of 109645 words
hijabi, k"b yace ni gaskiya banasan wannan hijabin da kike sakawa, nifa mijinki ne,?"" ke matana ne, raihana tace ai nasani k"b yace kindai san Allah yana san macen da take kyautata ma mijinta ko?"
" raihana tace Eh, yace to nidai gaskiya inasan idan nazo a daina saka wannan hijabin plx,
Raihana tace tom, k"b yace kuma banasan kina man wani zame zame idan na riƙeki to miye a ciki?"" ya ƙarashe maganar yana ta
ɓ
e baki, raihana tace tom, yaci gaba da
cewa Allah ya tsine kuma ya la"anci duk matar da batabin mijinta hada mala"iku, raihana tace na sani, k"b yace to don Allah ki barni ina ra
ɓ
arki inajin dumin jiki ko zan samu natsuwa, ya ƙarasa maganar cikin yanayin tausayi,
Raihana tace duk naji amma
kayi haƙuri duk da nasan ka bayar da sadakinka kayi haƙuri za"a
ɗ
aura mana aure in tare a gidanka kaga sai muci karenmu babu babbaka, k"b yace ai bakisan dalilin da yasa zan ƙara aure ba, raihana tace miye hujjar?""
k"b yace bana samun kulawa, raihana t
ace to zaka samu insha Allah dan a shirye nake da in kyautata maka 100% k"b yace to Allah yasa raihana tace amin,
haka dai sukaci gaba da firansu amma k"b firarshi tafi karkata wurin maganganun da kwalwar raihana ta kasa
ɗ
auka, daga baya yace mata zai t
afi, ta shirya gobe zaizo yakai ta gidan da zai ajiyeta, raihana tace nidai basai naje ba, kai nake so ba gidan ka ko wani abu ba,
k"b yace na sani amma ina so kije ki gani ne kawai, raihana tace tom, koda ya tashi tafiya haka yayi ta nuna baya san rab
uwa da ita da maganganu masu jan hankali amma duk a yaudarance yake yi, ita kuma raihana zuciyar ta sai kar
ɓ
a take, k"b yayi mata saida safe, ya tafi ita kua ta koma gida,
****
*D*a safe bayan raihana ta
ɗ
an gabatar da aikin gida ta
ɗ
an tattaro wasu "y
an kayanta zata wanke , tana zaune a wuri da zatayi wanki taji sallama, wani yaro ne tsaye yace ance raihana taxo, raihana tace waye yake kirana?"" yaron yace alhajine, raihana tace waye alhaji ne?"" yace wani ne, tsaki raihana tayi sannan tace jeka ina zu
wa, yaron ya fita, tashi raihana tayinta shiga
ɗ
aki ta
ɗ
auki hijabin sannan ta fito dan ansa koran me nemanta,
sannu injin raihana yawwa yace, ina kwana?"" lafiya qalau am nace baki gane ni ba ko?"" raihana tace naso in gane fuskar amma kuma ta shige ma
n, alhaji yace a ina kika santa ne?"" raihana tace a gidan da aka tashemu , yace sosai nine, sake gaisheshi raihana tayi sannan tace Allah dai yasa yanxun ma ba tashinmu zakayi ba?""
dariya yayi irin ta mutanen nan "yan duniya, tsoho ne amma shakiyin ts
oho, alhaji yace ai nan ba nawa bane, amma idan kina so zan siya maku shi, dariya raihana tayi sannan tace aimu bama buƙatar gida a haka ma mun gode ma Allah, alhaji yace to dama tun ranar ne nace bara inxo in sheda maki ina sanki,
Idanuwa raihana ta za
ro sannan ta sake kallon alhaji a yanda ta ƙiyasta shekarunsa sunkai 75, dariya raihana tayi sannan tace nama
ɗ
auka jikanka kaxo ma neman aurena,
alhaji yace nine na cancanci hakan , ina sanki dan samun irina zaiyi wahala yanxun, raihana tace dole ko
yayi wahala saboda duk namiji irinka daya san darajar kanshi ai bazai fara tunkaro ni yace zai aureni ba, alhaji yace kuma shi yasa kuke jibgaro ku rasa masu aurenku, saboda tsabar girman kai,
miye aibu na?"" a lokacin da yake nuna kanshi, yace idan ku
ɗ
i kike so ina dasu ina da gidaje duk abinda kike so na more rayuwa zan maki ki kuma haƙƙinki na aure ma duk zanyi to miye a ciki?""
dariya raihana tayi sannan tace to ngd amma kayi haƙuri ni an riga an gama maganar aurena, sai anjima ta shige gida,
alhaji yace ai bakusan arxiki ba tana ganin kamar zan tauye mata haƙƙinta sunfi san yara su auresu ai gashi ann shi yasa kullum ake sako ku kamar tumaki , tsaki yayi sannan yaja sa
ɓ
a yabar ƙobar gidan,
raihana tana shiga gida hijabinta ta cire ta zauna
tace inma banda iskanci wannan tsohon ko uwar mi zai iya yi?"" harda wani haƙƙinki na aure ma duk zan sauke maki, tana kwaikwayon maganar shi, tsaki tayi a daidai lokacin data fara wanki,
Da mare sakaliya ne, raihana tana zaune ita da umma suna fira , f
arida tayi sallama ta shigo gidan ita da wata ƙawarta wadda ba ƙawar raihana bace, ƙawar ƙwa dai, raihana cikin farin ciki tayi masu sannu da zuwa, suka iso inda suke zaune, bayan sun gaisa da umma farida tayi mata sannu da tsegumin raihana bata fa
ɗ
a mata
umma babu lafiya ba, haƙuri raihana ta bata sannan tace suje
ɗ
aki, tashi sukai suka
ɗ
unguma sukai
ɗ
aki da farida da raihana da ƙawar raihana,
bayan sun zauna ne, suka sake gaisawa, farida tace ke raihana mu mata mun boni, raihana tace miye ya faru kuma?
"" farida tace kinga wannan baiwar Allah?"" tace Eh farida tace kawatace, raihana tace ya"akayi kuma bansan ta ba?"" tace yanxun zan baki labari raihana tace ina saurarenki, lokacin da akace za"a bayar da labari idanun wanda suka zo tare da farida ya ciko
da hawaye tasa gefen gyalenta ta goge, sannan tace Allah ya tsine ma k"b albarka, raihana ta kalleta tace waye kuma k"b?"" ƙawar farida ta kalli raihana sannan tace k"b shi"umi kenan tantirin kwallon
ɗ
an iskane wanda ya kware wurin iya yaudara da cin amana
, idan kika ganshi baya da siffar macuta amma tsumma ne a nanna
ɗ
e kinga idan ka warwareshi baka san abinda zaka gani ba?""
k"b ya jefani masifa ya jefani jaza"i shine ya rusa man rayuwata shine mutumin da yayi nasarar rabani da iyayena, ya wargaza man d
uk wani farin ciki nawa, na tsine mashi kuma tsinuwa ta tabbata kanshi da duk maza masu irin wannan halin,
Raihana da kanta yake a dabaibaye ita a tunaninta kabir
ɗ
an yayar umma ne, tace ai dan iskane nida ya ta
ɓ
a
ɗ
auke man zani wata rana ina wanka, ƙa
war farida ta kalli raihana tace ashe kinsan shi?"" raihana tace
ɗ
an yayan umma nane,.....................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3
⃣
0
⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION*
📚
✍
🏻
*MEELAT MUSA*
🌹
*****
*Ina ta
re daku kuma ina alfahiri daku masoyana Allah ya barmu tare fatan alkairi a gareku na gode sosai da yanda kuke nuna man kauna, muna tare ina sanku a duk inda kuke saboda kune alfahari na,*
*Hafsat Isa mamman saƙonki ya isa zuwa wurin Asmeenat xeeyan tan
a gaisheki kuma zata kiraki insha Allah,*
*****
*R*aihana tace gaba da cewa ai idan mahauci ya kashe maka
ɗ
a idan kaga baƙin tsumma guduwa kake, nida babu kunya babu tsoron Allah ya fito yace man yana so yayi fasiƙanci dani!!!""" niko nace kaji masu
lima ma zance wuƙa, baza ta tsaya taji inda aka dosa ba, mtswww,
Farida tace ai matarshi tana haƙuri dan ance har gida yake kai mata yana zima dasu, raihana tace ke ai bai ta
ɓ
a aure ba, farida tace waike wane k"b
ɗ
in kike nufi ne?"" raihana tace haba da
Allah
ɗ
an umma sa"a ne fa, a gidan uwarwa yayi aure?"" farida tace ke bashi ba, raihana tace waye wannan k"bn?""
Farida tace wani
ɗ
an iskane mai tafiya da imanin mace a lokaci
ɗ
aya, idan ya kafa maki ƙahon zuƙa sai ya zuƙeki kakaf ya shanye ki ya
ɗ
aura
yeki sai yakaiki bola ya zubar, raihana tace kaji
ɗ
an iska, a ina yake?"" farida tace waye ma yasan inda banzan yake?"" raihana tace waike farida ya sunan ƙawar taki ne?"" bata haƙuri sai kuka take don Allah, farida tace sunan ta maryam batta tayi kukan ko
ta samu sa"ada dan ko kece abun ya faru dake inajin mutuwa zakiy,
Raihana tace Allah ya rabamu da mummunar ƙaddara, gaba
ɗ
aya suka amsa da amin, raihana tace wai miye ya faru?"" ajiyar zuciya maryam tayi sannan tace ya zama dole a fa
ɗ
a maki dan kema *z
awarace* dole sai munyi ƙarfi da ƙarfi munyi yaƙi da irin wa"anan mazan masu nemar hana zawara zaman lafiya, raihana tace to fa
ɗ
a inji, maryam tace kamar yanda farida ta fa
ɗ
a maki suna nan haka sunan yake maryam,
Nayi aure ina zaune da mijina cikin rufi
n asiri da kwanciyar hankali babu abinda na nema a gidana na rasa, duk abinda ake ci a gidan kowa a gidana anaci ana ci, mijina yana ji dani sosai nima inaji dashi babu abinda na nema na rasa,
Yarana biyu kuma yana nuna man kulawa sosai, kuma yana marta
ba man "yan uwana na, nima ina martaba nashi, muna cikin wannan zamane Allah ya jarabi mijina da karayar arxiki, muka koma abinda zamuci a gidanma babu shi dani dashi da yara duk muka shiga cikin halin damuwa da takura,
Ganin muna cikin halin wahaltuwa
ne na yanke shawarar fara sana"ana haka na fara siyar da abinci ina dafawa ana zuwa gida ana siya, kuma Allah yasa ma neman albarka, fara sana"ana mijina yaji da
ɗ
in haka dan yanxun shima ya samu natsuwa da kwanciyar hankali ganin abinci da abunsha baifi ƙa
rfinmu ba,
Muna cikin haka wata rana wata ƙawata taxo na fa
ɗ
a mata halin da nake , ta tausaya man sosai sannan nace mata gaskiya na gaji zan kashe aurena ace ina
aure amma nice nake cida kaina?"" tace man mufa mata wallahi bamu da adalci wani lokaci dan
Allah ya
ɗ
ora ma mijina lalura rashi sai ince bazan zauna dashi ba?"" tace man inyi haƙuri tunda ina sana"a ina samun
ɗ
an rufin asiri na, inyi haƙuri wata rana sai labari, haka dai tayi ta man nasiha, tare da nuna man inyi zamana ko a gida nake shima zama
n gidan sai nayi haƙuri ita dama rayuwa haka take juyawa take wata rana aji da
ɗ
i wata rana kuma aji babu da
ɗ
i, to dole duk musulmi sai yaga nau"in jaraba idan dai har ya yadda musulmin ne,
haka dai na yadda na
ɗ
auki shawararta da zata tafi ta ƙara jadda
daman ko a gida ne wata rana zan nemi wani abu in rasa, amma idan nayi haƙuri anan Allah yana gani aure nake kuma bautarshi ce , zai bu
ɗ
a man ta wata hanyar, nayi mata godiya,
Munyi haƙa da sati
ɗ
aya da ita, wata ƙawata taxo na ƙara fa
ɗ
a mata kamar yand
a na fa
ɗ
a ma ƙawar farko, sai tace man zauna ki kashe kanki da ƙuriyarki da yarintarki da kanki da komai ki zauna kamar baiwa?"" ai rainin hankaline ma , wallahi maryam na baki shawara ki kashe auren nan yanda kike ha
ɗɗ
a
ɗ
iyar nan sai kin samu wanda yafi sh
i, amma da shekarun idan kiƙa biye wahala sai ta mayar dake tsohuwa, haka tayi ta bani shawarar banza kuma nahau kanta na zauna, bayan ta tafi mai gida yana dawowa na tada mashi balbalin bala"i ya sakeni,
ajiyar zuciya tayi sannan tace kunsan abinda ƙaw
ar tawa tayi ne?"" gaba
ɗ
aya sukace ah ah maryam tace ni na raina mijina naga gajiyawar shi ashe ita sanshi take, ta kuma je ta aureshi ,,
Raihana ta zaro ido sannan tace subahanallah wannan wace irin ƙawa ce?"" maryam tace mabuƙaciya, tunda da nayi haƙ
uri da shawarar ƙawata ta farko da abin baikai haka ba, farida tace gaskiya, idan kana tare da mijinka dan ya rasa wani abu ai bai kamata kice zaki fita ba, hmmm inji maryam sannan tace ai ki tsaya kiji ƙarahen zance, raihana tace muna saurarenki,
marya
m taci gaba da cewa bayan na dawo gida mamana tace tunda ya sakoni wallahi itama bazata riƙe mashi "ya"yan shi kowa ya riƙe nashi, inaji ina gani ina san yarana aka rabani dasu aka maidai mashi, da yake yar barikice ta tattara yaran nan ta riƙesu tana basu
kulawa kamar ina nan,
raihana tace to wai zuwa tayi tace tana sanshi?"" maryam tace ni ina zan sani tunda ba"a gabana akayi ba?""" amma wata ƙawata tace itace ta sameshi tace mashi maryam bata sanka tunda har ta kasa haƙuri dan Allah ya jarabeka da tal
auci, to ni ina sanka kuma so na tsakani da Allah tunda ai kaga baka da ko sisi, ta dai ha
ɗ
a da "yar barikinta, tace zata zauna dashi, shi kuma ya aureta,
Bayan aurensu kuma Allah ya koro mashi arziki yanxun baki ga yanda ubangiji ya bu
ɗ
a mashi ba, dan
wallahi wahalar gani ma yake, kinga da nayi haƙuri da ban zauna lafiya ba?""" raihana tace gaskiya ai rashin haƙuri baiyi ba a rayuwa, maryam tace bari kiji zamana a gida,
maryam taci gaba da cewa ina zaune gida ina fuskantar matsalali na rasa inda zan
saka raina, idan mamana tana magana nima idan na saka baki ko na bada
shawara sai ƙanina yace rufe ma mutane baki shegiya ke wa zaki bawa shawara?"" wanda ma gidanki kin kasa control bare nan gida, tun bana biye mashi har na fara biye mashi, idan yayi abu
na rama sai zagi, tun yana zagina abun ya koma hada duka, haka nayi ta fuskantar matsaloli sosai,
muna cikin haka ne, Allah ya ha
ɗ
anin da tantirin
ɗ
an iskan lamba
ɗ
aya namijin da baya da kunya ko kawaici, gashi Allah yayi masa batsa a rayuwarshi, lokac
in daya fara zuwa wurina, rigigi ya tattago maganar aure, ga hidima yana kashe man ku
ɗ
i kamar hauka hakan yasa naji da
ɗ
i kuma nakd ganin na daice miji,
haka yaci gaba da zugani cikin shauƙin kauna tare da tattalinso tace
ɗ
an iska kuma ya kware wurin iy
a soyayya, abinda ya fara ceman shine yanxun yaushe zamuyi aurene?"" nace mashi duk lokacin daka shirya danni a shirye nake, yace to abinda nake so dake, kinga gidan da zamu zauna yanxun nake ginawa ban ƙarasa ba, nace mashi ai babu komai a
ɗ
aura mana aure
in yaso daga baya zan tare, yace man ai shi bayasan irin wannan sai inga kamar bada gaske yake so na, danshi gaskiya mabuƙacin mace ne sosai danshi a rana gaskiya kafin gari ya waye haƙiƙa yana iya kwanciya da mace so biyar ko fiye da haka,
nace mashi
wannan duk ba damuwa bane, dadai irin wannan maganganun ya fara jan ra"ayi na, niko gani nake duk kauna ce, ashe jugunan nan
ɗ
an iskan duk yaudara ce,
muna nan tare dashi duk ya
ɗ
auke man wasu buƙatuna babu abinda na nema na rasa, tarayyata da k"b lokac
i guda na canja idan kika ganni zaki
ɗ
auka wata matar minister ce, wannan hidima da yake man yasa na saki jiki dashi, idan yaxo fira muna dan rungume juna, yayi man kiss
ɗ
an ta
ɓ
a can
ɗ
an shashshafa can, ganin na saki jiki dashi yasa abinda yake man ya ƙara
lunkuwa,
wata rana yaxo yace man matarshi tayi mashi wulaƙanci saboda ni, kuma shi bai iya neman mata ba, kuma buƙace yake dan gaskiya idan bai samu an
ɗ
auke mashi zai iya mutuwa , kuma shi babu wanda ya isa ya rabashi dani , yana magana yana kuka, na
tausaya mashi sosai nace mashi yanxun miye abunyi?"" yace maryam ki taimaka man kada in fa
ɗ
a halaka nace to ai nima halakar nake tsoro, hmmm k"b ya ƙwararre ne, dan haka yace man ki rufa man asiri in baki sadakin aurena dake, ki taimaka man don Allah, kin
san da an bayar da sadaki mace ta zama matar mutum don haka gashi, haka ya fito da ku
ɗ
i 50k wai sune sadaki ya bani na kar
ɓ
a, ya
ɗ
aukeni muka tafi,
A hotel ya kama
ɗ
aki kukan ta ya tsanan ta cikin shashshekar kuka tace ya wulaƙantani sosai yayi man abin
da tunda nake duniya mijina na sunna bai ta
ɓ
a man kamar yanda yake fa
ɗ
i a maganganun shi cewa shi ba raggon namiji bane ba, lallai ranar na yaba aya zaƙinta, haka k"b ya goge ne fess na gurzu lallai na yadda shi namijin ne cikkake,
Raihana tace kema kin
yi hauka, ya za"ayi daga ke sai ke namiji ya baki sadaki?"" maryam tace gajiya da zawarci yasa na biye ma zuciya na fa
ɗ
a halaka, danni banma san matsayina ba,
Taci gaba da cewa haka k"b ya mayar dani gadon kwanciyar wurin samun natsuwarshi , ana cikin
haka ne yace man in shirya muje umara, nace mashi gidanmu baza"a bari ba, amma muyi aure kafin lokacin , k"b yace ai har yanxun ba"a ƙarasa guna mana gida ba, in ƙara haƙuri, wani irin ihu maryam tayi wanda har umma saida ta shigo
ɗ
akin da gudu, tace k"b y
a cuceni ashe cutar kanjamau ce dashi na bani na lalace ,
Rashin haƙuri yaja man nayi goma babu
ɗ
aya, na rasa mijina, na rasa "ya"yana da nake kauna , na rasa mutumcina, na rasa lafiyata na rasa farin cikina, na rabu da iyayena, kuma bazan samu mai aur
ena ba har abadan duniya waye zai aureni da cutar h i v, wayyo Allahana ta