Showing 51001 words to 54000 words out of 111085 words
lallai sai kinyi musu girki, ai jiki magayi gobe ba zai ce ki dafa ba.
Ta ƙare maganar tana 'yar d
ariya, Madina murmushi ta saki kama tayi mata adawo lafiya sai ta miƙe ta shiga
ɗ
akin momy ta kwanta a lafiyayyen gadonta tana sauke numfashi ba jimawa barci mai nauyi ya
ɗ
auketa.
Momy koda ta fita wani barka taje na
ɗ
iyar
ɗ
aya daga cikin 'yan meeting
ɗ
in
su na kawaye taje, bata jima ba ta wuce gidan Hajiya Saratu dan ba zata
ɗ
auki lamarin Madina da wasa ba, ba zata yarda 'yarta tasha wuya a gidan miji ba da ranta da lafiya. Ta samu Saratu tana aikin ha
ɗ
a turaren wuta dan sana'arta kenan, amma haka Momy ta
matsa mata suka tafi gidan mai maganin mallaka. Koda suka isa basu samu mutane ba sai mutum
ɗ
aya da suka jira ta sallama kafin suka shiga
ɗ
akin, nan suka gaisa momy sai raba ido take yi tana ganin irin yanayin
ɗ
akin an baza layu da tarkace sai kace na 'yan
bori, ko kafin suyi mata
bayani ta koro musu bayanin abinda ya kawo su, momy tace kwarai kuwa maganar da suka zo da ita kenan. Tayi murmushi tana cewa.
A yanzu haka uwargidansa zata bar gidan a cikin kwanakin nan kuma in ta tafi ba zata dawo ba rabuwarsu
kenan, sannan Madina ba itace zata riƙe yaran ba dan zamu saka masa tsanarsu saboda kar su zame mata matsala, zata mallaki Hamid da duk abinda take buri a rayuwarta, dan za muyi amfani da son da yake yi mata mu ƙara ruruta wutar soyayyarta ya zama baya ji
baya gani akanta, hatta iyayensa zai iya sa
ɓ
a musu akanta, 'yarki zata yi farin ciki na har abada mutuwa ce zata rabasu.
Idan haka ya faru nafi kowa farin ciki, nawa ne zamu bada ku
ɗ
in aiki dan yau nake so ayi komai.
Dubu
ɗ
ari da hamsin zai isa ayi koma
i.
Nan take momy ta zaro bandir
ɗ
in dubu
ɗ
ari, tace ta bata account number ta tura mata sauran ha
ɗ
e da dubu ashirin tukuici. Mai magani ta karanto account
ɗ
inta nan take momy ta tura mata dubu saba'in tace ayi komai a gama, mai magani ta tabbatar mata da
yau zata tsaya akan aikinsu har sai ta kammala, ba a buƙatar komai dan da aljanu zata yi aikin, nan suka yi mata godiya kana suka wuce sai da momy ta sauke Saratu a gida kafin ta wuce gidanta.
****
Asibiti.
Madina tana fita ba jimawa Sakina tace zata k
oma gida yara su ka
ɗ
ai ne me za a dafa musu da rana, Abba yace.
Wannan abincin ma zai ishe mu, sai dai ki dafa na dare anjima, kuma ina saka ran yau zamu koma gida dan da alama jikinsu da sauki Alhamdulillahi.
To Allah ya ƙara musu lafiya. Me za a dafa d
a daren?
Sakina tuwon masara nake sha'awa da miyar kuka lami wacce ba a saka nama ba.
Cewar Hamid yana dubanta.
Amma kuwa ba mu da garin masara.
Ni akwai a
ɓ
angarena kije ki duba a kitchen yana nan a cikin store kusa da buhun semo. Sannan muma girkin k
iyi damu gaba
ɗ
aya.
Cewar Hajiya, Sakina to tace musu sai ta yi musu sallama ta fice Alhaji ya bita da addu'ar sauka lafiya, ya mayar da dubansa ga Hamid yana cewa.
Daga jiya zuwa yau ya kamata ku gane gaskiya
ɗ
aya ce, wlh Sakina matar rufin asiri ce amma
gaba
ɗ
aya idonku ya rufe da wannan aure sam bakwa ganin kirkinta da haƙurinta, duk da abubuwan da kuke yi mata amma ita dai ta jure da komai naku, gashi ita wacce ta jawo muku kwanciyar a asibiti bata damu da ku ba kamar yadda Sakina ta damu, wannan ina ga
nin ya isheku ishara musamman kai da kake niman wulaƙantata.
Alhaji ni ai tuni na fara dawowa hayyaci na, duk da Sakinar ma ta koyi rashin mitunci, na dai kama kaina.
Cewar Hajiya, Alhaji ya saki murmushi.
Karma ki kama kanki wlh ki cigaba da yada girma
. Kai kuma ka cigaba da muzguna mata kaji.
Abba wlh ina iya ƙoƙari wajen yin adalci amma Sakina ta sauya hali, jiyan nan ƙiri ƙiri na sata tayi mini abu tace ba zata yi ba.
To waye ya sauyata ta zama haka in ba kai ba, ai ka guji
ɓ
acin ran mai haƙuri bai
iya ba in ya tashi nunawa, kadai ji tsoron Allah wlh ka zama adali.
In sha Allah zan kula Allah ya bani iko.
Duk suka amsa da amin kana suka yi shuru ko wanne da tunanin da yake yi a ransa, Hamid dai tunanin jiya yace taje gidansu ya tsaya masa a rai do
lensa ya janye maganarsa ko dan Abincin da zata riƙa dafa masa dan wlh baya jin zai sake cin abincin Madina, kuma dole ta tsaya Sakina ta koya mata girki in taƙi taje makarantar koyan abinci dan ba zai ta
ɓ
a
ɗ
aukar mata 'yan aiki ba, dolenta zata kula da gi
dansa kamar yadda Sakina take yi masa, wannan tunanin yasa yaji kamar ya kira Sakina ya ce karta tafi gida ya janye maganarsa, amma ganin ma ta zauna har zata yi musu girki yasan ba zata tafi ba tunda tasan halin da yake ciki yana bukatar ta a yanzu, kuma
koda taje gidan yasan su Yaya umma sai sun dawo da ita, hakan yasa yaji natsuwa a cikin ransa.
*****
Sakina.
Tana isa gida su Mufeeda suka shiga bata labarin abinda Madina tayi musu, hankalinta ya tashi sosai amma sai ta danne tace musu.
Amma babu wand
a ya ce mata wani abu ko? kunsan yiwa babba rashin kunya Haramun ne.
Bamu ce komai ba Mama amma wlh zuciyata bata yi mini fa
ɗ
i akan yadda ita da Abba suke yi miki.
Cewar Mufeeda, da sauri Sakina ta kalleta tana mamakin fitar maganarta dan bata zaci tayi
wayon gane abubuwa ba, ta kamo hannunta tana cewa.
Mufeeda munzo duniya domin muyi bautar Allah ne mu samu Aljanna, kinga duk abinda za a yi mini bazai dame ni ba domin Aljanna nake nima, kuma ina so ku zama masu haƙuri ku samu aljanna muci kayan da
ɗ
i mun
a yiwa wasu gwalo ko.
Ta ƙare maganar cikin barkwanci, dariya duk yaran suka yi da alama duk sun yarda da maganarta, ta miƙe tana cewa su cigaba da kallonsu tana zuwa, tana shiga
ɗ
aki ta saka key ta saki kuka mara sauti, tausayin yaranta ya shiga bin dukk
an bargon jikinta har take jin shakkar barinsu a gidan, bata san ya makomar rayuwarsu zata kasance ba.
Allah kana gani bana nufin kowa da sharri, ga yarana nan ka zame musu gatansu, na tabbatar kaine mai kashewa da yarawa, bani da tsumi ba ni da dubara ka
shiga cikin lamarina.
Kiran daya shigo wayarsa yasa ta share wayenta ta isa gefen gado ta zauna, yaya Umma ce nan ta seta kanta tayi sallama.
Sakina ya yara fatan kuna lafiya.
Lafiya lau Alhamdulillahi, Hamid ne dai da Hajiyarsa suke asibiti jiya ma a
can suka kwana.
Nan ta kwashe labarin komai a takaice ta fa
ɗ
a mata amma banda zancen yace ta tafi gida, yaya umma tayi musu fatan samun sauki ta
ɗ
aura da cewa.
Sakina shiyasa nace ki ƙara haƙuri, gashi ba aje ko ina ba Allah ya fara nuna musu, ko a abinc
i kin mata zarra, kuma ki daure ki jure ki basu wata guda komai zai dawo daidai.
To yaya umma koda yace na bar masa gidansa sai na zauna?
To ina zaki je? ina kike dashi daya fi nan? yaranki zaki duba ki bashi haƙuri ki zauna ko dansu.
Yaya bakya duba wu
laƙancin da zai biyo baya.
Wulaƙanci na nawa ne baki gani ba, ko kin koma gidan dawo dake za ayi tunda baba ba zai bari ki zauna ba, Auren nan kowa haƙuri yake yi Sakina.
Yaya wannan tunanin yasa mata da dama suke kamuwa da ciwo saboda yadda iyayenmu suk
e tsoron saki, kullum mace tana cikin halin damuwa ba a duba wannan sai dai ace tayi haƙuri ta zauna kodan yaranta, namiji yayi ta wulaƙantata saboda a gidansu yasan ba tada power.
Sakina ta fa
ɗ
a tana fidda kwalla, Yaya umma tace.
Kima daina wannan magan
ar, koya ce miki ki je gida ne kike wannan zancen.?
A'a kawai misali nake kawo miki.
To Sakina ibada fa kike yi, ki duba Aljanna kike nima ki rabauta, shiyasa iyayenmu suke bamu haƙurin mu zauna.
Gaskiya ne amma mazan zamanin nan sai addu'a yaya, wai ya
ushe ma zaki zo ne dan ya hanani fita.
In Sha Allah cikin satin nan in zan zo zan sanar dake.
Cewar Umma, nan suka
ɗ
an taba hira kana daga bisani suka aje kan wayar.
[7/26, 5:11 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakab
ir
Page 23.
Sakina ta miƙe ta taka kujerar miro ta sauko da akwatinta babban, dama ba komai a ciki ta bu
ɗ
e shi kana ta bu
ɗ
e waldrobe
ɗ
in kayanta ta shiga zuba kayan a akwati, da yake duk gogaggu ne haka ta dinga jerasu tana binsu daki daki, sai da ta zu
ba kala sha biyu kana ta zuba sauran undies
ɗ
inta da hijab kala uku, ta je gefen takalma ta
ɗ
auki kala uku sai jaka guda
ɗ
aya data zuba tarkacenta duk ta saka a cikin akwati ta rufe, ta jashi kefe ta yafa masa zani dan kar yaran su gani su tambayeta, sanna
n ta zauna gefen gado tana sauke ajiyar zuciya, ji tayi gwara tayi nesa da kowa in da zata samu natsuwa, inta huta sai ta dawo, dama tasan ko taje gida sai sun dawo da ita kuma Hamid
ɗ
in zai ƙara jin da
ɗ
in yi mata wulaƙanci, shiyasa tun a hanyar dawowa dag
a asibiti ta gama yanke shawarar dole ta bar masa gidansa na
ɗ
an wani lokaci, yaranta sune ka
ɗ
ai inta tuna take jin karayar zuciya, amma tasan Allah yana tare dasu shine ƙarfin guiwarta.
Sallar azahar ya sa ta miƙe ta gabatar da shi kana ta fito falo tasa
yaran suyi sallah sannan ta shiga kitchen ta
ɗ
aura musu abinci taliya ta dafa suka ci. Wajen ƙarfe hudu ta je gidan Hajiya ta
ɗ
ibo garin tuwo ta dawo ta
ɗ
aura girki cikin sauri ta samu ta kammala komai, zuwa ƙarfe shida ta gama tuwon da miya ta koma
ɗ
aki
tayi wanka ta sauya kaya zuwa shadda riga da zani, bata yi kwalliya ba ta fito falon taga yaran sun fita can lambu, wannan ya bata damar komawa
ɗ
aki ta ja akwatinta ta fito dashi zuwa gurin mai gadi tace ya fitar mata dasu ya tsaya a waje gurin kayan gata
nan zuwa, yace to cike da bin umarninta, sai ta koma
ɗ
aki ta saka hijab ta
ɗ
auki jaka ta rataya ta shirya tsaf kana ta fito zuwa can lambu ta taso ƙeyar yaran suka dawo falo tana dubansu.
Mufeeda ki kula da ƙannenki zan je na dawo, ko da su Abba sun dawo
kice na fita kawai in ya tambaya.
Mama ba asibiti zaki je ba.
Mufeeda tace tana tsareta da ido.
Gidan yaya umma zani bazan jima ba zan dawo.
To mama ki siyo mana alewar tofi musha.
Cewar Yaƙub, shafa kansu sakina tayi tana saka musu albaka cike da tsa
ntsar kewarsu da zata shiga, ta ce su zauna a
ɗ
aki kar su fito kana ta fita da sauri dan ana niman shida da rabi. Tana fita ta bawa mai gadi dubu
ɗ
aya tana ce masa sai ta dawo, a dawo lafiya yace mata kana ya koma cikin gida, sam bai kawo tafiya zata yi ba
dan yasan bata cika tafiya ba, balle yaga yaranta suna gida sannan ma mai gidan ba lafiya bai ga dalilin da zai sa tayi tafiya ba, ya bayar da ƙila saƙo zata kai ta dawo. Sakina tafiya tayi sosai akan titin layinsu kasantuwar unguwa ce na masu hannu da sh
uni ba a fiye samun taxi ko napep ba sai mutun yaje baban titi, amma cikin ikon Allah sai ga wani mai napep ta tare shi ta sanar da shi tashar motar kawo zai kai ta, yace dubu biyu ba musu ta shiga tare da kayanta ta zauna tana koro addu'a a ranta suka taf
i.
*****
Asibiti.
Ƙ
arfe shida likita yazo ya ƙara duba jikinsu ya sallame su akan zai riƙa zuwa gida yana duba su, Alhaji yayi masa godiya kana yaje ya biya komai ya dawo suka fara ha
ɗ
a kaya zasu tafi, a lokacin ne Madina ta shigo tare da momy
ɗ
inta, sh
ine ya dakatar da tafiyarsu suka zauna suka koro gaishe gaishe da ya jiki, sai momy ke cewa.
Itama Madina ashe bata jin da
ɗ
i waya nayi da ita tace zawo take ta yi tun da ta koma gida, shine na biya na
ɗ
aukota muzo na duba ku daga nan itama a ha
ɗ
a mata mag
ani.
Ashsha ashe shiyasa bata dawo tun
ɗ
azu ba, amma ya jikin 'yata da fatan zawon ya tsaya.
Ya tsaya, sai kasalar jiki nake ji.
To Allah ya ƙara sauki, Alhamdulillahi naki ma yazo da sauƙi. Yanzu tashi kije
ɗ
akin likita ya dubaki sai mu jira ki fito mu
wuce gida.
Cewar Alhaji, Madina ta ce to kana momy tayi musu sallama suka fito tare tana jin da
ɗ
in yadda momy ta shirya mata dan kar suga lafinta bata dawo ba, tun a hanya tace ga yadda zasu yi, dan haka har mota Madina ta rakata kafin ta wuce ita kuma t
a koma
ɗ
akin likita tayi masa bayani ya rubuta mata magani ta fito taje pharmacy ta amsa sai ta koma
ɗ
akin ta sanar da Abba ta gama, nan suka ha
ɗ
a kaya suka tarkato zuwa gida lokacin ana ta kiraye kirayen sallar magrib, a gidan su Abba suka sauka daga nan
ne driver ya taya su Hamid
ɗ
ibar kaya suka dawo gidansu, Hamid
ɗ
akinsa ya wuce ya kwanta yana mayar da numfashi dan gaba
ɗ
aya ba ƙarfi a jikinsa, abinda ya faranta masa rai bai wuce yadda yaji
ɗ
akinsa yana fidda ƙamshi mai da
ɗ
i ba, dan hatta zanin gadonsa S
akina ta sauya masa mai kyau, ya miƙe ya leƙa bayi ya tadda an gyara komai,
ɗ
akinsa fes gwanin sha'awa, nan ya ƙara tabbatar da zaman Sakina a gidansa shine mafitarsa, dan bai hango tsafta a gurin Madina ba, duk ƙazantar da yake gani a gurin Sakina to Madi
na ta damata ta shanye, shi yayi auren wayayyiyar mace dan ta rage masa damuwar da Sakina ashe wani damuwar zai ƙara kwasarwa kansa, tsafta dai ashe ba a wayayyiyar mace yake ba kawai daga hali ne da kuma tarbiyyar data samu, duk da yana mugun son Madina a
mma baya jin zai jurewa ƙazantarta, haka ya ha
ɗ
awa kansa ruwan wanka ya yi tare da alwala ya shirya ta wuce masallaci, a nan ya zauna yana jiran ayi Isha'i sai ya shiga gida gaba
ɗ
aya.
Bayan anyi sallar magrib sai ga Jidda tazo riƙe da kwando da kuloli a c
iki, Mufeeda ta tareta da cewa.
Mamanmu bata nan taje gidan Mama Umma.
Ina tuwon data girka na
ɗ
ibar mana.
Yana kitchen.
Cewar Mufeeda tare da wucewa kitchen
ɗ
in dan ta zuba musu suma su ci, Suna shiga ta nuna mata nasu a wani kula.
Mamanmu tace wanna
n ne naku miyar ne bata zuba ba tace in kun dawo saina zuba na kai muku.
To jidda tace ta
ɗ
iba miyar a
ɗ
aya daga cikin kularsu ta ha
ɗ
a da kular da aka saka tuwon ta fita daga kitchen
ɗ
in ta wuce. Mufeeda ta zubawa su Yaƙub da baba ƙarami nasu daban sannan
ta saka nata da
Rauda duk suka zauna a carpet
ɗ
in falo suka soma ci. Bayan sun kammala suka kwashe kayan suka mayar kitchen suka wanke hannu tare da shan ruwa suka dawo falo suka zauna, ana kiran sallar Isha'i suka wuce
ɗ
akin Mufeeda suka gabatar, bayan s
un kammala suka dawo falo suka cigaba da kallo, a lokacin ne Hamid ya dawo suka yi masa sannu da zuwa Rauda ta rungumeshi tana oyoyo Abba, ya
ɗ
auketa suka zauna a cushing yana cewa Mufeeda.
Je ki kira mini mamanku tazo ta bani abinci yunwa nake ji.
Laaa
Abba ai Mamanmu taje gidan mama Umma tun
ɗ
azu kafin ayi magriba, tace ba zata da
ɗ
e ba zata dawo amma kaga har yanzu bata shigo ba.
Ta ƙare maganar cikin ƙasa da murya tana langwa
ɓ
e kai, shuru Hamid yayi na
ɗ
an lokaci yana tunanin kar dai Sakina ta tafi gid
an da ya ce mata ne, bayan kuma ya dawo yana so suyi sulhu komai ya wuce, da sauri ya ciro wayarsa a aljihu ya shiga kiran Sakina sai dai baturiyar nan me yin magana tace layin a kashe yake, ya sauke wayar ya lalubo layin yaya umma ya kira, tana
ɗ
auka suka
gaisa har take yi masa ya jiki ya amsa yana cewa.
Dama na kira Sakina ce a wayar a kashe,
ɗ
azun tace zata zo gidanki kuma shiru bata