Showing 3001 words to 6000 words out of 111085 words
/>
in ta duba taga wainar ba zai ishe su ba, ga babansu kuma
tasan da safe shi zai ci, dan haka ta
ɗ
aura tuwon semo ba
ɓ
ata lokaci ta tuka musu mara talge, ƙarshe yaran waina
ɗ
ai-
ɗ
ai suka ci suka ƙara da tuwo ita kuwa tuwon kawai taci ta barwa Hamid wain
ar ta haƙura, hatta naman ma basu ci ba ta bar masa tunda Hajiya ta kwashe kuma ba zai yuwu mai maza a bashi kai da wuya ba.
****
Madina.
Zaune take tare da Kausar data zo mata yini gidansu wanda tun bikinta da suka yi sai yau ne mijin ya kawota da zumm
ar zuwa dare zai zo ya
ɗ
auketa, Kausar ne ta dubeta tana cewa.
Kin ce Hamid zai zo banga kuma kin yi wanka ba.
Wanka kuma? Haba dakatsami zanyi kawai
ɗ
an wlh sanyi nake ji.
Madina kina nan da wannam
ɗ
abi'ar tun na makaranta, meyasa ba zaki sauya ba, kar
fa kije gidansa kina yi masa haka, kuma kinga Hamid
ɗ
an gaye ne ga kwalisa.
Kausar kema kin san bazan bari ya tsaƙi wari a jikina ba kuma ko yanzu bana tsamin zufa, kawai dai hammata ta zan wanke nayi brush sannan zan bulbula turare kinga na kwauda komai
bamai cewa banyi wanka ba.
Sai ni dana san dakatsami kika yi ba, lokaci yayi da zaki sauya tunda ba makaranta muke ba da ake tsumulmular ruwa, nan gida kike in kin so kiyi wanka sau biyar akwai wadataccen ruwa.
Hmmm wai ce miki aka yi bana wanka ne? Mala
ma ki sarara mini.
Ta fa
ɗ
a tana miƙewa tare da yatsine fuska ta shiga toilet
ɗ
inta, da murmushi Kausar ta bita dan tasan halin Madina ciki da bai sai dai ta bawa wani labari, Madina tana son gayu amma kuma tana da mugun kuiya bata jure walahar gyaran jiki
nta dan wanka ma in da zata samu ayi mata zata so, hatta girki bata iya ba ko a makaranta sai dai su 'yan
ɗ
akinsu su girka taci, tafi amanna da shan cornflaks da sauran kayan da basu da wahalar ha
ɗ
awa dangin su Indomie da curstard, wanka kam sai ta kwana t
a yini bata yi ba sai dai a wanke hammata a fashe jiki da turare a fita babu maicewa bata yi ba tsabar yadda take wahalar da turaruka, da yake tanada gata ga mahaifiyarta data
ɗ
aure mata ga kuma samari da suke kashe mata ku
ɗ
i, sam bata san wahalar rayuwa b
a.
Madina su biyu rak mahaifiyarsu ta haifa duk mata, Aisha itace babba tana auren wani
ɗ
an siyasa wanda suke zaune a Abuja, duk da tanada kishiya amma bata da damuwa da ita domin gidansu daban daban sannan mijin yana mugun sonta, tana da ma'aikata kusan
uku bata san wahala ba sai hutu, kamar dai yadda mahaifiyarsu ta gina musu rayuwa a gidansu duk da ana tunatar da ita illar haka amma kullun hangenta yaranta ba zata auren dasu gidan wahala ba sai inda zasu huta, matan babansu uku momynsu ce amarya suna da
manyan yayyi maza da mata dan kusan sune ƙanana a gidan, lokacin da suka taso ƙiri ƙiri Momynsu take hana a saka su aiki wai ba za a bautar mata da yara ba dan anga sune ƙanana, ta gwammace ko girki ne tayi da kanta ko wanke wanke bata bari a saka su, ace
warta mugunta ne ai sauran yaran bata ga ana bautar dasu ba har suka yi aure sai nata da aka raina, mahaifinsu yayi iya kokarinsa akan ya fahimtar da ita amma tace zugoshi aka yi dan haka ya zuba mata ido, shiyasa Aisha tana samun miji tana tsaka da karatu
n secondary SS2 ta aurar da ita ganin mai mugun ku
ɗ
i ne, a
ɗ
akinta ta ƙarasa harta
ɗ
aura da jami'a yanzu yaranta uku. Madina kuma tana tasowa lokacin data gama jss ta sa aka kaita makarantar kwana, tana gamawa kuma aka samar mata ABU Zaria ta tafi, huku ka
wai ke kawota gida shima in tazo bata matsarwa sai dai ayi mata, jin da
ɗ
i da gata kam tana cikinsa dumu dumu, har zuwa sadda babansu ya rasu aka raba musu gado koya ya kama gabansa, Momynsu ta samu gida a cikin gadonsu dan haka nan suka koma ƙaramin filat
mai kyau sai ta cigaba da harkan zannuwa da kayan yara ta zama babban dila a cikin gidanta, shiyasa Madina take duk abinda take so domin Momy tana bata duk wata kulawa fiye ma da mahaifinsu yana raye, kuma kullun hangen momy Madina matar manya ce dan tafi
Aisha komai kyau fari da wayewa sosai, shiyasa da Hamid ya fito aurenta sai da ta yi bincike akansa ta tabbatar da yana kama manyan ku
ɗ
i Madina zata samu farin ciki a gidansa, shiyasa ta amince da auren, domin har mota Hamid yayi mata alƙawarin bata kuma z
ata riƙa zuwa aikinta data fara a gidan Sahad TV babban gidan tv dake tashe anan jihar Kaduna, wannan yasa hankalin momy ya kwanta da Hamid musamman yadda yake kashewa Madina ku
ɗ
i da siyayya kala kala baya gajiya.
Madina koda ta fito sauri sauri ta shiry
a cikin doguwar riga ready made ash da fari tayi rolling galen kayan akanta ta fesa turaruka kusan kala uku kana ta kalli Kausar.
Nayi ko banyi ba.
Kinyi ko ba wanka farar mace alkebban mata. Saboda kin ga kina da kyau shiyasa baki damu da yawan make-up
ba.
Natural yafi ai, bari naje falo na jira kan kiyi sallah.
Ke ba zaki ba yi?
Yau nake gama period
ɗ
ina jinin ya
ɗ
auke amma ina so na tabbatar shiyasa naki yin wanka.
In dai ke ce zaki iya bari ma sai gobe kuma wlh sallar yau tana kanki tunda jinin ya
ɗ
auke.
To malama Kausar naji wannan fatawar.
Ta fa
ɗ
a tana yatsine fuska ta wuce ta fita, da addu'ar shiriya Kausar ta bita sanin tasan halin Madina akwai sakaci sosai wajen kula da addini. Madina ta samu momy a falon tana duba wasu atamfofi da aka kawo
mata su
ɗ
azun daga kwatono, ta zauna tana cewa.
Mom Hamid zai zo yanzu.
Yauwa ina so ki yi masa maganar da nayi miki akan ba zaki zauna gida
ɗ
aya da matarsa ba dan gaskiya kayan dana yi niyyar miki sunfi ƙarfin kiyi ha
ɗ
aka da wata a falo guda.
Nayi maga
nar dashi jiya a waya yace yafi so na zauna tare da matarsa domin na koya mata yadda ake rayuwa, saboda ba tada wayewa ko ka
ɗ
an, shiyasa naga gwara na zauna anan in yaso naga bazan iya ba sai na saka ya sauya mini gida.
Amma kuma Madina ina guje miki hali
n namiji da da
ɗ
in baki, nafi so dai ki zauna a gidanki ke ka
ɗ
ai ya samar miki 'yar aiki da zata kula da gidan dan baqn yarda ki je kina wahala ba.
Mom kinga fa yace zai siya mini mota zai barni nayi aiki ina ganin ko na zauna a gidan matarsa ita zata yi w
ahalar gidan, ko banza ta zame mini 'yar aikin tunda dole tayi in tana son zamanta a gidan, dan yadda Hamid ya nuna mini yayi mugun tsanarta zaman dole yake da ita.
In hakane to ya saketa mana ana dole ne a wannan zamanin.
Ba zan iya kula masa da yara ba
shima abinda yace baya so ya
ɗ
aura mini
ɗ
awainiyarsu amma da tuni ya saketa, kinga ta zauna ta riƙe yaranta.
Amma ai yanada uwa sai ya kaisu can ta riƙe su in haka ne.
Kiran daya shigo wayar Madina ya katse maganar Momy tana dubawa taga Hamid ne sai ta
miƙe da sauri.
Mom shine yazo bari naje.
Ki gaishe shi.
Cewar momy Madina ta wuce tana murmushi, ta fita ta same shi a jikin mota a ƙofar gidan ya rumgume hannayensa sai zuba mata murmushi yake yi har ta ƙaraso, ita ma murmushin take mayar masa ta isa g
abansa ta tsaya.
Farin cikin Madina barka da zuwa ya hanya.
Lafiya lau Hasken Hamid.
Naga ka fito daga mota, yau hirar waje za muyi ko gida zamu shiga.
Na fito na fara tarban gimbiyata ce kafin mu shiga, kin ce mini Kausar tazo nayi zaton zata fito mu
gaisa ai.
Na barta zata yi sallah maybe kan ka wuce ta leƙo.
Cewar Madina cikin murmushi, sai dai kuma nan take cikinta ya mur
ɗ
a taji kamar zata yi kashi ga wani wawan tusa dawo turnuƙota sai ta soma matse cinyoyinta tana mayar da tusan dan ta san ba ƙar
amar mai wari bace saboda
ɗ
azun kwai taci dafaffe kusan guda biyar, kuma muddun taci sai ya dinga sakata tusa, duk yadda taso ta matse ta kasa nan take ta saketa a hankali buuss mara ƙara, Hamid ko hankalinsa yana kan waya da aka turo masa saƙo yanzu, amma
lokacin da wannan wari ya ziyarci masarrafar jin ƙanshinsa sai da ya
ɗ
auke numfashin wucin gadi kafin ya saki a hankali ya kuma tsakar warin daya ji tamkar zai suma, da sauri ya bu
ɗ
e motarsa ya shiga yana jin kamar zai yi amai, Madina kuwa kunya ce ta ruf
eta amma sai ta basar ta fuskar tamkar bata ji warin ba.
[6/26, 10:21 PM] Rahma Kabir: *KAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 3.
Madina dakewa tayi tana ce masa.
Hamid lafiya ka shige mota da sauri haka ko an turo maka da saƙ
on tashin halkali ne?
Hamid yana jinta ya kasa magana, sai da ya ja numfashi ya sauke a hankali kana ya ƙara jan iskar dake motarsa mai ƙamshi sannan iya sauke glass
ɗ
in mota yana cewa.
Madina wani irin wari naji mai hamami daya hautsina mini lissafi.
A
i tun jiya muke fama da warin nan mun rasa a ina aka yasar mana da mushen dambar data hana mu saƙat.
Hmmmm ai ni kam bazan iya zama ba dan wannan
ɗ
oyin ya farraka duk wani farin cikin dana zo da shi, dan haka ga siyayyarki ki je gida mayi waya.
Ya ƙare m
aganar yana miƙa mata ledan siyayyarta, Madina ta amsa tana yi masa godiya tare da sallama kana ta juya da nufin tafiya, wanda nan take wani tusan ya kuma kubce mata mara ƙara ta sake shi, warin ya ƙara kaiwa Hamid ziyara zuwa mararrafar jin ƙamshinsa, wan
i tari ne ya surnuƙeshi wanda yasa shi
ɗ
aga glass
ɗ
in motar da sauri tare da tayar da ita yaja baya da gudu, tamkar zai yi amai yake ji, gaba
ɗ
aya tusan ta gigita lissafinsa ya juya da motar ta wuce da sauri, sai da ya isa kan hanka kafin ya yi parking ya s
auke glass yana shaƙar iskar gari dan ji yayi tusan nata ya gauraye da ƙamshin motarsa, ya fesar da iska yana cewa.
Kayyasa kaga shegiya tana niman halakani da warin tusa kamar wacce ta ha
ɗ
iyi mushe, har da zabga mini ƙarya wai munshen dabba ce, dana san
wannan baƙar huƙubar zata yi mini da ban zo wannan hirar ba, gaba
ɗ
aya ta dama mini lisaafi, wannan dana cigaba da zaman hirar ƙarshe sai dai na nima numfashi na rasa a jikina ta sumar dani haka kurum.
Ya ƙare maganar yana tofar da yawu cike da takaici, ha
ka Hamid ya isa gida da ƙunshin haushin Madina, dan sosai abinda tayi ya fusata shi.
Madina kuwa koda ta shiga gida bata samu momy a falon ba sai kawai ta shige
ɗ
akinta ta samu Kausar ta idar da sallah, sai ta zauna gefen gadonta tana turo baki fuskarta
a dagule, Kausar ta dubeta tana
ɗ
an murmushi.
Mrs Hamid ba dai har ya tafi ba? Ko fa
ɗ
a kuka yi naga fuskarki a dame.
Uhum yau kwai dana ci ya tona mini asiri, bai tashi wulaƙanta ni ba sai da naje gaban Hamid, cikina ya mur
ɗ
a na sakar masa tusa mai wari
wanda ya sa shi gigicewa ya tafi ba shiri.
Kausar kwashewa da muguwar dariya tayi, sai da tayi mai isarta kafin ta tsagaita tana cewa.
Kai amma yau kin tafka abin kunya, gaskiya tusa bata yi miki adalci ba kut.
Hmmm wayancewa nayi na nuna masa mushen da
bba ce aka yar a makwarara, da yake tusan ba mai ƙara nayi ba.
To da dama dama, amma duk da haka kema kin yi wauta, taya zaki tsaya har ki saketa, da kinyi sauri kin ce masa kina zuwa ki ruga gida ki saki abinki sai kin huce ki koma. Amarya mai ru
ɓ
e
ɓɓ
en c
iki naso naga idonki a lokacin, ina ruwan mujiya hahaha.
Ta ƙare tana dariyar mugunta, Madina ko ha
ɗ
e rai tayi tana cin magani dan sosai dariyarta ke ƙular da ita.
Kausar yafa ishe ki haka ki sarara mini na sha iska, ina ce kowa ma yana tusan da kashi, d
an haka banga abin dariya anan ba, ko shi Hamid
ɗ
in zai ce baya yi ne.
Dariya dai Kausar tayi tana cewa.
Ni tafiya ma zanyi kafin nima ki kumbura mini ciki, bayan fitarki Babyna ya kira yace na shirya yana hanya, har ina cewa zasu ha
ɗ
u da Hamid ashe ba r
abon su ha
ɗ
u.
Kyaji da shi dai.
Madina ta fa
ɗ
a tana gyara kwanciya cike da takaicin Kausar
ɗ
in.
***
Hamid.
Yana isa gida ya fito daga mota fuska ba annuri, dan shi abu ka
ɗ
an ke harzuƙashi yayi ta fuffuka kamar fulawar daya ji yeast, kuma abin takaici
sai ya huce akan wanda bai ji ba bai gani ba musamman Sakina da ya raina, haka ya wuce falo fuska a
ɗ
aure, yana tura ƙofa ya ga pow
ɗ
in kashin Rauda a gefe tayi kashin an barshi a gurin, nan take zuciyarsa ta tashi ya wuce zuwa
ɗ
akinsa a guje kamar zai kif
a, toilet ya wuce direct ya shiga kelaye amai kamar zai amayar da hanjin cikinsa, bayan ya gama ya wanke baki ya fito ya kwanta a gado rigingine yana mayar da numfashi. Lokacin da ya shiga
ɗ
akinsa baba ƙarami ya ruga ya sanarwa Sakina da Babansu ya dawo ya
ga kashin Rauda a pow, gaban Sakina sai da yayi mummunar fa
ɗ
uwa saboda tasan sun jawo mata fa
ɗ
an famau, kuma sallah ta shiga yi lokacin Rauda na pow tace Mufeeda ta wanke mata inta gama shine suka bari har babansu yazo ya gani. Da sauri ta cire hijab ta fi
to tana kwalawa Mufeeda kira wanda ta fito itama da sauri riƙe da hannun Rauda tana cewa.
Muje in wanke miki kashin, ke ba dama a barki a pow sai kin tashi kiyi ta yawo da tutu a jiki.
Ai kin kyauta Mufeeda tunda kin bari har babanku ya dawo yaga kashin.
Sakina ta fa
ɗ
a cikin
ɓ
acin rai sai ta juya ta nufi
ɗ
akin Hamid
ɗ
in tun kafin ya fito ya yi mata tijara a gaban yara, tana bu
ɗ
e ƙofar ta shiga sai suka yi ido biyu da shi, a fusace ya miƙe tsaye yana dubanta.
Allah ya wadaran halinki Sakina, na shigo gid
a da niyyar samun sassaucin abinda ya sameni a waje da aka kusa sumar dani, amma sai na zo kuma na tarar da ke kuma kasheni kike son yi, so nawa ina fa
ɗ
a miki Rauda ta daina kashi a falo ta riƙa yi a
ɗ
akin yara, da ta gama a wanke mata.
Kayi haƙuri wlh Sa
llah na shiga yi ban san tayi kashin ba.
Ɓ
ace mini da gani shashasha ballaza mara tunani kawai.
Yanzu akan wannan shine na cancanci zagi irin wannan Hamid,
ɗ
azun kayi mini...
Bata rufe baki ba ya wanke ta da mari tare da nuna mata ƙofar fita.
Suf-suf t
a fice riƙe da kuncinta tana jin zuciyarta kamar ta faso ƙirjinta ta fa
ɗ
o dan tsananin takaici, bayanta ya biyo yana cewa.
Daga ke har yaran nan bana son sake ganin gilmawar wani a falon nan.
Bata tanka masa ba ta wuce
ɗ
akinta ta rufe ƙofa, Mufeeda suna
jin abinda babansu yace ta tasa ƙeyar ƙannenta zuwa
ɗ
akin su Baba Ƙarami, Hamid ya isa wajen kayan kallo ya kashe su kana ya wuce kitchen ya
ɗ
iba waina guda biyar ya zuba miya kama ya
ɗ
auki gorar ruwa da drink da cup ya fito dinning ya zauna ya fara ci, tu
nda ya soma ha
ɗ
iye wainar yake wani lumshe ido saboda da
ɗ
insa yakai masa karo, yana matuƙar son waina musamman irin wanda Sakina take yi masa, wani lokacin iya girkinta yakansa ya raga mata akan wasu abubuwan, dan Sakina ba baya ba tasan hannunta sosai ba
girkin zamani ba bana gargajiya ba duka gwana ce, wani sa'ilin ko fushi yayi da ita amma fa ba zai iya fushi da abincinta ba sai yaci, haka ya ci ya ƙoshi kafin ya bar mata kayan anan dining ya fice zuwa gidan iyayensa ta ƙaramar ƙofar daya ratsa ta gidans
a.
*
Sakina.
Zama tayi a gefen gado tana matsar kwalla duk wani motsinsa tana ji har fitansa, a lokacin ne ta
ɗ
auki wayarta dake wajen madubi ta kira yayarta Ummulkairi wacce ta zame mata tamkar uwa saboda mahaifiyarsu ta jima da rasuwa, Umma tana
ɗ
auka
r wayar Sakina tayi shuru tama kasa magana sai nishin kuka, Umma tace cikin