Showing 60001 words to 63000 words out of 111085 words
kana
ɗ
agawa kanka hankali, Sakina ba yarinya bace duk inda taje ma zata dawo, idan kuma auren ne ta gaji dashi ita ta sani Allah ya gani kana yi mata uzuri, dan da wani ne take yiwa wannan rashin kirki da tuni ya sauwaƙe
mata, kishi ne dai ta azawa zuciyarta na babu gaira babu dalili. Batun abinci ka riƙa zuwa nan kana ci dan wlh ban yarda ko ruwan tea Madina ta dafa maka kasha ba, saboda yarinyar nan ina ganin kanta ba dai dai yake ba, ace a gabanmu ta banka mana tusa ta
fice kuma ko kunyar hakan ban gani ba a tare da ita da ta dawo da mahaifiyarta ba, karin takaicina ji yadda ta diro mana falo jiya tana tsala kuka kamar anyi mata mutuwa, kai amma wannan yarinya sam gidansu ba bu mafa
ɗ
i irin sangartattun yaran nan ne da u
wa ba kwa
ɓ
a kaka ba tsanani, kai dai Hamid Allah ya jarabce da mata sai a hankali duk baka yi dace ba.
Haka Allah ya ƙaddara mini Allah yasa naci jarabawan.
Ya fa
ɗ
a yana cire hularsa tare da shafa kansa zuwa fuska, ya mayar da hular ya miƙe Hajiya tana c
ewa.
Ka samu ka kai yaran ka dawo ka ƙara hutawa dan kaima naga jikin naka ba ƙarfi sosai, ka haƙura da aikin zuwa gobe ko jibi In Allah ya kaimu sai ka fita.
Dama company kawai zan leƙa naga abinda ke faruwa na dawo.
To a dawo lafiya.
Ta fa
ɗ
a, ya amsa
da Amin ya wuce jiki ba kwari.
[8/2, 5:02 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 26.
Hamid koda ya shiga falo cewa Mufeeda yayi suje su shirya kayansu zasu je hutu gidan yaya umma, cikin tsananin farin ciki s
uka shiga murna da tsalle, haka suka fara shiga
ɗ
akin Mufeeda ya taya ta ha
ɗ
a kaya a jaka nata dana Rauda, bayan sun gama suka koma
ɗ
akin su Yaƙub suma ya ha
ɗ
a musu nasu, ya sa suka kai mota, ya kwashe kwai
ɗ
aya gani
ɗ
akin Sakina kired hu
ɗ
u, ya
ɗ
iba musu k
ayan tea ya ha
ɗ
a dai kayan abinci da yawa dan bai dace ya kai musu
ɗ
awainiya ba tunda yasan halin rayuwar da suka ciki, duk suka zuba komai a motarsu na fita anguwa, daga bisani suka fito suka shiga Hamid ya bawa driver dubu Hamsin akan in ya je ya bawa Um
ma, ya amsa yace to kana ya jasu zuwa gidan Umma. Koda suka isa gidan da gudu yaran suka shiga domin tunaninsu zasu samu mamansu a ciki, cikin fara'a yaya Umma ta tarbesu.
Sannunku da zuwa mutanen gomna road, kuna ta waige waige to ummanku bata nan ku shi
ga
ɗ
aki ku aje kayan.
Mufeeda da murmushi a fuskarta ta gaisheta, ta amsa fuska sake tare da danne damuwar da take ciki, su Yaƙub ma suka gaisheta nan driver yayi sallama ya gaisheta ya aje kaya yana komawa ya
ɗ
auko, har dai ya gama shigo dasu, sai ya bat
a ku
ɗ
in da Hamid yace a bata ta amsa tana yi masa godiya kana ya wuce,
ɗ
aki ta shiga dasu tasa yaranta suka kwashe kayan zuwa
ɗ
aki, ta zauna tana jansu da hira tare da kwantar musu da hankali da cewa mamansu taje ƙauyensu biki ne zata dawo, dan abinda tayi
tunanin fa
ɗ
a musu kenan dan su samu kwanciyar hankali.
...
Can bayan sallar La'asar Umma ta kira Hamid a waya bayan sun gaisa sai take ce masa.
Ɗ
azu sai naga yara driver yazo dasu.
Eh wlh nan
ɗ
in ne naga yafi dacewa su zo na tabbatar zasu fi samun kula
wa, sannan Hajiyata har yanzu jikin nata sai a hankali shiyasa nace bari su zo nan gurinki bayan kwana biyu sai su dawo in Hajiya ta warware.
To Allah ya taya ni riƙo, ya labarin Sakina har yanzu dai ba amo ba labari.
Wlh duk inda ya kamata na bincika na
yi amma ba labarinta, Ins Sha Allah zata dawo nasan fushi tayi dani.
To Allah yasa, muma nan mun bincika 'yan uwa duk bata je gunsu ba hatta yaya Jalila ta Kano mun yi waya da ita
ɗ
azun tace bata je can ba, haka ma maiduguri sunce bata je ba.
To Allah ya
bayyanata.
Ya fa
ɗ
a cikin sanyin murya, Amin tace masa kana suka yi sallama.
*****
Sakina.
Suna zaune farfajiyar gidan cikin baranda, Anty Jalila tana lissafin ku
ɗ
in kaya da aka aiko mata da shi daga shagonta, 'yarta Ra'isa ce ta leƙo daga falo tana ce
wa.
Umma na sauke shinkafar miyar ganyen za ayi ko stew.?
Kiyi mana stew tunda jiya miyar zogale muka yi, amma kisa albasa sosai.
To tace mata kana Ra'isa ta koma ciki ita kuma ta aje ku
ɗ
in a cikin jaka ta mayar da hankalinta gurin Sakina tana cewa.
Sa
kina anya bazan sanar dasu umma kin zo gidana ba, dan naga hankula sun tashi sosai, bana son fa
ɗ
ar baba malam dan nasan sai yayi fa
ɗ
ar
ɓ
oyeki dana yi.
Dan girman Allah ki rufa mini asiri karki sanar dasu, dan na tabbatar in suka san ina nan to ba zan sake
kwana ba zasu biyo hanya su tafi dani, kuma nasan gidan Hamid zasu wuce dani babu mai saurarata yaji damuwata, haƙurin da suke bani kullun shi zasu ce nayi.
Hmmm ai abinda ke cutar da mu kenan, iyaye ko yayyi suyita nuna suna tsoron saki bayan sakin nan
halal ne in har ya zama da cutarwa gwara a rabu, abun takaici ba za a saurari wace matsala yarinya ke fuskanta ba, sai dai aita bata haƙuri ace ta zauna ko dan 'ya'ya bayan ita ka
ɗ
ai tasan me take fuskanta na cutarwa a gidanta, Allah dai ya sauwaƙe.
Ameen
, shiyasa na tawo nan dan in huta wlh, dan na tabbatar in gida na tafi korani zasu yi suce na koma, kuma mazan yanzu ba irin mazan da bane da suke da dattako, na tabbatar in na koma wani wulaƙanci zan fuskanta daya fi na baya.
Wai ke Sakina taya kika yi s
ake har Hamid ke zabga miki mari baki
ɗ
auki mataki ba, na farko kin nuna kina mugun tsoronsa kuma bai dace haka ba, mace an fi so ta kasance tana shakkar
ɓ
acin ran mijinta ba wai tsoronsa ba, kina kafa kafa da duk abinda zai kawo muku sa
ɓ
ani musamman in ki
n san halinsa, tsoronsa ya sanya bakya jituwa da shi, baki zama ki tattauna matsalarki ko damuwarki akan sa, ba kya hira dashi dan ku ƙara fahimtar junanku da sanin ina makomar zamanku ya dosa. Auren soyayya kika yi da shi tun ƙuriciya ya kamata ace kinfi
kowa sanin waye shi da kuma kyakkyawar mu'amala, Sakina ba kida wani abokin hira ko shawara daya wuce mijinki, kuyi wasa da dariya ku yi barkwanci ku zaulayi juna saboda ba kida wani namiji da zaki yi haka da shi, to amma kina tsoronsa taya zamanku zai yi
miki
da
ɗ
i?kuma ba zaki ta
ɓ
a fahimtar ina ya dosa ba haka shima ba zai fahimceki ba, wannan tsoron da yake gani a tare dake ya sanya yake yi miki duk wulaƙancin daya ga dama. Sannan yana da iyaye akwai abinda ke ka
ɗ
ai ba zaki iya magance sa ba dole sai many
a sun shiga, ko kin fa
ɗ
awa umma haƙuri zata baki, amma in kika sanar da mahaifinsa na tabbatar zai tsawatar masa kuma dole zai rage yi miki wani abu saboda kince yana shakkarsa, musamman marin nan yafi tsaya mini a rai da kin kai ƙararsa ga mahaifinsa na t
abbatar bazai sake kamanta marinki ba, in kuma kika fahimci haka yake fusatacce to da zarar ya fara masifa bashi waje ki wuce ki barshi a tsaye ki shiga
ɗ
aki kisa key yayi ta bambaminshi, na tabbatar wlh sai yaji mugun haushi, kinga kin nuna masa yaje yayi
ta haushi shi ka
ɗ
ai kuma baki ce wani abu ba sannan bai samu damar marinki ba, sai ki
ɗ
an jaye masa da rashin magana yaga kin fita lamarinsa, da kanshi zai nima sulhu ba wai ki riƙa tusa kanki ba wai ku shirya, ke naki kawai ki yi masa duk wani buƙatarsa
da ya hau kanki, misali abincinsa ruwan wankansa da komai da yake buƙata, batun
ɗ
akinsa zaki iya kwana a ciki amma ba um ba um um ba walwala, wlh da kanshi sai ya nima ku shirya ko ya fara tambayarki meke damunki, a wannan lokacin kike da damar da zaki fit
o da damuwarki akan abinda yayi miki fa
ɗ
a akai, ko kuma ki nuna masa rashin jin da
ɗ
in yadda yake yi miki fa
ɗ
a a gaban yara da dai wani ƙorafi da kike dashi akansa, daga nan zai baki haƙuri, imma bai fa
ɗ
a ba zai yi miki magana masu da
ɗ
i, sannan in yaga yana
miki fa
ɗ
a ba kya tsayawa zai fara dainawa ko ya sameki da maganar meyasa kike niman raina shi yana magana kin barshi a tsaye, anan sai ki ce bawai raini bane kin gujewa kar fushinsa yasa ya mareki ne, ko ba kya jin da
ɗ
in fa
ɗ
arsa a gaban yara harya kai ga
marinki, ba kya so yaranku su riƙa yi masa wani kallo na rashin ƙima.
Sakina zaman aure da miji irin Hamid sai da dabara da iya sarrafa harshe, ni na tabbatar a cikin maganganun dana fa
ɗ
a sai kin kafa masa hujjar da zaisa ya daina marinki a cikin zuciyars
a, kuma in yaga baki ce masa uffan in yana fa
ɗ
a wlh zai shiga shakkarki kuma ba ko wani wulaƙanci zai yi miki ba, ki daina cutar da kanki da zancen haƙuri kina dannewa, dole kema ki riƙa nuna masa ba zaki
ɗ
auka ba ta hanyar fita harkarsa, duk lokacin daya
kawo kansa ki amayar da duk damuwarki, in kuka ne ma kiyi masa, cikin kissa ake karya zuciyar namiji irin Hamid.
Amma yaga komai yayi miki kinyi haƙuri kin sanye ya mareki ya hantareki duk kin shanye, kinyi kuka a gabansa kin kasa nuna masa kema da zuciya
a ƙirjinki, taya ba zai wulaƙantaki ba, to komai zai
ɗ
auko ya
ɗ
ora miki tunda kin zama damo sarkin haƙuri. Kuma namiji baka yin fito na fito da shi, misali yana miki fa
ɗ
a kina mayar masa da magana cikin zafi, ko ya zageki ki rama kina
ɗ
aga masa murya, to
wlh a wannan lokacin har dukanki sai yayi saboda duk namiji baya ƙaunar haka, amma in ya miki kika bashi guri ko kiyi banza dashi baki ce komai ba ya ƙaraci fadarsa, daga nan ki fita lamarinsa na kwana biyu duk hawa dokin daya yi sai ya nima sulhu.
A loka
cin ne Jalila taja fasali tana kallon Sakina wacce ta natsu tana saurarenta,
ɗ
ago kai tayi tana murmushi.
Anty zuwana gidanki tamkar nazo amsar maganin warakar matsalata ce, dan duk bayaninki na fahimci nima ina da matsala, musamman yadda kika zaburar dan
i tsoron Hamid dan tabbas ina tsoronsa, kuma wlh zafinsa yasa ni haka, amma yanzu na gano komai dan a da da ƙuriciya in yana masifa nakan biye masa muyi shiyasa ya ke marina, da hankali ya fara shiga sai kuma na soma jin tsoronsa wanda hakan yasa bana iya
rama duk abinda zai yi mini, sai dai nayi shiru kona bashi haƙuri kuma bazai fasa marina ba.
Hmmm yanzu saiki gyara ki nuna masa kina da 'yanci a cikin gidansa, naso ace ranar daya mareki a gaban su Umma suma su tanka masa, su nuna basu ji
ɗ
adi ba, amma s
ai suka yi shuru kuma suka dawo suna baki haƙuri, ita umma tayi dacen miji shiyasa duk in kika fa
ɗ
a mata matsalarki take baki haƙuri saboda ita bata san irin wannan matsalar ba a gidanta, sannan itama tana da ƙarancin wayewar duk da ta fiki shiga mutane.
Ai ita yaya umma yadda na fahimceta bata so ya sakeni ne, wanda kuma ko sauran yayyinmu na gida tunaninsu kenan da iyayenmu, saboda yanayin rayuwar gidanmu mun taso cikin gidan malamai, sannan tana ƙoƙarin kwantar mini da hankali tare da bani addu'o'i ina
yi.
Hakan shine dai-dai ba wanda yake ƙaunar saki Sakina, amma in zama da cutarwa sai kiga daga a samu lada sai a koma samun zunubi, yana
ɗ
aya daga cikin dalilan da mata suke kashe mazansu saboda iyaye basa shiga lamarin sai dai in yarinya takai ƙara a ba
ta haƙuri, yanzu musamman akan rashin saduwa da namiji zai jingine mace yaki sauke haƙƙinta sai yarinya ta kai ƙara ace tayi haƙuri, wai shin ita dutse ce ba tada buƙata sai dai namiji? hakan shiya kawo yawan zina ce zina ce da matan aure suke yi, laifin m
azan ne da kuma iyaye da basa tsayawa su kwatarwa mace haƙƙinta. Allah dai yasa mu dace ina ganin zuwa dare sai mu
ɗ
aura akan maganarki dan yamma tayi ina buƙatar yin wanka na kimtsa kaina.
Yau Alhaji zai dawo ne?
Sai in zai dawo ne zanyi wanka? To bari
kiji ni ina yin wanka ko wani lokaci na ca
ɓ
a ado dan in burge kaina, bana wasa da kwalliya domin duk wanda ya shigo gidana ya ganni zai tabbatar da na cika uwargidan Alhaji Rashid, wannan yana
ɗ
aya daga cikin abinda danginsu suke girmamani wlh, ni bana yin
kwalliya dan miji sai ya yaba, to daya ce nayi kyau da kar yace ni dai nayi dan tsaftar kaina kuma danna burge kaina. Misali yanzu ya dawo kwatsam ya ganni dagaje dagaje zai ce dama sai in yana nan nake zama cikin tsafta, amma ya dawo ya taddani tsaf ya k
ike tunanin zai ji a ransa. Ina mamakin matan da zasu ce lallai miji sai yi yabe su, in yaki kuma sai su daina dama danshi kike yin kwalliyar? musamman ke
da kika ce yana kushewa kin daina yi, to bari kiji maza da dama basu damu da yaban kwalliyar matansu
ba amma in sunyi zasu ji da
ɗ
in ganinsu tsaf, kuma Allah ka
ɗ
ai yasan ladan da mace zata samu da wannan farin ciki data saka masa a zuciya, namiji ko ya shigo da
ɓ
acin rai yaga matarsa tsaf sai yaji wani natsuwa na musamman koda bai fito ya fa
ɗ
a ba, dan haka
ki jaye aƙidar ke kin daina kwalliya dan yana kushewa, ki dage damtse kiyi domin kanki in ya yaba to in bai yaba dan kanki kika yi, kuma bai ganki wata iri ba da zai riƙa raina miki.
(A comments dana gani na saurara, wata cewa tayi in tayi kwalliya miji
bai yaba ba to next day inta tashi daga kauri abincin safe na rana dana dare zata ha
ɗ
a taƙi yin wanka dashi zata tarbe shi, to abin tambayar anan wa kika yiwa? ina ce kanki kika yiwa dan na tabbatar a wannan daren baki isa ya kalleki da mutunci ba, balle y
ayi tunanin kusantarki. Sannan abin misali mata nawa ya gani a waje ya tsallake ya shigo gida, idan kin
ɗ
auki wannan
ɗ
abi'ar dan ki ƙunsa masa baƙin ciki to abanza kika yi, dan na tabbatar akwai wata Uwani ko Jamila a waje da zata fara jan ra'ayinsa da wan
nan kwalliyar da ke kika kasa yi wata tayi ta burgeshi. Zuciyar namiji an ginata ne domin son abu fiye da
ɗ
aya, shiyasa Allah ya basu damar yin mace fiye da
ɗ
aya, ba ki isa kice dan kina matarsa yana mugun sonki ba ba zai ga wata a waje yaji ta burgeshi ba
, haka Allah ya halicce su to da zarar kin iya allonki wajen kama shi a jiki kina yi masa iya kyautatawa da kulawar data dace, shine zaisa hankalinsa ba zai yawan riƙa kaiwa ga matan waje ba, amma ki sani duk lokacin da kika yi sakaci to wa kanki kika yiwa
, dan kin bashi ƙofar mayar da ha kalinsa ga 'yan matan waje ne, da zarar kuma ya samu wacce taja ra'ayinsa, to ko ya aureta ko ya fara raba dare na ba gaira ba dalili yana hirar banza ko waya, wata ma a kan gadonki zai fara chart da ita, to kin saki ƙofar
da zaki ja shi a jikinki. Matsalar rashin kwalliya ka
ɗ
ai kan iya tattara hankalin namiji ya koma waje gurin 'yan matan da suke baza kwaliya da turare a titi. Idan kinso ki gyara dan kanki)
Sakina sauke ajiyar zuciya tayi tana murmushi.
Kenan in riƙa kwa
lliya ko da ya kushe domin kaina? gaskiya na fahimci karatunki kuma sai yanzu na tuna in yana kushewar ba wai a cikin
ɗ
aure fuska bane wani sa'ilin da murmushi a fuskarsa.
To Sakina wataƙila shi nashi hanyar yabawan kenan, ko kuma ya kushe amma yaji da
ɗ
in
ganinki a haka bai zo ya ganki kamar fuskar namiji ba, kuma wannan da
ɗ
in daya ji Allah ka
ɗ
ai yasan ladan da zaki samu, ance fa in kana da kyau to ka ƙara da wanka, mu riƙa tuna bawai dan mazan ka
ɗ
ai za muyi abu ba muyi domin Allah shida ya halasta auren,
mu sani komai muka yi a cikin gidan aurenmu akwai tarin lada da muke yiwa kanmu tanadi na aljanna, dan duniyar makaranta ce muka zo