Showing 99001 words to 102000 words out of 111085 words
santa ba dan ya jima baya Kaduna har aka yi auren bai dawo ba, Salim ya zo tsakiyar falon ya shiga ƙunduma mata ashar yana zaginta, Madina da
yake akwai baki bai
mutu ba ta shiga ramawa, hakan ya tunzura Salim yayo kanta gadan gadan Madina tana ganin haka ta
ɓ
oye bayan Ladi, da yake Ladin ba ƙiba nan ya finciketa ya cafki hannun Madina ya shiga kai mata naushi a baki dan so yake ko bai zubar mata da haƙora ba to y
a sasu suyi girgi
ɗ
i yadda zai yi maganin rashin kunyarta, Madina ta shiga kwarma ihu Ladi tana kama hannu Salim amma ina ta kasa hana shi kasantuwarsa namiji ne mai karfi da gwanji, nan fa ya ha
ɗ
a mata jini da majina, madina ganin fa dagaske zai nakasata y
asa ta kwasa a guje tayi hanyar kitchen, a lokacin ne Sakina ta shigo falon ganin su a ƙofar kitchen suna ta bugawa da dukan ƙofar yasa ta ƙarasa ciki da sauri.
Asma Lafiya meke faruwa.?
Hajiya dukan Madina suka yi duk sun yi mata jina jina.
Cewar Ladi
cike da tashin hankali dan jikinta har rawa yake yi, Sakina ta shiga koro salati tana tafa hannu.
Haba haba me tayi muku data cancanci haka, ina ce Hamid wanku ne, kome ta muku ba sai ku fa
ɗ
a masa ba ya
ɗ
auki mataki da kansa, gaskiya bai dace ba haka.
Sa
kina babu ruwanki ki barmu da ita mu nuna mata Hajiya tana da gatan 'ya'yanta, ita
ɗ
in banzanta zata yiwa Hajiyarmu rashin kunya ta zauna lafiya, wlh ba a haifi 'ya ba.
Cewar Asma, Sakina kasa magana tayi ta wuce zuwa
ɗ
akinta ta cire hijab tare da kiran H
amid a waya, sai dai tayi ta kiransa bai
ɗ
auka ba hakan yasa ta yanke shawarar kiran Abba, tayi sa'a kira
ɗ
aya ya
ɗ
auka ko damar gaisheshi bata yi ba ta soma da cewa.
Abba ka zo gida ba lafiya Su Asma ce suke yin rikici da Madina, nima yanzu na shigo gida
n na tadda suna yi.
Salati ya saki tare da kashe wayar ya fito daga
ɗ
akinsa yana riƙe da charbi, Hajiya ganinsa cikin sauri yasa ta shiga tambayarsa lafiya? Bai bata amsa ba ya fita, itama da saurinta tabiyo shi ganin ya shiga gidan Hamid yasa taji gabant
a ya fa
ɗ
i, tasan dama su Asma suna can kuma sun sanar da ita zasu jawa Madina kunne ita bata san da rikici suka je ba, haka suka shigo falon su Asma da suke surfa masifa ganin Abba
duk suka yi tsit ko wanne yasha jinin jikinsa, shikam tsayawa yayi tana bin
su da kallo
ɗ
aya bayan
ɗ
aya bai ce komai ba, lokacin Sakina ta fito itama ta tsaya Hajiya ce ta katse shurun.
Kuyi mana bayanin meke faruwa a nan?
Dukan Madina suka yi suka ha
ɗ
a mata jini da majina shine ta gudu kitchen ta kulle.
Cewar Ladi tana matsar
kwalla dan sam bata ƙaunar tashin hankali, shiyasa ta fita waje ta kira momyn Madina ta fa
ɗ
a mata dan taga abin nasu ba zai ƙare ba, karsu kashe Madina su jawo mata matsala ace a gabanta aka yi, Abba shuru yayi saboda tsabar baƙin ciki Hajiya ce ta fara yi
musu fa
ɗ
an famau, wani irin tsawa Alhaji ya daka mata wanda yasa ta yin shuru yana nuna ta da yatsa.
Ki yiwa mutane shuru na tabbatar da saninki suka zo gidan nan, yanzu fisabillahi har da kai Saleem ina yi maka kallon mai hankali, ashe Hamid ne ka
ɗ
ai ya
ro nagari a cikinku, na tabbatar shi bazai ta
ɓ
a yin wannan ta'asar ba, to wlh gaba
ɗ
ayanku sai kunsan kunyi wannan rashin tarbiyyar, mutanen banza kun girma amma kullun cin ƙasa kuke yi.
Abba zagin Hajiya tayi fa tanayi mata rashin mutunci, ai duk
ɗ
an hala
k shike kare mutuncin iyayensa.
Cewar Salim yana wani fuzga, Abba ya ce cikin
ɓ
acin rai.
Bazaka yi mini shuru ba sai na tattakaka anan shashasha kuma...
Bai ƙarasa me zai ce ba suka ji jiniyar motar 'yan sanda a gate
ɗ
in gidan, Momy ce ta
ɗ
aukosu da yak
e akwai wani station a unguwarsu nan kusa dasu, ba
ɓ
ata lokaci ta koro musu bayani tare da basu ku
ɗ
i mai coka akan azo a tafi da ƙannen Hamid, tayi alƙawarin yau sai ta nuna musu gatan da Madina take da shi, babu wanda ya isa ya ta
ɓ
ata ya kwana lafiya koda
kuwa Hamid ne da kansa, shigowar momy a fusace yasa duk suka zuba mata ido, ta kalli Ladi.
Ina 'yata take?
Tana cikin kitchen.
Madina! Madina!! Fito ga ni nazo tafiya dake, Ladi su waye suka duketa.
Ta ƙare maganarta ga ladi, nan Ladi ta shiga nuna su
Asma, 'yan sanda da suka shigo momy ta nuna su Kubura.
Gasu nan ku tafi dasu.
Haba Hajiya taya zaki ce a tafi dasu, kamata yayi ki tsaya ayi magana ta fahimta.
Cewar Hajiya da hankalinta yayi mugun tashi za a tafi mata da yara, Abba ya
ɗ
aura da cewa.
Dan Allah kiyi haƙuri laifi kam mun san anyi miki amma bai dace lamarin ya tafi a haka ba, ni zan
ɗ
auki mataki mai tsauri akansu In Sha Allah, yalla
ɓ
ai ina ganin zaku iya tafiya za muyi sulhu dan abin da family ne.
Alhaji wlh sai antafi dasu dan ko Hamid
ne ya ta
ɓ
a mini yarinya sai na
ɗ
aura shi balle su, ai itama 'ya ce da zasu kama su duketa, bazan ta
ɓ
a yin uzuri ba a wannan maganar dan 'yata Madina tana da gata nice Uwa da kuma ubanta. Koda mahaifinta ya fa
ɗ
i ya mutu ban bari tayi kukan maraici ba, dan h
aka oficer ku tafi dasu sai kun kwatarwa 'yata 'yanci daga na har kotun ƙoli.
Alhaji ya shiga girgiza kai cike da tsantsar
ɓ
acin rai yama kasa yin magana, a lokacin Madina ta bu
ɗ
e ƙofar kitchen ta fito tana ganin momy ta ƙaraso da gudu ta rungumeta, wanda
ga jini yana bin ƙafarta momy ta kamata tana bubbuga bayanta alamun lallashi. Madina ta
ɗ
ago kai tana cewa cikin kuka.
Momy kasheni suka so suyi cikina ciwo yake mini kinga jini ke zuba, gashi sun fasa mini baki da hanci.
Ai wlh sai sun biya bashin abin
da suka yi miki. Officer sai kun tawo.
Momy ta fa
ɗ
a tana jan Madina suwa farfajiya dan bata bari ma Madina ta
ɗ
auki ko
ɗ
ankwali ta rufe kanta ba dan so take ta kaita asibiti a duba lafiyarta. Su Asma ido ya raina fata Abba fita tsakar gida yayi ya tsaya y
ana kiran Hamid a waya, haka 'yan sandan suka tasa ƙeyar su Kubura zuwa motarsu dake ƙofar gida, Hajiya da Sakina suka bi bayansu suna basu haƙuri amma kamar ƙara zugasu suke yi har suka tafi dasu, su Amsa suna kuka dan basu ta
ɓ
a
ɗ
aukar lamarin zai kai ga
haka ba, wannan abu ba ƙaramin zubar da ƙimar gidansu yayi ba dan mutanen unguwar duk sun fito waje jin jiniyar motar 'yan sanda, Abba koda ya sanar da Hamid guri ya samu ya zauna a wani dakali da yake na filawa, ya dafe kansa saboda chajin da yayi masa ts
abar
ɓ
acin rai, Hajiya ma tsayawa suka yi cirko cirko a tsakar gidan sun kasa magana ko wanne da irin tashin hankalin da yake ciki, Ladi kuwa tana
ɗ
akin Madina tana ha
ɗ
a mata kayan sawanta a trolley kamar yadda momy tabata umarni a waya, koda ta gama haka
ta koma kitchen ta sauke sanwar abincin data
ɗ
aura ta kashe gas kana ta koma
ɗ
akin Madina ta fito da kayan ta shiga falo ta
ɗ
auki mayafinta da jaka kana ta fito, haka ta wuce su momy ba tare da ce musu komai ba ta fita ta samu abin hawa ta wuce gida.
Mom
y kuwa asibiti ta kai Madina likita ya dubata wanda ya tabbatar da firgici ne yasata zubar jini amma cikinta yana nan sai dai kuma yana cikin barazanar fita, nan suka bata gado momy tace ba zasu kwanta ba su basu magani likita ya riƙa zuwa gida yana dubata
bata son zaman asibiti, sai gabda magrib suka bar asibiti suka wuce gida.
Hamid koda ya ƙaraso ya samu labarin komai, tsabar baƙin ciki kasa magana yayi ya tsaya yayi shuru, Abba yana dubansa yace.
Yanzu meye abinyi?
Abba wlh ban sani ba tunda sune su
ka jawa kansu matsala, ko meye Madina tayi musu ai ya dace su sanar dani na
ɗ
auki mataki, kuma wlh Mahaifiyarta zata iya komai dan ganin ta wulaƙantasu tunda ba mutunci ne da ita ba hatta ni ban cira a gunta ba in dai akan Madina ce, dan haka a barsu su kw
ana in jikinsu ya gaya musu gaba ko ance su duki wani ba zasu yi ba.
Haba Hamid ya zaka ce haka? laifi dai sunyi amma ya kamata kayi wani abu kodan kare martaban gidan nan.
Cewar Sakina cike da damuwa, Hajiya dai ta kasa magana dan duk abinda zata fa
ɗ
a g
oyon bayan yaranta zata yi kuma tasan hakan ba zasu kwashe da Abba ta da
ɗ
i ba, Alhaji ya da girgiza kai.
Duk tsuntsu da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, dan haka sai gobe In Allah ya kaimu zamu je station
ɗ
in muyi belinsu, muje masallaci an kira sallah.
Ya
ƙ
are maganar yana miƙewa yayi hanyar fita gate, Hamid ya rufa masa baya ba tare da yace komai ba amma har cikin ransa baya jin da
ɗ
in ƙannensa zasu kwana a sation, Hajiya kuwa fashewa tayi da kuka ta koma gurin da Abba ya tashi ta zauna tana share kwalla, S
akina ta matsa tana bata haƙuri da cewa.
In Sha Allah a zasu kwana a gurin 'yan sanda ba zanyi magana da Hamid
ɗ
in.
Hajiya dai matsar kwalla kawai take yi ta kasa magana dan baƙin ciki.
[8/23, 6:25 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir Mrs
MG.
Wattpad @rahmakabir
Page 41.
Da kyar Hajiya ta miƙe ta wuce sashinsu Sakina ma ta shiga
ɗ
akinta ta gabatar da Sallah, tasan Hamid baya shigowa gida har sai anyi sallar Isha'i amma saboda abinda ya faru tana son yin magana dashi yasa ta kira shi a way
a sai dai kuma bai
ɗ
aga ba hakan yasa ta haƙura akan har ya dawo dan bai dace abar su Asma a wajen 'yan sanda ba tunda da aurensu. Hamid kuwa ana isar da sallar magrib suka wuce gurin 'yan sanda shida Abba dan dama da suka fita sunyi maganar zasu je duk da
Abba yaso abarsu su kwana jikinsu ya gaya musu Hamid ne ya dage akan gwara aje
ɗ
in, Hamid drivern gidansa ya kira ya fito masa da
motar kai yara makaranta da ita suka je gurin 'yan sandan, cikin ikon Allah DPO yana ganin Hamid ya gane shi dan ya ta
ɓ
a siya
n mota a gurinsa, kuma a lokacin yayi masa mutunci wannan yasa suka zauna suka tattauna maganar har dpo ya bada belinsu akan da safe zasu dawo domin ayi case
ɗ
in domin a kashe shi anan, suka yi masa godiya bisa karamcin da yayi musu ko sisinsu basu amsa ba
kana suka baro station
ɗ
in suka dawo gida, sai dai Hamid da Abba an sauke su a masallaci dan gabatar da sallar Isha'i, su Asma aka ƙarasa dasu gidan Hajiya kana driver ya dawo yayi parking mota a gidan Hamid.
Bayan sun yi sallah Hamid gida ya shigo ya sa
mu guri ya zauna a falo, yara yadda suka ganshi yasa suka bnatsu bayan sunyi masa sannu da zuwa, a lokacin Sakina ta fito ta zauna tana dubansa cikin kulawa.
Barka da shigowa.
Yauwa, akwai sauran Gurasar nan ne?
Eh gashi can na ha
ɗ
a maka yana dining ha
ɗ
e da zo
ɓ
o.
Kin kyauta kuwa, ku kunci naku ne?
Eh tun bayan magrib yara suka ci, ni na kasa ma ci wlh kasan tashin hankali hanani sukuni yake yi.
To sai ki tashi muje kici dama tunda naga kiranki
ɗ
azun nasan zancen su Asma za kiyi mini, to ki kwantar da
hankalinki munje da Abba sun dawo suna can gida.
To Alhamdulillah Allah ya kyauta na gaba.
Ta ambata tana miƙewa Hamid ya amsa da Amin sai ya miƙe suka wuce dinning, nan ta zuba musu suka fara cin abincin, Hamid yana yi mata hirar abinda ya faru a gurin
'yan sanda, sai wayar Hamid ya shiga ruri yana dubawa yaga Madina ce sai ya basar ya cigaba da abinda yake yi, har ya katse ta kuma kira bai
ɗ
auka ba Sakina ta dubeshi.
Hamid ka
ɗ
auka mana wataƙila mai kiran yana cikin uzuri ne.
Madina ce fa bana son dam
uwa sam.
Haba dai ai ya dace ka
ɗ
aga kaji uzurin ta tunda
ɗ
azun naji mahaifiyarta tace asibiti zasu tunda tanata zubar jini.
Guntun tsaki yayi ya
ɗ
aga wayar lokacin da kira na uku ya shigo yana
ɗ
auka ta fara da cewa.
Hamid ka nuna mini iya son da kake m
ini, yanzu na tabbatar da ba sona kake yi ba jikina kawai ya ru
ɗ
eka ka aureni, to ka sani sai Allah ya saka mini wlh, amma kasan yau nice da girki ga kuma abinda ƙannenka suka yi mini amma ka kira kaji halin da nake ciki ya gagareka, gashi har cikin jikina
suka nima zubar mini har zuwa yanzu zubar jini nake yi.
Madina yaushe kike da ciki? Sannan da wanne kike so naji? Bayan Mahifiyarki ta
ɗ
auki matakin da taga shine daidai, dan haka ni babu wata magana da zan yi dake iyaka in baki haƙuri sai kuma gobe in m
unje gurin 'yan sanda sun yanke hukunci, tunda daga ke har Momy baku
ɗ
auki aurena a bakin komai ba.
Haka ma zaka ce? to Allah ya isa ban yafe ba ka cuceni ka rusa mini rayuwata, nayi dana sanin saninka wlh Hamid kuma ina
ɗ
auke da cikinka ban...
Bata ƙara
sa ba ya kashe wayar ya dafe kansa saboda
ɓ
acin rai, kusan duk Sakina taji komai da suka tattauna batace masa komai ba ta cigaba da cin abincin, Hamid sai dai ya
ɗ
auki kusan minti goma a haka kafin ya iya saita kansa ya ja guntun tsaki ya cigaba da cin abi
ncin, idanunsa har ja suja yi tsabar
ɓ
acin rai, haka dai ya tusa abincin badan yana jin da
ɗ
insa ba sai dan ya gusar da yunwar da yake ji. Bayan sun gama Sakina ta tura yara
ɗ
akinsu su kwanta ita kuma ta rage kayan jikinta ta saka doguwar rigar barci ta sak
a hula ta zo falo ta zauna kusa da Hamid, dan ya kishingi
ɗ
a ne a doguwar kujera ya rufe idonsa, haka ta
ɗ
aura ƙararsa a cinyarta ta shiga matsa masa.
Abban Mufeeda dukkan tsanani yana tare da sauƙi, kuma ko wani abu in ya faru ƙaddara ce kuma rubutacce ne
daga Allah, ka sassautawa zuciyarta domin damuwa ko tunani bazai yi maka maganin matsalarka ba face addu'a da mayarda komai ga Allah, In Sha Allah sai ka ga ya warware maka komai cikin ikonsa.
Bu
ɗ
e ido Hamid yayi ya zuba mata ido itama shi take kallo fus
karsa cike da murmushi, ganin bazai yi magana ba yasa ta
ɗ
aura da cewa.
Koda ace Madina ce ba tada gaskiya to su Asma sun take dokar Shari'a bai dace su biyota har gidanta ba su duketa, dan haka kar zuciya ko fushi yasa ka yanke mata hukuncin da bai kamat
a ba kayi mata adalci kamar yadda suma kayi musu uzuri, sannan kaga ba tada lafiya ko yaya in ka nuna kulawa a gareta zata ji da
ɗ
i zata gane ka damu da ita, dan haka ita aka yiwa laifi ya kamata a rarrasheta a bata haƙuri. Kayi mini afuwa bisa wannan magan
ar da nayi maka nasan ba hurumina bana sai dai ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, bazan so nima haka ya faru dani ba duk da tana matsayin kishiyata.
Na fahimceki domin gaskiya kika fa
ɗ
a sannan ita gaskiya
ɗ
aci gareta, koda hakan bai mini da
ɗ
i ba dole in yarda
da zancenki domin daga ƙin gaskiya sai
ɓ
ata.
Nagode daka fahimce ni Allah ya daidaita lamarin yasa iyakarta kenan.
Ya amsa da amin kana suka cigaba da kallo, lokacin barci daya yi suka miƙe zuwa ciki.
****
Madina.
Tunda Hamid ya kashe mata waya ta di
nga rusa kukan baƙin ciki, sai duk taji ma ta gaji da aurensa dan babu abinda ya kawo mata face baƙin ciki da
ɓ
acin rai, ta kashe ku
ɗ
in ta domin biyan buƙatarta duk a banza, sannan ace ƙannensa suzo har
ɗ
aki su duketa amma ya rasa abinda zai saka mata sai
maganganu mara sa da
ɗ
i har yana kashe mata waya, a haka momy ta zo ta sameta tana kukan, ta zauna cike da
ɓ
acin rai tana cewa.
Kiyi ƙoƙari ki kashe kanka abanza saboda namiji, tun farko wannan nake ta guje miki kika ce Hamid yana sonki bai da matsala ya y
audareki da da