Showing 21001 words to 24000 words out of 111085 words
mai kyau. Madina da mamaki tabi ƙofar daya rufe bat
a yi tsammanin duk irin son da Hamid ke yi mata ba bazai iya yi mata wanka ba, ta
ɗ
auka ruayuwa zata yi da shi tamkar mijin novel data ke jin labarin hikaya amma sai abin ya zama ba haka bane, kenan duk masu rubuta miji ya yiwa matarsa wanka a daren farko
zance suke yi dan su ƙarawa labarinsu armashi, ashe hakan ba mai faruwa bane sai dai a duniyar turawa ko larabawa ake yin haka, tuntuni tana hasasho irin soyayar da zasu zuba ita da Hamid saboda tsantsar son da yake nuna mata, ashe bai kai yadda take tsamm
ani ba, guntun tsaki tayi ta miƙe tana jan ƙafa ta shiga bayi, ta jima tana gasa jikinta daga bisani tayi wanka ta fito ta shirya sauri sauri ta yi sallah ta koma ta kwanta, ga sumarta duk a jiƙe ta tsaya ta tsane shi ta gyara ya ga gareta, saboda barcin d
ata ke ji sosai, haka barci ya ƙara
ɗ
aukarta mai nauyi.
....
Sakina tunda suka tashi suke hidima a kitchen na abinda zasu karya, kunun tsamiya suka dama sai ƙosai da Yaya Falmata ke soyawa, suna aiki suna hira gwanin sha'awa, yaya umma tace.
Sakina me z
a a dafawa su Hamid ne naga gari ya waye sosai ana niman ƙarfe tara.
Hmmm yaya Umma bai fito yace ga abinda zan dafa ba, kin san halinsa ba ayi masa gwaninta, na zo na dage na ha
ɗ
a abu yace bashi suke so ba.
To ko zaki buga musu ƙofa ki tambaya ko ki kir
ashi a waya.
Waro ido Sakina tayi tana dafe ƙirji tare da cewa.
Ki rufa mini asiri kar kisa da sassafen nan ya rufeni da masifa, duk lokacin da suka tashi ya sanar da abinda yake so na dafa musu.
Dariya Falmata ta saki tana cewa.
Ya kamata ki rage wann
an tsoron da kike yi masa, haba Sakina kina abu sai kace 'yar shekara sha takwas, kin kai munzalin da ya dace ace Hamid yana shakkarki fa.
Um um fa Falmata ban yarda da wannan zancen naki ba, gwara su cigaba da tafiya a haka, domin ba a samun aljanna ciki
n sauƙi, ban yarda ki
ɗ
aurata akan keken
ɓ
era ba.
Cewar Yaya umma, Falmats tace cikin murmushi.
Yaya umma wlh maza irin su Hamid sai mace ta busar da idonta ta nuna musu iyakarsu kafin ake zama daidai, yanzu kina nufin ta cigaba da jin tsoronsa haka yana
wulaƙantata a gaban kishiyarta, gaskiya ya kamata Sakina tasan kanta cewar itama macece mai daraja.
Ki bata duk tsawarar daya dace amma ban yarda tayi fito na fito da mijinta ba, domin girma ne Allah ya bashi bai dace ace ta daina jin tsoronsa ba.
Sakin
a dai tana jinsu tasan yaya umma ba zata ta
ɓ
a yarda ta
ɗ
auki shawarar Falmata ba, domin ita komai nata cikin lalama da biyayya take son ayi shi, wanda kuma ita Sakina ta fara tunanin bin hanyar da Falmata ta sanar mata dan taga ganin Hamid Zuma ne dole sai
da wuta, a yanzu bata jin zata
ɗ
auki wulaƙancin da zaiyi mata gaban kishiya sai dai duk abinda zai faru ya faru
ɗ
in.
Miji goma ai ba uba goma bane.
Ta ambata a cikin ranta wanda tasan iyaka bai wuce ya saketa ba, kuma tuni ta fara shiryawa hakan dan ba
zata zauna ya
ɗ
aura mata cutar da zai halakata ba ko ya nakasata tana ji tana gani, Allah ma yasan tayi iya haƙurin da zata iya. Haka suka cigaba da aikinsu har suka kammala suka fito falo suka yada zango suna karyawa lokacin ana niman goma saura.
Hamid
a lokacin ya farka ya duba agogon wayarsa yana ganin lokaci ya waro ido waje dan ya yi barci sosai, ƙugin da cikinsa yake yi masa kawai ya tabbatar da yunwa yake ji, dan a irin wannan lokacin ya jima da fita aiki, ya sauko ya riƙe wayarsa ya fito falon, da
yake su Sakina sun bawa ƙofofin bedroom baya basu ganshi ba suna ta hira da kallon tv, shima bai bi ta kansu ba ya nufi
ɗ
akin Madina ya shiga, nan ya sameta ta jingina da filo itama bata jima da tashi ba ta shiga danna wayarta, Hamid ya sakar mata murmush
i yana cewa.
Barka da safiya farin cikina.
Madina ta gimtse fuska ga miyau daya soma cika mata baki tana cewa.
Nayi fushi.
Sai ta mulmula ta miƙa kanta gefen gadonta ta tirtsar da miyau, sai ta dawo inda take ta jingina da filo, cikin dan mamaki Hamid
yace.
Lafiya kike yawan tara miyau a bakinki sai kace mai ciki.
Wlh duk inna tashi barci haka miyau ke taruwa mini har sai na ci wani abu ko nayi brush kafin yake bari.
To tunda kinsan haka kike me zai hana ki tashi kije ki wanke bakin kafin kiyi mini m
agana, nifa wlh ƙazantar hakan nake gani.
Kana kyamata kenan?
Ta fa
ɗ
a tana tsare shi da ido, guntun murmushi ya saki yana zama a gefen godon.
Taya zanji kyamarki bayan jiya komai ma ya faru a tsakaninmu, kawai dai ni mutum ne mai saurin kyankyamin abu m
akamancin haka, ki
ɗ
aure ki daina.
Zanyi ƙoƙari duk da hakan ya zame mini jiki.
In har kina son farin cikina dainawar shi yafi. Me kike so kici yanzu na sa a ha
ɗ
a miki.
Ok ina son a dafa mini indomie da dafeffen kwai uku, sai farfesun nama ko wani iri d
a kuma ruwan tea mai zafi.
An gama ranki ya da
ɗ
e.
Ya fa
ɗ
a tare da miƙewa ya fito falon, takunsa da suka ji yasa suka daidaita zamansu ya ƙaraso suka shiga gaisawa, ya amsa fuska sake yana cewa Sakina tazo za suyi magana. Ta miƙe tabi bayansa suka matsa c
an gefen falon ya ce mata.
Indomie zaki dafawa Madina da dafeffen kwai uku, sai farfesun kaza ko naman kai nasan muna da komai a frigde sannan da tea mai kauri, ni kuma doya da kwai nake so yaji kayan miya irin wanda kika saba yi mini da yaji sai kunun gy
a
ɗ
a, dan Allah maza ki hanzarta na baki awa guda nasan zaki gama komai.
Kallonsa take tsaf har ya gama maganarsa, ta nisa tana cewa.
Haba Hamid abu kusan kala hudu kace zan gama a awa guda sai kace agogo, zan dai dafa indomie da kwai tare da tea, sannan
doya da kwai zanyi sai kuyi haƙuri da sauran dan lokaci ya ƙure, akwai kuma kunun tsamiya in zaka sha.
Ni kike fa
ɗ
awa haka Sakina? Ace na fa
ɗ
a miki abinda nake so kina kawo mini uzuri, tun kafin raina ya
ɓ
aci kije kiyi abinda na sanar dake.
Gaskiya abind
a na fa
ɗ
a maka sune zasu samu, sauran bazai yuwu ba sai dai zuwa anjima nayi muku shi a matsayin abincin rana kuma...
Bata rufe baki ba ya kwasheta da kyakkyawar mari.
[7/9, 8:53 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakab
ir
Page 11.
Sakina ta shiga duban Hamid cike da tsananin
ɓ
acin rai idanunta suna kawo kwalla, ya nunata da tsaya yana cewa.
Karki sake ki dafa komai na fasa bana so, kije da mugun halinki kuma wlh sai na
ɗ
auki mummnar mataki akanki, na kula da take take
nki rashin kunya kika koyo zaki fara sauke mini, to bazan
ɗ
auka ba ballagaza shashasha darajar yaran nan kawai kike ci wlh amma dana baki mamaki.
Hamid mamaki na nawa zaka bani ai ka gama bani shi, domin duk abinda zaka yi mini yanzu bana shakka ko tsoron
sa.
Ta fa
ɗ
a maganar cikin hargagi da kukan baƙin ciki, Hamid yayi kwafa ya zo ya wuce buguzum buguzum kamar guguwa, su Yaya Umma tun sadda ya mareta suka miƙe suna kallon ikon Allah, hatta Madina sai da ta bu
ɗ
e ƙofar ta leƙo tana kallonsu, bayan Hamid ya
wuce ne ta saki murmushi tana ta
ɓ
e baki ta koma cikin
ɗ
akin, su Falmata suka isa inda Sakina ke tsugune tana kuka yaya umma cikin
ɓ
acin rai tace.
Sakina dama haka yake yi miki? lallai Hamid ya cika cikakken mara mutunci, ace a gaban idonmu zai sharara mik
i mari saboda shi isassahe ne, to gaskiya da sake wannan wulaƙancin yayi yawa.
Hmmm yaya Umma dama ai shiyasa nake cewa ta rage tsoronsa
ɗ
azun kike cewa ba haka ba, kinga ai ya gwada miki shi
ɗ
in
ɗ
an akuya ne kinga zahiri, wlh Sakina ki tashi tsaye ki nun
a masa kuransa kiyi fito na fito dashi shege ka fasa.
A'a Falmata ba kiji me yake fa
ɗ
a ba cewar darajar yaranta take ci, abu kadan zata yi masa dan nuna masa iyakarsa ya ka
ɗ
ata gida, dan haka haƙurin dai zata ƙara yi, sannan zanyi magana da Hamza muga ta
ina zamu shawo kan lamarin dan bazai yuwu ya cigaba da ƙunsa mata baƙin ciki ba wani lalurar ya sameta. Sakina tashi mu shiga
ɗ
aki kar ma ya dawo ya ganki, Falmata tafiya ya kamamu da wuri dan bazan cigaba da zama ina kallon kayan baƙin ciki ba.
Falmata t
ayi ƙofa tare da kama hannun Sakina suka shiga
ɗ
akinta suna bata baki.
Hamid yana fita sashin su Hajiya ya wuce ya samu mutane a falo suka shiga gaisawa, can ya hango Asma a kitchen da alama suma abin karyawa duke ha
ɗ
awa, ya isa can ya samu harda Hajiya k
e ciki nan suka gaisa hajiya tana watse baki tace.
Ya kwanan yata amarya fatan ta tashi lafiya.
Alhamdulillah yanzu ma nazo naji me zamu samu na karyawa, wlh Sakina ba tada mutunci yanzu ta gama yi mini iskanci akan ba zata dafa mini abinda na umarceta d
a dafa ba.
Kai ma kaso ranka ya
ɓ
aci ne amma dama kasan baƙin kishi bazai bari tayi ba, dama tun
ɗ
azu nace a soya maka waina da miya.
To akwai farfesu na ko wani nama?
Eh akwai na kayan ciki da Alhaji yasa a dafa masa
ɗ
azun aka gama.
Dama Madina ke so
sai a ha
ɗ
o da ruwan tea.
To yanzu za a kawo, karka samu damuwa anjima ma duk nan za a baku abincin kar Allah yasa ta yi girkin, yanzu dai zaka san kayi aure gida biyu maganin gobara.
Cewar Asma, murmushi Hamid yayi sai ya shafa ƙasumbarsa yayi musu salla
ma ya wuce. Koda ya dawo falon ba kowa ya wuce
ɗ
akin Madina ya zauna bakin gado.
Ki tashi kiyi wanka ki shirya kafin mutane su fara zuwa bai dace a ganki haka ba.
Kash! nifa wlh zai wajen 12 nake wanka yanzu ina karyawa barci zan koma.
Haba Madina ya ki
ke manta cewar ke baƙuwa ce a gidan nan kowa so yake ya ganki, sannan nan gidan Hamid ne ba gidanku ba da kika saba yin duk abinda kike so, ko dan ki faranta mini ya kamata kiyi duk abinda na saka ki ba tara da nayi mita ba.
Zum
ɓ
uro baki Madina tayi bata
ce komai ba ta sauko ta wuce bayi, Hamid ya girgiza kai yana murmushi yasan zai sha fama da ita saboda ya kula tana da yawan shagwa
ɓ
a da shauni, fatansa Allah yasa ba tada ƙazanta saboda yadda zasu more rayuwarsu da kyau. Haka ya zauna zaman jiranta har ta
fito
ɗ
aure da towel a lokacin ne aka buga musu ƙofa, ya miƙe ya fito falon yaga Jidda da kwandon kulolin abinci a hannunta, ya wuce zuwa
ɗ
akin da yake mazaunin falon Madina ya murza key ya bu
ɗ
e suka shiga ta je kwandon sai ta wuce, shi kuma ya koma ya sam
i Madina ta sanya doguwar rigar shadda dark pink yasha aiki tun daga sama har ƙasa, kayan ba ƙaramin fito da kyawunta yayi ba, ta zauna tana shafa mai data
gama ta sanya kwalli da powder sai man baki sannan ta feshe jikinta da turare ta
ɗ
aura
ɗ
an kwali, ba
ƙaramin kyau ta yiwa Hamid ba, ta juyo tana rausayar da kai da fari da ido.
Ya ka ganni.
Kinyi kyau irin sosai
ɗ
in nan, Madina kin morewa jiki Allah yasa kita zama a haka kirki yi ƙiba sosai.
Dariya tayi ta isa ta zauna bisa cinyarsa tana cewa.
Wa jib
i zanyi ƙiba sai dai ba mai muni ba tunda kaga yadda jikin anty Aisha yake duk momy muka
ɗ
auko, itama ai kaga tana da jiki amma mai kyau.
Gaskiya ne tawan. Tashi zaki muje mu karya.
Wai Sakina ce da dafa ko kuma ya akayi? naji kun fara rigima
ɗ
azun wai d
ama haka take ba tada kirki.
Ka
ɗ
an ma kika gani in dai Sakina ce, sashin Hajiyarmu naje na yi magama ashe ma sunyi mana waina, gashi can a falonki sun kawo.
Wow aiko zan so cin wainar nan, amma farfesun fa.?
Ta fa
ɗ
a tana cuno baki.
Shima an samu na kay
an ciki.
Ina godiya Babyna, amma har yanzu banga tukuicin jiya ba nasan da yawa angwaye suna yiwa amarya kyauta.
Motarki tana nan a waje an rufeta da rigarta, itace kyautar.
Ni dai gaskiya yamin ka
ɗ
an ai nasan da ita, wannan kyauta ta mamaki ya kamata k
a bani.
Madina muyi yaruwar gaskiya da gaskiya kinji, ni bansan wannan bayanin naki ba muje mu karya yunwa nake ji.
Ya miƙe yayi gaba, Madina ta bishi da harara ita tana yi masa kallon wayayye yasan irin wa
ɗ
annan abubuwan ashe ba haka bane kallon kitse t
a ke yiwa rogo, guntun tsaki taja tabi bayansa dan tuni ya fice abinsa, koda ya shiga ya samu har an kawo flacks
ɗ
in ruwan tea, ya shiga ha
ɗ
a musu komai ta sameshi ta zauna a carpet
ɗ
in daya malale tsakiyar falon, haka suka karya ba tare da wani hira ba da
n sosai Madina take wani shan ƙamshi, Hamid ya kula da hakan shiyasa ya rabu da ita dan ba zai yarda ta saka shi yin abinda bai yi niyya ba, shi mamaki ma take bashi da irin wannan salo salo da take
ɓ
ullo masa da shi wanda bai santa da shi ba, ko da yake d
ama ance ana
ɓ
oye hali sai anyi aure komai ke fitowa to ya fara ganin zahirinta, dole ne ya nuna mata shi kaifi
ɗ
aya ne mace bata isa ta juyashi ba. Bayan sun kammala cin Abincin ya tattara kayan ya miƙe, da sauri ta miƙe itama.
Beb wai fushi kake yi dani
ne?
Ya zanyi fushi da amaryata kawai dai in ina cin abinci ban fiye son magana ba, bari na mayar musu da kayan in dawo in shirya in fita.
Haba Hamid ni ka
ɗ
ai zaka bari gaskiya ka jira 'yan uwana su zo sai ka tafi.
To Madinar Hamid bari na shirya ina zu
wa sai muyi hira ko, dan ban gaji da kallon wannan kyan naki ba.
Murmushi tayi masa sai ya fice ita kuma ta cigaba da zama a cushing
ɗ
inta tana danna waya, shuru shuru bai dawo ba har kusan sha biyu a nan ta fahimci jirgata yayi dan tuni ya shirya ya fice
bai jin zai biye mata.
Ana yin sallar azahar su Yaya umma suka tattara yanasu yanasu suka tafi, wanda Sakina bata so haka ba taso ace sai yamma zasu wuce, koda tayi musu rakiya zuwa gate sosai suka ƙara bata shawara akan In dangin mijin ko wasu 'yan uwa
n amarya sun zo suna nimanta da rigima karta kulasu ta cigaba da haƙuri kuma shima Hamid
ɗ
in karta sake shiga lamarinsa ta bashi lokaci, tace musu to kana suka wuce ta juyo tana jin kamar ta bisu, kitchen ta shiga taga babu wani abu da zata yi dan komai sa
i da suka wanke mata suka gyara mata, sai ta koma
ɗ
aki ta tasa ƙeyar Rauda ta rufe da key tayi kwanciyarta tana tunanin ya makomar zamanta zai kasance, tasan biyayyar data yi masa a da ba zata ta
ɓ
a kamanta irinsa ba a yanzu, sannan ba zata iya bin shawarar
yaya umma ba a yanzu dan ta gaji da halin Hamid, dole ne ta nuna masa itama akwai zuciya a ƙirjinta, girkin sati
ɗ
ayan data ce zata yi musu wlh ba zata yi shi ba, sai dai yasan yadda za suyi har tsawon wata gudan data
ɗ
ibar musu, da tunani barci ya
ɗ
auket
a, sai dai hayaniyar mutane da suke zuwa ya hanata barcin sai kawai ta zauna tana duba wayarta na hotunan da suka
ɗ
auka jiya.
Madina tunda 'yan uwanta suka zo sai ta mance da zancen Hamid, ga kuma dangun miji da suketa shigowa suna ganinta, haƙiƙa ba ƙar
amin farin ciki take ciki ba iri yadda 'yan uwan Hamid suke nuna mata so, ko ba a fa
ɗ
a mata ba mamanshi ma tana mugun sonta yadda ƙannensa suke nan nan da ita. Wajen ƙarfe biyar 'yan uwanta suka kaita sashin Hajiya kamar yadda ake yi a aladar Hausa Fulani
sun samu tarba mai kyau daga bisani suka dawo da ita
ɗ
akinta, zuwa magrib kowa ya watse aka bar amarya a
ɗ
akinta.
Hamid bai shigo ba sai bayan sallar ishai, ya riƙo musu tsire ita kuma Sakina ya siya musu kaza tunda jiya bai bata ba duk da yasan akwai
ɗ