Showing 6001 words to 9000 words out of 111085 words

Chapter 3 - ƘAZAMAR AMARYA completed.

tsananin kulawa.

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allahumma ajirnee fee musibati wa akliflee khairan minhaa, Allahu Allahu rabbi laaa ushrika bihi shai'a, Allahumma iyyaka na'

abudu wa iyya ka nasta'in. Sakina karki yarda Shai

ɗ

an yana shagaltar dake kusantar Allah a duk lokacin da kika samu kanki cikin ru

ɗ

ani da damuwa,

Allah shine ka

ɗ

ai gatanki a wajensa ne zaki samu sassauci. Ba sai kin fa

ɗ

a mini meke damunki ba domin nasan a

wannan lokacin da Hamid yake shirin ƙara aure to dole zaki fuskanci barazana a aurenki, ba duka maza bane suke iya kamanta adalci, mutunci da kuma girmamawa ga matansu lokacin ƙara aure ba, domin idonsu yakan rufe da hangen wacce zasu aura itace zanyin ida

niyarsu itace zasu samu farin ciki a gunta, dan haka Hamid ya kasance

ɗ

aya daga cikin irin wa

ɗ

annan mazan, shiyasa nake baki haƙuri ki cije ki jure har ayi auren nan a gama lafiya ba tare da kin ja wani rigima a tsakaninku ba.

Amma yaya Umma ya fara kaini

bango bazan iya jurewa ba, ji nake kamar na gudu na bar masa gidansa, Hamid baya ƙaunata kwatata nayi mamakin ma da yake zaune dani har yanzu bai iya saki na ba, domin bana ta

ɓ

a daidai a gunsa komai nayi kuskure ne.

Tunda kin fahimci haka sai ki ci magan

in zama da shi da haƙuri, Sakina duk wanda kika ga yayi haƙuri bai ci nasara ba to ka

ɗ

an yayi, kiyi ta addu'a kina fa

ɗ

awa Allah sai kiga auren nasa ya zame miki wani sauƙi acikin zamanku, In Sha Allah gobe ina nan zuwa mu yi magana.

To shikenan yaya Umma

Allah ya saka da alkhairi ya kaimu goben lafiya.

Ameen Ƙanwata Allah ya shiga lamarinki.

Sakina ta amsa da amin tana

ɗ

an sakin murmushi, haka suka rabu tana sauke ajiyar zuciya dan taji da

ɗ

in maganganun Yaya Umma, itace macen da take iya kai kukanta gunt

a dan ta zame mata uwa da uba, domin yaya Umma macece mai kirki da sanin yakamata, su biyu ne rak mata a

ɗ

akinsu, Yaya Umma itace babbansu sai Hamza ke bi mata sannan Sakina sai sauran ƙannensu maza su uku. Mahaifinsu malami ne yana da almajirai da yake ko

yar dasu karatu wanda zuwa yanzu tsufa ya cimmasa, sai babban wansu Aliyu da Hamza sune suka cigaba da jan ragamar makarantar. Matan baba uku mamansu ce ta biyu, gidansu akwai tarbiyya sosai ba ruwansu da wayewar zamani komai nasu cikin tsari na addinin mu

sulunci suke yinsa, dan baba Malam bai yarda da boko ba shiyasa yaran maza ma bai basu damar yi ba bale matan, tun rasuwar mamansu Yaya umma ta zame musu uwa dan Sakina gidanta ta koma da zama lokacin tana budurwa har ta aurar da ita a hannunta, duk da mij

inta talaka ne dan kayan koli yake sayarwa ita kuma tana dan sana'ar cikin gida, amma suna rayuwar farin ciki dan mijinta yana da zuciya sosai basu ta

ɓ

a kwana basu ci ba, yaranta bakwai dan har ta aurar da babbar 'yarta, shiyasa duk wani abu daya shigewa S

akina duhu ita take tunkara kuma cikin hukuncin Allah duk shawarar data bata in tabi to sai ta samu mafita, ta riƙeta da muhimmanci sosai kuma da yake mijinta yana da rufin asiri tana taimaka mata sosai da abubuwa, dan Hamid yana kulawa da danginta tanan t

ana matuƙar yaba masa dan sai yayi musu alkhairi bata sani ba sai in ta ha

ɗ

u da 'yan uwanta ne suke fa

ɗ

a mata, shine ma yakai

babansu Makka, shiyasa wani lokacin inta tuna da alkhairinsa sai ta riƙa jurewa da haƙuri da halinsa, dan dama dole ne duk mugun h

alin mutum bazai rasa wani hali na kirki ba.

Haka ta fito falo ta shiga

ɗ

akin yaran sai da ta tabbatar da su baba ƙarami sun kwana, kafin tasa ƙeyar Mufeeda itama ta kwanta a

ɗ

akinta ta kashe mata wuta ta rufe mata ƙofa, sai ta koma nata

ɗ

akin tare da Ra

uda suka yi shirin barci suka kwanta, da tunani barci ya saceta bata ma san yaushe Hamid

ɗ

in ya dawo ba.

[7/1, 4:17 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Wattpad @rahmakabir

Page 4.

Hamid yana isa falon Hajiya ya sameta zaune a carpe

t tana kallon tv ga kuma kular abinci da plate a gurin, ya zauna a capet

ɗ

in cike da fara'a yana gaisheta ta amsa tare da tambayarsa aiki.

Lafiya lau Alhamdulillahi, kuma wainar kuka ci? ashe Sakina ta aiko muku da ita.

Hmmm sai da naje na

ɗ

iba da kaina

dan ƙurilla taso yi mini, wlh Sakina ta sauya hali rashin mutunci tayi mini akan wainar nan ni kuma na nuna mata ina da iko akan lamarin gidanka, yanzu muka kammala cima.

Ikon Allah Sakinar ce tayi miki haka, aiko wlh sai na ci mutuncinta.

A'a karka yi m

ata magana ka rabu da ita nasan zafin kishiyar da zaka yi mata ne yasa tayi mini haka kuma aure babu fashi. Yau ka samu leƙawa gidan su Madinar kuwa.

Nan take fuskar Hamid ta sauya domin ya tuna da tukuicin wahalar tusar da ta ba shi

ɗ

azun, sai da ya sauk

i

ɓ

oyayyen ajiyar zuciya dan ji yayi kamar maƙaƙin warin yake ji a maƙoshinsa sai yace.

Naje sai dai ban jima ba na dawo, tace a gaishe ku.

'Yar albarka muna amsawa Allah yasa dai kar tayi halin Sakina. Ni da zaka ji tawa ma daka raba musu gida kai kanka

hankalinka sai ya fi kwanciya.

Ba ni da ra'ayin raba gidan nan dan ina so yarana su tashi kansu a ha

ɗ

e, ki dai taya ni da addu'a Allah ya ha

ɗ

a kansu.

Ameen amma mai matsalar dai itace Sakina dan haka ita zaka jawa kunne.

Kayya Hajiya kina bani mamaki b

isa yadda kika

ɗ

aurawa yarinyar nan karan tsana, kuma daidai gwargwado tana yi mana biyayya bata ta

ɓ

a yin wani abu na rashin kirki ba, banda ke da kullun kike zubar da girmanki a gurinta kin bi kin saka mata ido, shiyasa yaran yanzu suke cewa uwar miji haw

an jini kuma kema kina

ɗ

aya daga cikinsu wlh.

Cewar Alhaji da shigowarsa falo kenan ya tsinkayi maganar su, ya zauna yana duban Hamid zai yi magana Hajiya ta riga shi.

Ai dama Sakina bata laifi a gunka na rasa wannan dalili da kullun kake fifita ta akan

Hamid.

Saboda ita amana ce a garemu domin mun rabata da iyayenta dan haka dole ne mu fifita ta akan namu kar mu zama masu son kanmu da yawa, ni ba irin ki bace mai ƙaramin kwakwalwa, madadin ki

ɗ

aura Hamid akan ya kula da amanar daya

ɗ

auko amma kullun kec

e ke zugashi da yawan ƙorafi akanta, yanzu da Asma ce akewa haka zaki ji da

ɗ

i ace uwar mijinta ta matsa mata.

Ya ƙare maganar yana ware idonsa akanta, Hajiya ta ce cikin ha

ɗ

e rai.

Kai kullun in ana magana sai ka riƙa kawo wasu zance daban, ai tarbiyyar d

ana bawa Asma ba irin na Sakina ba ce, ita Asma tana da biyayya da kunya amma Sakina yanzu ta fitsare kanta bata ganin girmana.

To waye ya ja? ai kece kika yada girmanki ta take shi, in banda kin zama babbar banza ki bita har gidanta ki kwashe mata abinci

n data girka bayan ta zuba miki daidai wanda zata iya baki kika raina, taya ba zata raina ki ba. Kai kuma Hamid in kasan ba zaka iya adalci ba karka fara auren nan dan ban yarda ka wulaƙanta Sakina ba.

Abba in sha Allah ba abinda ma zai faru zan yi iya ƙo

ƙ

ari na wajen kamanta adaci a tsakaninsu.

Allah ya baka iko ka kuma daina biyewa mamanku dan zata kaika ta baro.

Cewar Alhaji sai ya

ɗ

auki remote ya sauya tasha zuwa na labarai, Hajiya dai bata kuma magana ba dan tasan halin Alhaji sai ya cigaba da kwafs

a mata a gaban Hamid, daga bisani ma tashi tayi ta wuce cikin

ɗ

aki tana kwalawa Jidda kira akan tazo ta kwashe kayan abincin. Hamid kallon labaran ya cigaba da yi tare da yiwa Abba hirar company, sai wajen goma da rabi ya yiwa Abba sallama y dawo gidansa.

AbdulHamid shine

ɗ

a na farko a gidan sai Asma'u ke bi masa wacce take aure a Zaria yaranta shida, Jidda itace babbar 'yarta data ke zaune tare da su Hajiya tun lokacin data kawota yaye shikenan Hajiya ta riƙeta a hannunta makaranta da komai anan take yins

a, shekarunta sha shida dan tana SS 2 a secondary, islamiyya tana ajin sauka, daga Asma sai Kubura itama tana aure a Abuja yaranta biyu, sannan Salim autansu da yake karatu a can

ɗ

an Fodio yana matakin ƙarshe na kammala digree

ɗ

insa. Tun sadda Hamid ya aur

i Sakina su Asma suke ganin rashin dacewarsu a ganinsu gidansu 'yan boko ne taya zai aure wacce bata da ilimin zamani, shiyasa sam basa wani shiri da Sakina komai nasu basa sakata a ciki dan ko haihuwa suka yi Sakina taje baya baya take dasu dan basa sake

mata, shiyasa ma bata damuwa da lamarinsu itama ta kama kanta dan ko Kaduna suka zo sai in sun gadama sun leƙota kafin take zuwa daga baya su kuma gaisawa. Shiyasa tunda Hamid ya

ɗ

auko zancen ƙarin auren nan suke mugun farin ciki musamman ma da suka ji way

ayya 'yar boko zai aura, haka suka ƙara mara masa baya akan gwara ya ƙara ko zai samu matar bita taro, shiyasa tunda aka saka bikin suke cikin shiri dan ankon tsadadden leshi suka fitarwa Family

ɗ

insu domin so suke ayi bikin kece raini, sun ci burin yin sh

agalin zamani dangin su Dinner da su kamu da dai sauransu, shiyasa tun biki yana saura sati biyu suka

ɗ

aura niyyar zuwa dan gaba

ɗ

aya sun ƙosa ma lokacin yayi.

...

Hajiya tana shiga

ɗ

aki Asma ta kirata nan suka tattauna akan maganar bikin daga bisani Hajiy

a ta fa

ɗ

a mata abinda Sakina tayi mata, wani ashar Asma ta wulwulo tana

ɗ

aurawa da cewa.

Wallahi duk randa na shigo Kaduna ha

ɗ

uwata da Sakina ba zai yi kyau ba, dan saina ga uban daya tsaya mata da take niman ci miki mutunci.

A'a Asma ki rabu da ita nasa

n duk haushin auren nan ne yasa tayi haka, da ki

ɓ

ata ranki abanza gwara ki cigaba da shirin biki mu tusa mata baƙin ciki.

Hmmm ai Hajiya ina nan ina shiri na ƙosa lokacin zuwanmu yayi, zata ga ƙarshen rashin mutunci kuwa.

Nan dai sukai ta mayar da magan

ar daga bisani suka yi sallama.

Washe gari da wuri Sakina ta shirya yaranta kamar yadda ta saba, hatta Rauda da bata zuwa makaranta tayi mata wanka ta sauya mata kaya masu kyau saboda Hamid ya garga

ɗ

eta akan karya wayi gari yaga gidansa kaca kaca da yara

, ko kafin ya fito su Mufeeda sun tafi makaranta a motar Bus dinsu da ya siya musu driver ke kaisu, ta gyara ko ina ta saki ƙamshin turaren wuta kana ta shiga kitchen ta gyara ko ina tare da dumama masa wainarsa da kumun tsamiya data san duk in zaici

ɗ

umam

en abinci to shi yake cewa tayi shiyasa bata rabo da garin kunu, bayan ta kammala ta je tayi wanka ta saka baƙar jallabiya wacce tasha aiki da fararen duwatsu sai ta saka ash

ɗ

in hula ta feshe jikinta da turare ta fito falo dan zaman jiran fitowarsa, saita

kunna tv ta soma kallon MBC 2 da suke wani action film, Rauda kuma tana wasa da kayan wasanta akan carpet. Bayan kamar minti sha biyar sai ga Hamid ya fito cikin shirin fita, yadda ya shaƙi ƙamshin turare mai da

ɗ

i a falon yasa shi jan numfashi mai da

ɗ

i ya

sauke a hankali ya tako hartsakiyar falon, Sakina ta miƙe fuskarta ba yabo ba fallasa ta gaishe shi tare da yin gaba zuwa dinning dan ta saka masa abinci, ba musu shima yabi bayanta ya ja kujera ya zauna yana danne danne a wayarsa, nan ta ha

ɗ

a masa komai

ta sallameshi kana ta dawo falo ta zauna, bayan ya kammala karyawa ya taso ya dawo falon ya zauna yana cewa.

Jiya naji wulaƙancin da kika yiwa Hajiyata wallahi Sakina ina mai matuƙar ja miki kunne akan haka, ki shiga hankalinki in ba haka ba zan yi miki m

ummunar hukuncin da zaki dana sani.

Allah ya huci zuciyarka amma ni banyi mata wani abu ba.

Mahaifiyar tawa ce take karya ko sharri zata miki. Sakina! Sakina in kina son ki cigaba da zama dani to dole ne ki martaba iyayena dan wlh akansu zan iya rabuwa d

ake.

Kayi Haƙuri zan kiyaye In Sha Allah.

Sakina ta fa

ɗ

a idonta yana ciko da kwalla ga mari ga tsinka jaka, Hamid yayi ƙofa.

Karma ki kiyaye, ni zan fita saura na dawo anjima na tadda gida kaca kaca, kuma sakwara zaki yi mini da miyar agushi zan aiko da

kayan cefane.

To adawo lafiya, yauwa Yaya Umma zata zo anjima nace bari na fa

ɗ

a maka dan ta sanar dani jiya.

In tazo ki gaishe ta ga wannan ki bata.

Ya ƙare maganar yana zura hannu a aljihu ya zaro ku

ɗ

i ya ƙirga dubu ashirin ya miƙa mata.

Ki duba stor

e

ɗ

inku in akwai sauran shinkafa ki

ɗ

ibar mata rabin buhu, tare da sauran kayan masarufi.

Angode Allah ya ƙara riƙo da hannunka ya sada ka da Alkhairi ya ƙara bu

ɗ

i.

Ameen ya fa

ɗ

a fuska a gimtse ya wuce, da ido Sakina ta bishi ga kirki ga rashin mitunci,

yanzu banda yaya umma tasan waye shi da ba zata riƙa yarda da ita ba akan ƙorafin da take fa

ɗ

a mata nashi saboda alkhairin da yake yawan yi mata, taja guntun tsaki dan sam bai burgeta ba duk wannan abin daya ce a bata, tunda ko wace mace farin ciki da kwan

ciyar hankali take nima a gidan aurenta komin talaucin mijin, yadda take ji a ranta da Hamid zai rasa komai ya talauce amma ya dawo yana mutuntata suna zaman lafiya zaifi mata wannan daular da suke ciki ba farin ciki.

Wajen ƙarfe

ɗ

aya da rabi na rana yaya

Umma tazo, lokacin Sakina ta gama ha

ɗ

a musu girkin rana jelof

ɗ

in shinkafar manja da busasshen kifi da naman sa, sai kuma zo

ɓ

o mai da

ɗ

i data ha

ɗ

a musu, a nan falo kan carpet suka yada zango, sai da suka ci suka ƙoshi kafin suka soma hira, wanda anan Sakin

a ta ke sanar da ita abubuwan daya bayar yace a bata, yaya umma ta saki murmushi.

Hamid Zuma ne ga zaƙi ga harbi, Allah ya saka masa da alkhairi ya daidaita zamanku.

Nifa wlh yaya Hamid ya fita a aaina a yanzu na fara addu'ar rabuwa dashi in hakan shine

mafi alkhairi, nasan yara Allah yana tare dasu ko ina raye ko bana raye zasu rayu dan ƙaddarar ko wani bawa yana tare dashi.

Karki ƙara fa

ɗ

ar irin haka Sakina komin lalacewar auren nan yafi miki rufin asiri akan ace babu shi, wata macen da zata ji labarin

ki sai tace dama itace ke saboda nata munin ƙaddarar yafi naki, Allah baya ta

ɓ

a jaraba bawa da abinda ba zai iya

ɗ

auka ba sai dai bawa yayi gajen haƙuri, kuma ni bazan ce ki cibaga da zama domin yaranki ba wannan ba hujja bace, ki dai cigaba da zama a mats

ayin auren ibada ne saboda ko wani ibada yana tafe da ƙalubale, Allah bai halicce mu hakanan domin muji da

ɗ

in duniya ba, ya halicce mu ne domin mu bauta masa, dan haka ina mai ƙara jan kunnenki akan ki cigaba da juriya Allah zai duba lamarinki In Sha Allah

matsawar kin dogara a gare shi.

Sakina ajiyar zuciya ta sauke dan sosai maganar yaya Umma ya ratsata.

Shikenan In Sha Allah zan cigaba da ƙoƙarin danne zuciyata, amma wlh lamarin da matuƙar ciwo a zuciyata.

Wata rana zai zama labari In Sha Allah, yanz

u abinda nake so dake ki cigaba da bashi dukkan kulawa karki gaji, nasan kina da tsafta amma ki ƙara domin mijinki yana son haka, ki kuma kula da shinfi

ɗ

arsa sosai kinji kafin zuwan amarya.

Sosai Yaya Umma ta bata shawarwari wanda yasa Sakina ta samu ƙarf

in guiwa da jin zata iya jurewa komai domin samun kyakkyawar sakamako a gurin Allah. Sai yamma lis yaya Umma ta tafi da kayan arzikin da Hamid yace a bata.

Da dare.

[7/1, 6:52 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Wattpad @rahmakabir

Page 5.

Da dare.

Sakina bata yarda tayi wani kuskure da zai fusata Hamid ba, dan har hira suka

ɗ

an yi a falo bayan ya kammala cin abinci, daga bisani ya shige

ɗ

aki ya barta da yara, itama ta tasa ƙeyar yaran ko wanne ya kwanta a

ɗ

akinsa, kana ta kwantar

da Rauda tayi barci sai ta tashi ta shirya cikin wasu kayan barci masu kyau ta gyara sumar kanta da yake a cefe ta feshe jikinta da turare kana ta saka hijab ta yiwa Rauda addu'a sannan ta fito ta jawo ƙofar a hankali ta nufi

ɗ

akin Hamid, tun kafin ta shi

ga ta ji muryansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login