Showing 75001 words to 78000 words out of 111085 words
tunda rabona da gidan ku tun biki.
Shiyasa nake sonki ƙawata sai kinzo amma ki tawo mini da abu mai da
ɗ
i.
Uwar kwa
ɗ
ayi.
Kausar ta fa
ɗ
a tana dariya tare da kashe wayar, Madina dariya tayi itama tana jin da
ɗ
in ƙaw
ancensu, duk cikin kawayenta babu wacce ta shaƙu da ita irin Kausar sai dai kuma halinsu ba daya ba, Madina tunawa da tayi da garga
ɗ
in maman Murja akan ta
ɓ
oye sirrin abinda take yiwa mijinta yasa ta fasa fa
ɗ
awa Kausar komai da da tayi niyya, karma ta fa
ɗ
a
mata tayi hirar da Habib asirinta ya tonu dan haka tayi alƙawarin riƙe maganar ko momy ba zata fa
ɗ
awa ba tunda dai buƙatarta ta biya, ba ita ta miƙe ba sai da aka fito sallar magrib, wanda duk kasala ke damunta wanda ta bayar ko gajiyar aiki ne, kuma kusa
n kwana biyu kenan data fara jin haka ga yawan kwa
ɗ
ayi da tara yawu a baki, yanzu ma miyau ne ya
cika mata baki ta fetsar da shi a bango tana jan guntun tsaki, ita kanta ta fara gajiya da tara yawun tana so ta koyi dainawa tunda Hamid baya so. Ta shiga bay
i tayi alwala ta tayar da sallah, a lokacin ne momy ta dawo Madina data idar ko addu'ar kirki bata yi ba ta fice da saurinta cike da farin ciki dawowar momy.
*****
Bayan kwana hu
ɗ
u.
Hamid duk yayi yadda zai yi dan ganin ya ha
ɗ
u da Sakina amma abun ya ci
tura gashi company da business
ɗ
insa na motoci suna buƙatarsa, kiran da Abba yayi masa ne ya katse masa tunani ya
ɗ
aga cikin sanyin jiki suka gaisa.
Hamid duk abunda kake ka dawo kazo ka kula da harkokinka tunda har ansan in da Sakina take na tabbatar za
ta dawo da zarar ta huce.
To Abba In Sha Allah, yau dama nake saka ran dawowa, yasu Hajiya?
Sunanan lafiya, sai ka kamo hanya da wuri tunda yanzu ƙarfe tara da wani abu na safe.
In Sha Allah dama na gama shiri can gidan yayarta zani muyi magana sai na t
awo.
To madalla Allah ya tsare hanya.
Hamid yace amin kana ya kashe wayar ya miƙe tare da
ɗ
aukar jakar baya daya siya ya saka kayansa, ya fito ya sallami hotel ya shiga motarsa ya mufi gidan Jalila. Da yake ya zama
ɗ
an gida yana isa falon ya nufa ya kwan
kwasa, Ra'isa ta bu
ɗ
e tana ganinsa ta gaishe shi cikin girmamawa ya tambayeta mamanta tace tana ciki, kana tayi masa iso cikin falon ya samu guri ya zauna, ba jimawa Jalila ta fito ta zauna suka gaisa sannan Hamid yace.
Dama na zo na sanar dake zan koma y
au tunda nayi duk yadda zanyi kinƙi bayyana mini in da Sakina take, dan haka ina mai ƙara bada haƙuri a yafe mini In Sha Allah abinda ya faru a baya bazan bari ya kuma faruwa ba.
In Sha Allah nayi maka alƙawarin a cikin kwanakin nan zan dawo maka da Sakin
a da kaina, tun shekaran jiya nake fa
ɗ
a maka haka kuma bazan karya alƙawarin dana
ɗ
auka ba.
Nagode sosai Allah ya saka da alkhairi ni zan wuce a gaida Alhaji in ya shigo.
Zai ji Insha Allah Allah kuma ya tsare hanya ya saukeka lafiya.
Ya amsa da amin ka
na ya ajiye bandir
ɗ
in kudi dubu
ɗ
ari a center table.
A bawa Sakina nasan tana buƙatar ku
ɗ
i a hannunta.
Sai ya ƙara ƙirga dubu talatin ya ajiye kusa dana Sakina.
Wannan kuma a bawa yara 'yan makaranta. Nagode.
Muma mun gode Allah ya ƙara arziki.
Anty
Jalila tace shi kuma ya wuce ya bar falon, sosai ya bata tausayi dan taso ace yadda yayi kwanakin nan ace tare ya tafi da matarsa, to amma bata gama shirya Sakina ba dan tana buƙatar su shiga kasuwa tayi mata siyayya, gashi ma ya bada ku
ɗ
i akan ga
ɓ
a, dan h
aka zata yi ƙoƙari cikin kwana biyu su gama koma ta taso ƙeyar Sakina ta koma gidanta hankalin kowa duk sai ya kwanta.
****
Hamid.
Wajen ƙarfe Sha biyu ya isa Kaduna, dan haka Masallacin Juma'a ya fara tsayawa aka yi sallar Juma'a dashi kana ya nufi gi
da danya yi wanka ya sauya kaya ya fita company. Koda ya iso gida ransa in yayi dubu toya
ɓ
aci dan yadda ya barshi haka ya dawo ya sameshi ya ƙara yin ƙura.
Wato yarinyar nan bata tsaya ta gyara gidan ba ta tafi gidansu.
Ya ƙare maganar yana jan tsaki, y
ana a tsaye ya lalubo number
ɗ
inta ya kira, data
ɗ
auka sai ta rigashi da cewa.
Masoyi ina shirin kiranka sai gashi ka kirani yau ko aiki ban samu zuwa ba ina fama da zazza
ɓ
i.
Madina yanzu ya dace ace na dawo gidana na taddashi a haka? ashe baki saka an g
yara ba kika tafi gida, ina ce na ce ki
ɗ
auki 'yar aiki, wannan ai wulaƙanci ne nazo na ga haka.
Haba Hamid ina ce maka bani da lafiya kana yi mini ƙorafin gidanka, ai dama na bari in ka dawo sai muzo da mai aikin ta gyara gidan, kuma ya dace tun kafin ka
taso ka sanar dani, da ka fa
ɗ
a ai ba zaka samu gidan a haka ba.
Hakama zaki ce mini.?
To ya kake so nace maka ka rufeni da fa
ɗ
a sai kace wata 'yarka, to sannu sarkin tsafta komai aka yi maka ba kada haƙuri ka riƙa yiwa mutane mita.
Hmmm ya iya cewa sa
i ya kashe wayar gaba
ɗ
aya saboda takaici, Madina ta kuma kira yaƙi
ɗ
auka, ta kira ya kai sau uku duk bai
ɗ
aga ba sai ta tura masa da saƙo.
Beb kayi haƙuri anjima zan tawo tare da mai aikin sai ta gyara gidan, kuma nace maka banda lafiya ko kace mini ya ji
ki kaji meke damuna.
Koda ya karanta tsaki yaja ya fito zuwa motarsa ya zauna ya kira Habib yana tambayarsa ko yasan company da zai kira suzo su gyara masa gida, yace bai sani ba amma ya shiga Instagram yayi searching ba zai rasa samu ba, yayi masa godiya
suka yi sallama sai ya shiga Instagram da ya jima bai hau ba, shi sam chart bai dame shi ba sai ma daya ha
ɗ
u da Madina ne ta sabar masa da yi, cikin ikon Allah yana bincikawa ya samu nan ya
ɗ
auki number
ɗ
insu ya kira sai dai an samu akasi su a Jigawa suke
amma da yake suna da contact
ɗ
in masu irin aikinsu saboda irin haka koda ya taso suka bashi na nan Kaduna, cikin kankanin lokaci Hamid ya yi magana dasu suka ce zasu zo washe gari asabar su yi aikin, nan suka bashi bayanin komai yadda zai tura musu da ku
ɗ
insu, bayan ya gama dasu sai ya wuce sashin su Hajiya ya samu Alhaji bai dawo daga masallaci ba, ya zauna a falo yana kwalawa Jidda kira, da saura ta fito daga
ɗ
akinta tana amsawa.
Kawu sannu da zuwa ya hanya.
Lafiya lau Alhamdulillahi
Me muka dafa a g
idan?
Tuwon shinkafa miyar taushe.
Zuba mini ki ha
ɗ
o da ruwa mai sanyi.
To, mun yi zo
ɓ
o a ha
ɗ
o maka da shi.
Yauwa ha
ɗ
o dashi.
Sai ta wuce shi kuma ya gyara zamansa ya jingina bayansa a jikin kujera.
[8/9, 9:47 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®R
ahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 32.
Hajiya ce ta fito falon fuskarta
ɗ
auke da murmushi.
Hamid kasha hanya, da fatan ka dawo lafiya, Allah yasa Sakinar ta biyo ka.
lafiya lau kuma na barta zata zo tare da yayarta, na sameku lafiya?
Lafiya la
u Alhamdulillahi, amma kuwa ya dace ace ta biyo ka yadda ka
ɓ
ata kwana hu
ɗ
u a can kana biko.
Hajiya bata gama shirye shirye bane shiyasa.
Wane shiri? ita ba Amarya ba, ba sabon aure zata yi ba, kawai dai su wulaƙanta ka ne suja maka rai saboda ka kai kan
ka, shiyasa naso ka rabu da ita ta dawo da kanta, gashi satin nan yara zasu koma makaranta.
Shiyasa nake tunanin gobe In Sha Allah zanje na
ɗ
auko su ni zan kula dasu in ya so in zan fita sai su zo nan sashin.
To ba damuwa gwara su dawo
ɗ
in Allah ya kaimu
. To ya ita wannan sakaryar fa ta dawo ko tana can gidansu?
Tana can anjima tace zata dawo.
Allah ya kyauta ya kuma baka haƙurin jure halayyar matanka dan duk baka yi dace ba.
Amin Hamid yace yana jin ba da
ɗ
i a zuciyarsa, ya rasa me yasa Hajiya ta kasa
gane Sakina ba tada matsala tafi Madina mutunci, koda yake shima yana da laifi dan yawan ƙorafin daya ke kawo mata yana
ɗ
aya daga cikin dalilan daya saka ta tsaneta, kuma zai yi ƙoƙarin gyara hakan.
Sai wajen kiran sallar magrib Madina ta kira Hamid akan
yazo ya
ɗ
auketa ba zata iya dawowa da kanta ba, saboda haushi ma cewa yayi ta kwana a gida da safe ta dawo ya kashe wayarsa, can sai ga text ta turo masa.
Wai masoyi fushi kake yi dani dan Allah kayi haƙuri bana son haka, kuma nace maka bana jin da
ɗ
in jik
ina amma baka nuna damuwarka ba ko dai ka daina sona ne.?
Koda Hamid ya karanta saƙon guntun murmushi yayi.
Madina kenan ga ban haƙuri ga ban haushi.
Ya fa
ɗ
a a zuciyarsa tare da sauke gauron numfashi sai ya tura mata da reply.
Saboda jikin naki nace ki
kwana dan nima a gajiye nake bazan iya fita da mota ba, Allah ya ƙara sauƙi, amma kin sha magani, ko sai kinga likita tukuna? gobe In Allah ya kaimu in kin dawo sai muje a dubaki.
Ya aje wayar Madina murmushi tayi da ganin saƙonsa, tasan duk in tace ko y
a daina sonta ne to yakan yi abinda zai nuna yana sonta
ɗ
in, kamar zata sanar dashi ciki gareta dan momy da kanta take fa
ɗ
a mata da wuya ba shi bane yadda ta ƙara haske da kuma
ɗ
an ƙiba, sannan ga yawan zubda yuwu da kwa
ɗ
ayi, shiyasa
ɗ
azun ta siyo pt strip
taga ya nuna mata positive, amma sai ta fasa fa
ɗ
a masa dan tafi so su
kasance a yanayi mai kyau saita fa
ɗ
a, wataƙila ma har kyauta zai yi mata kamar yadda take jin labarin wasu mazan suna yi, babban tunaninta ma ya bata motar da yayi mata alƙawari.
***
D
a safe masu gyaran gidan Hamid suka zo, maza da mata kusan su bakwai, cikin kwarewa da iya aikinsu suka gyara masa gidansa har da farfarjiya suka share, sai dai
ɗ
akin Madina yace kar su ta
ɓ
a iyaka nashi dana Sakina sai na yara sannan falo da kitchen suka g
yara, nan da nan gida ya dawo hayyacinsa, ya sallame su suka wuce sai ya yi wanka tare da kiran yaya Umma ya fa
ɗ
a mata zai zo ya kwashe yara saboda monday zasu koma makaranta, ta tambaye shi Sakina yace yaya Jalila tace zata kawota cikin kwanakin nan, a ha
ka suka yi sallama sai ya shiga gidan Hajiya suka gaisa daga nan ya fito ya wuce wajen sayar da motocinsa. Sai bayan La'asar ya samu damar zuwa
ɗ
ibo su Mufeeda suka dawo gida, da ihu suka shiga falo wanda yasa Madina saurin fitowa daga
ɗ
aki tana dubansu, d
ama tun ƙarfe biyu suka shigo gidan tana mamakin ganin yadda aka gyara ko ina amma banda nata, ta shiga fargaba sosai da tunanin ko Sakina ce ta dawo, haka dai ta danne yanayin da take ji ta nunawa Ladi aikin da zata fara yi mata na gyaran
ɗ
aki, in yaso wa
she gari in Allah ya kaimu tayi mata wankin. Turus tayi ganin yaran ga Hamid ya shigo tana binsu, Hamid da fara'ansa ya ƙaraso gabanta yana cewa.
Mara lafiya ya jikin ashe kin dawo?
Eh
ɗ
azun na dawo naga gida a gyare ko mamansu ta dawo ne?
Ta fa
ɗ
a tana
dubansa, Hamid ya yi murmushi.
Wato kinsan ita ce mai gyara min gida ko, to bata dawo ba company na kira suka zo suka gyara na biyasu, yara kuma na
ɗ
auko sune saboda ranar monday zasu koma makaranta.
To waye zai kula dasu?
Allah daya haliccesu shi ne ma
i kulawa dasu, kuma ina da Hajiya ga kuma ni yarana ba zasu tagayyara ba. Karki wani damu ko kashin Rauda bazan ce ki wanke mata ba. Ke Mufeeda ku shiga
ɗ
aki ku aje kayanku kuzo muje gidan Hajiya.
Hamid ya ƙare maganar cikin ha
ɗ
e rai dan ba ƙaramin haushi
Madina take bashi ba yadda take nuna kin yaransa ƙiri ƙiri, sai ya juya ya wuce
ɗ
akinsa dan ya rage kayan jikinsa, Madina ta bishi ganin sauyawarsa ta tsaya a jikin ƙofa tana ce masa.
Nifa bawai bana son yaranka bane Hamid, kawai ban iya
ɗ
awainiyar yara
bane shiyasa.
To kema da baki iya riƙe
ɗ
awainiyar kanki ba taya zan damu dan baki yi na yarana ba. Dan haka karki wani damu sai dai ina tunanin naki yaran in kin haihu waye zai kula miki dasu? tunda baki iya kula da
ɗ
an kowa ba.
Kafin lokacin ƙila zan ko
ya, kuma kasan ina da mai aiki zata taya ni.
Hakane.
Ya bata amsa a takaice, sai ta isa gefen gadonsa ta zauna.
Beb shine baka saka an gyara mini
ɗ
akina ba banyan biya kayi aka gyara gidan.?
Saboda kin samu mai aikin da zata yi miki, niko babu mai yi m
ini ko yarana. Anjima ki shirya zamu je asibiti likita ya duba ki.
Ni naji sauƙi.
Ta fa
ɗ
a tana turo baki dajin haushin maganarsa, bata kuma magana ba shima bai yi ba har sai da ya gama shiryawa cikin jallabiya ya kalle ta sai kuma yaga ta bashi tausayi y
a koma ya zauna yana dubanta.
Menene kuma kike
ɓ
ata fuska?
To ba kai bane?
Ta fa
ɗ
a cikin shago
ɓ
a, Hamid yayi murmushi yana son wannan shago
ɓ
ar tata yace.
To shikenan komai ya wuce yanzu me zaki ci? sai na ha
ɗ
a nayi mana oder da yara, mai aikinki kuma z
ata tafi ba kwana zata yi ba ko.?
Eh mai aikin gidanmu ce momy ta bani ita anjima zata wuce in ta gama aikin.
To yayi, in kuma ta iya girki sai ta yi miki kici mu kuma mu ci a gidan Hajiya.
To shikenan tuwo nake son ci bari zansa ta girka mini, amma ina
son ice cream da cake.
Angama gimbiyar Hamid yanzu kije ki shirya kanki kiyi kyau sosai, anjima zamu je mu siya ice cream
ɗ
in tare, yanzu bari na kai yara gurin Hajiya.
Da murmushi sosai a fuskarta tace masa to har tana kama hannunsa ta manna masa kiss.
Nagode Hamid
ɗ
in Madina ina sonka sosai.
Nima ina sonki Ƙazamar Amaryata.
Allah ni ba Ƙazama bace.
Ta fa
ɗ
a tana turo baki dariya yayi ya fice yana cewa.
Wani zaki fa
ɗ
awa wannan ya yarda amma banda Hamid
ɗ
in Madina daya sanki ya wayeki kamar hanjin ci
kinsa.
Dariya sosai itama tayi ta biyo bayansa, akan idonta ya tasa ƙeyar yaran suka wuce ita kuma ta koma
ɗ
aki gurin mama Ladi.
Hamid yana shiga sashin Hajiya da yara ta fito daga kitchen saboda hayaniyarsu da ta ji, da fara'a ta ƙaraso.
Hamid wai hark
a kwaso su?
Eh bamu da
ɗ
e da shigowa ba nace su zo su gaisheki.
Hajiya ta zauna a cushing yaran duk suka zauna a carpet suna gaisheta ta amsa fuska sake har tana zolayarsu, daga bisani tace suje suyi wasa su basu guri, yaran suka fice farfajiyar gidan Haj
iya ta mayar da dubanta ga Hamid.
Kai Hamid ka kwaso yara mamansu bata dawo ba kasan dai wannan mahaukaciyar amaryar taka ba iyawa zata yi da su ba ko.
Eh dama ganin Monday zasu koma makaranta yasa da
ɗ
aukosu sannan ai yaya umma tayi ƙoƙari dasu kusan wa
ta guda fa suna gidanta, shiyasa na ce gwara su dawo ni zan kula dasu tunda Mufeeda ta iya wasu ayyukan in yaso abinci sai a riƙa girkawa damu na makaranta kuma koni zan yi musu ko na siya musu su tafi dashi in yaso Rauda sai ta zauna a nan harsu Mufeeda s
u dawo su zo su
ɗ
auketa kafin dai dawowar mamansu.
A'a ba za ayi haka ba, ina ganin su dawo nan tunda ga Jidda zata yi musu komai nima zan tayata tunda na samu lafiya, in mamansu ta dawo sa koma gidanku.
To nagode Hajiya Allah ya saka da alkhari bari naj
e na ha
ɗ
o kayan nasu.
Yauwa ka dubo har uniform
ɗ
insu in ba a wanke suke ba gobe Jidda sai ta gyarasu kafin monday.
Ai suna nan a goge dan Sakina bata barin wanki, zan ha
ɗ
o su duka.
Ai Sakina akwai ƙoƙarin tsafta ba kamar ƙazamar amayarka ba, kai wanna
n yarinya ba zata rasa kwankwame ba.
Cewar Hajiya tana ta
ɓ
e baki, Hamid yayi dariya.
Wlh kuma ƙalau take ita kuma kalarta kenan.
Aiko an samu sa
ɓ