Showing 57001 words to 60000 words out of 111085 words
tire a gabanta.
Ki ci ki koshi ki aje duk wata damuwa karki hukunta kanki da y
unwa.
Sakina bata ce komai ba tabi unarninta, saboda itama yunwar take ji dan rabonta da abinci tunna rana, kuma shima ba cin kirki ta yi ba saboda zullumin abinda zata aika ya cika mata zuciya, ba laifi taci tuwon dan ta cinye malmale
ɗ
aya, ta kora da ru
wan kunun aya, daga bisani ta miƙe da zummar kai kayan kitchen, Jalila ta kallera tana cewa.
Ke zauna ba zan saka ki aiki ba kin shawo gajiyar hanya, kuma naga baki ci naman ba, to wlh ki sani sai kin cinye wannan dana zuba miki kafin kiyi barci, dan yaji
n gyaran mutuncinki na saka a ciki, saboda ki fara tayar da koma
ɗ
a tun yau kafin ki koma.
Kai yaya ni wani gyara zanyi bayan auren ma ya isheni gaba
ɗ
aya.
Kin ma isa, ai wlh aurenki da Hamid na zobe ne babu rabuwa, sai da ya gama kwashe albakatunki kika z
uba masa yara hu
ɗ
u sannan yace ya gaji dake, aiko bai isa ba zama daram idan ma dan aure ya ƙara yake niman wulaƙanta ki to sai ya ji a jikinta, dan ba zaki koma ba sai na tabbatar da duk wani martabarki ya dawo, saboda Umma ta sanar sani abinda mijinki ya
fa
ɗ
a mata cewar yace kije gida ke kuma kika yi
ɓ
atan dabo.
Wannan karan dariya Sakina ta saki dajin maganganunta, itama Jalilar dariya tayi tana cewa.
Ai kin kyauta da kika zo nan baki ƙara gaba ba, yanzu zauna ki fayyace mini labarin zaman aurenki tun
daga farko, bance ki
ɓ
oye komai ba wanda ya dace ace kin sanar dani, in ba haka ba yanzu zan kira su Hamza nace gaki a gidana su zo su
ɗ
auke ki.
Murmushi Sakina tayi tana zama a dadduma ta jingina da bango, sai ta soma bata labarin duk wata matsala da ta
tsaya mata a zuciyarta da Hamid, har sai da ta kawo zuwa abubuwan da suka faru na auren daya ƙara dama matsalar daya faru jiya, murmushi Jalila tayi tana duban Sakina.
Duk abinda Hamid yayi miki wlh kema kina da laifi dumu dumu a ciki.
Laifina kuma anty?
Ni da kullun nake burin kyautata masa, ko dai baki gane maganar da nayi miki ba ne.
Na gane maganarki, idan Hamid yana da matsala kema kina da matsala Sakina, mijinki ga dukiya ka kyau ka ƙuriciya, me kike zaton zai buƙata ya samu a gurin matarsa? Zai bu
ƙ
aci matarsa ta zama 'yar kwalisa tamkar yadda yake, wannan yasa shi har ya hangi Madina 'yar boko ya aurenta dan zatonsa a gurinta ne ka
ɗ
ai zai samu abinda yake so.
Yaya ina iya ƙoƙari na fa, kuma komai nayi baya yaba mini sai ya kushe, abinci na ne ka
ɗ
a
i Hamid zai ci ya yaba mini.
Jalila ta shiga duban Sakina tana jin kamar ta rufeta da duka dan takaici tace.
To saboda kin zauna kanki da murfi Sakina, kin ƙunshe kanki a gida ba kya fita, ko
ɗ
an islamiyar nan na zamani ba kya zuwa balle ki ƙaro ilimin
addini dana zamantakewa, na san ba zai ta
ɓ
a haka ki niman ilimi ba, amma kin mayar da kanki kamar tsohuwa, taya duk iskancin daya
ɗ
auko ba zai ya
ɓ
a miki ba, rashin boka hauka ne ko shine rashin wayewa? Ki kalle ni da kyau ni nayi makarantar boko ne? Kin ha
ngo rashin wayewa ko duhun kai a tare dani, ina ce kune kuka samu yin primary. Kina zauna a cikin garin Kaduna amma sai kace wacce take aure a daji haba Sakina haba, mijinki yana da arzikin da baki rasa komai ba, amma kin kasa jawo shi jikinki ki nuna masa
kulawa, ki goge ki zama 'yar zamani ya gagara, dududu shekarunki nawa.
Ta ƙare maganar tana kallonta fuska a ha
ɗ
e.
[7/30, 5:03 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 25.
Anty Jalila ta gyara zama ta
ɗ
aura da
cewa.
Sakina kin ta
ɓ
a zama kin fahimci me Hamid yake so a tare dake menene in kika yi yake kushewa ki gyara, yafi son kina saka ƙananun kaya ko kayanmu na Hausawa? Yafi son kiyi kitso ko yaga kin gyara sumarki kin tufke? kina zuwa salun gyaran kai duk ba
yan wasu lokaci? yafi son Jan ƙunshi ko kiyi zanen baƙi? wasu kalar kayan barci yafi so ko in kika saka yake yabawa? Me kika fahimci yake so a jikinki da zaki jawo ra'ayinsa gareki dasu? menene in kika ta
ɓ
a masa a jikinsa kike kunna masa sha'awarsa?.
Jali
la taja fasali tana duban Sakina da tayi shuru kamar ruwa ya cinyeta, da taga ba tada alamar yin magana ta
ɗ
aura da cewa.
Lokacin da kika je
ɗ
akinsa kika tadda yana waya da budurwarsa, me ya kamata kiyi masa domin aika masa da saƙo ba tare da kin yi magan
a ba? har ki jawo ra'ayinsa gareki ya watsar da wayar da yake yi, Sakina taya bazai koreki ba kin je kin ce masa kin so ku kwanta abu gwanin takaici, dama ai in ya ganki a
ɗ
akinsa barcin kika zo, wataƙila baki yi shigar da zaki
ɗ
auki hankalinsa ba. To wai
ma ya batun gyaran breast
ɗ
inki ko kin barsu haka kamar silifas balle ya riƙa ganin tudunsu yayi sha'awarsu. Bari kiji wlh zuciyar namiji tana da saurin karaya muddin aka ce Mace tasan kanta musamman a sha'anin gurin saduwa, komai fushinsa da fa
ɗ
arsa matsa
war kin san hanyar da zaki aika masa da saƙo dolensa zai ya sauko ya zama raƙumi da akala, amma sam sam ba kida sigar kalami, ba shagwa
ɓ
a ba karairaya, ƙila ba kya gyaran da zai riƙa manne miki saboda ba kida
ɗ
an
ɗ
ano, ta yaya bazai ce ya yiwa Amarya gyara
ba, to ke ko yayi gyaran akanki ba lallai ya samu yadda yake so ba, shi da yake mafa
ɗ
aci ne ba yida rufa rufa ƙiri ƙiri yake fito miki da matsalolinki, amma da yake ke kidahuma ce sam baki hango haka ba sai kike alaƙanta haka da ya daina sonki baya ƙaunark
i. Wataƙila tsaftar da yake fadar ba kida ita yana nufin tsaftar HQ, hammata, sumarki da bakinki yake nufi bai fito fili ya fa
ɗ
a miki bane, ya jima yana miki ƙorafi in da ace kin gyara wataƙila ko auren ba zai ƙara ba, amma sam tunaninki kawai ya baki ya d
aina sonki ne ko.
Sakina hawaye taji yana zuba a kuncinta jikinta yayi mugun sanyi da zantukan Anty Jalila, dan tabbas maganganunta sun zaburar da ita da hasko mata abinda bata ta
ɓ
a kawo tunaninsu cikin kanta ba, tasan tana wanka ta shafa mai ko kwalliya
ta daina yi saboda yana kushewa, ta san tana askin private part
ɗ
inta da hammata amma bata damu da gyaran HQ ba, brush kuma in tayi na safe bata ƙara yin wani, kitso kuwa duk bayan wata
ɗ
aya take yin sabo, ita bata zuwa saloon wanke kai sai dai a gida take
wankewa tunda yana siyo musu shampo, sannan ko wankan saduwa tayi haka kan zaita tsami har ya bushe, kuma sai yayi wannan watan kafin zata kwance ta wanke, da yake bata saka relaxa haka yake cukus a cure. Jalila kallonta take yi tana murmushi dan ta tabba
tar da lamarin Sakina akwai gyara.
Ban ce miki komai ba tukuna, har sai na fito miki da sauran matsalarki a faifai har zuwa na wulaƙancin da Hamid yake yi miki, ki tashi ki kwanta nima zanje sashin Alhaji na kwanta duk da baya nan amma bana so na takura k
i, mu kwana lafiya.
Nagode Anty Jalila, ko a iya bayaninki
ɗ
in nan kin hasko mini abubuwan da ban hangowa kaina ba, Allah yasa kaimu gobe lafiya.
Cewar Sakina tana miƙewa ta na
ɗ
e daddumar ta mayar inda yake ta cire hijab ta ninke, sai ta
ɗ
auki kwanon nam
an ta zauna gefen gado ta soma ci tare da jin wani kwanciyar hankali a ranta, tabbas in har tana da matsala dole ne ta tsaya ta gyara kafin ta komawa Hamid a sabuwar Sakina, Jalila ta
ɗ
auki tiren abincin ta aje mata sauran kunun ayar da ruwa a gefe ta fice
.
****
Kaduna.
Washe gari Hamid ya wayi gari cikin wani irin yanayi na damuwa, tunda ya dawo sallar asubahi bai iya komawa barci ba, har wajen misalin ƙarfe takwas na safe da kyar ya miƙe ya samu yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya shadda, ya fito fa
lo ya samu yaran sunyi jugum jugum kamar basu da lafiya ko tv basu kunna ba, tausayinsu ne ya shiga bin garkuwar jikinsa ya ƙarasa ya zauna yana miƙawa Rauda hannu cike da murmushin yaƙe a fuskar, taje ya
ɗ
auke ta, a lokacin ne duk yaran suka gaishe shi ya
amsa yana cewa.
Mufeeda kije ki ha
ɗ
awa su Baba ƙarami ruwan wanka suyi, sannan kema kiyi tare da Rauda ku shirya zamu je wani guri yanzu.
To tace masa sai taje ta amsa Rauda suka wuce
ɗ
akin su Yakub sai da ta ha
ɗ
a musu ruwan wanka tace Yaƙub ya cu
ɗ
a bab
a ƙarami in sun gama su saka kaya masu kyau, daga haka ta fito ta shiga
ɗ
akinta ta ha
ɗ
a musu ruwan wanka, sai da ta fara yiwa Rauda kafin ta fito da ita sannan ta koma tayi nata, Mufeeda yarinyar akwai kaifin hankali dan duk yadda Mamansu take yi musu ta s
ani dan haka shirya Rauda bai bata wuya ba dan har parmpers ta saka mata, suka shirya cikin shadda doguwar riga su Yaƙub kuma wani yadi suka saka suka fito Hamid yana cewa.
Yauwa yaran Abba, kun saka turare ko?
Gya
ɗ
a masa kai suka yi suna cewa eh sai yac
e su wuce suje su karya su dawo, a lokacin ne Madina ta fito cikin shirin fita aiki dan tun
ɗ
azu ogansu ke kiranta akan ta fito da wuri saboda akwai program
ɗ
in da zata yi ƙarfe tara kuma live ne shirin, ta dakatar da Hamid da cewa.
Barka da safiya Beb.
Tace fuskarta cike da murmushi tamkar wani abu bai faru ba jiya, Hamid juyowa yayi bai ce mata komai ba saboda yanayin shigar ta ya tabbatar da aiki zata, ta ƙaraso har gabansa ta rungume shi kana ta yi masa kiss a goshi, su Mufeeda suna ganin haka suka fi
ce gaba
ɗ
aya a falon, Madina tace tana murmushi.
Farin masoyi wai har yanzu fushi kake yi dani ne? Shiyasa fa jiya na baka damar ka huce ban zo
ɗ
akinka ba, ni dai dan Allah kayi haƙuri komai ya wuce, yanzu zanje aiki ana jirana ka bani key motata na tafi d
a ita tare da ku
ɗ
in breakfast
ɗ
ina dana lunch. Da dare kuma me zan dafa mana mu ci.
Ta ƙare maganar tana tsureshi da ido, Hamid ya saki guntun murmushi yana cewa.
Ai na riga na gama magana akan zancen motarki na fasa baki ita, maganar girki kuma zaki iya
dafawa kanki duk abinda kike so akwai komai a kitchen, ki sani ko a mafarki bana fatan sake cin girkinki daya nima hallakani, sannan batun breakfast da lunch shima zaki iya dafa duk abinda kike so ki tafi dashi, bazan jure kashe miki ku
ɗ
in abinci ba bayan
na wadataki da kayan abinci a gidana, ga 1k ku
ɗ
in mota nasan zai isheki kije ki dawo.
Ya ƙare maganar yana zaro dubu
ɗ
aya ya aje mata akan center table ya juya zai wuce, Madina da bata iya riƙe hawaye nan da nan ta soma zubar dasu tana cewa cikin raunin
murya.
Beb karka hukuntani da laifin da bani na aikata maka ba, barin Sakina gidan nan ban da masaniya bai kamata fushinta ya shafeni ba, ni duk abinda ya faru jiya iya gaskiyata na fa
ɗ
a, bazan amsa maka zanyi abinda nasan bazan iya ba. Dan Allah ka kula
dani da soyayyarka kamar yadda ka
ɗ
aukar mini alkawari kafin muyi aure.
Hmmm yace yana girgiza kai ya fice abinsa ko waigota bai yi ba, Madina zama tayi a cushing ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka, bata ta
ɓ
a zaton Hamid zai iya juya mata baya b
a har haka, tasan yana sonta amma kuma yana bata wuyar sarrafashi, kiran da ya shigo wayarta yasa ta saita kanta ta
ɗ
auko wayar a cikin jaka taga daga gurin aiki ne, yatsine fuska tayi taji duk bata da wani kuzarin fita amma dole ta miƙe ta gyara gyalenta
ta fice, ita da tayi aure tana ganin ta taka wani matsayi zata hau motar kanta ba ruwanta da napep amma ashe Hamid romon baka kawai yayi mata, ji tayi auren ya fara sire mata tun ba a je ko ina ba ya fara nuna mata halinsu na maza, ita kam data san haka za
i yi mata da bata aure shi ba. Koda ta isa ta sallami mai napep kafin ta shiga ciki ta aro farin ciki ta ya
ɓ
a a fuskarta ta shiga tana fara'ar dole ga yunwa tana ji, amma ta bari in gun gama program
ɗ
insu zata je wajen cin abincin office
ɗ
in nasu na karya.
Hamid rastuarant suka je da yaran suka karya da lafiyayyen abinci, daga bisani ya kaisu super market suka
ɗ
iba abubuwan da suke so kana suka dawo gida, yace su jirashi yana zuwa, sashin su Hajiya ya leƙa ya samu duk suna falo ya gaida su suka amsa, daga
bisani ya cigaba da matsa yatsunsa yana sonyin magana yana shakkar Abba, Hajiya ce ta kauda shurun da cewa.
Ya ƙarfin jikin naka?
Da sauƙi Alhamdulillahi.
Masha Allah ya kwanan yaran da fatan babu wata matsala.?
Lafiya lau suke, amm dama nace bai dace
a bar su a gida su ka
ɗ
ai ba shine nace zan ha
ɗ
osu da kayansu sai su cigaba da zama anan har zuwa sadda Sakina zata dawo, saboda gidan ba kowa Madina ta tafi aiki nima zan fita nawa aikin.
Hamid kace zaka kawo su nan? Haka kurum su nima ƙarasani da hayani
ya, har yanzu bana jin da
ɗ
in jikina ga yawan ciwon kai, ni bazan iya da hayaniyarsu ba wlh, ranar Asabar da suka zo kamar zan yi hauka saboda surutun da suka dinga sakani, dan haka ka barsu acan ai Madina ba da
ɗ
ewa zata yi ba, ko dama tana kaiwa yamma a gu
rin aikin ne.?
Haba Hajiya ai saiki shiga
ɗ
aki ki basu guri nan falo suyi wasansu.
Cewar Alhaji, Hamid ma ya ƙara da cewa.
Kiyu haƙuri In Sha Allah zan ja musu kunne, ita Mufeeda da Rauda su zauna
ɗ
akin Jidda, Yaƙub da baba ƙarami su zauna a
ɗ
akin kusa
dana Jidda.
Hamid wlh bazan iya ba Jidda ma ba lafiya ce da ita ba balle ta jure
ɗ
awainiyarsu, riƙon yaran nan dole sai mahaifiyarsu, kaje ka nimota duk inda take ta dawo ta riƙe yaranta. Itama da yake ta sakawa zuciyarta baƙin kishi ta kama hanya ta tafi
, ai kome ake yi mata ta zauna kodan 'ya'yanta, ta tafka rashin hankali wlh..
Abba kasa baki Hajiya ta yarda ta zauna da yaran nan, na tabbatar Sakina ba zata
ɗ
auki lokaci ba zata dawo kuma kaga inna barsu a gida Madina bata zama sannan bazan ta
ɓ
a yarda t
a yi musu abinci suci ba.
Hamid wannan matsalar nake ta maka hange amma baka ji ba, Sakina yarinya ce mai haƙuri amma sai da kayi yadda ka tunzurata tabar maka gidanka, ya kamata ace kana raga mata kodan yaranku amma idonka ya rufe, dan haka gashi ba aje
ko ina ba kasan matsayarka, Madinar da kafi so kake wulaƙanta Sakina akanta ta nuna maka ƙiri ƙiri ba zata riƙe maka yara ba, ga mahaifiyarka da tafi kowa nuna tafi sonka itama tace ba zata riƙe ba, dan haka wannan ya zama babban darasi a gareka, ni bazan
tsaya
ɓ
ata bakin tambayar meya ha
ɗ
aku ba domin nasan laifin naka ne, shawara
ɗ
aya ka
ɗ
iba yaran nan ka kaisu gidan yayarta Umma ina ganin nan ne ka
ɗ
ai mafitarka, kuma za a riƙe maka su da amana, iya abinda zan iya ce maka kenan.
Abba yana gama fa
ɗ
ar haka
ya miƙe ya fice daga falon gaba
ɗ
aya, Hamid sadda kansa yayi ƙasa yana jin kamar ya fasa kuka, idan Madina tayi masa haka ita nata kishi ne, amma ita Hajiya me yayi mata ace yaransa ba zata amshe su ba, sai dai in tsanar Sakinar ne ya shafesu, yana matuƙar
kyautata mata ko dan wannan yaci ace ta taya shi kula dasu, maganar Hajiyar ne ya katse masa tunani.
Nifa bana ce bazan riƙe yaranka bane kana sane da jiyan nan aka sallamomu har yanzu ban dawo cikin hayyacina ba, bazai yuwu ina lalla
ɓ
a lafiyata ba ka kaw
o su su ƙara mini wani damuwar, kamar yadda Alhaji ya fa
ɗ
a ka kaisu gidan Umma tunda sunyi hutu, alabarshi ko sati
ɗ
aya suka yi sai ka dawo dasu nan, nasan lokacin na samu lafiya sosai, ko kuma ƙila Sakinar ta dawo magana ta ƙare.
Shikenan bari na kaisu c
an
ɗ
in.
Yauwa ka kuma daina damuwa