Showing 108001 words to 111000 words out of 111085 words
waya, da sassarfa Sakina ta isa ta rungumeshi tsam a ƙirjinta dan niman kunya da mance inda suke tayi, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana jin wani kwallar farin
ciki yana barazanar saukowa daga idonta, Hamid ne yayi ƙoƙarin raba ta da jikinta suka tsaya kallon juna cike da yanayi na musamman, ko wanne da tunanin da zuciyarsa ke zuwa masa, shi dai Hamid tsantsar tausayin Sakinan yake ji daga cikin ransa, ita kuma t
santsar damuwa da ganinsa cikin rashin kuzari take yi, itace ta katse shurunsu da cewa.
Lafiya tun safe ina kira baka
ɗ
aga ba wlh na shiga cikin yanayin damuwa mara misaltuwa.
Ki kwantar da hankalinki Sakinar Hamid gani a gaban na dawo, ko baki fa
ɗ
a ba y
anayin da kika tarbeni ya gamsar dani damuwar da kika yi dani, bana jin da
ɗ
in jikina ne kuma nayi busy sosai yau a office da fatan keda yarana duk kuna lafiya.
Yayi maganar yana murmushin yaƙe, itama murmushin ta mayar masa kana ta tuna da abinda ta aikat
a na rungumeshi a farfajiyar gidan da tayi saita sunne kai tana cewa.
To Alhamdulillahi tunda Allah ya kawo mini kai gida lafiya, muje ciki ka watsa ruwa sannan kaci abinci kasha magani, amma meke damunka haka?
Baya wuce Maleria, me kika dafa mana.
Tuwo
n shinkafa miyar agushi yaji gamda da naman kai.
Tana fa
ɗ
a cike da farra a fuskarta, hannunta ya kamo suka fara tafiya.
Shiyasa nake matuƙar sonki saboda kin san duk abinda nake muradi, na tabbatar yanzu zanji na warke daga yanayin da nake ji na sabbin s
alonki, gashi kinyi kyau Masha Allah kin zama
ɗ
aya tamkar da dubu Sakina.
Ka daina ko
ɗ
ani haka mana aikina ne dana kula da kai tamkar kwai.
Dakatawa yayi da tafiyar da yake yi itama dole ta tsaya dan ya kama hannunta, suka kalli juna Hamid ji yake tamka
r ya ha
ɗ
iyeta.
Wai dama haka nake a gunki amma a baya kika barni ina ta garari, dan Allah Sakina ki cigaba da bani irin wannan kulawar karki gaji dani domin ke ce farin cikina, In Sha Allah ni kuma zan mayar dake sarauniyata sai abinda kike so zanyi.
Sak
ina ji tayi kamar ta shige jikinsa ta rungume shi amma ganin a waje suke yasata jansa suka wuce ciki ba tare da tace masa komai ba, shima bai mata musu ba suka shiga ciki, yara duk suna
ɗ
akinsu dan da wuri suka kwanta saboda yadda suka ga mamansu ba walwal
a, Sakina saida ta kai
ɗ
akin Hamid ta bu
ɗ
e ta shiga dashi ciki ta jingina shi jikin ƙofar ta shiga cire masa ma
ɓ
allin rigarsa suna kallon juna cike da tsantsar shauƙi, Hamid kasa haƙuri yayi ya tallabo kuncinta ya ha
ɗ
e bakinsu guri
ɗ
aya ya shiga aika mata
da zazzafar saƙo itama tana mayar masa, a takaice a wannan daren sun shayar da kansu wani irin danyan zuma mai tsananin zaƙi da wuyar misali, dan duk da Hamid yana cikin alhinin rabuwa da Madina amma fa Sakina ta rage kaso saba'in a cikin
ɗ
ari na damuwarsa
, dan ya tabbatar Sakina ce cikon addininsa kuma yasan a hankali in tana bashi irin wannan zazzafar ƙaunar zai manta da rayuwar da yayi da Madina.
**
Washe gari Hamid kafin ya fita aiki sai da ya fara zuwa gidansu ya samu Abba a
ɗ
akinsa, bayan sun gaisa s
ai yayi jim yana tunanin ta yadda zai fa
ɗ
awa Abba ya saki Madina, Abba ya kalleshi da kyau.
Akwai magana a bakinka meke faruwa.?
Abba jiya na saki Madina saki
ɗ
aya, bisa laifin daya cancanta ace na rabu da ita.
Da ido Abba yake binsa bai iya ce masa kom
ai ba bisa ga yana son gamsasshiyar bayani, Hamid baiyi ƙasa a guiwa ba ya cigaba da koro masa bayanin dalilinsa na sakin har ya kai ƙarshe, Abba ya sauke ajiyar zuciya.
Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a tsakaninku, na gamsu da bayaninka domin Allah
ba abin wasa bane duk wanda ya ce Allah bai isar masa ba to tabbas tun a duniya zai ga sakamako. Gaskiya lamarin yarinyar ya girma sosai tunda har ta iya aikata haka wanda tsantsar rashin tarbiyya ce da kuma rashin jagora na kwarai, dan haka na goyi da bay
anka akan wannan hukunci sai dai ina mai ƙara jan hankalinka akan wannan ya zama izina a gareka da masu tunani irin naka, Sakinar daka raina gashi itace alkhairi a gareka, ni bazan ta
ɓ
a hanaka ka ƙara aure ba amma kasan a ina zaka nima auren, wacece yariny
ar? ya gidansu yake? wani tarbiya gareta? kayi kyakkwar bincike akanta kafin a kaiga auren.
Gaskiya ne Abba kuma In Sha Allah na
ɗ
auki darasi sosai akan aurena da Madina, wanda kuma ya zama izina a gareni kuma na
ɗ
auki hanyar yin gyara koda a nan gaba.
T
o Alhamdulillahi daka fahimci haka, Allah yayi muku albarka.
Cewar Abba yana murmushi, Hamid ya amsa da amin kana yayi sallama da shi ya fito ya wuce aiki, dama saida ya fara gaisawa da Hajiya kafin ya isa
ɗ
akin Abba. Koda Hajiya ta samu labarin sakin Mad
ina a bakin Abba ba ƙaramin farin ciki tayi ba sai dai ta
ɓ
oye hakan a gaban Abban, tace ai Hamid ma ya haƙura da ƙara wani auren tunda Sakina ta yi hankali.
[8/27, 4:28 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 4
4.
Sai da aka yi mako guda kafin Hamid ya sanar da Sakina ya rabu da Madina, sai dai bai gaya mata dalilin ba rabuwarsu ba itama bata nima ta sani ba face addu'a da fatan Alkhairi data yi musu. Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin natsuwa da kwanciyar hank
ali.
Madina kuwa har office take binsa akan ya yafe mata amma Hamid yayi buris da ita, tasan Hajiyarsa ce ka
ɗ
ai zata iya saka baki ya mayar da ita amma kuma ta lalata alaƙarsu da kanta, da ace ta riƙe Hajiyarsa da muhimmanci kamar yadda suka nuna mata soy
ayya tun farko to da tabbas in tabi ta hannunta Hamid sai ya maida aurensu. Abbansu kuma bai bata fuska ba balle taje gunsa, yanzu ne ta gane Momynta ta taka rawa sosai akan alalacewar aurenta, dan da bata bi wasu hu
ɗ
ubobinta ba da tabbas tana zaman lafiya
a gidanta, yanzu ne ta gane ba gata tayi mata ba face ta cutar da ita ne, wannan ne ya haifar da rashin jituwa a tsakaninsu, wanda Madina gaba
ɗ
aya ta
ɗ
aura laifi mutuwar aurenta akan momy, ita kuma Momy tana ƙoƙarin son fahimtar da ita aurenta da Hamid ba
alkhairi bane, hakan yasa Madina ta samu kanta a cikin damuwa wanda hakan ya shafi aikinta bata iya mayar da hankali shiyasa aka bata hutun garga
ɗ
i, ita kuma ganin haka yasa ta shirya ta koma gurin yayarta Aisha dake Abuja. Tun tana lissafin Hamid zai mai
da aurensu kafin ta fita idda har tazo ta fita idda ba labarinsa, hakan yasa ta sadaƙar da cewa ta rasashi kenan har abada, saboda tabi duk hanyar da zata bi bata samu nasara ba, hatta abokinsa Habib yayi mata ƙoƙari amma Hamid ya kafe yaki saurarenta, Kau
sar ƙawarta ko tana nan da tsohon cikinta tana zaman lafiya da mijinta saboda ta saka aure ibada ne a cikin ranta, Madina tayi dana sani sosai da cizon yatsa dan tasan ta yiwa kanta illa na barin nagartaccen miji. A nan Abuja manema sun fara damunta sai da
i har yanzu ba wanda ya kwanta mata domin har gobe Hamid ne a zuciyarta.
Su Asma sun samu labarin mutuwar auren Madina, ita kam bata yi wani murna ba bisaga halin da take ciki a yanzu, domin mijinta yanata shirye shiryen ƙara aure har an kai sadaki, bata
ta
ɓ
a zaton duk wata mace haka take ji ba in za a ƙara mata kishiya ba sai yanzu, haƙiƙa ta jinjinawa Sakina da irin juriya da haƙurin dabta yi da
ɗ
umbin cin kashin da suka yi mata, lallai aka ce ciwon 'ya mace na 'ya mace ne sai yanzu ta gane haka, dan sos
ai auren mijinta ya gama karya garkuwar jikinta ya kashe mata baki duk wannan rashin mutuncin da masifa ta nimeshi ta rasa, Hajiya ma bata ji da
ɗ
in auren mijin Asma ba dan abun da ciwo amma haka ta dinga bata haƙuri tana bata misali da Sakina, akan haƙurin
data yi gashi ya zame mata riba, Kubura kam tunda taji mijin Asma zai ƙara aure ta ƙara shiga hankalinta.
****
Sakina tana zaune ita da yara a falo Hamid ya fito daga
ɗ
akinsa ya ƙaraso falon ya miƙa mata takardar visa da komai ta amsa tana dubansa, fusk
arsa cike da murmushi yake cewa.
Sati mai zuwa In Sha Allah zamu tafi Umara tare.
Wani irin tsalle Sakina tayi ta rungume shi ta shiga zuba masa godiya, Hamid ya jayeta daga jikinsa yana dubanta.
Kin cancanci fiye da haka Sakina domin kece hasketa, haƙu
rinki ne ya jawo haka.
Allah ya saka da alkhairi yasa kafi haka ya ƙara maka bu
ɗ
i na alkhairi, ya kare ka daga sharrin masu sharri ina alfahari da kai Hamid nagode.
Sakina ta fa
ɗ
a tana matsar kwallar farin ciki, Hamid lakace hawayenta yayi yana cewa.
Je
ki shirya muje mu yiwa yara siyayya dan a gidan Hajiya zamu barsu, saboda zamu yi kusan wata a can mu huta sosai.
Da sauri ta koma
ɗ
aki dan Hamid bai ta
ɓ
a fita da ita ba irin haka suyi siyayya a tare. Sakina shiga tayi na musamman na kece raini, koda ta f
ito sai da ta sha hotuna gurin Hamid kafin suka tafi da yake yanzu Rauda itama sun sakata makarantar su Mufeeda. A babban super market suka yada zango wanda suka fito suka jera sai suba ƙamshi suke yi gwanin sha'awa, suka shiga suka fara
ɗ
iban duk abinda s
uke so, Sakina ta isa gurin kayan kwalliyar mata taga wani tabarau nan ta
ɗ
auka ta saka a idonta sai ta juya tana cewa Hamid.
Ya ka ganni?
Kinyi kyau irin sosai
ɗ
in nan.
Yayi maganar yana ha
ɗ
e babban yatsarsa da manuniya, ta saki murmushi ta cire gilas
ɗ
in ta saka cikin siyayyarta taji a ranta daga ranar zata fara amfani da glass, lokacin da Hamid ya nufi
ɓ
engaren kayansu na maza yana dubawa ita kuma tana
ɗ
ibar nata danasu Mufeeda, sai kawai taji anyi mata sallama a bayanta, da sauri ta juya dan muryar b
a zata manta me ita ba, Madina ce cikin shigar atamfa da gyale tayi kyau sosai sai dai ta
ɗ
anyi rama, cikin sakin fuska Sakina tace.
Hajiya Madina ya gida.
Lafiya lau Alhamdulillahi, dama ina son ha
ɗ
uwa dake na baki haƙuri akan abubuwan da suka faru a ts
akaninmu.
Haba ai babu komai ya wuce.
Nagode ki gaida yaran.
Zasu ji ta bata amsa kana suka yi sallama ta cigaba da siyayyarta Madina ma ta
ɗ
iba wasu turaren da take so, koda taje biya aka ce mata anbiya mata tasan Hamid ne dan taga lokacin da yayi maga
na da mutanen, suka saka mata a leda ta amsa ta nufi titi ta tari napep ta wuce gida, satinta
ɗ
aya kenan da dawowa daga Abuja domin cigaba da zuwa aikinta, dan hutun da suka bata ya ƙare harta ƙara da nata, ganin suna ta yi mata barazanar zasu koreta gaba
ɗ
aya yasa ta dawo tare da kar
ɓ
ar ƙaddararta na rashin Hamid. A hanya Sakina take cewa Hamid taga Madina a cikin super market yace shima ya ganta basu dai yi magana ba.
Abban Mufeeda, Madina tayi sanyi sosai har ce mini tayi wai nayi haƙuri akan abinda tay
i mini.
Dole ta nina gafararki dan ta cutar dake ai, Allah yasa mu dace.
Daga haka suka yi shuru. Sakina dai tun ha
ɗ
uwarta da Madina abin ya tsaya mata a rai take ganin koda Hamid bai mayar da ita ba gaba zai iya ƙara aure, kuma bata san waye zai
ɗ
auko m
ata ba ita dai dazai mayar da Ƙazamar Amaryarsa da yafi mata, ko ba komai kowa yasan matsayinsa duk da tana kishinsa sosai amma ba zai rufe mata ido ta hanashi aikata abinda Allah ya bashi damar yi ba, yanada ku
ɗ
i da komai kuma yasan da
ɗ
in mata biyu nan ga
ba zai iya ƙara auren, hakan yasa Sakina ta samu Hamid da maganar, amma ƙiri ƙiri ya nuna baya ra'ayi duk da bawai baya son Madina bane kawai halinta ya tsana, tunda kuma ya gwasale Sakina bata ƙara kawo masa maganar ba har suka bar ƙasar zuwa ƙasa mai tsa
rki. Sabon amarci suka fara kamar ba zasu dawo ba, a taƙaice sai da suka samo
ɗ
an Saudiya dan da ƙaramin shigar ciki Sakina ta dawo gida. Anan ne ta soma laulayi ga rashin bawa Hamid ha
ɗ
in kai a gado, wannan ne dalilin daya saka shi fara tunanin wani auren
dan shi mutum ne mabuƙaci kuma bai yarda da zina ba, hakan yasa shi fara tunanin Madina dan yasan ƙila zuwa yanzu ta dawo hayyacinta tasan tayi ba daidai ba, bai yi ƙasa a guiwa ba yaje ya samu Abba da maganar ya nuna masa yana son mayar da ita ne duba da
ya fahimci ta yi nadama, Abba ya goya masa baya yace Allah ma muna yi masa laifi ya yafe mana balle a tsakaninmu 'yan Adam, kuma daya je a auro wacce bai sani ba gwara Madina daya tabbatar ba zata kuma aikata kuskuren data yi a baya ba, bayanin Abba shine
ya ƙarawa Hamid ƙarfin guiwa, baibi takan Hajiya ba dan yasan ba zata ta
ɓ
a yarda ba ya barta taji labarin a bakin Abba. Hamid bai
ɓ
oyewa Sakina ba kuma ta nuna amincewarta duk da a cikin ranta tana tsananin jin kishinsa, musamman yanzu da tasan mihimmanci
n sa a rayuwarta ga aurensu a yanzu yafi na baya da
ɗ
i, amma haka ta zage ta mara masa baya dan daya
ɗ
auko mata wata tazo ta farraƙa musu zaman lafiyarsu gwara ya auro ƙazantarsa ta san darajar raƙumi yayi nesa da ƙasa, a yanzu Madina ba zata gwada mata kom
ai ba dan ta fita nesa ba kusa ba a gurin Hamid.
A cikin wata guda aka yi maganar aka sake
ɗ
aura auren Hamid da Madina ya biya sadaki, Madina kamar zata yi hauka dan murna. A washe gari ta tare a sabon gidanta da tuntuni Hamid ya gama gyaransa ya rufe. Ta
soma rayuwa ita ka
ɗ
ai ba zancen 'yar aiki dan tayi alƙawarin koyan komai da kanta hatta girki ta mayar da hankali ta koya duk da har lokacin bata iya ba, Hamid da kansa yace ta samu mai aiki tace ita ba zata samu ba zata koya aiki da kanta sannan ma in ya
yarda zata riƙa zuwa Sakina tana koya mata girki dan tana so ta iya, Hamid yace ta dai nima wani gurin da ake girki ta koya baya son damuwa, bata yi masa musu ba haka ta samu online class na girki ta shiga sannan tana yawan kiran Kausar ko taje gidanta ta
fa
ɗ
a mata yadda ake yin girki da gyaran gida, ƙazanta dai tana ta
ɓ
awa sai dai ba kamar na da ba, in tayi kuskure Hamid yana fa
ɗ
a mata tana ƙoƙarin gyarawa, kuma a yanzu tana ƙoƙarin gyara alaƙarta da Hajiyarsq duk da har gobe bata sake mata ba, tsakaninta
dasu Aama ba mai zuwa gun wani kadaran kadahan, a gurin Sakina ce kawai take samun tarba mai kyau dan sosai take so su zauna lafiya tana yawan zuwa gunta suyi zumunci, ita Sakina bai fi sau biyu taje gidanta tare da yara ba amma ita ko yafi a ƙirga.
Loka
cin da Sakina ta ƙara haihuwar Namiji mai suna Salihu, to da Madina aka yi shagalin suna har tana gayyatar abokan aikinta, sunyi komai cikin girma da karamci duk da bata samu sakin fuska a gun su Kubura ba amma hakan bai dameta ba tunda a yanzu ba tada mat
sala dasu. Sannan itama tana da
ƙaramin cikinta wanda take fatan ta haifeshi taga jinin Hamid a tare da ita, tana mugun jin zafin kishin Sakina sai dai a yanzu tana controlling da daidaita tunaninta, kuma ta daina kaiwa momy ƙorafin Hamid dan bata son wata
matsala, abokiyar shawarta a yanzu Kausar ce ƙwarya, wacce kuma tana bata shawarar kwarai kuma tana ganin nasara akan duk shawarar data bata.
Hamid ya samu kwanciyar hankali sosai ga iyalinsa har wani ƙiba yayi, kuma a tsakanin matansa yana ƙoƙarin yi mu
su adalci, duk da Madina tana ta
ɓ
a ƙazanta amma haka yake haƙuri da ita ganin tana ƙoƙarin gyarawa, babu yadda ya iya tunda Allah ya jarabceshi da auren ƘAZAMAR AMARYA yasan hakan zai zama labari watarana.
Ƙ
arshe.
Alhamdulillah!
Alhamdulillahi da Allah y
a bani ikon kammala wannan littafi lafiya, Allah yasa za muyi amfani da darasin da ke ciki ya bamu ladansa, kuskure dake ciki Allah ya yafe mana yasa mu gama da duniya lafiya.
Ina mai miƙa
ɗ
umbin godiya a gareku masoya wannan littafi daga mutanen WhatsApp
, Wattpad, Facebook dama sauran kafar sada zumunta inda littafin nan yakai, haƙiƙa nasha addu'o'i da
ɗ
umbin yabo a gareku, Allah ya saka muku da alkhairi ya ha
ɗ
amu a Aljanna ma
ɗ
aukakiya. Ina matuƙar ƙaunarku Allah ya bar zumunci.
Ina