Showing 72001 words to 75000 words out of 111085 words
amarya.?
Kai dalla ana maganar girkin arziki kana kaw
o nata, ai wlh ko a mafarki bana tafan na kuma cin girkin Madina, In Sha Allah in dai Sakina ta dawo to dolen Madina ta je makarantar koyan girki, dan bazan ta
ɓ
a yarda da girkin masu aiki ba.
Hamid kenan a dai kiyaye adalci kar kuma yanzu ka juyawa Madina
baya ka koma gurin uwargida dan na san halinka.
In Sha Allah ba zan kuma aikata kuskuren baya ba.
To Allah yasa.
Hamid yace Amin kana suka cigaba da tattaunawa a tsakaninsu.
Hamid daya koma gida bayan sallar Ishai,
ɗ
akin Madina ya wuce domin yayi alƙa
warin gyara alaƙarsu kafin dawowar Sakina, dan ya
ɗ
auki niyyar kamanta adanci a tsakaninsu. Madina tana kwance lamama akan gado abin duniya ya isheta ga
ɗ
aki kaca kaca ga jibgin kayan wanki data aje a gefe bata kwashe ba, Hamid yana tura ƙofa tsamin
ɗ
aki y
a fara yi masa sallama, haka ya daure ya Shiga da sallama, cikin sauri Madina ta tashi ta zauna tana dubansa, ya sakar mata murmushi yana cewa.
Da girman kujerarki gimbiya Madina to na kawo kaina mu shirya.
Madina sai hawaye dan farin ciki gaba
ɗ
aya ta ba
yar da aikin malam ne ya fara kama Hamid tunda gashi ba aje ko ina ba ya kawo kansa, sai ta shago
ɓ
e fuska ta soma cewa.
Bayan ka daina sona.
Taya zan daina son ki Madinar Hamid, kawai dai ke
ɗ
in ce bakya jin maganata yanzu, ji
ɗ
akinki yadda ya koma kamar
ba amaryar wata guda da kwanaki ba.
Madina ta juya tana kallon
ɗ
akin ita kanta tasan ta hargitsa shi dan akwai akwati biyu data saukesu tana
ɗ
ibar kayan ciki ta aje a gefen gado bata ma rufe ba balle ta mayar dasu mazauninsu, Cikin shago
ɓ
a take cewa.
To
ai nace maka ni ban iya aikin gida ba amma baka yarda ba, ni dai dan Allah ka samar mini 'yar aiki.
Ya zanyi dake dole na samar miki domin bazan jure ganin gidana a hargitse ba, sai ki nimo mai kirki amma fa banda girki dan wlh dole kije ki koyi girki ki
riƙa yi mana.
Wayyo da
ɗ
ina, Dagaske ka yarda zaka
ɗ
aukar mini 'yar aiki.?
Dawasa zanyi miki zancen? sai dai ban yarda wata ƙazama ta gyara mini
ɗ
aki ba ta dai tsaya a iya sashinki da kuma falo da kitchen.
Nagode farin masoyi Allah ya saka da akhairi.
Madina ta fa
ɗ
a tana isa gareshi ta rungumeshi, sai dai tsamin daya ji a jikinta ya sashi saurin tureta yana cewa.
Ina ganin ƙila sai an nima maiyi miki wanka ko? Madina kinji yadda jikinki ke hamami anya kina wanka mai kyau kuwa, ga sumarki nan duk ya har
gitse ke baki yi kitso ba ba ki kuma gyara ba.
Kai Habib Allah nayi wanka tun safe, ina ga kaina ne ke tsami dan tun biki yake a haka.
Allah ya kyauta da amala kinci sunanki ƘAZAMAR AMARYA, award ya rage na baki kawai.
Ya fa
ɗ
a yana 'yar dariya, murgu
ɗ
a
masa baki tayi tana cewa.
Allah ni ba ƙazama bace kawai dai ni nace maka ban iya kula da gida ba kuma a hankali zan koya.
Ai har kanki baki iya kula da shi ba balle gidan, ni bari naje nayi wanka ina zuwa.
To in ka fito zamu je muci abinci a waje.
Ya z
anyi dake dole mu fita tunda gidan a hargitse yake ni duk kyankyani ma ya cikani.
Ya fa
ɗ
a yana ficewa, da harara tabi bayansa tana jan guntun tsaki.
Da sannu zanyi maganika domin yanzu ne na kama hanyar data dace dani.
Sai ta shiga kawar da kayan
ɗ
akin
tana mayar da abubuwan da suke ba a muhallinsu ba.
....
Washe gari da wuri Hamid ya bar gida yace aiki zai fita bai fa
ɗ
a masa in da zashi ba, har mota ta rakashi dan jiya dai sun raya daren amma fa sai da Hamid ya litasta tayi wanka ta wanke baki dan wlh
ji yayi ba zai iya kusantarta ba sai ta gyara jikinta. Bayan ya wuce ta koma cikin gida ta shiga kiran momynta, koda ta
ɗ
aga sai tace ta turo mata Ladi mai aikinta tazo gidanta ta gyara mata shi zata barshi a bu
ɗ
e kafin ta dawo aiki har girki tayi mata me
da
ɗ
i, momy tace zata turota nan Madina ta bata labarin sauyawar Hamid, ba ƙaramin da
ɗ
i itama taji ba tace In Sha Allah magani ya fara aiki, Madina dai dariya tayi dan tasan maganin matar nan da momy tasa ayi bai yi aiki ba sai na malamin da suka je da Mam
an Murja, tace ta samar mata yar aiki
ɗ
an yace ya amince momy tace tunda masu aikinta mutum biyu ne to Ladi zata so ta cigaba da aikin anan sai suyi mata biya mai kyau.
Amma yace baya son mai kwana.
To ai ba damuwa Madina In ta gama miki aiki sai ta dawo
nan ta kwana tunda dama anan take da zama.
Cewar momy, Madina tayi mata godiya kana suka yi sallama. Madina bayan ta yi shirin aiki gidan Maman murja ta tafi suka yi magana, sosai mama Murja ta ƙara ko
ɗ
a aikin malam tace ai haka aikinsa yake ci nan da na
n, tace mata in ta dawo zata shigo haka duka rabu ta tafi aiki.
*****
Kano.
Da wuri Sakina suka bar gida da kayanta kala biyar a cikin ƙaramin jaka, saloon Ra'isa ta fara kaita nan fa aka shiga gyaran kan Sakina tana jin abun sabo a gareta, anan ne taji
wasu mata suna maganar kyan maganin BOJUWA HERBAL'S BY SURAYYA. Ɗayar tana cewa.
Wlh tunda nayi amfani da kayanta nayi bye bye da cutar sanyi, ga kuma sauran kayan gyara dana sha ya saukar mini da ni'ima da
ɗ
an
ɗ
ano mai da
ɗ
i, ke wlh tun kafin na fara sani
n aikinsu a jikina na tabbatar da na samu sauyi, ranar Alhaji har da sambatu yayi mini ya dinga saka mini albarka, shiyasa ba wasa na ƙara kama kayan BAJUWA HERBAL'S dan ance siyan na gari maida ku
ɗ
i gida kuma tabbas ni na mayar da kudina har naci riba.
T
o Maman Nusaiba dame dame suke sayarwa ne nima naje a dama dani.
Suna kawo Saiwowin sanyi, da maganin sanyi. Saiwowin dahuwar kaza, dafaffiyar gimbiyar kaza. Silky kola na musamman. Tsumin sababi. Hakkin daka gangariya. Gumba special. Gaban ayu. Dukkan S
aiwowi da kayan daga Chad suke zuwa da su. Ga number
ɗ
inta ki tuntu
ɓ
eta in kin shirya kuma ganinsu akwai sauƙin rahusa. 08032773332 Surayya HALIN YAU.
Nan Sakina ta saka musu baki a cikin hirar tana cewa.
Aiko nima na gwada kayanta kuma naji sauyi sosai
a jikina tun kafin me gida ya shaida, ya kamata kema ki gwada.
Nan fa suka cigaba da tattaunawa har aka gama mata gyaran, Ra'isa ta sallami mai saloon suka yiwa matan nan sallama suka tafi gidan mai gyaran jiki. Suna isa Ra'isa ta barta anan ta wuce maka
ranta.
Wajen ƙarfe goma sha
ɗ
aya motar su Hamid ta sauka a ƙofar gidan Anty Jalila, dan da motarsa suka yi tafiyar shi da Yaya Ali a gaba sai Umma da Hamza a baya, suka sauka suka shiga buga gate, mai gadi ya bu
ɗ
e musu dama tuni Jalila ta sanar dashi da z
a suyu baƙi, ya shiga gaishe su Umma ce tayi gaba domin ta fara sanar da Jalila sun zo, sai ta sameta a falo cikin shiga ta alfarma, tana ganin Umma ta miƙe.
Lale mutanen Kaduna, sannunku da zuwa. Ina sauran tawagar naku dan nasan ba zaki zo ke ka
ɗ
ai ba.?
Umma dariya tayi tana cewa.
Na shigo in fara sanar dake tukuna kafin su shigo da har da mijinta muka zo.
Ehhh lallai abin babba ne to kice musu su shigo.
Jalila ta fa
ɗ
a tana komawa
ɗ
aki ta saka babban gyale ta fito, suma a lokacin suka shigo duk suka
zauna aka fara gaishe gaishe, daga bisani Ali yace.
Kin kyauta Jalila da abinda kika yi mana, baba yace zaki zo ki same shi.
Murmushi tayi tana cewa.
Ai abinda kuka kasa yi ne ni nayi muku dan haka bani da laifin komai mutuncin yarinya na kankaro mata.
To ina Sakinar?
Cewar Hamza, Hamid kam ya baza ido yaga ta ina zata fito shi duk ya ƙosa ma ya ganta, bai ta
ɓ
a zato wai dama yana son Sakina har haka ba sai yanzu, maganar Jalila ce ta dawo da shi hayyacinsa tana cewa.
Sakina bata nan tunda taji kunce z
aku zo tace wlh bazata biku ba dan bata shirya komawa gidan Hamid ba, shine ta tafi gidan wata aminiyata ta
ɓ
oye.
Wannan ai zancen banza ne, aiko dole ki fito da ita dan ba zamu bar garin nan ba sai tare da ita.
Cewar Ali, Umma tace cikin
ɓ
acin rai.
Hab
a yaya Jalila ya zaki biye mata ai da baki barta ta fita ba.
Sakina fa ba yarinya bace ku kyaleta ta yankewa kanta hukuncin data ga ya dace, ita ka
ɗ
ai tasan gashin ƙumar da take kunsa a gidanta, dan haka ku barta ta yi abinda ya dace akanta na tabbatar ha
r yanzu bata gama hucewa bane shiyasa, kuma nima ina ta bata baki har ta sauko ta amince ta koma gidanta.
Dan Allah da son maikin Allah ki kirata ta dawo na bata haƙuri, wlh Hamid
ɗ
in data sani a baya ba shine a yanzu ba nayi mata alƙawarin sauyawa.
Cewa
r Hamid cikin damuwa.
[8/8, 5:25 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 31.
Jalila tayi murmushi tace.
Bari na kira kuji.
Nan ta kira ƙawarta dama kuma sun gama ha
ɗ
a komai
ɗ
azun, data
ɗ
aga tace ta ha
ɗ
ata da
Sakina, sai matar ta miƙa mata Jalila tace.
Sakina ga su fa sun zo tafiya dake dan Allah kiyi haƙuri ki yarda ki koma
ɗ
akinki.
Yaya Jalila ki fa
ɗ
a musu wlh bazan koma gidan Hamid yau ba dan zuciyata bata gama warkewa daga baƙin cikin daya ƙunsa mini ba,
shiyasa na za
ɓ
i zuwa gidanki dan hankalina ya kwanta tunda ko naje gida mayar dani zasu yi ya cigaba da ƙunsa mini baƙin ciki, kuma ai da bakinsa yace na tafi gida sai ya nimeni in da yuwuwar ya cigaba da zama dani.
Yuf Hamid ya amshe wayar daga hannun Ja
lila data saka handsfree suna jin maganganun Sakina, Ya shiga magana cikin damuwa.
Wlh Sakina na sauya kuma a ranar damuka dawo daga asibiti dama nayi niyyar nace karki tafi gida muyi sulhu, amma sai na tadda kin tafi, dan Allah ki dawo mu tafi yaranmu da
ni muna buƙatarki.
Hamid kenan.
Abinda Sakina ta iya fa
ɗ
a kenan ta kashe wayar. Hawaye taji yana bin kuncinta wanda bata tantance na farin ciki bane ko akasinsa.
Hamid jiki ba kwari ya koma ya zauna yama kasa magana, suma shuru suka yi suna tunanin zucc
i, Jalila ta miƙe ta shiga fito musu da abinci dan Sakina ta girka sai Ra'isa ta taya ta, data gama ta zubawa Umma ta kama hannunta suka koma
ɗ
akinta, Hamid ƙamshin abincin daya ji ma ya tabbatar Sakina ce ta girka, Hamza da yaya Ali suka bu
ɗ
e ciki suka kw
ashi girki Hamid kam bai iya ci sosai ba saboda damuwa.
Jalila bayan umma ta kammala cin abinci ta korowa Umna bayanin komai, tace kuma nan da sati daya In sha Allah Sakina zata dawo, duk ta fa
ɗ
a mata plan
ɗ
insu akan su
ɗ
an bawa Hamid wahala yadda gaba ba
zai sake sha'awar yace taje gida ba ko ya cigaba da yi mata wulaƙanci, umma ta gamsu sosai dan itama ba zata mance marin da Hamid yayiwa Sakina a gabansu ba, ya dace ya kar
ɓ
i hukunci yasan muhimmancinta, dan haka bayan sun fito tace wasu yaya Ali ya kamat
a su juya dan bada shirin kwana suka zo ba, Hamid yace shi ba zai koma ba sai da Sakina, dan haka har tasha ya kai su ya
ɗ
aukar musu drop ya biya ku
ɗ
in mota ya juya cikin gari. A hanya Ali yake cewa.
Ai gwara Sakina ta wahal da shi ko yasan muhimmancinta.
Umma tayi murmushi sai ta basu labarin yadda suka yi da Jalila, duk suka amince suka ce gwara a gwara kansa bazai sake yi mata riƙon sakainar kashi ba. Hamid wani super market yaje ya siya ƙananun kaya riga da wando kala uku da kuma sauran kayan buƙatars
a ciki harda turare da da mai, tafiya ce da ba shiri dan bai yi tsammanin kwana ba amma tunda abu yazo a haka dole ne ya yi shiri dan yana so ƙafarsa ƙafar Sakina. Daga nan ya wuce wani hotel mai kyau ya kama
ɗ
aki, sai da ya samu natsuwa kana ya kira Hajiy
a yayi mata bayanin komai yace ta sanar da alhaji, Hajiya ta ja guntun tsaki.
Da alama Hamid so kake ka zama shanyayye, gaba
ɗ
aya ka sama sususu sai kace wani mara mafa
ɗ
i, tunda an san ga inda take kuma kaje tace ba zata dawo ba, to ba sai ka rabu da ita b
a in ta gaji zata dawo dan kanta, wannan ai ka bata ƙofar rainaka ne.
Hajiya nine nayi mata laifi dan haka yana da kyau na gyara kuskurena, ni dai ina so kiyi mana fatan Alkhairi, duk yadda ake ciki zan sanar dake ki gaida Abba.
To shikenan tunda haka ka
za
ɓ
arwa kanka Allah ya kyauta sai anjima.
Cewar hajiya cike da takaici kana ta kashe wayar tana jan guntun tsaki, shi kam Hamid ya saba da haka bai wani da mu ba, shi ya sara me Sakina take yiwa Hajiya ta tsaneta har haka, sai yanzu ya ƙara hango Hajiya
ma ta bada gudun mawa a matsalar dake tsanninsa da Sakina, kuma lokaci yayi da zai gyara kuskurenta ya riƙa riƙe sirrin gidansa a zuciyarsa ko hakan zai kawo daidaito da maslaha a zamantakewarsu. Nan ya kira Madina yake sanar da ita yayi tafiya zuwa Kano k
uma zai kwana biyu, sai tace ita ba zata iya zama ita ka
ɗ
ai a gidan ba dan haka gidansu zata koma, bai yi mata musu ba dan yasan ko yace karta je ba saurarensa zata yi ba, to kawai yace mata sai ya kashe wayar ya tura mata da ku
ɗ
i dubu ashirin, Madina tana
ganin alart ta saki murmushi tana jin farin cikin yadda in ta yiwa Hamid magana baya yi mata musu, sai ta kira Momy akan Ladi 'yar aikinsu ta zauna ba sai tazo ba itama gida zata zo anjima saboda Hamid yayi tafiya, momy tace mata to kana suka aje wayar mo
my tasa a gyara mata
ɗ
akinta.
Bayan ta bar wajen aiki gida ta dawo ta ha
ɗ
a kaya kala biyu da tarkacenta cikin wata jaka sai ta fito dashi falo ta aje, ta fita gidan Maman Murja ta bata cikon dubu hamsin da malam yace ta bata ta
ɗ
aura da cewa.
Wlh naga sa
uyi sosai game da Hamid gaskiya aikinsa Masha Allah, yanzu zanje gidanmu nayi kwana biyu saboda yayi tafiya, inna dawo zan zo muje domin ina so ayi mini aiki tsakaninsa da iyayensa, dan so nake sai naci Uwar Hajiyarsa son raina na nuna mata ni ba kanwar la
sa bace.
Da kyau ta wajena lallai kin hau kan layi sosai, ai wlh Hajiyarsa ba tada kirki dan ba ƙaramin takurawa Sakina tayi ba, kuma kinga yanzu ba Sakina dole kanki zata dawo ta saki a gaba.
Ai ni nafi ƙarfinta dan wlh ba ƙaramin shiri zanyi akanta ba,
sai na nuna mata ni ba irin Sakina bace kidahuma.
Wannan gaskiya ne ki nuna mata da bambanci yadda take hawan jini ke kuma ciwon ido zaki zame mata.
Fa
ɗ
i ki ƙara, ina godiya sosai maman Murja naji da
ɗ
in ha
ɗ
uwa dake.
Cewar Madina cike da farin ciki, nan
ta
ɓ
ata lokaci suka sha hira daga bisani tayi mata sallama akan sai sunyi waya ta fito ta tafi, tana shiga gida ta
ɗ
auki jakan kayanta ta fito ta tayi gaba, tun tana hanya
Kausar ke kiranta amma bata
ɗ
aga ba sai da ta isa gida ta samu momy bata nan, dan h
aka gado ta haye ta kwanta kana ta bi kiran Kausar, bayan ta
ɗ
aga sun gaisa Madina tace.
Ni nayi fushi kinata waƙar zaki zo amma shuru tun biki baki leƙo ni ba.
Shiyasa ashe kwana biyu kike basar dani ko chart nayi miki sai kin gadama kike amsani, wato m
iji da
ɗ
i har kin fara sauya hali, to da
ɗ
in abin nima da mijina balle naji haushi haka.
Ke banza meye na koro wannan zancen sai kace kin ha
ɗ
iyi radio, yaushe kike gida dan daga gurin aiki zan zo gidanki saboda Hamid yayi tafiya ina gida.
Dan yayi tafiya s
aiki koma gida? lallai kina juya Hamid son ranki, me kika taka haka ne.
Babu abinda na taka sai zallar soyayya da nake bashi, kuma kinsan gidan ba kowa shiyasa nace gwara na dawo gida.
To in hakane gobe zanje gidan yayar Habib
ɗ
iyarta ta haihu daga can z
an biyo nan gida, kinga na gaishe da momy