Showing 24001 words to 27000 words out of 111085 words
/>
an
yan kajin a freezer, bawai dan yayi niyar ma siya mata bane sai da Habib yace dole ya siya dan haka ake yi, ya zauna a falon ya kira Sakina a waya, data
ɗ
auka yace tazo falo itama Madina ya kirata, ba jimawa duk suka fito, Madina ta sauya wani shiga na les
hi riga da siket tayi kwalliya sai kyallin amarci take yi ko gyale bata yafa ba, Sakina kuwa harta saka kayan barci ta kwanta dan haka hijab kawai ta
ɗ
aura a saman kayan ta fito, duk suka samu guri suka zauna Madina ta zauna gefen Hamid tana cewa.
Sannu d
a zuwa Babyn Madina nayi kewarka sosai yau.
Ta fa
ɗ
a tana shafa gefen sajensa, Hamid ya saki murmushi.
Nima haka Madinata kin ƙara kyau sosai fatan kina lafiya.
Gya
ɗ
a masa kai tayi tana kallonsa fuskarta cike da murmushi, Sakina tana zaune tana kallon ik
on Allah bata ce uffan ba, koda Hamid ya kalleta
ɗ
aure fuska yayi yana cewa.
Ke kuma saboda mugun hali kin kasa ce min komai ko to kanki kike yiwa. Dama na kiraku ne na ha
ɗ
aku domin kusan juna da kuma sharru
ɗɗ
an da zan kafa muku. Sakina ga Madina nan aman
a aka bani ke ce zaki tayani dan ganin na yi adalci a tsakaninku, Madina ga Sakina yayarki ce dan haka ki bita abinda baki gane ba na gidan ki tambayeta. Bana son rikici bana son tashin hankali ku ha
ɗ
a kanku, sannan batun raba kwana na yanke yin kwana bibb
iyu ga duk mai girki In amarya ta gama wata
ɗ
ayan da kika bata, sannan ban yarda da raba girki ba duk me miji ita zata yi girkin duka gida, sai dai ke Sakina dole zaki yi haƙuri kina yin karin safe kullun saboda Madina tana zuwa aiki ke kina gida , kuma ki
na yin abincin yara na makaranta kinga sai kiyi duka, sannan girkin rana ma ki yi keda yara ita in ta dawo ta san me zata ci, girkin dare kawai nake nufin duk me miji zata ha
ɗ
a tayi duka gida, bana son kazanta ku riƙa gyaran min gida, Sakina aikin dai zai
fi yawa a gunki tunda Madina bata zama.
Hamid tunda Madina ta iya kar
ɓ
an kwana to zata iya
ɗ
auke duk hidimar gidan nan, nima na huta ai ba agogo nake ba da zaka cika mini aiki saboda son kai, wlh bazan yi komai a ranar girkinta ba ta gyara gida ta yi duk
abinda mace keyi na gida, batun karin safe da abincin rana kowa yaci nashi na daren me girki sai ta ha
ɗ
a tayi, wannan shine adaci.
Cewar Sakina data katse masa magana tana kawar da kai gefe.
Wato ban isa da ke ba kenan ko? ina bayani har kin samu zummar
saka mini baki ba tare da na baki damar yin magama ba ko, Sakina me kike son zama ne? Duk take taken iskancinki wlh bazan
ɗ
auka ba tom.
Hmmm tace masa bata kuma magana ba, Madina sai a sannan tace.
Beb mai zai hana ka samar mini 'yar aiki mai girki da k
uma gyaran gida, kaga zan samu sauƙin abubuwa in yaso kowa yaji da kansa tunda ta nuna ba zata taya ni ba.
Madina a tsarin gidana da ra'ayina babu zancen 'yar aiki, ke zaki yi girki, batun gyaran gida ki yi ƙoƙarta kiyi dan gaskiya ban yarda da ƙazanta ba
, kuma na isa da gidana dole ne Sakina tayi abinda na tsara.
Beb nifa...
Karki yi mini gardama tashi ki wuce
ɗ
aki ina zuwa.
Hamid ya katse Madina da zata yi magana, bata ƙara cewa komai ba ta miƙe rai a jagule ta wuce, tana mamakin Hamid yadda yake fa
ɗ
in ba zai
ɗ
auki mai aiki ba, ita fa wlh ba zata iya da wahalar gidansa ba dan ba
ɗ
awainiyar gidansa yasa ta aureshi ba.
[7/11, 8:40 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 12.
Hamid ya miƙe yana duban Sakina.
Ke kuma ki cigaba da cika mini ciki duk ranar dana tashi amayar dake ba zaki ji da
ɗ
i na ba, kuma wlh ina kan maganata baki isa ki sauya mini tsarin dana gindaya muku ba. Ga kaza nan kici ke sa yara ki tabbatar da safe kin ha
ɗ
a mana abin kari mai kyau.
Yan
a kaiwa nan a maganarsa ya wuce zuwa
ɗ
akinsa, Sakina tayi gunyun tsaki wanda ya tsaya a iya le
ɓ
enta.
Wlh bazan yi ba kayi duk abinda zaka yi.
Sai ta miƙe ta
ɗ
auki ledar kazar sai da taje kitchen kafin ta tsaya ta duba kana ta saka shi a freezer, ita sam
bata son irin gassasun kazan nan, kuma suna da soyayye ga kuma wasu
ɗ
anye a frigde, a ganinta dama bai
ɓ
ata ku
ɗ
insa ba ya siya shida amaryarsa kawai, ta gama abinda zata yi ta fito ta koma
ɗ
aki ta kwanta. Hamid sai da yayi wanka ya kimtsa kansa kafin ya ta
fi falon Madina, suka ci tsire da drinks tare da kallo a tv, sai wajen sha
ɗ
aya tukuna suka dawo
ɗ
akinsa, a ranar nan suka kwana cike da soyayya.
Da safe.
Sakina da wuri ta kimtsa yara 'yan makaranta suka tafi, sai ta shiga gyaran
ɗ
akunansu, tana tsaka d
a moping
ɗ
in
ɗ
akinta sai taji maganar Hamid, da sauri tazo ta murza key ta koma bakin gado ta zauna, Hamid fuska a ha
ɗ
e ya fito saboda rikicin da suke yi da Madina akan tun
ɗ
azun yake godo da ita tayi wanka taƙi yi wai sanyi take ji, ƙiri ƙiri wankan tsark
i ya gagareta tun asubahi wai sai gari ya waye zata yi karshe juya masa baya tayi ta koma barci, har yaje Masallacin asubahi ya dawo tana kwance, Hamid da haushinta ya koma barci. Da kuma ya farka yanzu ya samu idonta biyu tana danna waya yayi mata maganar
wanka wai zata yi amma sai ta karya ita yunwa take ji, bai kuma yi mata magana ya fito falon ya ganshi caf sai ƙamshi yake tashi, yasan aikin Sakina ce sai ya wuce gurin dinning yaga wayam ba komai a kai, ya girgiza kai tare da wuce wa kitchen nan ma ya s
amu komai naf kamar ba ayi girki ba, ya fito a fusace yana kwalawa Sakina kira tana jinsa tayi banza dashi harya ƙaraso ƙofar
ɗ
akinta ya mur
ɗ
a yaji a rufe, sai ya bu
ɗ
e murya yana cewa.
Sakina ina breakfast
ɗ
inmu dana ce ki ha
ɗ
a mana, me kike nufi dani ne?
wlh zanyi matuƙar sa
ɓ
a miki dan na gaji da iskancin da kike yi mini.
Sakina ta miƙe ta iso bakin ƙofar
ɗ
akin ta tsaya tana cewa.
Madina ita ce ta dace ta dafa muku abinda zaku ci, dan tun jiya ka mari girkin dana ce zanyi muku na sati
ɗ
aya, wlh Hamid ba
zan amsa girki ba har sai ta gama wata
ɗ
ayan dana baku.
Haka kika ce ko.?
Eb haka nace.
To mu zuba ni da ke.
Sakina bata tanka masa ba ta koma ta cigaba da moping
ɗ
inta, Hamid rai
ɓ
ace ya koma
ɗ
akinsa, Madina ta matsa gefen gado tana shirin fetsar da m
iyon daya cika mata baki, Hamid ya daka mata tsawa.
Kar ki kuskura ki soma zuma mini miyau a bangon
ɗ
aki, wlh bazan
ɗ
auki wannan ƙazantar ba, maza ki tashi ki fita kije can
ɗ
akinki kiya ba dai a nan ba.
Ya ƙare maganar yana nuna mata hanyar ƙofa, Madina
da wani irin kallo ta bishi sai ta sauko daga gadon ta shiga toilet
ɗ
insa ta zubar da miyan ta kuskure baki ta fito ta tsaya tare da kama ƙugunta.
Hamid nice fa Madina ko idonka ya rufe ne da kake niman yi mini tsawa, to gaskiya ba a yi mini haka karka ƙa
ra daka mini tsawa, ohhh saboda Sakina ta kunno maka masifa shine zaka zo ka sauke a kaina to ai bani nakar zomon ba.
Da tsananin mamaki yake kallonta dan tayi maganar ne cike da tsiwa tana zare ido kamar tana yiwa
ɗ
anta fa
ɗ
a, Hamid yasa hannunsa a kirjin
sa alamar nuna kansa.
Ni kike fa
ɗ
awa haka?
Zan fa
ɗ
a maka fiye da haka matsawar kana kaifafa harshenka akaina, haka kurum kwana na biyu da zuwa gidanka ka fara
ɗ
aga mini murya, me nayi maka da zaka
ɗ
auko fushin matarka ka huce a kaina.
Ta ƙare maganar ci
kin yanayin son yin kuka, sai ta wuce ta
ɗ
auki gyalen data yane kanta ta ra
ɓ
a ta gefensa ta wuce ranta a ha
ɗ
e, Hamid baice mata komai ba dan ba ƙaramin mamaki ta bashi ba yadda take yin magana kaitsaye mai cike da garga
ɗ
i, girgiza kai yayi ya sauke ajiyaya
r zuciya ya wuce ya fara shirin fita aiki. Bayan ya kammala ya fito ya shiga
ɗ
akin Madina nan ya samu ta fito daga wanka ta saka wata doguwar riga wanda ya fito da surarta sosai, saida yaji ta burgeshi amma sai ya kawar da abin da yaji ya kalleta cikin sau
ke kansa.
Haba Madina fushin ne har yanzu? To kiyi haƙuri bana son kina
ɓ
ata fuska, yanzu ga wannan number
ɗ
in na wani rastuarant ne dana saba yin oder a gunsu, ki kira ki sanar dasu duk abinda kike so zan tura miki 20k nasan zai ishe ki.
A lokacin ne ta
ɗ
an saki fuska tana cewa.
To ai kaine kake yi mini fa
ɗ
a shiyasa nayi fushi.
Ta fa
ɗ
a tana turo baki, murmushi yayi dan duk in tana yi masa shago
ɓ
a burgeshi take yi, sai ya isa gareta ya rungumeta yana cewa.
Bazan sake ba, amma ki daina zuba miyau a bang
o bana son haka dan Allah, da fatan kinyi sallah.
Ta gya
ɗ
a masa kai alamar tayi, sai yayi mata kiss a goshi ya raba tsakaninsu yana cewa sai ya dawo, hannu ta
ɗ
aga masa tana murmushi.
Bye my Hamid.
Kanne mata ido yayi yana murmushi sai ya juya ya fita,
bai bi takan Sakina ba yayi ficewarsa sai dai taji ƙugin fitar motarsa, hakan bai wani dameta ba dan tasan halinsa zai yi fiye da haka ma, ayyukanta ta gama ta samu ta watsa ruwa tabi lafiyar gado dan ta huta.
Madina bata yi wani oder ba fitowa tayi ta sh
iga kitchen ta isa gefen inda kayanta suke da komai yake sabo, ta
ɗ
auki abin suya ta dawo ta duba inda aka aje kwai ta fasa guda shida ta yanka albasa da koren tattasai ta soya shi, kana ta ha
ɗ
awa kanta tea mai mugun kauri ta cika sugar yanda take so, sai
ta
ɗ
auki biredi da taga saura, ta jerasu a tire ta fito dinning ta cika cikinta tsaf kafin ta mayar da kayan zuwa wajen wanke wanke, ta fito abinta zuwa falo ta zauna tana chart. Wajen goma da mintuna su Asma suka shigo suka sameta a nan main falo, tana ga
ninsu ta saki murmushi suka ƙaraso ciki suka zauna tare da gaisawa sai Kubura tace.
Gaskiya kina burgeni komai naki cikin sauƙi har kin fara fitowa nan.
Wannan ai shine wayewa Kubura ko kin mance Madina da iliminta.
Cewar Asma data bata amsa, Madina tac
e cikin murmushi.
Ban da
ɗ
e da karyawa ba nace bari na zauna na shaƙi iskar nan falon, ya Hajiya da Abba fatan duk suna lafiya.
Alhamdulillah lafiya lau, dama mun zo yi miki sallama ne anjima duk zamu koma garin mu. Ina Uwargidan take ne ko ta fita?
Waya
sanin mata tunda ta gama yiwa yayanku rashin mutunci ta kulle kanta, rabona da ita tun jiya da dare.
Ai ta saba yi masa haka, yanzu dai in ta bata masa rai nasan ke zaki faranta masa, dan Allah ki kula mana da yayanmu.
Karki ji komai ai ina sonsa dan ha
ka dole ne zan kula da shi.
Sun ji matuƙar da
ɗ
in maganarta sai suka
ɗ
an ta
ɓ
a hira daga bisani suka yi sallama akan sai sunyi chart ko waya, da ido ta rakasu har suka fice tana kwafa.
Da yake na auri yayanku ne dan kawai na ƙare da wahalarsa ko, to zanyi
maganin wannan shisshige mini da kuke yi, nasan duk na munafurci ne, da ai kafin ya aure ni Sakina kuka sani.
Ta fa
ɗ
a a zuciyarta tana cigaba da dubar wayanta. A ranar da dare Hamid ne ya shigo musu da abincin dare da ya yi musu oder, bai bi takan Sakina
ba dan ko yaran ma bai gansu a falo ba bai kuma nime su ba,
ɗ
akinsa ya wuce ya kimtsa sai ya nufi wajen Madina dan yau a
ɗ
akinta zai kwana ba zai yarda da ƙazanta ba dan yadda ya bar
ɗ
akin haka ya dawo ya same shi ba shara balle a gyara shinfi
ɗ
ar gadon, ya
saba Sakina kullum ita ke yi masa da ya dawo zai samu
ɗ
akin yana ƙamshin turare, sai da ya karka
ɓ
e gadon da kansa ya gyara sai ya saka air freshner,
ɗ
akin ya
ɗ
au ƙamshi kafin ya fito ya sameta a falonta tana kallon tv.
Washe gari.
Kamar yadda Hamid ya b
awa Madina dubu Ashirin dan ta siya abinci jiya yau ma haka ya bata, dan baya so ya
ɗ
aurawa hajiyarsa aikin
ɗ
awainiya dasu, saboda duk mutane sun watse ba mai tayata aiki sai Jidda ita kuma tana zuwa makaranta, shiyasa koda ta tambaye shi Sakina tana basu
abinci yace eh kawai dan kar yaja maganar tayi tsawo. Yau har jikin mota Madina ta raka shi ya wuce suka rabu cike da kewar juna. Sakina tana jin fitarsa ta fito ta cigaba da aikinta, Madina ta shigo ta samu tana goge Centre table da fara'a Sakina ta
ɗ
ago
tana cewa.
Amaryar Hamid ya baƙunta?
Madina kallonta tayi sama da ƙasa kana taja tsaki ta wuce abinta tana yatsine fuska, da sakin baki Sakina ta bita tana mamakinta ko da yake ba abin mamaki bane tunda wanda take zama danshi shine ya fara wulaƙantata ya
nuna bata da daraja dole itama ta
ɗ
auki hanya, amma tayi da 'ya zata nuna mata itama ta iya rashin mutunci dan ba zata
ɗ
auki rashin kunya ba domin ta girme mata, tana gama aikinta ta shiga
ɗ
aki ta kwanta sai ta kira yaya Umma, nan suka
ɓ
ata lokaci suna ma
gana wanda duk haƙuri yaya Umma ke bata, duk da ma bata fa
ɗ
a mata komai dake faruwa ba, dan tayi alƙawarin danne damuwarta har sai ya kai wani matakin daya fi ƙarfinta ne kafin zata fa
ɗ
a mata, kuma in tace mata ga irin hukuncin data
ɗ
auka akan Hamid na ƙin
yin girki fa
ɗ
a zata yi mata, shiyasa ta bar maganar a zuciyarta.
Madina kuwa tea ta ha
ɗ
a tasha da cincin da diblan
ɗ
inta na gara da aka kawo mata, sai ta bi tafiyar gado ta kwanta ta yi barci.
Wajen sha biyun rana Sakina ta fito ta
ɗ
aura sanwar tuwon sa
mo da miyar ku
ɓ
ewa busasshe da zata yi musu tun daga rana har dare, bayan ta yi talge sai ta
ɗ
aura sanwar miya ta samu guri ta zauna dan dama ta saba haka in tana girki har sai ta gama take fita daga kitchen, a lokacin ne Madina ta shigo kitchen
ɗ
in
koda t
a ga Sakina sai ta kawar da kai ta wuce gefen kayanta, ganin kayan jiya data
ɓ
ata an aje mata a gurin ba a wanke ba, sai taja gunyun tsaki ta ƙara
ɗ
auko wasu masu kyau ta aje, tazo ta
ɗ
ibo kwai guda shida ta kunna wayarta ta soma kallon video
ɗ
in yadda zat
a ha
ɗ
a kwai, sai da ta dafa guda uku kafin ta fasa uku ta yanka wa
ɗ
annan data dafa ƙanana a cikin ruwan kwai ta yanka albasa da tarugu guda
ɗ
aya tasa maggi da curry a ciki ta juya kamar yadda take kallon video, wata baturiya ce ke yi tana bayani da turanci
, sai ta aje wayar ta kunna gas
ɗ
inta dan tana da nata itama ba ruwanta dana Sakina, ta soya wannan kwan kamar yadda matar ta nuna a video
ɗ
in, ta zuba a plate sai ta
ɗ
auki coke drink ta fice falo ta zauna tana ci tana sauraren waƙa music tare da ka
ɗ
a kai,
bayan ta kammala ta
ɗ
aura ƙafa akan center table sai ta cigaba da chart, a haka ne Jidda ta shigo riƙe da kula a hannunta, ta ƙaraso gunta ta gaisheta kana ta miƙa mata tana cewa.
Hajiya ce tace in kawo miki dambun shinkafa ko zaki ci.
Da sauri Madina t
a amsa ta bu
ɗ
e sai ƙamshi ke tashi, ga soyayyen naman sa a gefe zai kai yanka shida, tana cewa.
Aiko in son dambun shinkafa na da
ɗ
e ban ci ba, ki ce mata nagode ina gaisheta.
To Jidda tace mata kana ta wuce, Madina ta miƙe ta