Showing 9001 words to 12000 words out of 111085 words
yana waya, sai da ta tsaya jim ta fahimci da Madina yake wayar, kamar zata juya ta koma
ɗ
akinta sai kuma ta danne zuciyarta tunawa da shawarar da yaya Umma ta bata, sai kawai ta kama handle ta mur
ɗ
a ta shiga
ɗ
akin da sallama,Hamid ya waig
o daga rufda cikin da yayi yana kallonta ga wayar a kunnensa yace cikin ha
ɗ
e rai.
Lafiya?
Sakina sai da ta ha
ɗ
iye miyau kafin ta danne abinda taji a ranta ta samu gefen gadon ta zauna tana cire jihab
ɗ
inta ta ninke, da kallo ya bita ya tashi ya zauna, a
lokacin Madina take cewa.
Baby Hamid waye ya katse mana hirarmu ne naji kayi shuru.
Madinar Hamid ki yi haƙuri zan sake kiranki.
Sai ya gimtse kiran ya mayar da dubansa ga Sakina da take ta sakin murmushin yaƙe.
Meya faru? lafiya kika zo nan.?
Haba Ab
ban Mufeeda ya kake tambayata dan na zo mu kwanta.
Na kira ki ne?
Ya fa
ɗ
a yana ha
ɗ
e rai.
Yanzu sai ka kira ni ne zan zo mu kwana tare. Ina ce ba yau muka saba haka ba ko ka kwana
ɗ
akina ko na kwana a nan.
To ban gayyace ki ba ki tashi kije ki kwanta a
ɗ
akinki, haka kurum kin katse mini hira saboda jaraba ta kunno ki, ina ce yau kusan kwana biyar baki kwana anan ba, to duk ƙulaficinki sai dai ki mayar da shi dan na fara gyara dan tarban amarya ba zaki zo ki
ɓ
ata mini shiri ba.
Wani irin kallo Sakina tak
e binsa dashi cike da mamakin furucinsa, wanda nan take hawaye suka cika mata ido har jikinta ya soma rawa saboda tsananin dukan da maganarsa tayi mata a zuciya, cikin hasala ya cigaba da cewa.
Shekara nawa muka yi muna a tare, dan haka yanzu kya sarara m
ini na yiwa Amarya tanadi, in ma wani abin kika sha ya tsayar miki da jaraba to sai ki san yadda zaki yi, ki tashi ki fita mini a
ɗ
aki.
Sakina lumshe ido tayi hawayen daya taru a idonta ya sauka a kuncinta, bata ce masa komai ba ta miƙe riƙe da Hijab
ɗ
int
a dan tama kasa mayar da shi a jikinta, jiki a sanyaye ta fice daga
ɗ
akin ko rufo masa ƙofar ma ta kasa yi ta koma
ɗ
akinta tare da rufe ƙofar da key ta zauna a ƙasan tiles ta saki wani wawan
kuka mai tsuma zuciya, da yake dare ne kukanta har falo ana ji da
n da ƙarfi take yinsa saboda wani abu data ji ya danne mata ƙirji, jikinta har ciccira yake tana fidda gumi, haka fuskarta ta dame hawaye da majina tana yi tana gogesu da hijab
ɗ
inta data ƙanƙame da hannunta, tunda take ba a tana wulaƙantata irin wannan ba
, Hamid ya kai ƙololuwar ci mata fuska ya muzantata mafi muni data ji kamar ta ha
ɗ
iyi rai dan baƙin ciki, sai da tayi mai isarta kafin daga bisani ta sassauta kukan ta ja jikinta zuwa jikin gado ta jingina bayanta tare da lumshe ido hawaye ne kawai ke gang
arowa a kuncinta, alwashi da alƙawari ta riƙa
ɗ
aukarwa kanta ba zata kuma kai kanta
ɗ
akin Hamid ba zata nuna masa ita 'yar halak ce, zata nuna masa zata iya rayuwa ba tare da ya kuma kusantarta ba, nan take ta yiwa kanta alwashin bashi wata guda da amarya
ba tare da ta amsa girki ba, yadda zai samu damar sauke duk wani gyara da ya yi akanta, koda ta amsa girki bata jin zata bashi ha
ɗ
in kai kowa kuwa ya kawo kansa yana magiya sai ta jashi a ƙasa kamar yadda ya wulaƙantata yau, dan ba zata ta
ɓ
a iya yafe masa
wannan ba dole ne ta nuna masa ita macece 'yar halak, haka ta raba dare a haka sai da taji kanta yayi mata nauyi saboda sara mata da yake yi, kafin ta miƙe da kyar ta shiga bayi ta
ɗ
auro alwala ta dawo ta kwanta tayi addu'ar barci kana ta cigaba da jan ist
igafari a ranta, tayi alƙawarin binne wannan damuwar a ranta ba zata fa
ɗ
awa yaya Umma ba dan ya kamata ta koyawa kanta riƙe damuwa ta kuma iya ƙoƙarin magance shi da kanta, a haka barci ya
ɗ
auketa.
Washe gari Sakina ta saka Mufeeda ta shirya musu abin kar
i dan tace musu ba tada lafiya, suka yi mata sannu da fatan samun lafiya, Mufeeda ce ta taimakawa ƙannenta suka shirya har suka tafi makaranta, da yake falon a gyare yake Sakina bata wani damu ba ta rufe
ɗ
akinta da key ta kwanta ta bar Rauda a tsakiyar gad
o tana wasanta.
Hamid koda ya fito daga
ɗ
akinsa baiga kowa a falon ba haka ya wuce dinning yaga wayam, kwafa yayi ya juyo cikin zafin rai ya isa ƙofar Sakina ya mur
ɗ
a sai dai ya samu a rufe, sai ya shiga bugawa tana jinsa tayi banza dashi, nan ya fara mas
ifa da zage zage wanda yasa Rauda ta rarrafa ta maƙale jikin mamanta ta kwanta, dan sosai yarinyar take tsoron baban in yana masifa, Hamid ya ƙaraci kumfar bakinsa ya wuce ya
ɗ
auki jakarsa ya fita ransa a matuƙar
ɓ
ace da tunanin irin matakin da zai
ɗ
auka a
kan iskancin da Sakinar tayi masa naƙin yi masa abincin kari.
A taƙaice sai da suka
ɗ
auki kusan sati basu saka juna a ido ba, dan sosai Sakina take kaucewa ha
ɗ
uwarsu kuma ta daina girki sai dai ta sa Mufeeda ta girka abinda zata iya dafawa, ita ko saboda
hora kanta da tayi da yunwa da kuma zaman ka
ɗ
aici sai da ya sakata ramar dole, da rana takan fito falo ta zauna ta yi kallo yamma nayi sai ta shige
ɗ
aki tare da garga
ɗ
in yaran kar wanda ya takurata kuma kar suyi
ɓ
arna. Hamid ba ƙaramin
ɓ
acin rai ya shiga b
a dan shima ya
ɗ
auki fushi da ita ganin ta gama raina masa wayo, ga yadda ya horu da abincinta tunda ta daina yi ya shiga damuwa, kullun sai dai yaci abinci a waje kan ya shigo, cin dole yake yi badan ransa yana so ba, shi kansa bai san yana ƙaunar abincin
ta ba sai a wannan lokacin, shiyasa ko tafiya baya so tayi dan yana shiga wani yanayi kan ta dawo, amma haka ya danne yaƙi saukowa ya bata haƙuri a ganinsa shi ta yiwa laifi, sannan ma gwara ya koyawa kansa rage sabo da
abincinta tunda Madina zata zo ta fa
ra girka masa me da
ɗ
i dole kuma yaci ya saba da nata, hakan yasa ya cigaba da jan zaren fushinsa ya fita sabgarta kamar yadda itama ta fita nashi.
Haka suka ƙara kwashe sati guda a haka wanda ya kama saura sati biyu bikinsa, wannan lokacin shirin biki kaw
ai ya sa a gaba wanda suke ta tsare tsare da abokinsa Habib Mijin Kausar, a cikin hirarsu ne ma ya bashi labarin irin zaman da suke yi da Sakina, cikin ha
ɗ
e rai Habib yace.
Haba Hamid kai kuma saika biye mata, ai bai kamata matsayinka na babba ba kayi hak
a, laifi fa kayi mata tunda aure zaka ƙara, a wannan ga
ɓ
ar lallashi da tarairaya take buƙata bai kamata ka nuna bata da ƙima a gunka ba.
Hmmm baka san halin Sakina bace gaba
ɗ
aya ta sauya ta koyi taurin kai, ni ta yiwa laifi amma tafi ƙarfin ta bani haƙuri
, kusan sati biyu rabon da tayi mini girki, wai kishi hauka ne ko akanta aka fara ƙara aure.
Duk da haka kaine ya kamata ka sauko ku daidaita kafin a
ɗ
aura auren nan.
Hmmm Hamid yace yayi shuru yana nazarin maganar Habib, duk da ma bai sanar dashi asalin
wulaƙancin daya yi mata ba wanda a ganinsa bai
ɗ
auke shi laifi ba ra'yinsa ya sanar mata, kuma ya dace tayi masa uzuri tunda shekara kusan sha biyar suna tare dan ya nima ta bashi lokaci saboda amarya zata yi fushi haka, tsaki yaja yana cewa.
Wlh raini n
e bana so, in taga ta nima mu shirya zata
ɗ
auki kanta wata mai daraja.
Dama ba mai darajar ka
ɗ
auketa ba ashe, ai mace 'yar mulki ce duk sarautarka saika sauke shi ka bita matsawar bata kauce addini ba.
Ni yanzu ka dama mini lissafi, kaga mu bar maganar
nan kawai.
Cewar Hamid, Habib fa
ɗ
a ya rushe da shi wanda ya nuna masa
ɓ
acin ransa sosai kafin Hamid ya yarda zai nima su shirya, daga haka ya cigaba da bashi shawarwari na yadda zai kyautata mata har ayi auren lafiya a gama, haka suka rabu Hamid yana tuna
nin maganganunsa.
Bayan sallar magrib kafin ya dawo gida sai da yayi musu siyayyan kayan ciye ciye dan yasan ba lallai tayi girki ba, ya kashe ku
ɗ
i sosai duk kuwa cikin shawarar Habib ne. Daya iso gida ya samu su Mufeeda a falo suna kallo, suka yi masa sa
nnu da zuwa kana ya aje ledojin hannunsa a center table ya wuce direct
ɗ
akin Sakina ya shiga bugawa, daga ciki yaji muryanta tana cewa.
Amma Mufeeda bana ce karku dame ni ba, meye kike buga mini ƙofa.
Sakina ki bu
ɗ
e ƙofar ina son yin magana dake.
Cewar
Hamid yana
ɗ
an ha
ɗ
e rai dan ba ƙaramin daurewa yayi ba ya kawo kansa, ita kuma dama zaman haka ya isheta tana so su shirya amma bata so ta nuna masa har sai in ya kawo kansa, a da ita ce ke shige masa yana wulaƙantata a haka har su shirya amma yanzu ya dac
e taja ajinta itama ya gane tanada daraja shiyasa ta yi masa haka, bata ce masa komai ba ta miƙe ta zura hijab tazo ta bu
ɗ
e masa sai ta juya yabi bayanta zuwa ciki, duka suka zauna bakin gado tare da yin shuru dan taƙi yi masa magana, Hamid ya gama ƙuluwa
amma haka ya danne ya nisa yana cewa.
Yanzu dai kin nuna mini wuyanki ya isa yanka Sakina, to kanki kika yiwa bani ba, kuma wannan
ɓ
uyar da kike yi ya isa haka, kina sane da bikin nan ya kusa gwara ki warware ayi komai lafiya ba tare da kin bada ƙofar da
'yan uwana zasu gane baƙin halin da kika sauyawa ba ki gogawa kanki baƙin fenti, tun jiya su Asma suka zo amma kin kasa zuwa ki duba su, dan haka ki gobe In Allah ya kaimu ki shiga ku gaisa sannan ki zauna ki tattauna maganar shagalin bikin, sannan kayan k
atakon
ɗ
akinki ki yi kyauta dasu, kujerun falo ma ki bawa wanda ya dace, jibi Ins Sha Allah za a kawo sabbi a saka.
Allah ya kaimu lafiya angode Allah ya ƙara bu
ɗ
i.
Ameen, ki tashi ki je falo na yi mana siyayyan abinda zamu ci, sai ki gyara komai kafin i
n fito daga wanka sai muci a dinning.
To tace masa sai ya miƙe ya fice, da ido ta raka shii tana murmushin takaici, ita duk maganganunsa ba wanda ya
ɓ
ata mata rai sama da wai taje ta gaishe da ƙannensa wanda in da halacci sune ya dace su fara zuwa su duba
ta tunda ƙannensa ne, kwafa tayi da alƙawarin ba zata je
ɗ
in ba sai dai yayi duk abinda zaiyi, iskanci ne yasa basu shigo gunta ba tasan dama ba sonta suke ba suna murna da aurensa, dan haka yadda suka
ɗ
auketa itama haka zata bi dasu kowa ya zauna a mazaun
insa, ib bata nuna musu ita ma akwai zuciya a ƙirjinta ba haka zasu riƙa takata, daga su har wansu zata yi maganinsu, taja guntun tsaki ta miƙe ta fice.
Wannan shine dalilin shiryawarsu sai dai ko ka
ɗ
an Sakina bata sake gigin kai kanta zuwa
ɗ
akin Hamid ba
, shima bai nuna yana buƙatar ta ba hakan yasa ta cigaba da lamarinta, musamman da biki yazo itama tana ta nata shirin, duk da ba taro zata yi ba amma 'yan uwanta zasu zo suyi mata ƙara.
[7/2, 10:58 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG
.
Wattpad @rahmakabir
Page 6.
Biki saura kwana biyar Hamid ya kawo mata kayan fadar kishiya akwati biyu da kit, duk da kaya a ciki masu kyau leshi uku atamfa biyar da shadda biyu sai material biyu da sauran takalmi da jaka, kala biyar aka
ɗ
inka mata a ci
ki, koda ya nuna mata ta yi murna da godiya har tsokanarsa tayi tana cewa.
Kaga yadda kake ta sheƙi ko dai kaima kaje anyi maka gyaran jikin ango ne.
Kai Sakina bana son sharri.
Allah ba sharri nake maka ba naga ka ƙara haske sai dai kayi rama ka
ɗ
an kum
a wlh hakan ya ƙara maka kyau.
Wahalar zurga zurga ne yasa na rame ga kuma kashe ku
ɗ
i da nake tayi, jikina da aljihuna yana gaya mini.
Allah dai ya nuna mana ya sanya alkhairi, ni kasan babbar kyautar da zanyi maka kuwa.
Cewar Sakina tana
ɗ
an murmushi,
Hamid aje wayarsa yayi a gefensa yana dubanta dan sosai yaji da
ɗ
in yadda take farin ciki da zuwan aurensa, saboda yaga ta sake sosai ta aje duk wani kishi da yake gani a tattare da ita, yace.
Sai kin fa
ɗ
a Sakina.
Hmmm babu wani kyauta da zanyi maka da za
i burgeka saboda nasan kana da ku
ɗ
i, shiyasa nayi tunanin na baku kyautar cin amarci na wata guda kai da Amarya hakan zai sa ku fahimci juna sosai kusan ina kuka dosa, ni kuma zan yi mata girkin sati
ɗ
aya daga nan taja ragamar kirki har sai ta cike wata gu
dan dana baku.
Washe baki Hamid yayi yana dariya kana ya ƙara dubanta.
Anya wannan kyautar taki takai har zucci kuwa?
To meye a ciki? naga dai duk gyaran da kayi na amarya ne to ina so ka zube duk wani gyaran da kayi gunta, kan wata guda na tabbatar da
komai ya kankama ƙila ma in rabo na kusa ta kunsa.
Sakina kenan in dai da gaske kike yi to ina godiya Allah ya bar soyayya, duk da nasan da biyu kika bayar da kwanakinki saboda abinda ya faru kwanaki shiyasa zaki ce haka.
Haba ai abinda ya faru ya wuce g
ani nayi ya dace in yi maka wannan halaccin tunda ni tsohowar zuma ce mun jima muna tare, ya dace na bawa Amarya dama itama.
Hmmm shikenan nagode Allah ya bamu zaman lafiya gaba
ɗ
aya.
Sakina ta amsa da Amin fuska cike da murmushi, sai dai zuciyarta cike y
ake da ƙuna akan zafin kishin da take ji akansa, duk da tana ganin karin auren zai iya zama wani mafita a gareta, kuma Hamid bai cancanci ta wahal da kanta gurin kishinsa ba tunda ko tayi ma baisan tana yi ba, amma jin kishi ya zama wajibi taji shi saboda
duk wata mace dole ne taji babu da
ɗ
i in mijinta zai ƙara aure duk lalacewarsa kuwa , Abun da ciwo sai dai ko wacce da irin nata dauriyar.
Lokacin data koma
ɗ
aki tayi shirin barci a sannan ne ta shiga tunanin maganar da tayi da Hamid, yadda ya nuna yaji da
ɗ
in kwanan data basu yasa ta ƙara tabbatar da baya ƙaunar ta, a yanzu ta gane darajar 'ya'yanta take ci shiyasa yake cigaba da zama da ita, dan sam bata gabansa balle wani sauran daraja, hakan ba ƙaramin ciwo taji yayi mata ba kuma itama dole ne zata cire
shi a ranta ta zauna zaman ibada dan kuwa yanzu ne lokacin da zata yi zaman haƙuri, fargabanta irin yadda zaman zai kaya da amaryar a gidan tasan zata ƙunshi baƙin ciki da halin Hamid, dama zai raba musu gida ita hakan zaifi mata kwanciyar hankali, amma ta
san bata kai wannan matsayin ba da zata saka yayi mata abu, dan ta gwada yi masa magana akan raba gida basu kwashe ta da
ɗ
i ba, da wannan tunanin barci ya kwasheta.
Da safe bayan ta sallami yara da Hamid sai ta shirya ta shiga sashin Hajiya akan amsa kiran
ta dan tun jiya ta sanar da Hamid ya fa
ɗ
a mata taje yau, da sallama ta shiga falon basu ma ji ba saboda mata ne da
ɗ
an dama a ciki ga hayaniya da suke yi na kallon kayan akwatin amarya da za a kai anjima, sai da ta ƙaraso ciki sosai ta kuma yi musu sallama
a sannan ne wasu daga ciki suka amsa suna cewa.
Uwargidan Hamid ce da kanta.
Nice ina kwananmu fatan mun tashi lafiya.
Wasu suka amsa mata da lafiya lau, su Asma kuwa kawar da kai suka yi suna cigaba da hira tamkar basu ganta ba, itama bata bi ta kans
u ba ta samu cushing ta zauna tana cewa Jidda.
Hajiya tana ina? kije kice mata na zo.
To tace mata kana miƙe da sauri ta wuce
ɗ
akin Hajiya dan ta kirata, Kubura ce ta daga wani crazy English wears riga da wando tana cewa.
Anty Asma kinga wannan kayan ba
ƙaramin yiwa Madina kyau zai yi ba gata fara ga tsayi, gaskiya yaya Hamid ya iya za
ɓ
ar mata.
Fa
ɗ
i ki ƙara yanzu ne yasan zai yi aure ai.
Cewar Asma tana miƙa mata hannu suka tafa tare da yin shewa,