Showing 90001 words to 93000 words out of 111085 words
ƙarfe biyu da mintuna Madina ta kira Hamid akan yazo ya
ɗ
auketa suje gidansu momy tana son ganinsu dan lokacin ta tashi daga aiki, Hamid yace ta wuce daga nan zai samet
a a can, bata yi mamaki ba dan tasan an sauya mata Hamid
ɗ
inta dan in da dane jikinsa yana rawa zai ce to dan yasha
ɗ
aukota daga gurin aiki ya mayar da ita gida lokacin da suke soyayya kafin suyi aure, amma kamar kiftawar ido komai yana niman zama tarihi,
tayi ƙofa ta miƙe ta gyara fuskarta da powder kana ta yi sallama da mutanen office
ɗ
insu ta wuce gida. Koda ta isa minti bai fi goma sha uku ba da isarta shima Hamid yazo, bai tsaya kiranta ba ya shiga gidan kaitsaye tunda ya zama
ɗ
an gida shima, sannan ma
an san da zuwansa tunda momy ce tayi kiransu, daya isa ƙofar falo ya buga tare da bu
ɗ
e murya yayi sallama, Ladi mai aiki ita ce ta zo ta bu
ɗ
e masa da yi masa iso ciki ya samu guri ya zauna suka gaisa kana ta shiga kitchen ta kawo masa ruwa da lemun gora d
a kofi a tire ta aje a center table ta wuce, ba jimawa sai ga momy ta fito tare da Madina duk suka zauna Hamid cikin girmamawa ya gaisheta kana suka
ɗ
anyi shuru, Madina dai bata ce masa komai ba sai cika take yi tana batsewa akan ƙararta daya kawo, dan sun
fara maganar a
ɗ
akin momy kafin zuwansa, daga bisani momy tayi gyaran murya ta soma da cewa.
Na samu saƙon ka a gurin Aisha akan Madina, shiyasa nace kuzo tun kafin abin ya
ɗ
auki lokaci.
Ta ƙare maganar tana jan fasali, Hamid ya
ɗ
an sunkuyar da kai yana
cewa.
Hakane, kuma abin yaci tura ne yasa har na fa
ɗ
a wa Anty Aishan.
To dama baka san cewa Madina 'yar gata ka aura ba?
Na sani.
Hamid ya bata amsa yana mamakin tambayarta, sai yaji momyn ta cigaba da cewa.
To gaskiya in har Madina tana ƙazanta ko k
ai ne kaso haka saboda bata saba da wahalar aikin gida ba, anan gidan kafin tayi aure masu aikinmu mutum biyu ne suke yi mata duk hidimar da take so, dan haka in har bata iya girki da gyaran gida ba karka ga laifinta domin bata saba da su ba, sannan kuma d
uk yadda kake da arziki ai abin kunya ne ace matanka suke yin hidimar gidanka, kamata yayi masu aiki keyin komai dan kana da ku
ɗ
in, dan haka abinda zan fa
ɗ
a maka bana aura maka ita bane dan taje ta yi wahala ba, a'a gidan aurenta so nake yafi nan gidan jin
da
ɗ
i, batun kuma wanka wannan duk zanyi mata fa
ɗ
a zata bari dama anan mai aiki ce take ha
ɗ
a mata ruwan da komai iyaka nata tayi ne ta fito, kaga kuma kana sama mata masu yi ba zaka ƙara ƙorafin ƙazantarta ba.
Momy data kawo nan a maganarta tayi shuru tan
a dubansa dan fuskarta ma a ha
ɗ
e yake saboda haushin daya bata, Hamid dai sunkuyar da kai yayi ƙasa kamar ruwa ya cinyeshi bai ta
ɓ
a zaton haka daga momyn Madina ba, kenan duk iskancin data ke yi masa
ɗ
aurin gidi ne daga gun mahaifiyarta, yanzu ya tabbatar
da maganar Habib na cewar ya auri 'yar mace, momy jin bazai yi magana ba sai ta daura da cewam
Shiyasa na kiraku kuzo domin in fa
ɗ
a maka haka dan Madina kam bata san duk wannan wahalar ba, in dai zaka riƙeta amana to zaka
ɗ
aura daga kulawar da muke yi mat
a ne ka ƙara akan namu. Sannan ina so in baka shawara ka raba mata gida da uwargidanka, dan gaskiya wannan gidan naka yayi ka
ɗ
an da aje mata biyu, nasan ba wannan ne ka
ɗ
ai gidanka ba, ga kuma alƙawarin mota daka yi mata tace har yanzu baka bata ba, Hamid y
a kamata ka zama mai cika alkawari ka fa
ɗ
a ka cika, Ke kuma ban sanki da rashin kunya ba, ki daina yi masa rashin kunya tunda ba haka na tarbiyyantar dake ba, dan haka zaka iya tafiya ita kuma zan ƙara yi mata fa
ɗ
a.
To nagode Hajiya sai anjima.
Hamid ya
fa
ɗ
a yana miƙewa tare da zaro dubu goma daya waresu a aljihunsa tun kafin ya shigo gidan ya aje akan center table yana cewa.
A Kara cefane ba yawa.
Mai yawan kenan angode ka gaida gida.
Cewar momy, Madina ta miƙe tabi bayansa har ya kusa fita gate kafin
ta dakatar dashi da cewa.
Hamid ka ƙara mini ku
ɗ
in mota sai anjima zan dawo.
Tsayawa yayi ya zaro ku
ɗ
i a aljuhunsa ya cire dubu biyu ya bata ta amsa ba tare da yace mata komai ba ya juya ya fita, bata damu da yanayinsa ba ta koma cikin gida dan sosai ta
ji da
ɗ
in maganganun da momy tayi masa, ƙila zata samu sassauci daga abinda yake yi mata.
Hamid da kyar ya iya tuƙa kansa yana tafe yana tunanin abinda momy tace masa, gaba
ɗ
aya jikinsa babu ƙarfi dan ba ƙaramin sare masa guiwa tayi ba, dana sani sosai ya s
amu kansa a ciki na auren Madina, yana jin da wuya aurensu yaje ko ina dan baya jin zaiyi abu
ɗ
aya daga cikin maganar momy, dan aiki dai ya ji zai iya barinta kuma yace ta kawo mai aikin gyaran sashinta, banda wannan baya jin zai iya yi mata wani abu dan i
tama ba kyautata masa take yi ba kuma duk zuciya tana son mai kyautata masa, sannan ma in har mota ce to a yanzu Sakina ce ta cancanci ya bata mota dan ya tabbatar itace matar rufin asirinsa wacce take bashi dukkan kulawa da ƙauna ta gaskiya, hawaye yaji y
a cika masa ido tunawa da wasu abubuwan da yayi mata a lokacin da zai auro Madina, tabbas ya kamata ya sakawa Sakina da alkhairi bisa haƙurin zama dashi da tayi na wulaƙancin da yayi mata, haka ya koma gurin aiki jiki a sanyaye dan baya jin da akwai wanda
zai sanar dashi wannan abin da maman Madina tayi masa, dan yasan ba za a fa
ɗ
a masa shawara mai da
ɗ
i ba akan haka, addu'a kawai zai dage dayi Allah daya ƙaddara masa aurenta shine ka
ɗ
ai zai kawo masa mafita.
****
Sakina.
Wajen ƙarfe hu
ɗ
u ta fito tsakar g
ida ta aika Iro ya siyo mata ku
ɓ
ewa
ɗ
anya da man shanu, ta koma ciki ta
ɗ
aura sanwar tuwon Masara, sai sauran pepper chicken fin nan ta ƙara gyara shi ta adana. Koda Iro ya kawo mata cefanen har ta yi talge tana shirin tuƙa tuwo, nan ta shiga aikin
ɗ
aura m
iya ta kuma soya man shanun ta adana man sai ta
ɗ
iba ka
ɗ
an tasa a sanwar miya, ta zuba ƙashi a ciki ya shiga dahuwa, sai wajen ƙarfe shida da rabi da gama komai ta jera su a dinning kana ta koma
ɗ
aki tayi wanka, fitowarta an soma kiran sallar magrib dan ha
ka sai da ta fito tasa yaran suka shiga
ɗ
aki dan yin Sallah kana ta zo ta gabatar da nata sallar. Data idar ta zo madubi ta shiga shiryawa, kwalliya ta yiwa fuskarta
ɗ
an daidai kana ta ciro
ɗ
aya daga cikin kayan da suka siya da Jalila, riga da siket 'yan k
anti, rigar fara ce kuma 'yar daidai ta kama jikinta kuma in ta daga hannunta sama cibiyarta zata fito saboda 'yar ƙarama ce, sannan siket
ɗ
in iya guiwa mai fa
ɗ
i da baza pink color ne kuma da ratsin baƙi baƙi a jiki, ita kanta data saka kayan sun zauna a j
ikinta ba ƙaramin kyau suka yi mata ba, ta
ɗ
auki ƙaramin baƙin gyalenta na abaya ta
ɗ
aura tare da ba
ɗ
eshi tayi
ɗ
auri mai kyau, sai ta feshe jikinta da turare ta tsaya tana kallon kanta a madubi sai taga kamar ba ita bace, sai kuma ta soma kunyar fita da ka
yan har yaranta su gani balle kuma Hamid ya ganta da su, to abu ne da basu sa
ɓ
a gani ba tasan sai ta zame musu abin kallo, to wannan kallon nasu ne zai sa taji kunyar, haka ta gama ta adana komai ta dawo bakin fado ta zauna ta shiga taraddadin yadda zata f
ita, a haka ne har aka kira sallar isha'i sai ta miƙe ta
ɗ
aura zanin sallarta ta saka hijab ta gabatar, koda ta idar tana zaune a dadduma tana lazumi, a lokacin ne taji shigowar motar Hamid, ta yi saurin yin addu'a ta miƙe ta na
ɗ
e kayan sallar ta adanasu t
a koma jikin madubi ta gyara fuskarta da soson powder kana ta ƙara fesa wani turare ta juya ta nufi ƙofar fita sai da ta tsaya jim tana lissafi, wanda a lokacin har Hamid ya shigo yaran suna yi masa sannu da zuwa Rauda kuma ta isa gareshi da gudu ta rungum
e shi, ya duƙa dan ya
ɗ
auketa a lokacin ne Sakina tayi shahada ta fito, ta tsaya jikin ƙofa ta kasa tafiya tana kallonsu, dai dai lokacin Hamid ke
ɗ
agowa da Rauda ya
ɗ
auketa sai kuma ya sauke kallonsa ga Sakina da take tsaye tana sakin murmushi, mutuwar ts
aye yayi ya shiga kallonta kamar wanda ya warke cutar makanta, gani yake kamar zigo take yi masa a wani shiga da bai ta
ɓ
a ganinta dashi ba, yadda ya buga fosta yana kallonta baki bu
ɗ
e yasa yaran suma duk suka waiga suga me Abbansu yake kallo, ganin Mamansu
da wannan kayan yasa suma suka zuba mata idanu, Mufeeda kuwa tsintar kanta tayi tana murmushi tare da gimtse bakinta dan kar dariyarta ta fito, Baba ƙarami ya miƙe ya nufi Sakina.
Laaaa Mama kinsa kayan yara.
Daƙuwa tayi masa da hannu.
Kaci gidanku na
ce.
Sai duk suka tuntsire da dariya, Hamid shima ya kasa riƙeta ya shiga yi, ya aje Rauda ya ƙaraso gaban Sakina.
Wai Sakinata ce haka ko wata ce aka sauya mini, wannan irin bazata haka, gaba
ɗ
aya tunda kika dawo kike bani mamaki fa, meye wannan sirrin da
kika samo ne a Kano matar Hamid? Kin ganki kuwa, kinyi matuƙar yin kyau sosai bana wasa ba, gaskiya na siya wannan wanka ki saka masa farashi ko nawa ne zan biyashi.
Ya ƙare maganar yana ciro wayarsa daga aljihu ya shiga wajen
ɗ
aukar hoto ya seta camera
ya soma
ɗ
aukarta a wayarsa, ita kuwa banda murmushi ba abinda take yi bakinta ya ma kasa rufuwa, idanunta har wasu ruwa ruwa suka yi na hawayen farin ciki, daga bisani Hamid matsowa yayi kusa da ita ya shiga
ɗ
aukar su salfie, yaran sai dariya suke yi suna
cewa sunyi kyau, a dai dai wannan lokacin Madina ta fito daga
ɗ
akinta dan hayaniyarsu taji yayi yawa, dama tunda ta shigo gidan ta lafe a gado ta kasa motsin kirki, yadda taga suna hoto gwanin burgewa yasa taji wani tuƙuƙin baƙin ciki ya turnuƙota, sai taj
a dogon tsaki ta juya a fusace ta shiga
ɗ
aki tare da banko ƙofa, wanda hakan yasa Hamid ya juya ya kalli ƙofar ya dawo da kallonsa ga Sakina suka ha
ɗ
a ido sai suka sakarwa juna murmushi, Sakina tana cewa.
Muje kayi wanka sai muci abinci.
Gaskiya abinci z
an fara ci dan yau babu wani abincin kirki a cikina bayan na safe, da yunwa na shigo gidan.
Muje to mu ci.
Ta fa
ɗ
a tare da kama hannun Rauda data matso kusa da ita, suka yi gaba Hamid ya bita da kallo zuciyarsa cike da farin cikin ganinta a haka, duk wan
i
ɓ
acin rai da ƙuncin da momyn Madina ta saka shi a ciki, ji yayi ya tafi sai farin cikin ganin Sakina, ji yayi da tun farko haka matarsa ke yi ƙila da bai kalli kyale kyalen Madina ba balle ya auro ta, ya tabbatar zuwanta Kano Anty Jalila ta yi mata sabon
karatu, kuma ga dukkan alamu ta
ɗ
auki darasin kamar yadda ta
ɗ
aurata akai, babu abinda zai cewa Jalila sai addu'a da fatan gamawa lafiya.
[8/19, 6:54 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 38.
Koda suka kamma
la cin abincin a falo suka yada zango suka cigaba da kallo, wajen ƙarfe tara Sakina ta sallami yara duk suka shiga
ɗ
akinsu suka kwanta, dan yanzu Rauda ta fara yarda ta kwana da Mufeeda hakan yasa falon ya rage sai su ka
ɗ
ai, Sakina ta muskuta tana dubansa.
Ya kamata kaje ka watsa ruwa naga lokaci ya tafi.
Hmmm kinsan kuwa na sha'afa, gaba
ɗ
aya yau
ɗ
in nai kin rikita mini kai ba ga kwalliyarki ba ba ga abinci ba, komai yayi Masha Allah, wai in tambayeki mana.
Ina jinka Abban Mufeeda.
Yauwa! menene sirrin
ne naga gaba
ɗ
aya duk kin sauya? Jalila ina ga ta baki wani maganin daya sauya ki ba kika dawo 'yar caras dake ko? wai dama haka kike duk tsawon lokacin nan kika nima mayar da kanki tsohuwa.
Ya ƙare maganar yana 'yar dariya, itama dariyar tayi bata ce koma
i ba dan ba tada amsar da zata bashi saboda basu saba hira irin haka ba, Hamid ya
ɗ
aura da cewa.
Da tun farko nasan zaki iya sauyawa da tuntuni na turaki Kano kin ƙaro cos a gun Jalila, ƙila da babu abinda zaisa na ƙara ma aure wlh.
A'a fa ka daina wanna
n maganar dan bazan mance irin giyar soyayyar amaryarka daka sha ba, ka dinga amayar mini da
ɗ
okin zuwanta a gidan nan, dan haka kayi shuru kawai.
Hmmm Sakina kenan, ba zaki ganne bane amma ina mai ƙara baki hakuri akan faruwar wasu abubuwan, Allah ya huc
i zuciyarki yanzu muje nayi wanka sai ki ha
ɗ
o mini cofee nasha kafin mu kwanta.
To tace masa tana murmushi ta miƙe tayi gaba ya bita a baya, sai da ta fara ha
ɗ
a masa ruwan wanka kafin ta fito ta wuce
ɗ
akinta ta fara kuskure bakinta da mouth wash, ta wanke
kwalliyar fuskarta ta fito ta shafa mai a fuskar da man baki, sai ta ciro kayan da zata saka, sai dai tsayawa tayi tana tunanin saka su dan bata ta
ɓ
a saka irin su ba bata so Hamid ya gano ta zaƙe da yawa, dan haka ta mayar da kayan masu shara shara ta
ɗ
au
ki wasu masu kyau riga zuwa rabin cinya da dogon wando, ta saka su tare da shafe jikinta da humra mai sauƙin ƙamshi ta saka turaren data ware na barci a jikin kayan ta zura hijab da nufin fitowa, ta isa kitchen dan ha
ɗ
a masa cofee.
Madina tunda taji sun b
ar falon sai ta fito da sauri ta wuce kitchen dan ta
ɗ
iba abincin da suka rage taci kamar dai jiya, ta bu
ɗ
e taga tuwo nan take ta ha
ɗ
iye miyau dan sosai cikin jikinta ya saka mata ƙaunar tuwo, ta bu
ɗ
e miyar taga miyar yauƙi ne nan ma taji da
ɗ
i sosai dan ha
ka cikin sauri ta
ɗ
auki plate ta saka tuwon da miya ta ja kujera ta zauna ta soma saka loma tamkar tana cin nama saboda mugun da
ɗ
in da yayi mata, a wannan yanayin ne Sakina ta shigo kitchen
ɗ
in, Madina tayi saurin aje plate a gefenta ta miƙe tare da
ɓ
oye h
annunta baya tana wani cin magani da zazzare ido kamar mage a kwali, sosai ta bawa Sakina dariya dan sarai taga yadda ta zura lomon tuwo a bakinta lokacin da ta shigo, sai ta gimtse dariyar tayi kamar bata ganta ba ta isa gefen inda kayan kitchen
ɗ
inta yak
e, nan ta shiga ha
ɗ
awa Hamid cofee
ɗ
insa harta gama Madina tana nan a tsaye kamar fosta ita bata cigaba da abinda take yi ba bata kuma fita ba, Sakina ta yi kamar ta fita sai Madina ta koma ta zauna ta
ɗ
auko plate
ɗ
inta ta zabtari ƙaton loma, takai bakinta
kenan Sakina ta ƙara shigowa zata
ɗ
auki cokali kuma da gangan ta ki
ɗ
auka dan dai ta ƙara kama Madina, ai Madina tsayawa tayi ga lomar tuwo takai baki bata ƙarasa ci ba ga kuma plate a hannunta, wani sabon fosta ta kuma yi, a wannan lokacin Sakina sai da
tayi dariya mai sauti.
Da
ɗ
i na da gobe saurin zuwa. Allah na gode maka.
Ta fa
ɗ
a tare da ficewa tana dariya, Madina wani ha
ɗ
e rai tayi tana cin magani, sai dai duk rashin kunyarta sai da taji nauyin ganinta da Sakina tayi da abincinta tana ci, tunawa tayi
da lokacin da tayi mata rashin mutunci kan an
ɗ
ibar mata dambun da Hajiya ta kawo mata, maganar Sakina yana nufin habaici ta sakar mata kenan, taja guntun tsaki ta kai loman bakinta tana cewa a ranta.
Ko meye ma ki fa
ɗ
a sai na ci dan uban mutum, ai Hamid
ne ya kawo abincin ba ke ce kika siya ba, dan dai kin dafa naci...
Ta ƙare da sake jan tsaki, haka ta tura tuwon