Showing 54001 words to 57000 words out of 111085 words

Chapter 19 - ƘAZAMAR AMARYA completed.

dawo ba kice mata tayi haƙuri zan turo driver ya

ɗ

aukota.

Sakinar ce tace ta zo gidana? To gaskiya bata zo ba dan nasan

waya ka

ɗ

ai nayi na ita

ɗ

azun da safe.

To shikenan ƙila gida ta tafi bari na kira yaya Hamza naji sai anjima.

Hamid wani abun ya faru ne?

Wlh

ɗ

an sa

ɓ

ani muka samu jiya nace ta dawo gida kuma wlh barazana kawai nayi mata amma har zuciyata bana nufin haka,

yau da safe dama nayi niyya nace na janye maganata sai kuma na kwana Asibiti,

ɗ

azun muka dawo da magriba shine na samu bata nan.

Yaya umma shuru tayi tana tuna maganar da suka yi da Sakina

ɗ

azun, hankalinta yayi mugun tashi dan alamu sun nuna a cikin mag

anar Sakina lallai ba gida zata je ba.

Allah yasa tana gidan nima bari na kira na tambaya.

Abinda tace masa kenan ta kashe wayar, ta kira Falmata ko taje can gidanta, nan ta tabbatar mata da bata je ba, Hamid shima ya kira yaya Hamza yace yana a gidan ya

nzu haka kuma Sakina bata nan, cikin tashin hankali ya shiga kiran duk inda yayi tsammanin zata tafi amma Sakina bata je can ba, Yaya umma hankalinta yafi na kowa tashi dan kasa haƙuri tayi ta tafi gidansu suka ha

ɗ

u da yayyinsu maza tana basu labarin hirar

da suka yi

ɗ

azun, hakan ya tabbatar Sakina ta tafi ne kuma ƙila tayi nisa. Cikin daren nan haka suka dinga kiran waya amma ba labarin Sakina hankalin Hamid in yayi dubu to ya tashi, bai ta

ɓ

a zato Sakina zata yi zuciya irin haka ba har ta iya barin yaranta

ta bar gidan, yasan duk barazanar da zai yi mata dole zata

ɗ

auka saboda yasan tana mugun son yaranta, sai gashi a daidai lokacin da yake buƙatarta ta tafi ta barsu, sai da ma ya shiga

ɗ

akinta ya tabbatar da lallai tafiya tayi dan bai ga babban akwatinta b

a kuma ta

ɗ

iba kaya a waldrobe

ɗ

inta, jiki a sanyaye ya fito ya nufi

ɗ

akin Madina da ke kwance tana cin biscuit da hajiyarta ta siya mata

ɗ

azun, ya zauna gefen gadonta ya dafe kai damuwa ƙarara ya bayyana a fuskarsa, Madina ta

ɗ

ago ta zauna tana cewa.

Mas

oyi ba dai jikin naka bane naga fuskarka da damuwa.

Sakina ce ta kwashe kaya ta bar gidan yanzu haka maganar da ake yi ba a san in da ta tafi ba.

Wani irin ta bar gida sai kace wata yarinya, ina zata tafi har ta iya barin yaranta? ku dai bincika dai.

Da

gaske nake miki ta tafi dan nine naja ta tafi saboda abinda ya ha

ɗ

aku jiya da kika fa

ɗ

a mini nace da safe ta safi gida to sai ga rashin lafiya ya kama ni, na

ɗ

auka ta haƙura saboda rashin tafiyata har mu sasanta ashe da niyyar zata tafi

ɗ

in a ranta.

Shike

nan ni zata jawo mini zagi ace nayi sanadin barinta gidanka, gaskiya ayi ƙoƙarin sanin inda take ta dawo dan wlh bazan iya rainon yaranta ba.

Da sauri Hamid ya juya yana dubanta jin wai ba zata riƙe yaransa ba ƙiri ƙiri.

Madina nayi zaton yarana yaranki

ne ashe ba haka kike

ɗ

auka ba, yau ko uwarsu tana nan na

ɗ

auka zaki riƙe su tamkar naki, ashe da gaskiyar Sakina tace ba zata bari ki bautar mata da yarinya ba tunda gashi tun ba aje ko ina ba kin nuna ba yaranki bane.

Nifa ba haka nake nufi ba kawai dai

kasan ba ni da wadataccen lokacin kula dasu saboda aikina, sannan ga shi ban saba da raino ba gidanmu ni ka

ɗ

ai ce kuma nima komai yi mini ake yi.

Madina ta fa

ɗ

a cikin shago

ɓ

a. Hamid ya girgiza kai yana cewa.

Aikin ai bai zama dole sai kin je ba tunda bak

i rasa komai a gidana ba, ina ganin in hakan zai zama takura zaki

ɗ

auki hutu saboda yaran ko ki aje shi gaba

ɗ

aya na riƙa biyanki albashinki duk wata.

Narantse da girman Allah babu wanda ya isa ya hanani aikina, baka san wahalar karatuna ba dan haka banga

dalili saboda raya kace na aje ba, gobe In Sha Allah sai na fita aiki.

Ta fa

ɗ

a a hasale, Hamid binta da kallo kawai yake yi cike da mamaki, bai ce mata komai ba ya miƙe ya fice daga

ɗ

akin, a fusace ta sauko a gadon tabi bayansa tana cewa.

Wlh Hamid baza

n iya da wannan damuwar ba, dan matarka tabar gida kace wai saina riƙe maka yara, kaje ka nimota duk inda ta shiga ta dawo dan yaranta ehe.

Hamid tsabar ransa ya

ɓ

aci ya juyo a fusace ya kifa mata mari, ihu ta saka tana tsalle tare da fa

ɗ

in Allah ya isa b

ata yafe ba, bai kula ta ba ya wuce a zuciye ta ruga da gudu ta bar part

ɗ

in zuwa sashinsu su Hajiya kamar mahaukaciya. Hamid kam zama yayi a cushing yana tambayar yaransa sunci Abinci, suka ce masa eh, sai ya miƙe ya je kitchen ya

ɗ

iba tuwon ya saka miya

ya

ɗ

auko ruwa yazo kujera ya zauna yana ci dan sosai yake jin yunwa ba zai iya jurewa ba, saboda damuwar da yake ciki bama jin da

ɗ

in abincin yake yi ba, haka ya tusashi yana jin cekar Sakina yana damun zuciyarsa, yasan duk inda taje zata dawo amma babbar d

amuwarsa ina taje? kuma yaushe zata dawo gareshi? duk babu wanda zai amsa masa wannan tambayar.

[7/29, 5:39 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Wattpad @rahmakabir

Page 24.

Madina tana isa sashin su Hajiya ta fa

ɗ

a ciki ko sallama b

abu, wanda kukanta shine abun da ya fara yin iso garesu, daga Alhaji har Hajiya a cikin tashin hankali suke miƙe tsaye suna kallonta dan duk suna zaune cikin falon kuma zatonsu ya basu ko Hamid ne rai yayi halinsa, tunda ga bigiren da suke ciki na rashin l

afiya, Alhaji yayi ƙarfin hali yace mata.

'Yata kukan me kike yi haka? wani abun ne ya ƙara samun Abdulhamid?

Madina ta seta kukan tana share hawaye tare da koro musu bayanin wai ya hanata zuwa aiki akan sai ta riƙe masa yara saboda Sakina ta bar gidansa

ba a san inda ta nufa ba, ba Alhaji ba hatta Hajiya sai ta taji mugun takaicin Madina yadda ta tayar musu da hankali sosai, Alhaji bai iya ƙara magana ba ya yi hanyar fita Madina ta rufa masa baya tare da Hajiya, duk da bata jin ƙarfin jikinta amma dole t

a bisu taji kanun labari. Koda suka isa falon sun tadda Hamid yana cin abinci tare da yara suna kallo, baiyi mamakin ganin iyayensa tare da Madina ba dan yasan tunda ta fita to can tayi, yanzu ne ya ƙara tabbatar da Madina sargartacciya ce ga rashin wayo d

a rashin hankali gaba

ɗ

aya ba tada lisaafi, balle ta riƙa yiwa kanta tunanin abunda yake daidai, bai iya yiwa su Abba magana ba suma basu yi masa ba duk suka samu guri suka zauna suna kallonsa, har sai da ya kammala cin abincinsa ya miƙe ya kai plate kitche

n ya wanke hannu ya dawo yasha ruwa kafin ya cewa su Mufeeda su shiga

ɗ

aki su jirashi, tace to tare da jan ƙannenta suka shiga

ɗ

akinta a sannan ne Abba ya soma magana.

Madina taje mana da maganar kace ba zata je aiki ba zata riƙe maka yara saboda Sakina t

a bar gidanka, to ni bazan tambayeka meya faru da ya saka Sakina ta bar gidanka ba, sai dai ina so ka sani wajibi ne ka cikawa yarinyar nan alƙawarin da kasa muka

ɗ

auka a lokacin da muka je niman aurenta, na lallai dole zata yi aiki kuma muka amince, Madin

a ba zata zauna dan riƙe maka yara ba kasan yadda zaka yi dasu.

Abba ai har motar da ya ce zai bani yace ya fasa ba zai bayar ba.

Cewar Madina tana turo baki, Alhaji ya dube ta yana cewa.

Ban san lokacin da ya yi miki wannan alƙawarin ba, dan haka bazan

iya cewa komai akai ba idan ya ga dama ya baki in bai gadama ba ya riƙe wannan tsakaninku ne. Hajiya tashi mu koma gida.

Ya ƙare maganar yana dubanta, Hajiya cike da damuwa tace.

Ka bari yayi mana bayanin abinda ya ha

ɗ

asu da Sakina ta tafi tabar yaranta

, kasan dai a wannan ga

ɓ

ar Madina ce ta dace ta riƙe masa su tunda ko ni ba ni da ƙarfin riƙe su, meye amfanin yin mata biyun? yanzu koda ace Sakina tafiya tayi ko taje wani sha'ani Madina ba zata kula masa da yara ba, ai wannan ba magana bace tunda tasan

mai mata da yara ta aura, dolenta ne ta saka a ranta zata yi hidimarsu.

Ni bazan saurari maganar matsalarsa da Sakina ba domin na da

ɗ

e ina ja masa kunne akan karya ƙure fushinta, na tabbatar tunda ta iya tafiya tabar yaranta to ya kaita bango ne, sannan k

ina maganar Madina ta kula masa da yara kinga tana da natsuwa da hankalin da zata iya riƙe su? Ita kanta bata gama riƙe kanta ba balle ta kula da wani, ko so kike ta riƙa dafa musu abincin da kullun sai sun ziyarci asibiti, dan haka duk tsuntsun daya ja ru

wa shi ruwa kan duka kuma duk wanda ya siya rariya yasan zata zubda ruwa, tun lokacin da akace mini 'yar mace ce nace ya haƙura domin ba lallai a sameta da tarbiyyar da muke tunani ba fiye ga wacce namiji ya zama jagorarta ba, amma me yace? cewa yayi yarin

yar tana da ilimin zamani dana addini mahaifiyarta ta kula da tarbiyyarta sosai, ba yi da tantama akan ta zai samu farin cikin da yake buƙata. Gashi yau kwananta tara a gidan abubuwa da dama sun faru wanda tuni na gano wannan tafiyar cike yake da Gargada,

Allah ya sauwaƙe, ki tashi mu tafi gida shi da ya kwanto kura yasan yadda zai yi da ita ai.

Abba ya fa

ɗ

a cike da

ɓ

acin rai ya juya ya soma fafiya, Hajiya ma kasa magana tayi dan duk bayanin Alhaji gaskiya ce zuwa yanzu bata hango Hamid zai cigaba da samun

farin ciki in dai a gurin Madina ce, sam bata yiwa yarinyar kallon mai hankali balle tarbiyya, sun riga da sun tafka kuskure, Sakinar da suke ganin ita mara mutunci ce ashe gwara ita sau dubu da Madina, haka suka fice a falon ba um ba um-um, Hamid ya dafe

kansa duka biyu yana jin wani abu yana hajijiya da shi, tabbas yayi za

ɓ

en tumun dare dan ya tabbatar da maganganun Abba a bisa gaskiya suke, gashi ba aje ko ina ba ya fara gane kurensa, Madina miƙewa tayi tana ya mutse fuska.

Duk yadda zaka

ɗ

aukeni da ka

i da iyayenka to ku

ɗ

auka

ɗ

in, ni ban taso na saba da wahala ba, a kullun rayuwar farin ciki nake ciki wanda Mahaifiyata ke bani, dan haka irinsa nayi mafarkin samu a gidanka, sai dai ashe ni nayi kuskure bansan haka halinka yake ba da tun farko wlh bazan

ta

ɓ

a aurenka ba, yaudarata kayi da tarin soyayya da nuna mini gidanka ne aljannar farin cikina, ina da masoya wa

ɗ

anda samari ne ba su da mata amma saboda kaifin harshenka da yaja linzamin soyayyarka a zuciyata, nace dole sai kai, dan haka wajibi ne ka shay

ar dani wannan Aljannar duniyar da ka riƙa hasko mini, dan zama ni da kai mutu ka raba, ba zaka lasa mini zuma a baki ba kace ka daina ba wlh, dan baka isa ka mayar dani ƙaramar bazawara ba ka gama tatse albarkatun jikina ba ehe Alhaji Hamid.

Madina ta fa

ɗ

a tana tafa hannunta cike da tsiwa kana ta wuce zuwa

ɗ

akinta ko a jikinta, Hamid sauke Hannunsa yayi ya juya bita da kallo harta shige

ɗ

aki, wani irin yanayi yaji a zuciyarsa na ƙunci wanda bai san ya zai misalta shi ba, yana so ya gano meya aikata ne hak

a da Allah ya jarabce shi da auren Madina wacce ta zame masa ƙadangaren bakin tulu, haka yaji yana niman inda zai fitar da magana ko yayi kuka, wata ƙila ya samu sassaucin ƙuncin da yake ji a zuciyarsa da bai ta

ɓ

a jin irinsa ba, innalillahi wa inna ilaihir

raji'un! ya soma ambata a ransa, ya bu

ɗ

e baki yana cewa.

Allah na tuba ka yafe mini ban san ko akwai abinda na aikata na kuskure ba da ƙaddara mini auren yarinyar nan ba, ni dai nasan nayi shi ne domin samuwar farin ciki, sai dai ba aje ko ina ba ka fara

jarabtata da zazzaafar sakamako wanda ban san me na aikata ba.

Ya ƙare maganar cikin fitar hawaye guda

ɗ

aya mai zafi daga idonsa na dama, sauke ajiyar zuciya yayi ya miƙe ya wuce

ɗ

akinsa ya kwanta, haka ya dinga saƙa da warwara akan meya aikata ne daya c

ancanci wannan hukuncin, har barci ya kamashi bai hango komai daya yi mara kyau ba, dan ko daya nima auren Madina bai ta

ɓ

a kama hannunta da sunan suyi wata masha'a ba, duk so da Sha'awarta da yake fuzgarta basu ta

ɓ

a yin wani kuskure da shai

ɗ

an ya jasu suyi

ba, hasalima Madina kunyarsa take ji shi kuma bai ta

ɓ

a tunanin yayi mata wani abu ba har sai da suka yi aure ya samu damar sauke duk wani kwa

ɗ

ayinsa akanta.

*****

Sakina.

Koda suka isa tasha, motar Kano ta nima wato drop dan bata so ta takura kuma bata

so dare yayi mata a hanya, nan aka samo mata wata mota sharon ta shiga ta biya ku

ɗ

i mai yawa kamar yadda driver ya yanka mata, haka ta zauna mazaunin tsakiya da kayanta a gefe ba

ɓ

ata lokaci suka kama hanya, sai dai suna wuce unguwar Rigachikun ta kashe w

ayarta gaba

ɗ

aya ta mayar a jaka ta lumshe ido tana jin kamar ta koma saboda yaranta, amma in ta tuno da wulaƙancin Hamid sai taji gwara tayi nesa da shi ko hakan zai zama silar samun 'yancinta, shiyasa bata yi tunanin zuwa ko ina ba sai Kano gidan anty Jal

ila wacce tasan zata tsaya mata sosai fiye da 'yan uwanta na jini. Yaya Jalila tana da zafi da fa

ɗ

a sosai bata

ɗ

aukar raini shiyasa a dangi kowa yake shakkar abu ya ha

ɗ

asu, dan zata wanke mutum daga biri har wutsiya, kuma ba a gulma ko munafurci da ita, ir

in macen nan ne da ake tsage gaskiya da gaskiya, tasan in har taje mata da matsalarta zata yarda ta zauna a gurinta domin ta huta tare da wasu shawarwari da zata samu. Haka ta riƙa shakar iskar hanya tana jin wani sanyi yana ratsa jikinta wanda take nan ta

ji kamar zazza

ɓ

i take ji, hakan yasa ta

ɗ

aga glass

ɗ

in gefenta ta cigaba da kallon hanya, tun gari na da haske har duhu ya rufe sai hasken fitulun motoci da suke karakaina a hanya. Awa biyu da rabi ya kaisu cikin garin Kano saboda ba tsaye tsaye a hanya da

nma ana ta gyaran hanya da ƙila tun akwa biyu sun isa, direct gidan driver ya wuce da ita tana yi masa kwatance har suka isa, ta sauka da kayanta ta yi masa godiya dan tun kafin su tawo ta sallameshi shima godiya yayi mata ya juta mota ya wuce, ita kuma ta

ƙarasa gate

ɗ

in gidan ta buga, mai gadi ya bu

ɗ

e, ganin baƙuwa ce ga kaya ya bu

ɗ

e mata da sauri tare da amsar akwatin ta shiga ya bita da kaya a baya, ta kama hannun ƙofa ta tura da sallama, da sauri anty Jalila ta juyo dan ta bawa ƙofa baya tana zaune a k

ujera, ganin Sakina ce yasa ta miƙe tana salati.

Sakina dama nan kika tawo? duk kin tashi hankalinmu, yanzu na gama waya da yaya Ali yana tambayar ko nan kika zo? nace masa a'a ashe kina hanya, aiko bari na kirasu yanzu na shaida musu dan hankalinsu ya kw

anta.

Dan Allah yaya karki kira kowa bana son susan ina nan tukuna.

Sakina tayi maganar tana ƙarasawa gaban Jalila da sauri ta amshe wayar data fara dannawa, ido Jalila ta bita dashi kamar mai karantar wani abu a fuskarta, daga bisani ta sauke numfashi t

a huya gurin kayan da mai gadi ya aje ta jasu zuwa

ɗ

akinta tana cewa.

Muje kiyi wanka kiyi sallama kici abinci sai muyi magana.

Ba musu Sakina tabi bayanta zuwa

ɗ

akinta, ita Jalila da kanta ta ha

ɗ

a mata ruwan wanka Sakina ta shiga tayi tare da alwala ta

fito, Jalila ta miƙa mata wata doguwar riga mara nauyi kamar ta barci.

Ki saka wannan dan tsayawa bu

ɗ

e akwati ki ciro kaya zai

ɓ

ata lokaci.

Sakina ta amsa kana ta shirya ta gabatar da sallar magrib da Isha'i tare da shafa'i da wuturi, data idar sai ga Ja

lila ta shigo da tire cike da abinci, tuwon shinkafa miyar zogale tare da kunun aya sai soyayyar naman rago da aka ba

ɗ

eshi da yaji kamar suyar salla kona mai jogo, ta dire mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login