Showing 96001 words to 99000 words out of 111085 words
data shigo ta rainata har take jifarta da maganganun da Hamid ke fa
ɗ
a mata, ya sauke ajiyar zuciya.
In Sha Allah zan gyara kuma nagode da tunatarwa, Allah ya bani
ikon yin adalci a tsakaninku.
Ameen ya rabbi. Kaga ba dan ina aiki a kitchen ba da nayi maka rakiya mun je mun dawo.
Ta fa
ɗ
a tana murmushi, Hamid ma murmushin yayi yana cewa.
Kuma fa, sai dai zan so ki gama girkin da wuri na dawo na ganki irin ba sauƙi
ɗ
in nan, yadda zaki ƙara rikitani in susuce akanki, dan fa ban mance da jiya ba yana cikin kundun tarihina.
Dariya sosai Sakina tayi shima yana tayata a haka suka rabu ya wuce, Sakina ta samu kanta cikin tsantsar farin cikin da baya misaltuwa, gani take y
i tamkar an sauya mata Hamid, wai shine yanzu suke hira har yake yi mata barkwanci, lallai giwa tayi lafiya, sai ta
ɗ
aga hannunta duka biyu tana cewa.
Allah nagode maka daka sauya mini mijina ka ƙara mana zanan lafiya da kwanciyar hankali.
Sai ta sauke h
annu tana cewa amin a ranta ta cigaba da aikin da take yi.
Hamid koda ya fita wajen abokinsa ya nufa inda suka saba ha
ɗ
uwa suyi hira, shine ma dai bai damu da zuwa sosai ba amma kusan kullun suna ha
ɗ
uwa sai dai su bashi labarin abinda suka tattauna in sun
ha
ɗ
u. Sai bayan sallar magrib yaje
ɗ
auko Madina ya ki shiga ya kirata a waya akan ta fito su wuce, ta fito falo tana turo baki.
Ni wlh dama kin ce masa kwana zanyi tunda ba nice da girki ba, sannan ma ai bani da lafiya.
Maza ki wuce ki tafi bana son shi
rme, ai da yake yasan baiyi mutuncin ba sai ya tsoge a waje ya ki shigowa, gaskiya Madina ba kiyi dacen miji ba, haka zaki ta lalla
ɓ
awa tunda kin riga kin shiga, Allah ya kyauta kawai zan ce.
Kai mom Hamid fa yada da da
ɗ
in sha'ani matarsa ce kawai ta juya
masa kai da asirinta.
To ta Allah ba tata ba, duk da ni bana son shiga hurin malamai amma ya zama dole na shiga na fita dan na sama miki farin ciki, ban yarda ki zama mara galihu ba a gidansa.
Cewar momy ta fa
ɗ
a tare da miƙewa ta kama hannunta ta rakata
tsakar gida, anan suka yi sallama ta fita ta same shi ya bu
ɗ
e mata gefensa ta shiga ta zauna ba tare da tace masa komai ba, ya kunna mota suka wuce. A hanya sai da ya tsaya yayi musu siyayya dangin kayan fruits da kuma biscuit na 'yan makaranta, Madina ta
ce zata sha youghot sai ya siya mata ha
ɗ
e da ice cream gaba
ɗ
aya gidan kana suka wuce gida.
Kamar yadda Hamid ya more a daren jiya yau ba bai yi ƙasa a guiwa ba ya gwangwaje, itama Sakina ta bada ha
ɗ
in kai yadda ya kamata, haka suka wayi gari cikin farin c
iki da kaunar juna. Tun daga wannan ranar ya zamana Hamid yana
ɗ
okin girki yazo hannu Sakina dan kullun ƙara rikita masa lissafi take yi da sabon salonta, Madina kuwa sai da ta shafe sati na jinya daga bisani ta warke, sai yawan kwa
ɗ
ayi da ƙarin kazanta, s
auƙinsu mai aikinta Ladi tana zuwa kullun tana yi mata aiki harma da Sakina, dan yanzu Hamid yace mai aikin ta riƙa share falo da
ɗ
akunansu da mopping, nashi
ɗ
akin ne dai yace bai yarda ba sai Sakina ce ke gyara masa, sannan kuma wanke wanke duka take ha
ɗ
a
wa ta yiwa Sakina sannan dana Madina, abinci kuma Sakina take girma nata da yara in tana da miji ta yi dashi, in kuma Madina ce da girki to mai aikinta ke girka mata nata shi dai Hamid maƙewa yake gurin Sakina yaci ko ya je gidansu yaci a gun Hajiya ko yac
i a waje. Madina saboda wauta har lokacin bata sanar da Hamid tana da ciki ba, ta bari sai aikin da Malam ke yi mata ya kama shi kafin ta fa
ɗ
a mishi yadda ƙila zata samu kyauta a gurinsa
ko ya bata motar da yayi mata alƙawari. Kusan duk bayan kwana biyu sa
i ta shiga gidan maman murja, wanda sun yi mugun sabo sosai kuma Sakina bata san da haka ba, dan bata shiga sabgar kowa sai hidimar gidanta. A haka aka shafe wata
ɗ
aya da sati biyu, wanda yayi dai dai da wata uku da auren Hamid da Madina, cikinta kuma wata
biyu da sati uku, da yake ba tada tumbi bai nuna ba sai ƙiba data yi da fari sosai, Sakina ta gane ciki gareta sai dai kuma tunda Hamid bai fa
ɗ
a mata ba itama tayi shuru da bakinta, kuma shi sam bai sani ba dan bai fiye shiga sabgar Madina ba saboda rashi
n kunyarta da take zabga masa dan ba fasawa tayi ba, ita kuma da yake shashsha ce bata fa
ɗ
a masa ba har lokacin.
A ranar Asabar Salim ƙarnin su Hamid ya dawo daga Sokoto ya kammala karatunsa, a washe gari kuma su Asma suka zo garin domin bikin wani
ɗ
an ka
nin Hajiya da za ayi, sunta saka rana zasu zo akan su duba jikin Hajiya tun sadda tayi fama da gudawa ita da Hamid amma basu samu zuwa ba har dai Hajiya ta dakatar dasu akan su bari sai bikin su zo gaba
ɗ
aya, to da cikin Madina suka sauka dan sunyi alwashin
sai sun haifeta akan rashin mutuncin data yiwa Hajiya dan basu mance ba. Sakina kuwa tun jiya Hamid ya fa
ɗ
a mata da zancen zasu zo hakan yasa ta wayi gari da shirya musu gurasa da rana, saboda bata mance da hu
ɗ
ubar Anty Jalila ba akan ta kyautata musu wat
a ƙila wannan yasa ta samu sassaucin ƙiyayyar da suke yi mata. Bayan ta sallami yara masu zuwa hadda, Hamid kuma yana barci a
ɗ
akinsa dan ranar baya fita sai da rana, hakan yasa ta samu damar yin gashin gurasa, mai yawa tayi dan suma shi zasu ci da ranar,
Allah yasa ba ita ce da girki ba dan haka zuwa ƙarfe sha biyu ta gama, ta ha
ɗ
a musu shi a babban kwanon samira da ha
ɗ
insa gaba
ɗ
aya yaji ƙulu da mai da kayan miya data yanka, data gama ta shiga
ɗ
aki tayi wanka ta shirya cikin rigarta ready made cikin wanda
ta siya a kano, ta yi kwalliya daidai misali kana ta gabatar da sallar azahar, data idar sai tayi rollin da
ɗ
an kwalin kayanta ta fito ta shiga
ɗ
akin Hamid ta samu ya fita masallaci, kitchen ta wuce ta
ɗ
auki wannan samira data ha
ɗ
a gurasa ta fito zuwa sash
in Hajiya.
A falo ta samesu suna ta zuba hira, ta shiga da sallama ta zauna a carpet kamar yadda ta gansu zaune, ta dire musu kwanan a gabansu tana cewa.
Maraba da baƙin Abuja da Zaria fatan kun iso lafiya.
Ta ƙare maganar fuskarta
ɗ
auke da fara'a, sum
a da dariyarsu suka amsa mata nan suka shiga gaisawa, Hajiya tace.
Ashe kin samu labarin zuwansu.?
Eh tun jiya Hamid ya sanar dani zasu zo, nasan kuma sunfi zuwan wuri shiyasa nayi tunanin sun ƙaraso, nace bari nazo mu gaisa gama gurasa nayi ta marmari n
asan Kubura kina sonsa sosai.
Ta ƙare maganar tana bu
ɗ
e musu samirar, ai basu Asma ba hatta Hajiya sai da ta ha
ɗ
iye miyau tana cewa.
Sannu da aiki, ashe kin iya yin gurasa ko aiki kika bayar ayi miki?
A'a nice nayi, zuwana Kano na koya a gurin anty Jali
la.
Gaskiya kuwa gashi tayi kyau kinyi ƙoƙari Allah yayi albarka, dama bamu gama abinci ba kinga sai muci wannan, ke Jidda jeki
ɗ
auko kula a zubawa Alhaji dan nasan zaici in dai girkin Sakina ce.
Hajiya ta ƙare maganar da Jidda, nan fa aka shiga rabon gu
rasa Sakina tana zaune suna hira a haka Hamid ya shigo ya same su, yaji da
ɗ
in ganin Sakina tare da 'yan uwansa ya zauna yana cewa.
Hajiya ina kuka samu gurasa?
Au ashe kaima baka san da ita ba, to Sakina ce tayowa ƙannenka gashi kowa zai ci na marmari.
Aiko banda labari, Madam irin wannan kayan arziki ba zaki sanar dani ba, to ina nawa.?
Yayi maganar yana duban Sakina yana dariya, ta bashi amsa tana murmushi.
Naka yana gida na aje maka.
To kuwa ki sani yau shine abincin rana na dana dare.
A'a fa na r
anar dai, dan girkin dare yana gurin Amarya.
Ta fa
ɗ
a tana dariya. Ya muskuta ya saka hannu a plate
ɗ
in Asma da aka zuba mata ya
ɗ
auki
ɗ
aya yakai bakinsa, sai da ya tauna yaji da
ɗ
insa kana ya kalli Sakina.
Wai dama kin iya wannan abun shine bakiyi mana, a
iko wlh yau ko kinƙi dole ki aje mini shi da dare dan shine abinci na.
Ya fa
ɗ
a cike da santi, Kubura ta sa dariya.
Yaya ko dai ayi maka waigi ne dan na kula kamar santi ya
ɗ
ibeka.
Nan dai suka dinga barkwanci wa juna suna dariya, haka Sakina ta kai har
aka gama girkin nan gidan aka saka mata ta zauna taci ta ƙoshi, dan ita tunda tayi gurasar taji ya hau kanta ta bari da dare zata ci tunda tayi mata auki zai kaisu suci da dare. Wajen ƙarfe uku tabar gidan suka rabu cike da mutunci, bayan fitarta ne Hajiya
tace.
Wlh naji da
ɗ
in sauyawar Sakina da haka take yi ina ma Hamid zai ƙara aure, koda ya kara ai da muna tare da ita.
Wlh nima dai naji da
ɗ
in karramamu data yi Allah yasa ta
ɗ
aure, kinsan wasu matan basa dawowa hayyacinsu sai anyi musu kishiya, kuma kar
in abun burgewa ba kuga tayi shiga mai kyau ba da kwalliya, gaskiya kam ta sauya sosai.
Hmmmm ni ne zan gaya muku Sakina ta dawo Asalin sunanta, wato ta zame mini Natsuwa a gidana.
Cewar Hamid, Hajiya kam ba ƙaramin jin da
ɗ
in furucinsa taji ba, haka suka
cigaba da hirar zumunci.
_Gobe In Allah ya kaimu ba zan samu typing ba an yi mini haihuwa zani suna sai jibi In Sha Allah_
[8/22, 7:45 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 40.
Bayan sallar la'asar Sakina t
a shirya ta shiga gidan Maman Murja dan su gaisa dan tunda ta dawo take son shiga bata samu hali ba, hakan yasa ta kira Hamid ta sanar dashi zata shiga maƙota yace sai ta dawo amma karta jima, a haka suka rabu ta saka hijab ta fice ita ka
ɗ
ai dan Rauda tana
gidan Hajiya tun
ɗ
azu. Koda ta shiga gidan Maman Murja da fara'a ta tarbeta nan suka yada zango a falo suka shiga gaisawa, daga bisani suka shiga yin hira har maman Murja tana cewa.
Sakina kin zama Hajiya ganinki sai an cika form, kwanaki na samu labarin
kin bar gidanki nayi ta nemanki a waya ban samu ba, haba Madam yanzu an wuce lokacin yaji kodan yaranki zaki zauna, sannan na zo miki da hanya mai
ɓ
ullewa amma kinki amsar tayina.
Maman Murja kenan, ni dai wlh bazan sa
ɓ
i Allah ba saboda Namiji in gyara d
uniyata in
ɓ
ata lahirata, sisina bazan kashe akan Hamid ba, na kai ƙararsa gurin Allah kuma Alhamdulillahi ina kan samun nasara, dan haka ki aje wannan maganar ni na shigo ne mu gaisa dan mun jima bamu ha
ɗ
u ba.
To ai shikenan na rabu dake amma ki sani anc
e in kana da kyau ka ƙara da wanka, sannan ke in bakya niman maganin da zai share miki hawaye ba to ita amaryanki ba zata zauna ba dan na ganta idonta a feƙe yake, anya ma kina yin zaman lafiya da ita kuwa?
Lafiya lau Alhamdulillahi muke zamanmu, babu mai
shiga harkan wani tunda girkinmu ba
ɗ
aya ba kowa da nashi.
Amma ace falo guda komai naku
ɗ
aya a raba girki, lallai Hamid yana ƙoƙari da aikin cefane. Ai da nice ke hatta amaryar zan mallaketa sai abinda naso tayi a gidan, wlh sai na mayar da ita 'yar aik
i tayi ta mini bauta tunda harta aure mini miji, koda yake ni No kishiya a gidana dan bazan bari ba.
In kuma Allah ya ƙaddara miki baki isa ki sauya ba, kedai ki nima za
ɓ
in Allah da fatan alkhairi, sannan ni bazan biyewa son zuciya na sa
ɓ
awa Allah saboda
wani jin da
ɗ
in duniya da ba zai tabbata har abada ba. Mutuwa ka
ɗ
ai ta isa bawa wa'azi. Ni nazo ne ma dan in tallata miki hajata dan ina so na fara sayar da kayan mata dan tayar da koma
ɗ
a, nasan ke me mutane ce ki tayavni talla in har kika kawo mini custome
rs kema kina da kasonki.
Kai Sakina! kice da zafinki kika dawo gidan Hamid, aiko na tayaki murna dan zama haka ba da
ɗ
i, ga kuma kishiyarki tana aikinta kinyi wa kanki farar dabara.
Cewar maman Muryar cike da murna a fuskarta, nan dai Sakina ta shiga yi m
ata bayanin kayanta dan har tayi oder
ɗ
insu q gurin Surayya daga Kano jibi za a aiko mata dasu, dan Hamid ne ma ya bata jali mai tsoka, shima yaji da
ɗ
in business
ɗ
in da zata yi hakan ya tabbatar masa da Sakinarsa ta fara wayewa da rayuwa, nan dai sukai ta
hirar kasuwancin suka aje zancen malamai, dan in Maman Murja zata kwana tana yiwa Sakina zancen ba
ɗ
auka zata yi ba.
....
Madina da yake yau ba tada aiki tana kwance a gado mai aikinta kuma ta shiga kitchen dan ta
ɗ
aura mata abincin dare inta gama sai ta
wuce gida. A lokacin ne su Asma suka shigo falon suka yi sallama, Ladi ta leƙo daga kitchen tana amsa musu, ganin su Asma ne ƙannen Hamid yasa ta gaishesu dan ta ganesu tun lokacin biki, suka tambaye ta Madina tace tana
ɗ
aki bari ta kira musu ita, Kubura t
ace barta zamu sameta a can, Ladi tana jin haka ta koma kitchen ta cigaba da aikinta. Asma ce ta fara yin gaba zuwa
ɗ
akin Madina dan basu bi takan Sakina ba saboda ba gunta suka zo ba, falonta suka fara bu
ɗ
ewa suka shiga nan suka yi sa'ar taddata kwance ka
n doguwar kujera ga popcorn a kusa da ita tana ci wanda momy tayi mata aikensa, tana ganinsu ta miƙe ta zauna suna kallon juna, a yadda taga fuskokinsu ya tabbatar mata da ba alkhairi ya kawo su ba dan haka ta yatsine fuska.
Lafiya zaku shigo babu ko sall
ama?
Kema kinsan lafiya ba zata kawo mu ba dan baki isa muzo inda kike ba hakanan, ashe dama ke matsiyaciya ce ba kida mutunci bamu sani ba, muna yi miki kallon salaha mai tarbiyya ashe 'yar mace ce ke ba kwa
ɓ
a, ki rasa wacce zaki raina ki ciwa mutunci sa
i Hajiyarmu, to mun zo mu muna miki cewa Hajiya tana da 'ya'yan da zasu
ɗ
auki mataki akan duk 'yar iskan data nima takata.
Cewar Asma tana nunata da yatsa, Madina ta miƙe tana 'yar dariya tare da tafa hannu.
Ku koma ku kira Hajiyar ni da ita zanyi ba kub
a cikon benci, ashe ma tsorona take ji data aiko mini ku. To bari kuji wlh duk wanda yayi mini kan kara sai nayi masa na itace, rashin mutunci na iya shi kala kala kuma ina dai dai daku, kai inma akwai wa
ɗ
anda suka fiku ina daidai dasu, ni ba Sakina bace d
a zasu laftawa rashin mutunci ku zauna lafiya.
Haka kika ce? Kaji 'yar iska Hajiyar tamu zaki yiwa raini.
Cewar Kubura tare da isa inda Madina take a zafafe ta ko
ɗ
a mata mari, aiko bata sauke hannunta ba Madina ta rama, nan fa dambe ya kaure, Asma tana g
efe sai girgiza jikinta take yi tana kiran number din ƙaminsu Salim, yana
ɗ
agawa tace.
Ka zo gidan yaya Hamid amaryarsa ta zagi su Hajiya.
Kutumar kaza kaza, ai wlh gani nan zuwa dama tunda na dawo Hajiya take bani labarinta, ashe ba tada mutunci.
Asma
ta kashe wayar bata amsa masa ba, ganin fa
ɗ
ar nasu kamar na kaji suke yi yasa ta cire gyale ta aje ta rufar musu, wato suka ha
ɗ
u ita da Kubura suna dukan Madina, tun tana kai musu hannu danta rama harta kasa ta shiga kare kanta, dama da niyyar suyi mata du
kan tsiya suka zo gidan, dan sunce koda Yayansu zai rama mata sai sunyi maganin iskancinta ko gaba ba zata sake yiwa Hajiyarsu rashin kunya ba. Madina ganin fa sun tarar mata gata dama ba kwari ba nan ta fara kuka tana zaginsu, amma basu fasa dukanta ba ha
kan yasa ta nufi ƙofa da mugun sauri ta bu
ɗ
e ta fita falo, a lokacin ne Ladi ta fito tana tambayar lafiya? dan tun
ɗ
azu take jin hayaniya bata
ɗ
auka daga
ɗ
akin Madina bane, ganin Madina yarkace yarkace yasa ta gane ba lafiya ba, su Asma suka fito suna haki
a lokacin Salim ya shigo yana cewa ina take? ya ƙaraso ciki Kubura ta nuna masa ita, dama bai