Showing 12001 words to 15000 words out of 111085 words
sauran matan ma wasu daga ciki suka shiga yaba kyawun a
marya da suka ga hotonta a wayar Asma dan tuni Hamid ya ha
ɗ
asu suke zumunci a waya, Sakina tana jinsu amma tayi kamar bata gurin, tasan da biyu suka yi haka tunda sun san tana nan, fitowar Hajiya yasa ta miƙe da sauri ta isa gareta ta tsuguna tana gaisheta
Hajiya tace.
A'a miƙe bana son wannan ladabin naki na munafurci, ni da baki
ɗ
auke ni da mutunci ba ina zaki yi mini ladabin kunama.
Jikin Sakina a sanyaye ta miƙe tsaye ganin duk hankalin mutanen falon ya dawo gunsu, ta kuma sake miƙa mata wani gaisuwar
Hajiya tace.
Lafiya lau, dama na aika kizo ne akan na ji me kike taƙama da shi ne da ba zaki zo ki ji ya yanayin bikin zai kaya ba, sannan ace su Asma sun fi sati a garin nan kin kasa leƙosu, ai koda ƙannen Hamid ne matafiya ne su, ya kamata ki leƙo ku g
aisa.
Ayi hakuri Hajiya nayi zaton da suka zo sun koma ganin basu leƙo ba.
Hmmm ni ma da baki
ɗ
aukeni a bakin komai ba balle su, Allah dai ya kyau da wannan baƙin halin da kika sauya, ga akwati can kije ki gani na amarya kar ki ƙorafin ba a nuna miki ba.
To Sakina tace zuciyarta yana yi mata suya, haka ta matsa kusa da kayan akwatin bata saka hannu ba sai ta shiga kallo saboda wasu mata suna
ɗ
aga su, data gama iya kallon da zata yi ta juya ta isa inda Hajiya take zaune tace cikin dakiya.
Hajiya na gama
kallon kaya sunyi kyau Allah ya sanya alkhairi ya bada zaman lafiya, zan iya tafiya ko akwai wani aikin da zanyi muku.
Ohhh Sakina har kin gama kallon kayan da yawa fa.
Ai Umma ko hannu bata saka ba balle ta
ɗ
aga kayan ta gani.
Cewar Kubura.
Hmmm ai ba
ƙ
in kishi ba zaisa ta ta
ɓ
a kayan ba, kuma hakan bazai sa a fasa ba aure ba fashi, in kinso ki gyara halinki in kin ƙi kuma kya yiwa kanki dan yanzu Hamid ya samu mai faranta masa tunda ke kin zama mai baƙin hali.
Cewar Hajiya, Hawayen daya ciko idonta ya
zubo a kuncinta tama kasa magana, domin taruwa mata suka yi kowa yana fa
ɗ
ar abarkacin bakinsa, ƙanwar Alhaji ce data fito ta ji abin da suke mata yasa tayi magana tana cewa.
Haba da wanne zata ji? da auren da zai yi ko da wannan ƙorafin naku, idan ma tayi
kishi ai halal ne tunda da zuciya a ƙirjinta, kuma ko wace mace dole taji zafin haka, Sakina wuce abinki Allah ya kawo amarya lafiya kowa halinsa shi zai zaunar dashi, aniyar kowa zata bishi, kije ki ƙara haƙuri wata rana sai labari.
Mariya me kike nufi
da maganganunki? nifa bana son tashin hankali in kinsan ba alkhairi ya kawoki ba ki kama kanki.
Cewar Hajiya cike da ha
ɗ
e rai, Mariya ta juya tana kallonta.
Ni da gidan
ɗ
an uwana aiko ba inda zani sai naga abinda ya turewa buzu na
ɗ
i, kuma wlh duk wanda y
ace tukunyar wani ba zata tausa ba to nashi ko zafi bazai yi ba, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta.
Nan fa hayaniya ya kaure, aka samu 'yan uwan Hajiya suka shigar mata, Mariya ganin ita ka
ɗ
ai ce ta fara zuwa a 'yan uwan Alhaji hakan yasa ta kama han
nun Sakina suka fito suka wuce gidanta, a falo suka yada zango ta dinga bawa Sakina haƙuri tana tausanta, ita ko banda zubda kwalla ba abinda take yi dan shine ka
ɗ
ai zai sa taji sauƙin zafin da zuciyarta keyi mata, sunyi mata wulaƙancin da ba zata ta
ɓ
a man
tawa ba, Mariya sai da ta tabbatar da ta samu natsuwa kafin tayi mata sallama ta koma sashin su Hajiya.
Wannan
ɗ
an sa
ɓ
anin daya faru sai da su Asma suka fa
ɗ
awa Hamid bayan ya dawo, suka fa
ɗ
a masa ƙarya da gaskiya, haka ya shigo sashinsu ya tasa Sakina a
gaba ya dinga yi mata fa
ɗ
a, ƙala bata ce masa ba har ya kai aya a zantukansa ya wuce
ɗ
akinsa, murmushin takaici tayi hawaye yana zuba a kuncinta ta juya ta shiga
ɗ
aki tana jan salatin Annabi s.a.w wanda hakan shine zaisa taji sauƙin halin da take ciki, ya
nzu ta ƙara tabbatar da auren nan da zaiyi babu wani sauƙi da zata samu kanta a ciki, dan alamu sun nuna wani sabon baƙin ciki ne zata ƙunsa, kiran daya shigo wayarta yasa ta miƙe ta isa inda ta saka chargy ta ciro sai taga yaya Umma ce, ta
ɗ
auka da sauri
dan ya kusa tsinkewa.
Sakina ina wuni ya shirye shirye.
Alhamdulillah yaya Umma.
Ta fa
ɗ
a cikin rawar murya.
Yana ji muryanki wani iri meke damunki?
Yaya Umma bazan iya jurewa da zaman gidan Hamid ba wlh na karaya.
Ta ƙare maganar cikin matsanancin ku
ka, Yaya Umma ta miƙe daga zaunen da take a tsakar gida ta shiga
ɗ
aki tana cewa.
Sakina hakanan zaki cije ki jure, wlh jarawaba ce ki
ɗ
aure zaki ci In Sha Allah, kuma dama aski in yazo gaban goshi yafi zafi.
Yaya
ɗ
azun su Hajiya sunci mini mutunci a cik
in mutane yanzu kuma Hamid ya gama sauke mini nashi masifar, ina zan saka raina, ni ban hanashi aure ba ban tayar da hankalina nace kar yayi ba, amma duk da haka ban fita ba agun danginsa da kuma shi kansa, basa ƙaunata basa son zaman aurena da shi gwara n
a bawa Shalelen amarya guri tazo ta basu farin cikin da suka ce na kasa basu.
Kul! kul na kuma jin kin ambaci wannan maganar, ki dage da nafilar dare kina fa
ɗ
awa Allah damuwarki In Sha Allah zaki samu sassaucin halin da kike ciki. Ina ganin jibi zan zo ga
ba
ɗ
aya har sai an kammala biki saboda babansu ya tafi ƙauyensu zai kwaso amfanin gona na nomar daya yi.
To yaya kizo mata tun gobe ganinki zai sa na samu natsuwa tunda ba kowa a guna, abin yayi mini yawa ina cikin damuwa.
Haba Sakina yayi wuri inna zo go
be, amma zan zo sai na tafi da yamma washe gari sai na tawo gaba
ɗ
aya.
Yauwa yaya Umma nagode Allah ya kaimu sai kinzo.
Cewar Sakina tana
ɗ
an jin wani sanyi a ranta.
Matar Hamza ma jibin tace zata zo dan nayi magana da shi.
Aiko naji da
ɗ
i wlh Allah ya k
aimu.
Yaya Umma ta amsa da amin kana suka yi sallama.
Madina.
[7/3, 6:55 PM] Rahma Kabir: *ƘAZAMAR AMARYA*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 7.
Madina tunda biki ya matso ta zama busy, shirye shiyre take ba kama hannun yaro duk wani gya
ra daya tace tayi to tayi shi, dan har gyaran jiki aka soma yi mata kusan kwana biyat da ya wuce, yanzu ma jikinta an shafe shi da kurkur ha
ɗ
e da kayan gyaran fata tana zauna daga ita sai
ɗ
aurin ƙirji akan wata kujerar ƙarfe a
ɗ
akinta, da ƙawayenta da mai
gyaran jiki duk suna
ɗ
akin sai hira suke yi, yayarta Aisha ce ta shigo riƙe da ƙaramin
ɗ
anta da take goyo, Madina tace.
Anty Aisha har masu kawo lefen sun wuce ne?
Eh sun tafi, Kausar zaku iya zuwa ku ga Akwatin.
Aisha ta fa
ɗ
a tana duban ƙawayenta, da s
auri suka miƙe duk suka fice har da mai gyaran jikin, dama tayi hakan ne domin su bata guri dan tayi magana da Madinar, Aisha ta kalleta da kyau tana cewa.
Gaskiya Madina ban ji da
ɗ
in ganin lefenki haka ba, Hamid yayi ƙaranta da yawa a yadda muke zaton za
i yi miki ba haka yayi ba, domin kuwa babu kaya sosai kwata kwata zannuwa basu fi talatin ba sai sauran kayan tarkace, kuma akwati set
ɗ
aya ne guda hu
ɗ
u da kit wanda mukai zaton ki samu set biyu.
Madina zabura tayi ta miƙe tana zaro ido cike da damuwa ta
dafe ƙirjinta tana cewa.
Amma Hamid yaci mutuncina ban zaci haka ba wlh, yadda yake ta kuranta ya kashe mini ku
ɗ
i a akwati, muje na gani.
Ta fa
ɗ
a tana bin gefen Aisha ta fita zuwa falo, Aishan ma bayanta tabi, suka tadda mutanen falon sunata
ɗ
aga kaya sa
i yabawa suke yi, mom dai ta
ɓ
e baki tayi tana cewa.
Ni kam Wlh bai burgeni ba lefen, yadda dai nasan Hamid yana da ku
ɗ
i ai Madina tafi ƙarfin wa
ɗ
annan kayan.
A'a fa Hajiya wlh yayi ƙoƙari domin duk zannuwa masu tsada ya saka babu na banza a ciki.
Cewar
wata kasar momy, Madina ji tayi idonta ya kawo kwalla dan gaba
ɗ
aya ganin kayan baisa tayi farin ciki ba sai damuwa data samu kanta a ciki musamman furucin mom data yi, momy ta mele baki.
Hajiya Sa'a yaron fa yana da mugun ku
ɗ
i wlh, kawai dai ya nuna shi ƙ
aramin mutum ne amma yadda yake da arziki ya dace yayi kayan da suka fi haka, yace ma zai bata mota ai ya dace yasa key
ɗ
in a ciki.
Nan dai mutanen falon suka shiga mayar da magana wasu suna yaba kaya wasu kuma suna zancen ƙila ƙaryar arziki yayi musu amm
a yadda madina take da kyau da ilimi ai ta wuce wa
ɗ
annan kayan, da sauri Madina ta juya zuwa
ɗ
akinta ta fashe da kuka, jikinta yana rawa ta
ɗ
auki wayarta ta kira Hamid bugu
ɗ
aya ya
ɗ
auka yana cewa.
Amaryata kuma farin cikin Hamid ya aka yi.?
Abdulhamid.
Madina ta ambata cikin kakkausar murya, Hamid dake zaune saida ya gyara zama dan bai ta
ɓ
a jin ta ambaci sunansa gaba
ɗ
aya kaitsaye irin haka ba, yace cikin bata dukkan matsuwarsa.
Meya faru ne Madina? naji muryarki wani iri.
Dole kaji muryata haka domin
ka bani mamaki, yanzu fisabilillahi ban fi ƙarfin kayan daka saka a akwati ba, duk ku
ɗ
in ka ace akwati set
ɗ
aya zaka yi mini sannan kaya 'yan ka
ɗ
an, gashi kasa family sai ƙorafi
suke yi acewarsu yadda na ha
ɗ
u ga ilimi bai dace aga akwatina haka ba, sannan
kace zaka bani mota ai kamata yayi ka saka key
ɗ
insa a cikin akwatin.
Haba Madina ya kike magana kamar baki san yadda na keta fafutukar faranta miki ba, kin kuwa duba kayan ciki gaba
ɗ
aya kuwa, to babu zanin daya gaza dubu sha biyar a ciki daga haka ne zuw
a dubu
ɗ
ari biyu da wani abu fa, duk kayan ciki masu tsada ne, ai in baki yaba mini ba bai dace ki kushe mini ba, dan haka ni gaskiya abinda zan iya yi miki kenan. Maganar mota kuma ni ban iya ƙarya ba bazan saka key
ɗ
in a ciki ba haka nayi niyya, idan kin
zo gidana sai na baki.
Haka ma zaka ce ko.
To ya kike so nace miki, kinga Madina abinda kika gani shine iya ƙarfina, bazan yi abinda zan dawo ina dana sani ba bana ƙarya a rayuwata kuma...
Bai gama maganar ba ta kashe wayar ta jefar a gado tana matsar
kwalla, Kausar da mai gyaran jiki da suka shigo suka tsaya suna kallonta dan duk sunji wayar da tayi, sauran ƙawayen suna can basu gama kallon akwatin ba, Kausar tace cikin ta
ɓ
e baki.
Lallai sannu Madina ai wannan kukan da
ɗ
i kike yi, ni banga abun kushewa
a kayan nan ba domin Hamid yayi matuƙar ƙoƙari, harda zinari fa a ciki wanda Habib ya fa
ɗ
a mini kusan na dubu
ɗ
ari tatwas ne shi ka
ɗ
ai, ni akwatin da aka kawo na aurena wlh ko rabin naki bai kai ba kuma haka muka kar
ɓ
a muna murna, idan zaki aje rayuwar ƙa
ryar nan da zai fi miki, dan wlh aure da kike gani ba abin wasa bane rayuwar gaskiya da gaskiya ake yi a ciki.
Ai kinsan dani da ke akwai tazara a tsakaninmu, dan haka ni wannan kayan daya zuba bai mini ba wlh, dan yadda yake da arziki yaci ace yayi mini
set biyu.
Hmmm gaskiya ki gode Allah Madina dan wlh zamanin aurena ni akwati biyu da kit na samu, a wannan zamanin da muke ciki na hannu baka hannu kwarya to ki godewa Hamid dan yayi ƙoƙari.
Cewar mai gyaran jiki, Madina ta tashi tsaye a fusace tana kama
kanta.
Kunata wani yayi ƙoƙari kunsan adadin dukiyarsa ne, na fiku sanin waye Hamid, kuma yadda ya nuna mini wlh babu ƙaranta a lamarinta, dan haka kuja bakinku kuyi shuru.
Tana gama fa
ɗ
a ta fice daga
ɗ
akin, da ido suka bita mai gyaran jiki ta ta
ɓ
e baki
.
Gaskiya wannan yarinyar ba tada godiyar Allah, ƙawarki ce ita amma sam halinku ba
ɗ
aya ba tana sa
ɗ
aukar kanta da nisa.
Ga ta ga duniyar nan ai ya isheta riga da wando, kuma in dai namiji ne zata ha
ɗ
u da shi wlh saiya gyara mata zama. Duk wannan gigiwa
r sai ya sauke mata shi
Cewar Kausar cike da jin haushin Madina dan sosai taji
ɓ
acin rai ya kamata, waje ta samu ta zauna tana jan tsaki.
**
Hamid.
Yana zaune ne a office
ɗ
in Habib na company motocinsa yaje dan su yi maganar bikin, a lokacin ne Madina
ta kirashi tana yi masa wannan bayanin mara tushe wanda yasa ransa ya
ɓ
aci sosai, bai ta
ɓ
a zaton haka daga gareta ba yadda take nuna masa salaha ce ita kuma abin duniya bai dameta ba, bayan ya aje wayar ne ya ja tsaki yana duban Habib tare da bashi labarin
abin da ta ce masa a wayar, dariya Habib yayi yana buga table
ɗ
insa.
Madina duniya, kasan fa yarinyar
ɗ
iyar macece sai yadda aka yi da kai, dama tuni na hango maka wannan matsalar saboda suna da buri da yawa dan yayarta babban
ɗ
an siyasa take aure, Kausa
r tasha fa
ɗ
a mini labarinsu, dan haka tunda kasa ƙafarka saika ida wlh, yanzu tashi zaka yi kaje ka ƙara ha
ɗ
a wani akwatin ka kai mata.
Kutt wlh babu abinda zan ƙara kaiwa, haba akwatin dana kashe sama da miliyan biyar shine ba zasu gode ba, a wannan kara
n zan nuna mata bata isa ta juya ni ba wlh, ni bana ƙarya a lamarina.
Ai na zata so ya rufe maka ido zaka yi mata duk abinda tace tana so. To bama wannan ba naji kayi maganar zaka bata mota to ita Sakina ina nata motar ko ka bata nata ne.
Wani sheƙeƙe Ha
mid ya dubeshi yana 'yar dariya.
In bawa Sakina mota karan hauka ne ya cijeni, matar da bata da ilimi taya zata iya da mota, akwai motar dana aje musu a gida in zata fita anguwa, ko Hajiyarmu in zata fita driver yake jansu a ciki, dan haka ita ta isheta b
azan yi asarar ku
ɗ
ina ba tunda ba iya tuƙawa zata yi ba, Madina ma ganin ta iya driving ga kuma aikinta da zata riƙa zuwa yasa nace zan bata mota, kuma Sakina ba fita take yi ba sai tafi wata biyu bata je anguwa ba, dan haka in na bata mota kamar na
ɓ
ata k
u
ɗ
ina ne.
Hamid kana zaton hakan shine dai dai ko, to Wlh bari kaji muddun baka yi adalci a tsakanin Sakina da Madina ba Wlh baza ka ga daidai ba, Sakina ya dace ka fara bawa mota ita da kuke tare kafin Madina, idan baka yi wasa ba wannan son zuciyarka sh
ine zai rusa maka gidanka Allah.
Ba amin ba, kuma na dai gama magana bazan bata mota ba saboda ina da dalili.
To in ba zaka bata mota ba ya zama wajibi ka bata wani abu da zai yi daidai da ku
ɗ
in motar da zaka bawa Madina, wannan shine adalci.
Hmmm sai d
ai fa kayi ni na gama maganata kuma....
Bai ƙarasa maganar ba saƙo ya shigo wayarsa, ya duba sai yaga Madina ce cikin sauri ya bu
ɗ
e saƙon kamar haka.
_Hamid dana san haka zaka yi mini wlh da bazan ta
ɓ
a yarda da maganar aurenka ba, domin ina da samari mas
u mugun ku
ɗ
in da suka fika amma haka na za
ɓ
eka saboda ina sonka kuma ina kyautata zaton
zaka yi mini duk abinda nake so, dan haka ni na fasa aurenka ka aiko a kwashe kayanka da ku
ɗ
in auren bana yi_
Hamid hular kansa ya cire yana duban Habib tare da cewa.
Wannan yarinyar ba tada hankali wai saƙo ta turo mini ta fasa aurena, idan ta isa Allah ya tsinan duk tsawon lokacin dana
ɗ
auka ina tanadin aurenta tace haka.
Wani wawan dariya Habib ya kwashe dashi yana buga table
ɗ
insa.
Da alama taci kai, amma nasan d
ai fa
ɗ
e take yi kawai dan ta rikita ka.
Habib bari naje na ganta mu sasanta dan bazan ta
ɓ
a yarda da wannan mugun wasan ba, wlh har hantar cikina sai da ta ka
ɗ
a, yadda naje jin sonta a raina in tayi mini haka ai kasheni kawai zata yi da raina.
Dariya sosa
i Habib yake yi masa,