Showing 48001 words to 51000 words out of 176330 words
/>
a gaba daya ya yamutse yasha squeezing,fuskar nan ta hqutsine kamar dakalin kashi sqboda tsabar bqcin ran da take,ciki da baqinciki uwa uba kwana biyun nan bata saurari wanka ba,gabanta hadiza ce riqe da kwanon da yasha uwar lamba shinkafa da wake da manqu
li ce aciki da barbaden yaji
''haquri fa zakiyi kici tunda dai na ba gidanki bane,mu bamu da wani miyar nama da zamu zuba miki,kina kallo haka suma qanna naki suka ci''
''idan naci wannam abun Allah ya tsinen hadiza,wai ma meye amfamin kudaden da na ring
a satowa ina kawo miki duk ina kika kaisu
?
,kinje kin rabawa garadan soro sun cinye kuma gashi nan auren da ake ta tattali din ya tsinke....''
da sauri hadizan ta kaiwa bakin kamilar dula kin zata mata tonon silili cikin jama'a
''don ubwnki sharri zakimin
''
''ba wani sharri wlh gaskiya ce da bakina sai a hanani fadan gaskiya ta...''
binta ce ta atse cece kucen ta fito dakin,inna hadizan hannunta dauke da wayar jamilan wadda ta tasamma dubu dari biyu da hamsin tana ta digar ruwa
''kinga aikin da kulu
ta miki''ta fada tana miqa mata wayar
hannu jamia ta dora aka ta kurma ihu tana fadin kulu ta kasheta,ita kadai ce ta rage mata kadara shine don baqar zuciya zata tsoma mata ita a ruwa wallahi to ba zata yarda ba
kukan kura tayi ta banka dakin nasu da g
ugu inna hadizar tabi bayanta tana fadib kada ta nakasta mata yarinya amma ina kota kan uwar bata bi ba
tsaki hindatu taja tana fadin
''jarababbu,ku kashe kanku dai''
naira talatin talatin suka biya zuwa caffe din dake qasansu,su taradda gun cike da
dalibai masu duba jarabawarsu,hakan ne ya dan janyo musu jinkiri,sai da suka jira har kusan shida sannan suka samu sarari,babu jimawa aka gano result din hindatu,ba ita mai jarrabawar ba hatta maryam tayi farinciki ainun,don makin hindatun ya kai dari biy
u da biyar,sai da ta rakata ta samu ota sanna itama ta tari tata ta wuce gidan
🍂🍃🍂🍃🍂🍃
kamar yadda layukan suke shiru gidan shima yake shiru lokacin da ta isa
tana shirin shiga ita kuma na shirin fita kunnenta maqale da waya,cikin dinkin fi
tted gown take na material ruwan zuma,dan siririn dankwalin kawai ta nade wuyanta da shi,ganin ta nufota gadan gadan yasa tayi hanzarin matsawa gefe dob ta lura idab batayi hakan ba tsaf zata bangajeta ne ta wuce,saddiqa ce uwar girman kai da dagawa,duk da
hakan
bata tsira ba sai data yi mata kallon biyi babu taja tsaki bayan ta cire wayar a kunnenta sanna ta wuce
su biyun kuma na kwance cikin kujerun falon wato abida da salma kowa na sabgar gabanshi,abida na charting salma na danne dannen laptop da ba
ta san me tak yi ba,sai t v plasma din falon dake ta zuba aiki babu mai kallonta,babu wadda ta amsa sallamarta cikinsu,bata damu ba sam don ba yau ta soma ganin hakan ba,har zata wuce daki sai ta jiyo motsi cikin kitchen din haka ta sauya akalar tafiyar ta
ta can,baba uwani ce ke wanke kwanuka,ta qaraso kitchen din dafe da bakinta
''ayyah,baaba uwani ayimin afuwa na barki da wahala jiya da yau''murmushi tayi tana taunar goro
''haba 'yar nan ai an zam daya babu komai,ke dai ya kika barosu
?
''
''lafiya baaba
suna gaidake''ta amsa mata tana karbe soson wanke wanken
''to madala muna amsawa,inace yanzu kika shigo gidan
?
''
''eh baaba''
''to amma shine zaki wani,karbi wanke wabke,bani in qarasa kije ki huta ga kiran sallar magariba can anayi''
''a'ah baaba,hab
a gaskiya bazan baki ba,ki huta kema nasan tun jiya kike dawainiya''
''hmmm,wallahi ke dai bari 'yar nan,inda ace abdullahi ne sai ni sai hajiya aikin da sauqi,tofa ina wadan can marasa kunyar yaran kawai sun isa su saka ka gaji,ga daya ta dadu,wancan
tace ita kaza za'a dafa min waccan tace kaza''
wani takaici ya kama marya
''kuma kika dafa baaba
?
''
''to ya za'ayi meramu sai haquri''
ta ajjiye kwanon hannunta
''bana jurar raina babba baaba,babu wadda zaki sake dafawa komai saidai idan maami ta sak
a ki,duk mai buqatar wani abu ta shigo ta dafa ai itama tana da hannu''
sai da suka qarasa komai sannan suka bar kitchen din tare bayan baaban ta gaya mata mami na asibiti da azahar ta fita zuwa bayan isha'i zata dawo,yadda ta barsu a falin haka ta da
wo ta taradda su babu wadda ta motsa don tayi salla
tara saura ta fito din ta debi abincinta,zaunen dai suke duka su uku wannan karon kowacce taci ado,abida cikin matsatstsun riga da wando,salma cikin fitted gown,saddiqa kuwawata gown ce wadda bata da
hannu duka saman qirjin a waje,mamaki ya cikata tamkar irin matan gidan nan dake tsammin dawowar mai gidansu a lokacib,babu tababa zaman jiran dawowar abdallah suke,takaici ya isheta kamar ta rufesu da duka,duk su suke jawowa abdallan ke daukar kansa on t
op,yake rage qimar mata,koma meye sune sila
tasa kanta gaba zata wucesu dauke da plate din abincinta
''ke malama a bawa mutane abinci ko su zasuyi serving kansu
?
''
a nutse ta waiwayo
''su waye mutanen
?
''ta tambayi salma cikin gatse,amma da yake sam
ba ganewa take ba sai tace
''mtseeww,gani kuwa kina kallona''
''ayyah,to ai na dauka a qoshe kuke ko''
ta shige dining area din ta zuba mata ta ajjiye mata
''ni da kika raina sai nayi magana zaki zuban
?
''inji abida
maryam ta dubi plate din hannun
ta
''sai kayi magana zansan kana so ai,ga wannan kici na zuba wani''ta fadi bayan ta ajjiye mata shi a gabanta,ba bata lokaci tasa qafarta ta shure shi take yayi dai dai a gun,wanda ba don tayi saurin ja da baya ba har a jikinta zai samu masauki
''lallai
ne ba qaramun raini ne tsakanina da baqauyar yarinyar nan ba''cikin qanqanin lokaci ta yar da wayar hannun ta ta miqe tayo kanta,qyam ta tsaya hannayenta harde da qirjinta tana kallon abidan,qarasowarta dab da ita ta daga hannunta saidai kafin ta aiwatar
da komai muryar mami ta karade falob
''kai,meye haka abida
?
''dolenta ta sauke hannun nta cikin hayaniya take fadin
''wallahi mami sai na hora yarinyar nan''
''me ya hadaku kuma yau maryamu
?
,ban sanki da fad ba fa''hankali kwance ta gaya mata abinda
ya faru,girgiza kai kawai mamin tayocikin takaici tace wuce amaryamu''
cike da takaici ta isa dakinta,tayi imani a lokacin da abidan ta taba jikinta ko siyar wace ce ita ba zata daga mata qafa ba,bata ga amfanin alkunya ga mutumin da baisan darajar dan ad
am ba,cikin ikon Allah abdul ya kirata,shi ya ebe mata kewa har bacci yayi awo gaba da ita
🍃🍂🍃🍂🍃
cikin bacci ta dinga jin yunwa na rage mata dadin baccin wadda ta tilastata farkawa,wayarta da ke gefan pillow dinta ta dauka ta duba lokaci,shabiyu
da arba'in da takwas na dare,cikin mutuwar jiki da kasala ta sauko daga adon ta shiga toiket ta dauraye bakinta ta daura alwala ta fito ta tayar a sallah,raka'a hudu ta samu tayi tayi addu'oo'inta ta shafa
a hankali ta bude qofar dakin nata ta fito d
on samawa kanta abinci a dining,tayi mamakin ganin qwayayen falon duka akunne,ganin laptop da waya kusa da ita yasa ta bayar salma ce qarshen tashi tabar falo a haka
jingine yake da bango falon hannayenshi harde a qirjinshi,idanu kawai ya zuba mata fu
skarsa qunshe da qaramin murmushi,yayin ita kuma take gaf da ahi har tana iya sheqar hucin nashi numfashin,hannayenta dafe da bangon kusa da kafadarshi
''fyaden kema zakimin
?
''ya tambayi salma kanshi tsaye,cikin lumshe idanu ta kada kai
''ko kadan,kawai
ina da buqatar inji dumin jikinka ne,dubi kwalliyarnan duk kai na yiwa amma tun dazun nake jiran dawowarka,na hana idanuna bacci don kada ta tashi a tutar babu''
murmushinsa ya qaru fiye da na dazu,yasan kalma daya zaiyi amfani da ita wadda zata sata taji
haushi
''sai ance mutum kaska ne yace shi bashi bane''
a maimakon yaga taji haushi kamar kullum sai yaga ko a jikinta,murmushi ta kuma yi
''to meye idan ma kaskar ce,duk akan sonka ne,nidai ko hugging dina ayi kawai na wuce dumin da naji da qamshin tur
arenka ya isheni''
ya janyeta ya bada nisa tsakaninsu yana fadin
''saboda tsabar raini ma naga sai da kika nemo irin turarena da shi kike amfani ko''
''idan zan kwanta na fesa jina nake kamara qirjinka nake kwance''ta fada tana sake matsowa daf da s
hi,hannunta ta dauke daga kan makunnin da takeson kashewa wanda hakan ya haddasa motsin awarwarayenta da suka jawo hankalin abdallah,jiki na rawa ta juya zata bar gurin,tuni ya saki briefcase dinshi da ya dawo da ita daga office ya biyo bayanta da sauri,ga
nin tana niyyar takawa a aguje yasanya shi dada hanzarinsa don ya fuskanci idan ya qyaleta zatq sake masa irin fassarar da tayi masa kwanaki,taku uku ya cimmata tare,da fusgota baya,tayi taga taga ta fadi jikinsa cikin tsoro da daukewar numfashi
*mrs muhammad ce*
👑
📚📚📚
✍
🏻
✍
🏻
✍
🏻
✍
🏻
[9/17, 12:53 PM] 80k: *ABADAN*31
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*_home of expert and perfect writers_*
jikinsa ta fada qeyarta ta samu masauki a tsintsiyar hannun
shi fuskarta na facing tashi fuskar,yabi oily eyes and golden eyes dinta da kallo wadanda suka dada sheqi saboda hasken farin qwai daya mamaye falon ya haska cikinsu,ya kalli dan qaramin bakinta da yake motsi yana tattara kalmomin kayi haquri cikin rudewa
Ranshi ya baci,wai me yarinyar ta maida shi ne
?
,dan iska
?
,haka wancan karon tayi masa fa
?
,tana so tace masa a age dinta bata taba ganin romance tsakanin mutum biyu ba saboda tsabar rainin hankali
?
idan ma hakanne yau zai koya mata hankali,a hankali ya soma
kusantar da bakinsa zuwa nata,numfashinsu ya soma gauraya,tsoro da rawar jikin maryam ya dadu,don tuni zuciyarta ta gama ayyana mata abinda abdallahn ke shirin yi
karon farko tattausan lips dinsa suka taba haduwa da na wata diya mace kamad yadda yake hak
a a gurinta,baisan yadda akayi ya tsinci kanshi da tsotson lausasan lebunan nata ba cikin rashin sani
''hasbunallahu wani'imal wakeel''kadai take ambata cikin zuciyarta,gudun zuciyarta ya dadu har numfashinta na qoqarin janyewa,hawayen dake malala kan fus
karta ne ya soma taba fuskarshi da sajen bakinsa na quater millon
''abdallah
!
,meye haka kake yi
?
''salma ta fada cikin qaraji da wani irin yanayin baqin kishi da bata taba shiga irinshi ba,a nutse ya saki bakin maryamun ya juya yana kallon salmar wanda hak
n ne ya bawa maryam qwarin gwiwar hada ragowar qarfinta don ta tsere masa,saidai tana tashi taji ya cafko dantsenta idanunsa na kan salma,kallon 'yan sakanni ya mata ya maida idonsa ga maryam
cikin fada da tsawa yaso yi mata maganar amma sai ya gaza,kasal
a ce ta saukar masa lokaci guda tamkar mai jin tsananin barci
''gobe ma idan kinganni tsaye da wata kimin kallon dan isaka,zaki ga yadda ake iskanci ra'ayil ain''ya fada yana kallo tsakiyar qwayar idonta da hawaye ya cika yake zuba kana ya cikata,da gudu
kuwa ta bar gurin sai ya bita da kallo yayin da salma ita kuma ta tsare shi da idanunta wadanda suma tuni suka kawo qwalla
''haba,haba abdallah,irin wannna cin fuska haka da me yayi kama
?
cook dinka
?
''ta fada tana nuna hanyar da maryam din tabi da yatsa ''
abdallah ka rasa bakin da zaka tsotsa sai nata,ni me na gaza da shi
?
just hugging dina kawai nace kayai ka kasa sai gashi ka buge da kissing house girl''
''hey
!
stop''ya tsaidata cikin hade girar sama data qasa,ya qara taku biyu ya iso gareta ya tsaya agaba
nta
''kada ki sake ambatar nayi kissing yarinyar can,kaifi tayimin nayi punishing dinta,ina fata kun fahimta''
murmushin takaici ta saki sannan takama qugunta da hannu daya tana girgiza kai
''kada ka maidani jahila mana abdallah,sau nawa ina maka laifi
ka taba punishing dina ta wannan hanyar''
har ya juya vaya taba dauke briefcase dinsa sai ya waiwayo
''ita tana showing kanta a matsayin kanta a matsayin mai nutsuwa tana min kallon abinda ban taba aiwatar da shi ba,kinga gwara nayi mai dalili ko
?
''
gir
giza kanta ta sake
''ko jikina kunne ne bazan yadda ba,kayi ne da manufar wulaqantani da nunama duniya iyakata''
''well,idan hakan kika zaba shikenan daidai ne''ya fadi yana kewayeta ya fice daga sashen bayan yasa key dinshi ya kullesu ta baya kamar yadd
a yazo ya tarar da su,dama abincinshi ya shigo yaci ya sameta zaune ita daya afalon
kamar ta dora hannu aka tayita rusa ihu haka ta ji,hawaye shabe shabe ta shige dakibta bayan ta qudiri abinda zata aiwatar musu a gobe
Qarfe goma ta gama breakfaat di gid
an ta shiryashi a dining,Allah Allah take ta kammala komai ta shige dakinta don bata son haduwa da kowa uwa uba abdallah da take masifar jin haushi tsoro da tsanarsa,ta yanke ma zuciyarta abdallan yana layin 'yan iskan maza ne kawai,tuni ta bashi wannan su
nan
tana gefan gadobta tana shafa mai bayan sanya doguwar rigar atamfa da tayi mai dogon hannu taji wayarta na b'urari,sunan mami ya soma yawo saman screen din,haka kawai gabanta ya fadi,cikin rashin kuzari ta sanya robar lotion din dake hannunta a gefant
a kana ta daga wayar,tana qoqarin gaidata taji tace
''ki sameni yanzun a sama''
''to mami''ta fada cikin rawar murya,kasa ci gaba da shiryawar tayi sai ta zaro blueblack din hijabibta ta ware shi daga gugarsa ta sanya ta miqe ta fice a dakin
kallo daya
ta yiwa mamin gabanta ya fadi don zata iya cewa a iya saninta da ita bata taba ganin yanayin fuskarta haka ba,gefanta salma ce zaune fuskarta jazur idonta a tashe,a salube ta qaraso,qasa ta zauna daga can gefe tana fadin
''barka da safiya mami''
''matson
an''tace da ita tana nuna mata gabanta ba tare da ta amsa gaisuwar tata ba
''maryam,me ya faru jiya da misalin daya da wani abu na dare tsakaninki da abdallah
?
''wata mummunar faduwar gaba ta ziyarce,tsoro da fargaba suka mamayeta ,bata raba dayan biyu wan
i abun salman ta gayawa mami mai muni a kanta
kimanin minti uku mamin na saurarenta babu amsa,don bata da bunda zata ce din
ta fadi gaskiya
?
,bazata iya ba,tasan mamin mai yarda ce da gaskiyar abunda ta fada din amma bata burin shiga tsakanin soyayyar da
da mahaifiyarsa don ta dan dana hakan ba lamari ne mai dadi ba kona second guda
ta musanta kuma ya zamo mata zunubin qarya,idanun mamin na kanta tana jin babu dadi cikin zuciyarta,don har ga Allah 'yar cikinta take kallib maryam,dan yanzu ba'a shaidarsa d
uk da ta shqida da nagartattun halayen abdallah,amma yaran zamani koda yaushe yana iya sauya halayyarsa,tsoronta daya kada ya yaudari maryam din ya bata rayuwarta,hakan idan ta tuna shike qara hasalata da sa mata suya cikin zuciya
''dake nake magana kinhi
shiru''
shirunne ya sake biyo baya,tuni hawaye ya soma ambaliya cikin idanunta tana sa gefan hijabinta tana sharewa
''to tunda kinqi magana bari na kira ahi shi mai gayya mai aikin yayi bayani''
''a'ah mami,tun farki na gaya miki ba laifinshi bane''
s
alma ta fada da sauri har tana kamar zata dafe hannun mamin da ya dauko waya don kiran abdallah
wani kallo mamin tayi mata
''bana hukunci da ji daga bakin bangare daya ba tare da dayan ba,koma mene da nashi laifin kuma tilas ya bayyana nan,''
mami ta qa
re maganar tana kara wayar a kunnenta
shiru ne ya biyo baya har ahigowar abdallah,sanye yake da kayan training ajikinsgi wanda da alama yana filin motsa jiki ne,hannunahi daya handkhercief ne yana tsane gumin suma da fuskarshi,daya hannun kuma gorar ruwan
swan ce dake fidda gumin sanyi bisa dukkan alamu a falon qasa ya daukota
da zolayar mamin ya shigo falon saidai yanayin fuskarta kawai ya bayyana mishi ba lafiya,shi sam bai kula da su ba cikin falon ba sai da mami ta jeho masa irib tambayar data yiwa ma
ryam sannan ya kuka da salma
cikin ko in kula yace
''nothing happened,nasan dai sha biyu da rabi na dawo gida,so ina jin yunwa sai na bude nan na shigo naci abincina,sai waccan da na hadu da ita zaune a falo tana game''
''ita kuma maryamu a ina kuka had
u da ita
?
''ta fada tana nuna masa ita wadda kanta ke duqe
yatsan bata yabi da kallo har zuwa gun maryam,sai ya yamutse fuska
''wace kuma maryamu
?
''ya fada yana shanye ragiwar ruwanshi,sai ran mamin ya baci,ita zai bunne,tasan waskewar abdallah sarai tund
a ita ta haifeahi,kadan daga aikinshi ma yace bai tabajin sunan ba sai yau
''ni zaka ninke a baibai
?
,ko ka manta cewa ni na haifeka na raineka
?
, a hannuna kayi wayo
?
,naci kashinka da fitsarinka
?
,yaushe abdallah ka sauya hali
?
,ita da na tambayeta ai tasan
baku da gaskiya shi ya sanya tayi shiru bata ce komai ba,amma kai da yake madainiyar wayonka ta tambayeta sai ka nemi raina mata wayo ko
?
''
ya danyi qasa da ido dob sam kalaman mamin basu yimishi dadi ba,bazai iya yaushene na qarshe da rayi masa irin wann
a fadan ba
muryarshi a sanyaye yace
''idan ita ta gayamiki ai sai ta bude baki mami ta fadi abunda na mata ko
?
''
''ta gaya min ne tunda tare kuka aiwatar,mai kishina binda ya faru ne ta fada salma,har yaushe ka farq neman yaran jama'a,ko kunyar ina ciki
b gidan bakayi ba
?
,kasan illar da girman zunubin abinda kuka so aikatawa badan Allah ya kawota ta hana afkuwar lamarin ba,mai makon kuma ka gode mata sai cin mutunci ya biyo baya
?
''
sumewa ne kadai maryam bata yi ba a zaune kukan da take aboye sai ya koma
na fili,ran 'yan maza yq baci take idanunshi suka sauya kala,ya zubawa salma ido wadda runi dana sanin abinda ta