Showing 141001 words to 144000 words out of 176330 words

Chapter 48 - ABADAN COMPLETE

HUGUMA   

10 Sep 2026

30

ke musu sanda tana aure gidan jabir

sai ta bude hannayenta tana fadin

''kamar baku ga yayarku b

ane,ku taso mu gaisa mana asiya''

ai kuwa har rige rigen zuwa suka dinga yi,sai taji farinciki ya rufeta,zaman lafiya babu abinda ua kasihi dadi haka dan uwa,baka da kamarshi cikin duniya,hamsin hamsin ta fidda ta raba musu su biyar tace su sayi alawa

Ganin har suka gama budurinsu,aka gama shigowa da kayan da mama ta hadota da su samfurin kayan masarufi babu wanda ya leqo daga matan gidan ya sanyata tambayar lubanatu wadda gaba daya maryam ta karanci nutsuwa sosai a tattare da ita

''ina wai matan gid

an ne

?

''

''au...''ta fada tana murmushi tare da dafe bakinta

''na manta ban gaya miki ba,sun fara zuwa makarantar matan aure qarfe tara na safe zuwa daya na rana mamata da maman hindatu(maman maryam din)ke zuwa,ya hindatu ce ta sanyasu''

cike da nuna ka

ra tace

''inna hadiza fa

?

''

sai da ta kalki qofar dakin nata kana ta tabe baki

''tana ciki tana bacci,tata makarantar kenan''ta fada tana bushewa da dariya,daquwa maryam ta mata

''mamarki ce itama''daki lubabatu ta shiga ta daukowa maryam maqullin daki

n maman tace

''adda ga key din ko''ta karba kana ta budr dakin maman ta shiga

ta bi dakin da kallo ya sake kyau ya canza,cike yake da tsafta da qamshi,wani kewar dakin ta kamata,sai ta cilla mayafinta da jakarta saman kujera,kai tsaye ra shige dakin

maman ta fada gadonta data yi kewarsa matuqa

Tana son gadon umman nata tana jin dadin kwanciya a kai,gadon da tasha dabdalar quruciyarta a kai har yanzu katifarshi ce a kai,duk da canza kayan daki da taga umman nata tayi amma bata canza abarta ba,ta

sake juyawa tana tuna rayuwarta cikin gidan quruciyarta zaqi da madaci kala kala,a haka bacci yazo ya sureta.

Can cikin barcinta taji kamar ana kiran sunanta,a hankali ta dinga bude idonta har ta budesu tarwai kan fuskar mamanta,farinciki ya kamata,y

aushe rabon data ganta,tana tsaye cikin unifaorm ash colour doguwar riga da hijabi,sun mata kyau kuwa unifaorm din sosai

''ki tashi kiyi sallah kina ta bacci har anyi azahar''sai ta miqe tana mutstsuka ido

''ashe har kun dawo mama''

''eh kina ta bacci h

ar girki akayi aka gama baki sani ba,halan bacci kika koyo''murmushi tayi ta miqe zata fice a dakin tace

''sannunku da dawowa''

''yauwa''maman ta amsa tana rataye jakar makarantar ta data daukota daga falo gami da cire hijabinta ta linke ta saka a sif

Duk inda tayi maman kallonta take,godiya take wa Allah cikin zuciyarta,farinciki fal ranta,lallai addu'a bata faduwa qasa banza,duk wanda ya kalli maryam din koda makaho ya shafata yasan ba a wahala take ba,babu shakka Allah ya share mata hawayenta na s

hekara da shekaru wanda ya jima yana zuba,hirarsu suke gwanin sha'awa da maman bayan baaba huwaila ta aiko mata da abincin rana don girkinta ne,bata zauna ba sai data shiga dakin baba huwailan suka gaisa,kayan dakin mama datq cire ne jere a dakin nata,ba l

aifi sunyi kyau kam,cike da sanyin kiki da nadama ta dubi maryam

''na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun lokaci bai qure min ba ni da yarana,maryam na cutar da ke a baya na kuma so na sake cutar da ke amma da yake ALHERI ne cikin zuciyarki sai All

ah ya kareki ya kuma sanya kika mana zarrah a rayuwa,maryam don girman Allah ki yafe min ni da yara na gaba daya''

sam magiyar da take mata bata yi matq dadi ba,ko da can baya ta sani cewa shedan ke rudarsu da duhun kai,bata taba riqar baaba huwailan ba

''baaba,tamkar mahaifiya kike a gurina,nikam dama ban riqe ki ba,na yafe miki Allah ya yafemu baki daya''

Data zo cin abinci duka qannenta ne kewaye da ita suna hirarsu abinda bai taba faruwa ba tsakaninta da su ba tarihin rayuwarta,nan take jin duka

baaban su ya maidasu makaranta,sosqi taji dadi don babu gatan da zaka yiwa yaro da ya wuce ka bashi ilimi(har kullum haka iyayenmu ke gaya mana,burinsu kenan (rabbirham huma kama rabbayani sagirah)

maryam ta dubi mama''ni ka ban ma ga baaban ba''

kub

rah tayi caraf tace''baaba yana kasuwa,sai shida zai dawo''ta juya ta kalli mama

''kasuwa kuma mama''

''eh,kin manta da shagonsa da abdallah ya bude masa cikin kwari

?

''

''abdallah,a cikin kwari

?

,yaushe abdallahn yayi haka ba ta taba sani ba,koda mami ba

ta taba mata magana makamanciyar wannan ba''cikin zuciyarta tayi maganar amma a fili sai tace

''au na manta fa''

''ai kullum malam sai ya yiwa yaron nan addu'a,yanzu kam qlhmdlh malam ya dauje duk wani,nauyi na gidansa da a da baya iya daukeshi,abdallah

kam ba baya ba wajen alkhairi,abu daya zaki mana maryam ki wanke mu kiyi zaman aure mai cike da biyayyar miji,duk yadda kika zauna da mijinki kina nuna masa irin kalar tarbiyyar da kika samu kenan,kibi mijinki maryam ki riqe abdallah hannu biyu,bawai don a

rziqin da yake da shi ba,a'ah ko daya,kinfi kowa sanin cewa ba wannan ne gabanmu ba,nagartattun halayen abdallah kadai sun isa su sama masa kowacce kalar mace ta gari,ina fata kin fahimceni''kanta ta gyada

''na fahimta mama''

''Allah ya albarkaceku ke da

shi baki daya''

''ameen ameen mama''ta fada cike dda jin dadin addu'o'inta

kafin ta rafi sai data tambayi yan qannenta me suke so ta saya musu kowa ya fadi abinda yakeso wanda bai wuce sabon unifoarm,jakar makaranta da lunch boxs,excercise book,luba

batu ce mai registration na placemen da sauran tarkacen kayan karatu,bata bar gidan ba sai data hadasu da lubabatun da kulu sukaje aka siyo,murna da tsalle kam sun sha shi,ko idon inna hadiza bata gani ba bare jamila ko binta,tana tsammanin ma basa gidan d

on idan banda isyaku data gani dazun da take shigowa gidan babu wanda ta gani cikinsu

*mrs muhammad ce*

πŸ“šπŸ“šπŸ“š

✍

🏽

✍

🏽

✍

🏽

[8:18pm, 10/9/2017] Huguma

πŸ‘‘

:

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

🌺

*ABADAN*

🌺

πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–

🌺🌺🌺🌺🌺🌺



πŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–

πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–



πŸ’–

*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊπŸ’–



πŸŒΊπŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–πŸŒΊ



πŸ’–

Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

πŸ’‘

*_home of expert and perfect writers_*



β–Ά

6

⃣

0

⃣

*Daga abi musa al asha'ari R.A yace:Manzan Allah S A W yace da ni''ya Abdullahi dan qais,shin bana nuna maka wata taska daga cikin taskokin aljanna ba

?

LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAH''a ruwayar nisa'i ya qara da ''LA MALJA'A MINALLAHI ILLA ILAIHI''*

*Daga abu hurairah R.A yace: Manzan Allah S A W yace ''duk wanda ya fadi SUBHANALLAHI WA BI HAMDIHI sau dari za'a kankare masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi''*

_ruwayar bukhari da muslim_

Bata bar gidan ba har baaban ya dawo,a tsa

itsaye suka gaisa saboda an soma kiran sallar magariba ya daura alwala ya fice yace yana dawowa,itama alwalar tayi ta shiga dakinsu tayi sallah,tana idarwa kiran hindatu ya shigo,a dokance take cewa

''Allah yasa adda baki tafi ba,gamu nan ni da jabir''

'

'da daddaren nan''

''wlh,daga asibiti muke kuma akace kina gida''

''ina nan ban tafi ba baaba nake jira,sai kun iso''ta fada sanan kowacce ta kashe wayarta

Tana dakin baaban ita da shi bayan baaba huwaila ta ajjiye masa kwanukan abinci ta fice,hira

suke yi abinau gwanin dadi,abin ya faranta ranta sosai,ashe akwai lokackn da zata ga rana irin wannan

?

,lallai komai yayk farko zaiyi qarshe,basu damu da yadda inna hadiza keta kai kawo bakin qofar dakin ba,baaban ya dubeta bayan ya ajjiye carbin hannunshi

''maryam,ina fata zaki yafemin,na dade ina daukan haqqinki,na yi watsi da duk wani haqqi naki da Allah ya doramin,tun kina mitsitsiyarki na watsar

da duk wani haqqi naki da Allah ya dora min,gashi daga qarshe ta inuwarki muke samun rufin asiri,ki yafemin

maryamu,haqiqa na dau darasi a rayuwata,na qiku don kuna 'ya'ya mata,ina neman dq namimi,ido rufe,sai gashi yarin yana daf da lalacewa,Allah ya sa baiyi girma mai yawa ba,duk da haka har yau na kasa saitashi kan hanya madaidaiciya saboda na riga da na bata

shi na nuna masa gata,duk da haka na godewa Allah da ya ganar da ni gaskiya tun da wuri,a yanzu ne nake ganin budi cikin harkokina da nake yalwatawa iyalina nake daukan duk wani nauyinsu bakin gwagwado,kimin afuwa maryam''

Itakam bata jin dadin yadda

mahaifinta wanda yayi sanadiyyar zuwanta duniya ke faman roqonta haka

''nikam baaba wallahi abunda kamin bazan taba iya biyanka ba,banga wani da zaka yimin ba na riqeka,komai qaddara ne kuma nasan haka lah ya qaddara dama zanyi rayuwata''

''duk da haka,n

a sani maryamu ki yafe min''

''na yafe maka baaba har abada duniya da lahira''

''na gide madyamu na gode,Allah ya albarkci rayuwarki,ki sake yimin godiya gurin yaron nan abdullahi,babu shakka babu abinda zamu iya cewa da shi,tsakaninmu da shi fatan alkah

airi ne''

har yanzu mamamin abdallah bai saketa ba,yaushe ya shiga jikin yan gidansu ne wai haka

?

,yaushe suka saba soaai har yake musu alkhairai bai taba nuna mata ba ko sau daya

Suna cikin dakin suka jiyo shigowar hindatu,shigowarta ne ya tunowa da

baba sabon babur da jabir din ya siya masa ya dinga zuwa kasuw ko wata guda ba'a rufa ba yace maryam din ta tayashi godiya

Nan cikin dakin itama ta ahigo bayan sun gama gaisawa da mama suka sha hirarsu da baban,har kusan qarfe tamwas da rabi suna tare

,tuni ta kira baaba sule tace ba sai yazk daukarta ba don hindatu tace su zasu maidata

har soro suka rakosu baaba huwaila da yan qannesu,a tsakar gida sukayi sallama da baaba,suna kallo su jamila da binta na leqensu ta window

cikin mota suka tadda ja

bir din,hannunsa ya dunqule yana mata jinjina irin ta sarakai''Allah yaja da ran antinmu,Allah ya taimakeki uwar gidan abdallah mai nasara''dariya ya bata ba kadan ba

''haba jabir,ka mance cewa ka girmeni irin wanan gaisuwa haka

?

''

''ai yanzu kece babba,

ko kin mance kin bani 'yar qanwa,gimbiya hindatu,wadda ba qaramin yabawa da zaben da nayi nake ba har yau''dariya ya bas gaba dayansu har suka fara taciya suna hira abinsu

sai da suka fara biyawa ya yiwa hindatu siyayya ya hada harda maryam din kana s

uka ajjiyeta a gida sannan suka nufi nasu gidan

πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚πŸƒπŸ‚

kwana bakwai mami bata bari an dakayar da gyaran da ake mata ba,tamkar ana shirin canza mata fata,ita kanta mai gyara ta yaba yadda gyaran ya karbi jikin maruym di sosai da sosai,baaba uwan

i kuwa zama take kawai tana kallon maryam din

''gaskiya meramu anya ba canza miki fata hajiyar nan me gyaran jiki take ba

?

''duk sanda ta fadi hakan dariya take basu ita da mami

Kusan tun ranar da sukayi waya da abdalla kan zuwanta gida basu sake samu

n kiranshi ba,ana gobe kwanaki bakwai din da ya diba zasu cika mami ta nemeshi don taji goben zai dawo,saidai ta nemi layin nasa yafi sau goma bata sameshi ba,har cikin dare tana iransa bata sameshi

da safe ma hakan ce ta faru,damuwarta ta kasa boyuwa

ta tadda maryam a kitchen tana goge freezer tare da sake jera kayan ciki don mamin ta hanata yin kowanne aiki

''ni kam maryam kina samun abdallah a waya kuwa''maryam din ta waiwayo ta dubi mamin sai ta rasa amsar da zata bata,don ita kanta tasha kasa kun

ne cikin dare lo da rana taga ko zata samu koda texs nasa,Allah ya taimaketa tin kafin tace wani abu mamin tace

''sam ba'a samun wayanshi,na kira na kira duka akashe''

jikinta taki yayo sanyi gaba daya,gabanta ya dan fara faduwa kada kadan ta juyo gaba d

aya ga mamin tace

''to mami ni cewa nayi ko chargy ne babu a wayoyin nashi

?

''

kai ta girgiza

''bana jin haka,saboda ba cikin wani qauye bane cikin tsakiyar abuja ne fa,kusa da villa,kinga ta yaya za'a rasa chargy a wayoyi

?

''

sbiru ya sake ratsa tsakani

,bayyanar damuwa kan fuskar maryam wadda ita kanta batasan ta bayyana bayasa mami riqe hannunta

''kada ki damu in sha Allah he is safe''

kai ta gyada asanyaye,sai ta kasa qarasa ci gaba da aikin ta biyo bayan mami ta fita a kitchen din ta koma dakinta ta

kwanta

Maganganunshi na qarshe ta dinga tunawa

_''Allah ya qaddara saduwarmu,sai Allah ya dawo da ni,kimin addu'a don muhimmin aiki zan gabatar,wanda ko shine aiki na na qarshe da zan aiwatar in sha Allahu sai na gabatar da shi,ki sakani a addu'o'i

nki,idan kuma na mutu shikenan sai a darus salam''_

Wani irin juyi tayi cikin matsananciyar faduwar gaba ta tashi ta zauna sosai kan katifarta,sai taji kanta ya sara ta dafe goshinta da sauri kana ta maida jikinta fuskar gadon ta jingina

kusan wuni t

ayi sukuku zuciyarta ba dadi,duk motsin da tayi maganansu ya qarzhe a airport ke mata amsa kuwwa a kunnenta,ko falon bata sake fitowa ba saboda rashin kuzari,mami keta leqota don kada ta takure ranta ta sa damuwa,ta karanci wani kalarson abdallan mai qarfi

cikin zuciyar maryam din,da taga ta leqo ta sai ta qirqiri murmushin dole,gaba daya walwalarta ta ragu,ta dinga kiran layin abdallah a jejjere kamar wadda aka bata aikin yi amma ko da wasa bata shiga ba is switched off computer keta faman gaya mata

,

Cikin kwana biyu duk yadda taso hana kanta damuwa zuciyarta tace batasan wannan ba,bata taba jin damuwa irin ta wannan lokacin ba,bata taba jin ta damu da wani abu a rayuwarta ba kamar wannan lokacin

cikin kwana na uku ta gaza daurewa

fitowarta a w

anka kenan wanda tun safe ta kasa yinsa sai kusan daya na rana ta samu tayi,mai kawai ta shafa ta fesa turare ta zira doguwar riga ta nade kanta da mayafinta,takalmanta plate ta jawo ta saka kana ta fito,babu kowa bangaren don mami ta fita asibiti don haka

ta fito waiting parlour ta zauna tana kallon shigewa da ake tayi da sabbin furniture bangaren nene a da,bata cikin nutsuwarta batasan wa zai zauna anan ba bata kuma damu data sani din ba,abinda ke cunkushe kadai a ranta ya isheta jarraba

number din h

isham ta laluba ta kirashi,daga yanayin yadda taji sun gaisa har yana zolayarta ta tsinke da lamarin,sai kawai ta fasa tambayarsa ta kashe kiran,lambar abdallah ta sake trying wanda ta maida kiran tamkar ibada a gareta saidai amsar daya ce kamar kullum is

switched off,ita kanta ta fuskanci yanayin damuwa kan fuskar mamin duk da bata kai tata ba,jin zuciyarta take kamar ana hura mata wuta

son abdallah

kewar abdallah

duk su suka mata rubdugu,kalamansa na qarshe a gareta ke sake sanya mata karaya,kawai sai

ta zame a gun ta kwanta rub da ciki,batasan ya akayi ba ta tsinci kanta ne kawai tana kuka tuquru,bakinta na fadin

''kada ka yimin haka abdallah,kada ka guje ni,kada ka tafi ka barni''take furtawa a hankali cikin kuka,Allah ya taimaka mutanen dake aikin k

afa kayan furniture din sun kammala sun fice

Kuka tayi mai yawan gaske har yasa idanunta suka kumbura baya ga zafu da radadin da suke mata amm hakan baisa ta haqura ba,sai da bacci ya lallabo ta taimaketa ya saceta,bacci ne mara dadi wanda tana yinshi

tana sayke ajiyar zuciya ma kukan da ta yi

Hannu taji kan wuyanta a hankali ta soma bude kumburarrun idanunta wanda hasken daya cika falon yasa ta gaza budeshi gaba daya,mami ta gani tsaye a kanta tana fadin

''bacci kuma a waiting parlour maryamu

?

''

ta tambayeta ba tare data lura da yadda idanunta suka sauya kala ba

''tashi ki koma daki idan baki gama ba kiyi a can amma nan ai yayi waje''

sosai tayi qoqarin tashi amma ta kasa,ga zaton mamin magagin bacci ne don haka ta kama hannunta don tayata tashi

n,zafin da taji da hucin zazzabi ya sata furta

''subhanallahi,maryam me ya sameki haka

?

''sai a lokacin ta lura da yadda idonta ya suntume fuskarta tayi jawur

''ya salamu ya Allah,maryam''mamin ta fada a rude,zare wayar hannun maryam din tayi don ta miqar

da ita,number din abdallah ta gani kan scrren din wayar,sai ta dubi maryam din

''abdallah dai maryam

?

duka a kanshi kika yiwa idanunki haka

?

,sai kace an ce miki ya mutu ne''kalmar mutuwa data ambata wa abdallan sai ta sake karyar mata da zuciya,take taji

ko,mutuwar ma yayi ne tunda gashi mami ta fada

?

,sabbin hawaye suka soma tsiyayowa,sai mamin ta dafe kanta don ta fuskanci abinda ya sakata kukan

''babu abinda ya samu abdallah maryam,tashi maza mu shiga ciki ki je ki watsa ruwa ki karbi magani,zafin zazza

bin nan yayi yawa kada ya zama wani abun kuma daban''

mamin ce ta taimaka mata har ta shiga toilet kana ta fita ta bar mata dakin ta haye samanta don tayi wanka,itama ta hada mata magungunan da zata sha da zai saukar mata da zazzabin,zuciyarta fal da

fafinciki jinjinawa da yaba tsaftatacciya kuma ingattaciyar qauna kuma mai qarfi da ya samu daga gun matarshi,wanda tayi imanin koda bafa duniya zai samu kyakkaywan kulawa a rayuwarshi

Ta kammala watsa ruwan ta canza kaya,da qyar ta iya bada sallar

azahar da la'asar da suka shigeta ta dawo ta nade a gado,har yanzu zazzabin tana jinsa cikin qashinta,a haka mami ta taras da ita

Sai data tilastata taci abincin da ta shigo da shi sannan ta bata maganin ta sha,tana nan a gurinta har bacci ya sake dau

karta sanann ta fita dakin

Bata farka ba sai da wani amai mai zafi ya farkar da ita,da gudu ta miqe kanta na sarawa ta shiga bandakin ta dinga kwarashi,mami wadda ta idar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login