Showing 147001 words to 150000 words out of 176330 words
roqonsa qasa qasa saitin kunnanshi kada ya bude sai yasa rigarsa
''sai na cire wanann
ma na zauna da boxer ki da kanta ma idan mami ce anjima zata kaimu gidanmu''kunu tasha tana miqo masa rigarsa kana ta fece bandaki ta saka maqulli ta buya,bai kuwa saka rigar ba ya budewa mamin,ita kanta sai da taji kunya ta kamata,ta kautar da kanta sana
n tace
''ba kai nake nema ba diyata nake nema,kasan bata gama warkewa ba akwai sauran magungunanta da zata sh''
shima sai ya hau sosa kai don ya gama fuskantar inda mamin ta dosa
''mami ki kawo sai na bata''
hararasa tayi gafara min ni na wuce,haka zak
a dirka mata maganin bata ci komai ba tun safe
οΌ
,baka iya kula da mutum ba sai sakarci ka iya''ba shiri ya matsa ma ta shigo,ta kalli gadon da suka yamutsashi don akai suka yini salla ke sauko da su ta dauke kanta tana kiran sunan maryam din,gyaran murya ta
yiwa mamin kamar maiyin wani abu a bandakin
sai ta samu gefan kujera ta zuan bayan ta ajjiye maganin kan madubi,shima gefan madubin ya jingina yana fadin
''kinsan kuwa mami cikin wadanda na kama tare da alhj hamza da yaranshi harda adnan
οΌ
,mami as
he yana daga cikin manyan yaranshi,duka poising da naci sau biyu har da hadin gwiwar alhj hamza din''salati mamin ta saka tana tafa hannayenta
''kai Allah ka tsare mana imaninmu ya Allah,wadan nan mutane wadan nan mutane sun cika butulu,amma dama hausawa
sunce idan zaka gina rakin mugunta ka ginasho gajere wataqila kai zaka fada,yanzu gashi su suka fada din,nene kam ba ita ba labarinta har yau ita da zubaida,yanzu don Allah meye ranar wanann
οΌ
''
kanshi a duqe yake jijjiga kai,har yau yana jin takaicin yadd
a mutanen suka ci amanar mahaifinaa da mahaifiyarsa,har yau yana tuna yadda babanshi da mamanshi suka hada gwiwa aka auro nene gidan cikin halin qunci da wahala ita da yayanta amma yau da ita akayi yunqurin rusa su badon Allah baya bacci ba ya basu kariya
da kariyarsa,kasa cewa komai yayi don idan ya tuna su bacin ransa ne ke tashi qwarai da gaske,badon mami tace ya qyalesu ba dukkanau sai ya nemo su yayi shari'a da su har
igiya tayi saura,amma gashi a yau ya samu adnan wanda ko tantama baya yi hukuncin kis
a ne zai rataya awuyansa sabida irin barna da kisa da suka dinga yi
shuru shiru maryam bata sake motsawa ba,babu yadda mami batayi ta fito ba amma ta kasa,shi kuwa abdallah na gefe yana musu dariya,da mamin ta gaji tilas tace
''aishikenan gasu nan id
an kin fito din kyasha,ki tabbatar da kinsha kuma sabidayau hajiya lailan tace kisha shi''ta juya ga abdallah dake masu dariya
''ka shiga tsakaninmu ko,zaka dara da kyau musamman idan na saka ranar tarewarku nan da watanni goma''
''lokacin ta haihu kenan
ta gama wankan jego''
π
,ya fada qasa qasa yana duban sama
''me kace
οΌ
''mamin ta tambaya,da sauri yana dariya yace
''babu komai mami,Allah bani na shiga tsakaninku ba,kunyarki dai kawai take ji''
''gafara min,ka maidani wata kakarka ko,tamu ce ni da kai
''ta fadactana rabeshi ta fice qasan zuciyarta cike da farinciki,ta tabbatar cewa irin qaunar da take sha'awa danta ya samu ga matarsa ya gama samunta sai godiya ga Allah,abdallah kam ta sani bamai wasa bane gun kula da nunawa iyali soyayya tuntuni ta sani
halinshi ne a qidarsa ce
Wanka kawai ta zarce da yi bayan ta ji fitar mamin,kayan jikinta ta maida don ta tabbatar abdalla yana dakin,towel ta rufawa kanta sabida jikqewa da sumar tata tayi,yana tsaye bakin madubin hannunshi daya ya dafe amdubin d
a shi dayan kuma yana ruqe da yar kwalabar maganin yana karanta rubutun lrabcin dake jiki,ta qarasa gaban madubin da sauri da niyyar tattare magungunan don batason ya gane na meye,ajjiye kwalbar yayi ya zare towel dake kanta yaci gaba da goge mata ruwan ga
shin nata na burgeshi tare da bata sha'awa
''baby kici abinci gaskiya kisha maganin nan''
''na ciwon kaine kuma ya riga da ya sauka''ta fada akunyace
dariya ya saka kana yace
''eh kam gaskiya ne,na gani ai''
ta tsargu don haka tace
''qarya nayi k
enan
οΌ
''ta fad tana hade rai din kada ya bullo da wani abun,ai kam bai fasa ba sai da ya ja habarta yana dariya yace
''gaskiya na sake tabbatar da irin son da mami na kemin,ya Alah ka sake jamin da ranta ka qara mata lafiya da tsawon rai mai amfani,kice gy
arani kawai take yi ni ban ma sani ba,i luv my momma''sai kuma tayi shiru bata data cewa don ta tabbatar ya gani
sai ya leqa fuskarta bayan ya jawota ua rungumeta ta baya kana ya dora habarsa kan kafadarta yana cewa
''kina zaton Abdallah bai iya larabci
ba ko yammata,zan baki mamaki kamar yadda na saba,kwanan nan zan daina magana dake da hausa''
dariya ta subuce mata
''ni din ma akace ban iya bane
οΌ
''
''i know baby na,ke din gwanace ta kowanne bangarr tunda kika iya sace zuciyar abdallah tun ruwanki bai
isa alwala ba shi kuma da ya tashi ramawa sai ya haukataki baki daya ko
οΌ
''diddira qafarta ta shiga yi cike da shagwaba taba kukan qarya,anan ya lalace yana ta faman kallonta,don ba qaramin kyau tayi masa ba ji yaje kamar ya hadiyeta ya huta
Bai fita
adakin ba kuwa sai da aka kira sallar magriba,yana fita ta rufe da key don tasan idan batayi da gaske ba ma yana iya cewa adakin zai kwana mata tundavyaga mami mai dauke kai ce wunin sur ta fita a harkarsu tana cikin mutanen dake ta aikin bangaren mero
ππππππ
Tun kafin ta tashi abacci yake ta faman doko mata kira tazo yana son ganinta,har qaryar bashi da lpy ya mata,tana jin kiran nasa ta shareshi don haka jiya ya dinga buga mata qofa har ya bata kunya don baaba uwani ta jisu tana ji tana gaya m
asa qila tayi bacci ne
Takanas ya tashi ya taho dakin nata ya soma buga mata,cusa kanta tayi qarqashin fillow tana kuma qudunduna cikin bargon,qasa qasa yake kiran sunata
''wayyo abdallah wallahi kunya kawai kake bani,tun jiya kasa na kasa hada ido d
a mami na''haka ta dinga fada cikin zuciyarta,likimo taci gaba da yi har ta daina jin bugun nasa
Qarfe tara da rabi ta fito a wanka taba gaban madubi daure da zani ta lulluba towel a kanta ta ji ana knocking,sai da ta tambaya taji baaba uwani ce don h
aka kai tsaye ta bude mata ta juya tana fadin
''shigo baaba yanzu nake shirin zuwa kitchen din nasan kina can kina aiki ke daya,yau bacci ne ya danneni wlh''
''wani baccin zaki sake kuwa yanzu yanzun nan''taji muryar abdallah,kafin ta waiwayo tuni ya run
gumeta ta baya hannu daya yasa ya sakawa qofar muqulli,ya sake matseta gam ajikinsa yana lalubarta
duk inda ta ruqe hannunshi sai ua zame har sai da yayi iya yinsa kana ya saketa,zatq gudu toilet yace
''wallahi kika gudu ina da spare key idan na bude ki
zaki dandana aguna''tilas ta tsaya yana dubansa ya birkice gaba daya,sai ya koma gefan gadon ua zauna,ya dauki kusan minti ashirin kafin ya daidaita,ya sake kallonta tana zaune kan dressing chair ta juya masa baya
''kinsan jiya da qyar na iya bacci kuwa b
aby,kuma kika hanani ko duminki naji ma''
A shagwabe tace ''kayi haquri,mami sai taha rashin kunyarmu yayi yawa a matsayinmu na hausa fulani,kuma kunya kaga wani yanki ne daga cikin imani''
kai ya gyada
''alright,naga kamar tsoro na kike baby tun
yanzun,idan shine ma pls ki cire shi a ranki,don ni mitum ne da keson maida matarsa ta zamar masa tamkar qawarshi,jeki saka kayankin kizo mu gaisa''ba musu ta bude kayan
sawarta ta ciro atamfa,a hankali ya tashi ya isa gareta ya ruqe hannun ya maida atamf
ar yana fadin
''atamfa atamfa dai baby,yau kam ba atamfa nakeso ki saka min ba''yayi maganar idonshi akan kayan nata yana lalubawa,wani material ya ciro mata dinkin fitted gown,orange ne da adon baqi,ta dubeshi bayan ta marairaice
''yayi tsiraici da yawa
wannan,kuma kasan bamu kadai bane cikin gidan''ya tubure mata shi au yakeso ta saka masa,da qyar ta lallabashi ya haqura ya sauya mata wani lace riga da skert tare davalqawarin koda anjima ne zata sa masa wannan din
Toilet tayi nufin shiga ta saka ka
yan yace sam bai yarda ba shikam,sai baya ya juya mata ta sanya underwears,bata kai ga fara sanya kayan ba ma ya juyo shi tana ji tana gani ya shiryata cikin lace din,ba qaramin kayu kuwa tayi ba,zagayata yq dingayi yana qare mata kallo kafin daga bisani y
a jata cikin jikinsa yana shaqar qamshinta,sun jima a haka ba tare da ta hanashi ba kafin daga bisani ya fidda mata mayafi yace ta saka
Da qyar ta iya zuwa gun mamin ta gaidata ta kasa hada ido sam da ita,ita kuwa murmushin take,dadi take ji cikin ran
ta da Allah ya bata suruka mai kunya ba irin surukan zamqni ba da idanunsu ke tsakar ka,suna ganin ai an dade tare da suruka an zama daya idanunsu ya soye don haka babu wata kunya tsakaninsu,qarshe zamewa tayi kitchen gurin baaba uwani
Suna kitchen su
na aikin girkin rana ita da baaba uwani,duk da yadda abdallah yaso hanata taqi,sabida ta sani sarai idan ta biye masa kadan daga aikinsa suyi wunin daki bai ko jin kunyar idin mami,ga gidan yau ba laifi akwai mutane,murya ta jiyo cikin falo tamkar ta inna
wuro,da azama ta fito falon nan sukayi kacibus,ita dince kuwa,farinciki ya kama maryam din don ma kunyar mami ta hanata sakewa,ita inna wuron ta yo gaba ne sabida anjima kadan za'a taho da mero amarya,hidima sosai mami ta dinga yi da inna wuron,ina kasa in
a ka ajjiye ta,jinta take kamar babbar yayarta,mutanen nada wata irin qima da matsayi mai yawa a idanunta,ba zata taba mancewa da su ba,alkhairinsu mai tarin yawa ne a gareta ita da iyalinta,daki guda aka bude nata daya daga cikin dakuna hudun dake corrido
r din dakinsu maryam
*mrs muhammad ce*
π
πππ
β
π½
β
π½
β
π½
[4:09pm, 10/11/2017] Huguma
π
:
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
πΊ
*ABADAN*
πΊ
ππππππ
πΊπΊπΊπΊπΊπΊ
ππΊππΊ
ππΊπ
πΊπ
π
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLA
HI MUSA HUGUMA*
πΊππΊππΊπ
πΊππΊπ
πΊππΊ
ππΊ
π
Β© *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
π‘
*_home of expert and perfect writers_*
βΆ
6
β£
2
β£
*Daga abdullahi dan mas'ud R.A yace:Manzan Allah S A W yace''i
dan kuka kasance ku uku,kada mutum biyu(su kebe)su gana (su ware cikon dayan da suke tare),har sai sun cakudu da wasu mutanen(sun fi uku kenan),saboda dalilin haka(kebewar tasu su biyu su barshi shi kadai)zai iya bata masa rai/baqinciki''*
_ruwayar bukh
ari da muslim_
_MASOYANA NAGA SAQONNINKU,SAIDAI,BAN KAI GA DUBAWA BA WAYAR TAYI RESTORE DI SAQONNIN,SABODA HAKA AYIMIN AFUWA NA RASHIN GANIN REPLY,INA GODIYA YABAWA TARE DA JINJINAWA QAUNAR DA KUKE GWADAMUN TA BAN MAMAKI,ALLAH YA SO KU KAMAR YADDA K
UKA SONI_
π
Abdallah ya kasa ya tsare,shikam yace an takura shi saboda baqin da auka dinga yi cikin gidan sun hanashi ganin maryamansa wadda tana cikinsu ana hidima da ita,duk da mami ma ta hanata yin wani abin saboda gyaran jikinta
Gab da magariba aka iso da mero gidan,a qalla mutum ashirin 'yan rakiyarta,kai tsaye suka fara da kawota gurin mami,maryam ce ta kamata ta mata iso saman mamin
''masha Allahu,Allah ya sanya albarka,ku kaita gidanta ta hita tunda dai mina tare ai babu dam
uwa''cewar mamin din haka ta sauko da ita suka nufin sashen sa yake a yanzu mallakinta
Bakin yan uwan meron harda na labaran yaqi rufuwa,kowa sam barka yake yana fadin ashe wani jinkirin alkhairi ne,gashi llkaci daua ta sanadiyyar wannma nawam Allah m
ero kin shiga daular da duk cikin ahalinmu ko a tarihi babu wanda ya taba shigarta,ya baku mazauni ya miki kayan daki ya bawa mijinki aiki ai babu abinda yayi saura tsakaninku face biyayya da fatan alkhairi''cewarsu,kallo kam sin shashi din lungu da saqo n
a gidan cikindaren banu inda basu leqa shi ba,itakam maryam wami abun su bata dariya wani anun su bata mamaki
maryam ta yaye lullubin da meron ta qudundune kanta aciki tana fadin
''to ai ba kowa adakin daga ni sai ke ko,sai ki bude kan hakanan kisha
iska''itakam ko kadan bata ma kin zafi sai sanyi sanyi da take ji sakamakon ac data ratsa dakin,ta yaye mayafin tana kallon maryam,ita din ma kallon meron take tana murmushi tare da fadin
''umm,su mero amarya''murmushin itana tayi tana fadin
''yauahe rab
on da kimin daiya mairamu
οΌ
,da kin dauka zan auri yaya abdullahi ne ko
οΌ
,ai ko wani abi gaya min ba nasan yafi qarfina,a wautata dai na soshi da farko,daga baya indo ta ankarar da ni,duk abinda fa kika ga munayi tsarawa mukayi,shiri ne kawai harda hadin baki
n inna wuro,amma ba gaske bane''
Dariya ta kama maryam tace
''wato harda inna wuro kuka so haukatani ko
οΌ
,to shikenan nina zan rama,nan da watanni zan bawa labqran qanwata ya aura kema kiji yadda akejin kishi''dariya ta qyalqyale da shi sannan tace
'
'kiyi haquri adda mairamu,wallahi ina sin labaran dina,musamman ma yanzu da mukayi aure''dafa ta tatyi tace
''kada ki damu nima wasa nake miki,Allah ya bar kowa da masoyinshi''
''ameen adda''
''yau kuma na zama adda kenan ko
οΌ
''ta fada cikin sigar tsokan
a''fuskarta ta rufevtana dariya
''eh ai innata cectace duk abinda ban san ba na tambayeki kada nazo nayita yin shirme,tunda kin girmeni''
jinjina lanta tayi tana murmushi,mintuna kadan suka qara maryam din ta miqe tana fadin zata ta kwanta sai da safe di
n qila angon ya kusa shigowa don tana jin lokacin da ya kira meron a wayar da ya siya mata yar nokia mai torch,ta tambayeta me take da buqata ta kawo mata
girgiza kanta tayi kamar zatayi kuka,banu komai adda ni kawai tsoron kwana nake anan,murmushi tayi d
on ta fuskanci me take nufi
''hmmm,ni dake duka jirgi daya ya debo mu ai,ban san me ke a ciki ba balle na taimaka miki''ta fada cikin zuciyarta,amma a fili sai tace
''kada ki damu ai yanzu labaran din zai qaraso,bake daya zaki kwana ba,kiyi,haquri kinji'
'a sanyaye tace ''to,amma wayata ba caji ko zaki ara min igiyar cajinki''
''bara naje na dauko miki minti biyu''ta fadi tana juyawa tare da ficewa daga bangaren
ππππππ
Shida mamin ne tsaye cikin falon hannunshi dauke da kayan bacci na maza,tun
dazun yake mata rigima ahifa nazai koma bangarenshi ba
''hooo abdallah,to wai ya kakeso ne da ni,na gaya maka an kwashe maka kayanka dagadakin sabida duka dakin baqi ne a ciki,gobr zasu koma garinsu ko so kake na koresu daga dakin kai ka shiga ka kwanta
bayan ga bangarenka can,abinda yasa dama ban barka ka koma daga dawowarka ba gyara ne akeyi kuma an riga da an kammala an maida komai muhallinsa''
cikin shagwaba kamar wani qanqanin,yaro yace
''amma mami for god sake sai kace maye za'a kaini can ni kadai
na kwana''
''ohhh,da can da kake kwanar mayen ne kai,ko wani abun ya gutsiri namanka
οΌ
''
kai ya mirgina
''Allah mami ki rage sona,ina ma laifin kive in kwana dakin maryam tunda ita kadai ce,kawai sai a kaini qarshen gida ni daya tal kamar maraya''
dari
ya taso kamata amma sai ta dake
''anzo gurin,dama abinda yake ranka kenan kakeson fada,to anqi din,ko kunyar baqi ba zaka ji ba ka tsallakesu ka tafi dakin matarka kwana
οΌ
,kaga kaina ciwo yake ka wuce sashenka kaje ka kwanta har abinci nasa an kai maka,ida
n kaqi kuma ka kwana a parlour shikenan''daga haka ta kama step din bene ta haye tana masa dariya cikin ranta
Sai data haye baki daya sanan ha dawo da kallonsa parlour din,yaja qwafa cikin zuciyarsa yana cewa ''duk a gama boye maryam din da yi masa wa
sa da hankali zasu gamu ne sai ya bata punishment''haka ya juya ya fito ba haka yaso ba cikin ransa
Cikin sa'a ya hangota tana fitowa daga bangaren meron,da azama cikin qwarewa irin tasu ta SS ya labe,sam bata lura da shi ba tana gyara yafen mayafin d
oguwar rigar jikinta taji an kamota baki daya anrungume tsam,ta tsorata sosai ta bude bakinta da niyyar yin magana
''kina yin magana sai na cinye lips dinki''ta saki ajiyar zuciya jin muryar abdallah ne,sai ya tuna mata lokutan baya da yake tsora tata iri
n hakan
Luf tayi a jikinsa ta saki ajiyan zuciya ta lumshe idonta,wani yanayi take ji na daban,dumi qamshin jikinsa gami da qamshin mint mouth fresh dinsa tare da maganar da yake mata cikin kunne suka kashe mata jiki,kwanciyarta a jikinsa ya bashi d
aman sa hannunshi yana shafa kafadarta zuwa yatsun hannunshi
''ina zaki je
οΌ
''
muryarta low tace''charger zan daukowa mero''
''kishiyarki''ya fada cikin sigar tsokana,sai ta saki murmushi tana sake narkewa a jikinsa
''yanzun ki qyale wata mero muje mu k
wanta,yau sashen mami a cike yake ya mana kadan''
ta dan zaro ido
''amma babu kowa a dakina ni ai,ni kadaice''
''i know,amma duk da haka ya mana kadan tunda tare nakeso mu kwana''
''amma mami fa.......''
''shshshshsh
οΌ
''ya fada yana dora yatsanshi kan
lebensa bayan ya juyo da ita da sauri suka koma suna fuskantar juna,idanunsu cikin na juna ya riqe qugunta
''bana son musu,just say yes...''sai ta sauke qwayar idonta,a hankali ta furta
''to''
''good mero na,bari